Showing 345001 words to 348000 words out of 429394 words

Chapter 116 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1036

yanda ya iya haka ya sake yamutsata kamar na dazun har seda ta samu nutsuwa kafin tayi wanka suka kwanta zuciyarsa fal cike da tunanin mafita. Tabbas idan har yanayinta ya fara canzawa zuwa ga yawan buqata rabuwarsu ita ce maslaha duk kuwa surutun da za'ayi gara ayi akan ya cutar da ita kota fada wata halakar da baya fata a dalilinsa baze yafewa kansa ba. Dakyar bacci ya daukeshi saboda tunanin da yake ta famanyi.

A bangaren Hajiya ma haka ta kasance da ita ta kasa bacci tana saka da warwara daga qarshe ta yanke shawarar takawa qafa da qafa taje ta samu Mama Hauwa washe gari, hakan kuwa akayi qarfe Goma na safe a gidan tayi mata Mama Hauwa ta tareta da murya a ranta kuma tana mamakin zuwan Hajiyar dan haka kawai bata taba zuwa gidan ba seda kwakwkwaran dalili, ita ce take leqata lokaci lokaci tun ma a zamanin baya daga baya itama ta watsar suka zamana se idan abu ya farun sannan za'a hadu sudai yaransu da Allah ya qulla Aminta a tsakaninsu kullum suna tafe gidajen junansu.

Bayan ta ajiye mata Kunun gyada da Alala me kyau da tayi na karyawa gamawarta kenan tayi wanka tana shirin zama ta karya Hajiyar ta shiga.
"A qoshe nake Hajiya kedai ki karya se muyi maganar data kawoni dan zanfi so kici ki qoshi tukunna" Hajiya ta fada se Mama Hauwa tayi sak kafin ta saukeajiyar zuciya taja kwanukan ta shiga cin abincin a ranta tana addu'ar duk ma abinda Hajiyan tazo dashi Allah yasa Alkhairi ne. Seda taci ta qoshin kuwa ta kwashe komai kafin ta zauna tana cewa
"Ina jinki Hajiya, Hajiya ta janye tagumin data rafka kafin cikin nutsuwa ta shiga zayyanawa Hajiya Hauwa komai game da matsalar Khalil da kuma hukuncin da yake shirin yankewa.

Mama Hauwa tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta zuciyarta na bugawa da qarfi tausayin Khalil din ya rufeta kwari ainun, dukda sun san da maganar kwada masa abu da tayi amma basu zata munin abun ya kai haka ba kuma harda Mansur sunyi maganar se yanzu ta fahimci irin jimamin da yaketayi ku ya da nauyi ya hana ya fayyace mata ainihin abinda yake faruwa amma wannan yarinya Umaimah lamarinta se Allah. Numfashi ta ajiye tana kallon Hajiya tace
"Abun babu dadi Hajiya amma duk abinda kaga ya samu bawa da sanin Allah kuma in sha Allahu shi ze warware komai wata rana se kiga komai ya zama labari tamkar ba ayi ba. Sannan Hajiya wannan al'amari a hannunsu yake su zasu yanke wa kansu shawarar abinda ya kamata suyi su da suke yan zamani duk dabarun jiyar da kai dadi wanne ne basu sani ba? amma ina ganin rabuwa ba ita bace Maslaha su zauna suyi magana shi yafi idan anyi haquri da sannu se kiga Allah ya bashi lafiya sunci gaba da zamansu qalau"

Hajiya tayi qasa da kai irin maganar Maman ta bata kunya ita kuwa ko a jikinta taci gaba da cewa
"Allah kuwa Hajiya me ake nema ne dama dai ba wancan abun ake tunani ba dan dai kawai za'ace ita yarinya ce baya ga haka Allah na tuba masu lafiyar ma nawa ke zaune basa samu wasu sun manta ma ana wannan a cikin aure sannan ni ashe ido na ne be gani daidai ba zuwan da sukayi na qarshe ma gani nayi kamar tana da shigar ciki ashe ba haka bane to idan ma Haihuwa ce shi rabo ai lokaci ne in a nesa yake se kiga anja lokacin har lafiyar ta samu a zo a hayayyafa" se sannan Hajiya ta iya cewa

