Showing 99001 words to 102000 words out of 429394 words

Chapter 34 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1016

tabi bayansa tana qara nana ta masa irin kallon rainin da matar tayi mata dan dagaske abin yaci mata zuciya dan bata son wukaqanci a rayuwarta.

Qarar wayarta ce ta dakatar da ita daga taya Khalil cire kayan jikinsa, yace
"Yawwa gashi can ana kiranki a waya" dan ta dame shi da shegiyar mita shi kuma ya gaji kansa ma ciwo yake dan wunin Site sukayi. Fita tayi tana cewa
"Ni ka kora ko, zaka sake cewa na tayaka wani abune nima sena rama" ta fice kafin ta qarasa wayar ta katse ta dauka Maman Nihal ce tana shirin kiranwa wayar ta sake daukan qara seta daga tareda Zama akan kujera suka gaisa tana tambayarta ya taje gida tace lafiya lau, godiya tayi mata akan zuwan da tayi Umaimah nata bagararwa dan gudun kar Khalil na jiyota yazo ya tusata da tambaya se Maman Nihal din tace

"Kinga ban kiraki da wuri ba, order kayan gadon Hamida ne ya iso har an kawo kayan ma nan Kano shi muka tafi dubawa daman dazu can Anty Hadiya zataje ta fara yin gaba se na bita daga baya, duk ma raina ya baci wallahi dan akwai kayayyakina da nayi order babu su a ciki kuma na amfanin bikin ne yanzu ban ma san yaya zanyi ba"

"Se haquri shiyasa ni daman ban yarda da harkar order nan ba nafi gane naje shago na dauki kaya na biya kudi" Umaimah ta bata amsa, qorafi Zainab taci gaba dayi mata akan kayan nata da ba'a sako mata ba Umaimah dai ca take se haquri to me zata ce mata fitowar Khalil daga daki ta sakata yi mata sallama ta ajiye wayar suka qarasa kan Dining ta shiga zuba masa abincin,

"Ina aka samo Turkey?" Ya fada lokacin daya kai naman bakinsa, taste din da qamshin spices din basuyi kama da na gidansa ba dan bakinsa da hancinsa akwai iya tantance qanshi da dandano.
"Anty Hafsa ce ta aiko mun dasu dazu harda Dambun nama da Samosa da spring rolls da wani ko meat bag sunansa oho tasan kana sonsu shine ta bawa Salman dazu da yaje gidan ya kawo mun" Umaimah ta sake yanko wata qaryar a karo na biyu dan bata da wata Mafita seta jingina abin da Anty Hafsa, tasan dai ko haduwa sukayi baze tambayeta ba dan akwai yar kunya tsakaninsu.

Gyada kai yayi yaci gaba da cin abincinsa suka gama suka koma cikin palour harta zauna yace ta dakko masa snacks din, sosai dadinsu ya ratsa shi ya kalleta yace
"Amma yayi dadi ita takeyi?"
"Anya kuwa inaga siyowa tayi sedai na tambayeta naji" ta bashi amsa tana janyo wayarta ta dannawa Maman Nihal kira tana dagawa tace

"Honey ne yaci snacks din nan yake santi shine nace bari na tambayeki a gida akayi ko siyowa kukayi"

"Ba ita bace, bari na kai mata wayar" taji muryar wani yaro ya fada, daga nesa ta jiyo Maman Nihal din cikin fada tana cewa
"Uban waye ya daukar mun waya,muttaqa dan ubanka ba nace ka dena daga mun waya idan an kira ba bani a bata" ta wafce wayar Umaimah na jira taji anyi magana se taji dif an kashe,
'Waye kuma Muttaqa? Yau Maman Nihal ce take hayaniya haka ita da kullum take murya a qasa kamar sarauniya kodai duk bacin ran kayanta da suka bata ne, qila tunda Allah kadai yasan Asarar nawa tayi' Umaimah tayi kidanta tayi rawarta a zuciyarta, Khalil dake faman cin snacks yace
"Me tace yayi mun dadi sosai fa damab akwai conference meeting da zamuyi ranar Juma'a ni aka bawa kwangilar abinci a menu din akwai snacks se tayi mana"

"Bata jina sosai bari na sakw kiranta yanzu" Umaimah data zama maqaryaciyar qarfi da yaji ta fada tana sake kiran wayar Maman Nihal ta daga da sallama murya qasa qasa irin ta wanda yake cikin damuwa tace

"Yi haquri qawata dazu kin kira yarom me aikina wani me shegiyar qiriniya ya shigo ya dauki wayar, a garin na karba ma kinga ya fadar mun da ita screen ya tsage ni ban san ya zamu kwashe da Abban Nihal ba idan ya dawo dan kinga ba ko sati biyu wayar bata rufa ba"

"Wai subhanallahi Allah ya mayar da Alkhairi, daman Honey ne yace snacka yayi masa dadi yana so zeyi order zasuyi amfani dashi a kamfaninsu ban sani ba a gida aka yi miki ko siyowa kukayi" Umaimah ta fada bayan data jimanta mata wayarta. Se Maman Nihal tace

"Oh dan Allah ai da kince shi zaki kaiwa da an qara miki da Frozen muna dasu da yawa a freezer a gurin wata Baker *MUNATCAKES* nake yin order gaskiya gwanace a harkar yin snacks duk irin wanda kika sani kuma duk wanda yaci seya tambayi a ina akeyi, kin tuna birthday cake din Amal da kika gani kika ce yayi kyau shima ita tayi dan ma bakici kinji dadinsa a baki ba wallahi so soft and moist, yanzu kayan garar Hamida ma ita muka bawa aikin"

"Dan Allah kice har kayan gara tanayi, ta iya Alkaki? Dan kinsan a sabgar gara ba abinda nake so kamar shi" Umaimah ta fada se Maman Nihak tayi dariya tace
"Duk abinda kikasan anayi da fulawa to *MUNATCAKES* Ogar sa ce, snacks irinsu Samosa, Meatpie, Whole cake, cupcakes, springrolls, meatbag, Cinamonrolls, Doughnut su gireba da duk sauran abubuwan da ban lissafo ba tana yi kuma akan farashi me sauqi" se Umaimah tace

"Toh shikenan ki turo mun da lambarta dan Allah yanzu se nayi order nima, zan tambayeta naji ma idan tana koyarwa nima na koya"
"Ai kuwa tana yun class na koyar da abubuwan idan kina so din se ki shiga bari na tura miki number Abban Nihal ya dawo mayi magana kota Online ne" Maman Nihal ta fada kafin Umaimah tayi magana ta katse wayar ba'a bata lokaci ba ta tura mata da lamabar *(07046462003 MUNATCAKES)*

"Kaji order ne ga number matar ta turo bari na kirata yanzu" Umaimah ta fada tana kallon Khalil daya kusa tada tulin snacks din gabansa, ta cicciba ta miqe tana cewa

"Me da me za'ayi order? Kuma pieces nawa?"
"Ta tura miki da menu se mu gani" ya bata amsa ta shige dakinta mintina kadan ta fito bayan sunyi waya da me snacks ta tura mata Menu din a whatsapp, kusa dashi ta zauna ta karanto masa kudin ko wanne ya gama lissafi ya fada mata a dadin daya ke buqata da rana da lokaci da inda za'a kai musu suka gama deal take ya tura mata da kudinta.

Gulma na cin Umaimah so take ta bawa Khalil labarin irin haduwar gidan Maman Nihal amma bata so ya gane ta biya gidan, haka ta hadiye gulmarta duk da ta qudure a ranta wata rana seta jashi yaga gidan idan zeyi musu gini wata rana yayi irinsa da tsarin gidan ya burgeta matuqa.

Haka aka ci gaba da gungurawa zumunchinsu da Maman Nihal nata qara danqo dan a rana idan basuyi waya ba suyi sau uku wato safe rana dare chatting kuwa yanda kasan marasa aikin yi, Khalil yayi fadan yayi Nasihar amma kamar yana qara tura ta ne dan duk uzurin da Umaiman takeyi Maman Nihal ta kira ko tace ta hau WhatsApp zata ajiye ta tafi nata dayaga lamarin nata ya zarce na masu hankali se kawai ya zura mata ido yasan dai duk daren dadewa wannan qawancen ze watse.