"Nima haka na gani kuma jiya munyi magana dashi a yanda na fahimta dai qila da akwai cikin dan be musa ba dana fada" Mama taja Kabbara tace
"Kin gani ko? Allah kadai yasan abinda ya boye cikin auran nan dan haka ayi haquri a bi komai a sannu shi kuma Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne zan saka Sumayya ko Unaizatu suje gidan suyi magana da ita idan ma akwai wata damuwa wadda nake fatan babu zasuji Allah ya shige mana gaba"
"Amin Hajiya mun gode Allah ya saka da Alkhairi na sani abubuwan da suka faru daga fara neman auran nan zuwa yanzu yanzu da a waje Khalil yaje da ba'ayi shi ba koda anyi da yanzu gari kaf ya gama jin abinda ake ciki Mungode" Hajiya ta sake fada Se Mama Hauwa tace

"Haba dai Hajiya mu daku ai daya ne dan ni yanda Mansur yake a gurina haka na dauki Khalil shi yasa banji ko dar ba na bashi auran Humaira domin nasan ze kula da ita kuma Alhamdulillahi bana nadamar hada auransu ba"

"Allah ya jishshemu Alkhairi Hajiya, bari naje se na sake zagayowa" daga haka sukayi sallama ta tafi. Hajiya na tafiya Mama Hauwa ta kira Unaizatu, sunfi fahimta da Humairan dan haka ita zata saka tayi mata wannan aikin. Washe garin ranar kuwa Unaizatu tayiwa gidan Humairan tsinke da sassafe dan ba qaramin kaduwa tayi da jin Al'amarin ba taya ma za'a yi yarinya qarama kamar Humaira da bata san komai a cikin rayuwa ba ace tayi irin wannan zaman? Gangan kenan. Bata nunawa Mama komai ba tace mata dai goben zata je a ranta ta qudure niyyar baiwa yar uwarta shawarar data kamata dan ba zata zuba ido a saka yarinya qara ma a tasku ba. Sanda taje ta tarar da Khalil a gidan be fita ba saboda Humaira data tashi bata jin dadi suka gaisa cikin mutuntawa shi ya kawo mata Ruwa da lemo da abin tabawa dan basu rigada sun dauki me aiki ba tunda Ruqayya ta tafi seda ya ajiye mata komai kafin ya shiga ya kirawo Humairan data dan kwanta ta huta.

Tana ganin Unaizatun ta fasa ihun murna ta fada jikinta Khalil ya bude ido yace
"Kiyi a hankali fa karki jima kanki ciwo, seya juya dakin yana cewa
"Tunda kin samu abokiyar hira bari naje Anwar yana jirana bazan jima ba zan dawo" be jima ba ya fito a shirye yayi musu sallama ya fita bayan ya cewa Unaizatun karta tafi ta jirashi jintana cewa ba dadewa zatayi ba ya fita ya barsu.

Humaira kuwa rasa inda zata saka ranta don murna tayi, Anty Unaizan bata taba zuwa gidan ba tayi nacin harta gaji se yau gata bagatatan tazo mata.
"Muje ku gaisa da Hajiya Anty se na girka miki duk abinda kike so" ta fada tana kama Hannunta Unaiza tayi dariya tace
"To yar Hajiya ai can na fara shiga kafin nazo nan ya jikin tace baki ji dadi ba"
"Ni ai na warke kawai bana so ya fita ne daman shiyasa na langwabe" Hunaira ta fada tana tura baki se Unaizatu ta kama haba tace
"Lallai yarinyar nan to idan be fita ba so kike ya zauna kuci soyayya kenan?"
"Eh mana Anty ni bana so yana fita yana barina ni kadai gara ya zauna inyiyi masa shagwaba yana lallashina"