Bikin Hamida qanwar Maman Nihal saura kwana uku ta dira gidan Umaimah kai mata kati, dukda Umaiman ta shaida mata babu lallai Khalil ya barta musamman idan yaji bikin na waye dan ya tsani Maman Nihal din nan kamar me amma tace ita dai babu ruwanta zata kai mata Kati kuma duk yanda zata qoqarta tazo mata biki tazo tunda dai Edd dinta da saura ai kuma ta rigada tabi yan uwanta kaf ta gama gaya musu sabuwar Aminiyarta zata zo.

Ranar da ta kai mata katin aka taki Sa'a Khalil baya gari sun tafi Danbatta tasan kuma dawowarsa se dare dan basu tafi da wuri ba. Tarba tayi mata ta mutunchi dukfa bata kai irin wadda Maman Nihal din tayi mata toh ai zaren ba kalar yadin bane.
Suna zaune a palour Umaimah Maman Nihal nata yaba gidan wai ya bata sha'awa dan qarami amma an qawatashi sosai duk wanda ya shigo dole yayi sha'awarsa wayar ta ta dauko qara ta daga da sallama daga nan tayi shiru alamar tana sauraron me magana ne kusan minti biyu ta ajiye wayar tana cewa
"Shikenan nagode ai hakan ma kin mun qoqari amma dai mutanen nan sun cuceni wallahi sedai Allah ya saka mun, dole yanzu na nemi wata mafitar da zan fitar da kaina kunya".

Bayan ta ajiye wayar duk yanayinta ya canza daga raha da walwala zuwa damuwa dan har tagumi ta rafka hannu biyu, Umaimah dai ta kama bakinta tana kallonta bata ce komai ba, can Maman Nihal din taja numfashi cikin muryar damuwa tace

"Nidai wannan Order babu abinda ta janyo mun se asara da bacin rai, na tattara duk kudadena na narka da niyyar idan kaya sun zo da masu su sun karba sun biya in maida wasu yanzu gaba daya kinga abinda aka kawo mun sun zama asara.
Ni bama ta tawa nake ji ba yanzu Abban Nihal ya bani kudi na siyi sarqar da zanyi fitar biki da ita dan baya so na saka daga cikin tsofaffin nawa na hada da kudin duka nayo sari, gashi da bin kwakwkwafi tun satin daya wuce daman yake tambayata ina sarqar dana siya nace ban karbo ba wallahi ba qaramin aikinsa bane ya tijarani a taron bikin nan idan be ga na saka tsohuwar sarqa".

"Ikon Allah, yanzu toh ganewa zeyi idan kika saka tsohuwar?" Umaimah data zuba mata ido ta fada, se Maman Nihal ta sake marairaicewa tace
"Uhm baki san mutumin nan ba kamar wanda Aljanu suke fadawa abu, tunani nayi da naje nayi musanye a kasuwa na karbi wata amma nasan dole se ya sani dan shi yake bada Design din a Dubai ayi mana idan ma na kai aka chanza ze gane tunda duk yan Gwal din Kasuwar Rimi mutanensa ne" Maman Nihal ta sake fada, Umaimah ta tabe baki a ranta tace

"Saboda shi yafi kowa ko kuma na'ura ya saka a jiki da idan an siyar ko an chanza zeji a jikinsa, yanzu ina laifin wannan ta wuyanta idan taci bikin da ita?" A fili kuma tace mata
"Toh se ki kai wata kasuwar daban ba wadda kika san yasan mutanen ba, idan ma kina so akwai abokin Honey shi a Sabon gari yake nima a gurinsa aka siya mun tawa se na hadaki dashi ki kai masa taki ya baki aron wata da an gama biki ki karbo ta ko"

"Eh to wannan ma dabarace, ina takin na gani se ki bani number sa yanzu dana je gida na bayar a akai masa" Maman Nihal ta fada,se Umaimah ta miqe ta shiga dakin Khalil, akwatin sarqar ta dakko gaba daya hatta da Receipt din yana ciki ta bata, Zainab ta bude sarqar tace
"Wai wai cancadi gaskiya matar nan kina shanawa Honey yana ji dake irin wannan sarqa haka" ta fada tana kara sarqar a wuyanta, Umaimah ta kalli dambasheshiyar sarqar dake wuyanta da ta tabbatar idan aka auna tayi darin tata a nauyi amma take wani santi akanta tace