"Ikon Allah" Unaizatu ta fada jin abin bana wasa bane, seta miqe tana cewa
"Muje dakinki to magana nazo muyi" Humaira ta miqe tayi gaba Unaizatun na biye da ita a baya suka shiga falonta. A Bedroom suka qule kan Gado Unaizatu se qare mata kallo take ganin yanda ta canza gaba daya ta cika kamar ba ita ba ga wani haske data qara masha Allah kamar seka wanke hannu ka taba. A nutse kuma cikin dabara take bugar cikinta dan taji koda wata matsala daga bakinta amma bataji komai ba hakan yasa ta gyara zamanta dakyau tana kallonta tace
"Kinsan abinda ya kawoni maganar rashin lafiyar Mijinki ce jiya Hajiya taje gurin Mama tayi mata bayanin komai akan abinda ya same shi dalili daya sa tace mu tambayeki kenan kar kiji kunya ko nauyi ki fadi tsakaninki da Allah idan kina son zama dashi"

"Bangane ba Anty wani abu ya samu Yaya Khalil ne daga baya ko daman be warke bane?" Humairan ta fada cikin rashin fahimta se Unaizatu ta gyara zama tana kallonta tace
"Yace miki ya warke ne ko ke kinga alamar hakan?"
"Toh Anty tunda aka sallaameshi daga Asibiti ya warke kenan shekaran jiya nema dai daya dawo naga kamar bashida lafiya kuma yace qalau yake gashi nan ma kin ganshi ai yanzu" Humairan ta sake fada innocently se Unaizatu taja tsaki tace
"Bana son sakarci ki nutsu ki gaya mun gaskiya tun bayan da kika tare wata Mu'amalar aure ta shiga tsakaninku ne?"

Kafin ma ta rufe baki Humairan ta juya baya ta rufe fuska wai kunya Unaizatu ta dana mata duka a baya ta gantsare tareda yin ihu dan dukanya shgeta bata barta ba a fusace tace
"Dan ubanki ki juyo ki bude baki kiyi mun magana kunyar uwar me zakiji ana neman yanda za'a kwatar miki yanci kin zauna kinawa mutane yarinta da shirme nace kun taba kwanciyar aure da Khalil bayan kin tare a gidan ko yaya?"
Baki ta tura kamar zatayi kuka tana soshe soshe ba tareda ta bari sunhada ido ba tace
"Sau daya ne ranar da aka kawoni da daddare"
"Bayan nan fa? Tunda aka sallamo shi daga Asibiti ya nemeki?" Ta sake jefa mata wata tambayar zuciyarta na bugawa da jin ya kwanta da Humairan, sam bata so haka ba, taso ko rabuwar zasuyi ta fita a yanda tazo amma aikin gama ya gama.

Baki Humairan ta sake tunzurawa tace
"No shike nan sau dayane to wai tambayar mecece ma haka bayan bake kikace karna ringa yin hira da kowa ba koda kece ko Anty Sumayya kuma yanzu kin zo kina ta tambayata"

A hasale Unaizatu tace
"Dole kimun rashin kunya mana tunda yanzu mun zama kai daya kema kin san Namiji, to bari kiji tunda naga har yanzu yarinya na damunki baki ma san abinda yake faruwa ba Rashin lafiyar da Mijinki yayi kayan aikin sa ne ya samu matsala, a taqaice dai ina nufin dake dashi yanzu marabar ku kadance dan baze iya miki abinda sauran Maza sukeyi ba. Daman zuwan da nayi Mama ce ta turo ni akan na tambayeki kina son Mijinki zaki ci gaba da zama dashi da lalurar sa ko kuwa ba haka ba? Sannan in miki dalla dalla zama dashi da lalura yana nufin babu haihuwa tunda ba harka yawwa dan nasan kanki ba ja yake da kyau ba".

Tayi fakare tana kallon Unaizatu danharga Allah kam bata gane me take nufi ba, maganar haihuwa kadai ta tsinta wannan kuma in ta fassara daidai tana nufin Khalil baya haihuwa to Mu'ayyad da Bibi yayan waye?
"Kin tsaya kina kallona kamar wawiya ko baki gane me nake nufi ba?" Unaizatu ta sake fada ganin irin kallon da take mata seta daga mata kai alamar haka ne bata gane ba, takaici ya qume Unaizatu, bayan yarintar Humaira harda rashin wayewa saboda gaba daya rayuwarta ta tashi ne tsakanin Makaranta se Mama, qawayenta kuma duk yara ne kamarta lissafinsu da tunaninsu be san wadannan abubuwanba a da suna jin dadin rashin wayewar kannata domin hakan ma wani mataki ne na kariya daga fitina amma yanzu titsiyen nanda tayi mata na seta fadi komai gatsal gatsal yasa taji haushin rashin iliminta ko yaya ne a wannan bangaren.

Cikin dakewa tace
"Ai kin san Manhood a biology ko?" Seta sake daga kai alamar ta sani ta zaburo mata tace
"Ki bude baki kika sake daga mun kai kamar qadangaruwa sena mareki kin sani ko baki sani ba?"
"Na sani" Humairan ta fada tana sunkuyar da kai a ranta tana hakaito na Khalil daya kusa kasheta dashi.
"Yawwa to shi wannan abin nake nufi tsohuwar kishiyarki data kwada masa abu akai hakan yasa ya samu matsala baze iya kwanciya da Mace ba kinga kenan baze iya baki ciki ba" Unaizatu ta fada tana basarwa saboda kar Humairanta kawo mata raini ita kuwa dafe qirji tayi ta gwalalo ido tana kallonta jin abinda tace kafin bakinta na rawa tace

"Daman a nan ta buga masa? Innalillahi shi yasa Yaya Khalil ya ringa ciwon ciki kamar ze mutu koda yake ai ance nan ne makasar Maza daman kenan kashi taso tayi?'
"Oho dai koma menene kinji abinda ake ciki, kuma dai kinsan shi aure badan aci abinci kawai ayi kashi ake yinsa ba akwai biyan buqata ta sha'awa, wannan abinda kike cewa kina ji a jikinki idan kin sha magunguna lokacin to shi ake nufi da Sha'awa koda yake ai kin ma san komai rainamun hanka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?li kikeyi tunda kina zuwa Islamiyya an karanta muku komai" Inji Unaiza, Ita dai Humaira na cike da Jimamin abinda taji dan har idonta ya tara hawaye tausayin Khalil ya kamata ta tuna wani dan Ajinsu a makaranta suna Ball aka buga masa ita a gurin ya Suma dalilin cire shi kenan ita bata masan ya rayu ko ya mutu ba anan ne ma taji Mazan Ajinsu na fadar nan ne Makasar Maza yanzu ashe abinda ya samu Yaya Khalil kenan gaskiya Allah ya saka masa Maman Mu'ayyad muguwa ce.

"Toh yanzu dai seki zauna kiyiwa kanki tunani ki gani zaki iya zama dashi a haka ko kuwa saboda ke yarinya ce baki san komai ba a yanzu amma dukda haka babu me miki dole ke zaki zabarwa kanki abinda kike ganin shinr mafita a rayuwarki"

"Wai yanzu Anty kina nufinna bar Yaya Khalil saboda ya samu lalaura? Kin manta a dalilina hakan ya same shi nasan badan ya aureni ba babu abinda ze saka tayi fushi haka harta kwada masa abunda ze janyo masa matsala kuma ko ba wannan abun ya rasa ba ko qafa da Hannu Yaya Khalil ya rasa zan zauna dashi saboda shi nake so ba wani abu nasa ba" Humairan ta fada kanta tsaye tana kallon Unaizatu da tayi suman zaune tsabar mamakinta, damanta iya magana haka babu shirme babu shiririta a ciki? Tabbas gaskiya ta fada ta dalilinta Khalil ya samu lalura amma a ganinta wannan ba hujja bace da zata saka Humairan ta tauye kanta ta zauna dashi, maganar data ci gaba dayi ta tsayar mata da tunanin da takeyi jin tana cewa

"Kuma ma Anty ni daman ko kadan banji dadin abinda yayi mun bama banda wahala babu abinda nasha duk yaji mun ciwo rashin lafiyarsa sa ce fa tasa na warke babu shiri ni banma san ya akayi na denajin zafin da nake ji ba danma ranar Anty Jalilah ta taimamun sosai ta ringa sakani a ruwan zafi ta bani magani amma daman na rantse bazan ma sake yarda ayi ba se Allah ya dubeni ma gaba daya abin ya dena aiki shikenan a dadina iya wanda mukeyi ma ya wadatar yafi dadi wlh".

Ajiyar zuciya Unaizatu ta sauke haka duk yanda taso ta fahimtar da Humairan abinda yake da akwai ta ce ita fa ba haka ba, soyayyar da yake gwada mata ta isheta duniya da lahira harda cewa
"Anty dan baki ji abinda yake mun bane shiyasa kike cewa haka"
"Indai kalar nasa ne bana fatan naji Humaira shikenan Ubangiji yasa hakan ne yafi Alkhairi Allah kuma ya bashi lafiya idan da rabo" daga haka ta miqe zata tafi Humairan ta ringa naci da magiyar ta zauna amma taqi haka ta tafi ta barta tana hawaye.

Khalil be jima ba ya koma gidan ya tarar da ita tana kuka ya ringa rarrashinta kukan yasa zafin jikin data kwana dashi ya dawo dole ya dauketa suka wuce Asibiti, gwajin farko ya nuna tana da shigar ciki, dukda yaji qila wa qalan hakan a bakin Hajiya amma yayi matuqar Mamaki ya kuma godewa Allah domin ko iya haka ya tsayar masa da rabonsa sun ishe shi, ya kuma haihu da Humaira. Magunguna suka rubuta mata kafin suka kama hanyar gida, yanda yake tuqi a hankali kamar baya so bini bini ya kalleta ya tambayeta ya dai kamar ba'a taba daukar ciki a gidansa ba se wannan koda yake wannan din na daban ne dan haka dole ya ririta shi. Da suka koma gida da kansa ya ringa lelenta ya dafa mata doya da sauce da tace tana so ya bata a baki yayi mata wanka tsaf tayi sallar La'asar tana so tayi bacci amma ya hanata saboda rashin alfanun baccin bayan la'asar musamman ga me ciki.

Tana kwance a jikinsa yana shafa kanta tana zuba masa shagwabar da tasa yake qara narkewa a sonta, so yakeyi yaje gurin Hajiya tun jiyan be samu sun zauna yaji yanda sukayi da Mama Hauwa ba ga kuma wani Al'amarin ya bullo wanda yake ganin dalilinsa kadai baze iya rabuwa da Humaira ba, ze je ko ina ne a fadin duniya ya nemi magani saboda yaci gaba da zama da ita
"Yah Khalil" ta kira sunansa a shagwabe seya kalleta yace
"Yau kuma Yah Khalil na dawo?"
"To yi haquri Heartthrob, dazun da Anty Unaizatu tazo take gaya mun abinda ya sameka me yasa baka gaya mun ba nifa duk bansanme ya faru ba, shine wai Anty take tambayata idan zanci gaba da zama dakai a haka" ta sake fada kamar zata fasa masa kuka seya dagota suna fuskantar juna zuciyarsa na bugawa amma ya dake saboda besan abinda zata ce masa ba, daman yasan zuwan Unaizatun nada nasaba da maganar da Hajiya tajewa Mama yana fatan koma menene yazo masa da sauqi
"I'm sorry Babe, ban san taya zaki karbi al'amarin ba, bana so kice zaki rabu dani zan qarasa mutuwa ne kawai dan na rasa komai nawa, amma kiyi haquri tunda yanzu kin sani"

Hannunsa ta saka ta saqalo wuyansa tace
"Ni na gaya mata ina nan tareda Mijina ko qafa da hannu da ido ya rasa ballantana wannan mugun abun me jiwa mutane ciwo" ta qarasa tana rufe fuskarta da wuyansa. Wani farin ciki ya dirar masa fargabar da yake ciki ta bace, kalmar mugun abu da yake jiwa mutane ciwo ta bashi dariya matuqa harya kasa riqeta daman be samu damar ya tsokaneta akan abubuwan da ta ringayi a daren farkon nasu ba, tashin hankalin daya riskeshi ya saka duk be tuna wannan ba se ya shiga qoqarin cireta daga jikinsa yana cewa
"Thank you wife, ki kalleni ina so ki kalli idona dan kifi jin abinda zan gaya miki"
"Nidai Aa ka fada ai kunne ne yake ji" ta fada tana sake maqalqale shi seya birkitota gaba daya a dole ta saki wuyansa ta kulle idonta gam tana dariya dan kunyar abinda ta fada ce take cinta Khalil

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login