"Zagina dai kawai kikeyi Maman Nihal kin ganta bata fi wuyan Amal ba ko"
"Wallahi dagske ta burgeni, design din very unique kuma tayi kalar nauyi kinsan irin ta manyan Hajiyoyin nan da idan aka auna se sikelinda kansa ya girgiza" Zainab din ta sake fada, kafin Umaimah tayi magana ta sake cewa

"Allah yasa Abokin Megidan naki yana da irinta"
"Ai kuwa babu dan lokacin ita kadai ta rage itama matarsa ya daukarwa Allah yayi rabona ce, bakiga yanda wasu suka ringa nacin ta ba har wata tace ma zata qaramun kudi na bar mata naqi" Umaimah ta bata amsa, seta maida sarqar ta zaro awarwaron tana gwadasu tace

"Ai kuwa gashi zanyi miki fashinta har gida yanzu dan musanye zamuyi, ni kota wuya na ce ki karba kawai ki bar min ita na yafe na se kinyi mun ciko ba idan kuma ba haka ba ki bani aro" ta qarasa tana duba receipt din, se Umaimah tayi dariya tace

"Haba ni na isa in saka wannan sarqar so kike a tareni a hanya a kwace,gata nan dai kiyi amfanin bikin idan kin gama se ki dawo mun da ita" Umaimah ta fada dukda yanda takejin zuciyarta sam bata Aminta da bada aron ba, kashedin Mama take tunawa da tace seta ci uban ta idan taji labarin ko gwaji ta bawa wata balle aro dan tasan zata aikata amma kuma mutum kamar Maman Nihal data fi qarfin yar sarqarta ta nuna tana so meye dan ta bata aro dai na kwana daya.

"Aa kibar kayarki wasa nake miki zanje gurin nasa in karbi wata dukda dai naso wannan din wallahi" Zainab ta fada tana miqa mata sarqar se Umaimah tace

"Kice dai kin rainata bazaki iya saka qaramin abu kamar wannan ba"

"Karki mun sharri ni bance haka ba, tunda kin dage zan karba amma sedai na bar miki ta wuyana a gurinki, In sha Allahu da an tashi daga Kamun ba dan dare bama zan biyo na kawo miki da sassafe kuwa zan bawa Walid tunda yaga gidanki" ta fada tana qoqarin cire dan kunnenta Umaimah ta tareta da cewa

"Haba dan Allah meye haka kamar wata da zata gudu, ki bar abinki wallahi babu komai kije da ita duk sanda kika gama amfanin seki dawo mun da ita dan ni ba sakawa zanyi ba se ranar Suna idan Allah ya sauke ni lafiya".
Dagewa Maman Nihal tayi akan sefa ta barwa Umaimah tata sarqar akan dole ta qyaleta ta cire sarqa da dankunne harda Qwandalelen zobenta ta aje mata akan Centre table kafin ta maye gurin su dana Umaiman ta zura Akwatin a jakarta daidai nan wayarta tayi qara ta dauka tana cewa gata nan zuwa

"Masu daura gado ne sun gama zanje na sallamu suna jirana" Ta fada tana miqewa Umaimah ta miqe tareda daukar mayafinta suka fita zata rakata Maman Nihal dinna cewa ta barshi saboda yanayinta tace ai seta rakata har bakin mota, suna kaiwa Get Yaya Naziyya ta turo qofar da ta rigada ta bude, sukayiwa juna kallon cikin ido da Zainab, idonta akan sarqar ta juya ta kalli Umaimah dake cewa

"Lah Yah Naziyya daga ina haka zuwa ba notice?"
"Kona koma ne?" Ta fada tana harararta se ta saka dariya tace
"Ni na isa bismillah shigo sannu da zuwa, Maman Nihal ga Yayata Naziyya ki daina mun gorin baki san kowa nawa ba".

Washa baki Maman Nihal tayi ta miqawa Naziyya hannu sukayi musabaha sam ita Naziyyar fara'arta batayi mata ba, kai matar ma gaba daya batayi mata ba ko a ina Umaimah ta kwasota se Allah.
Sallama sukayi ba tareda Umaimah ta rakata motar ba ta wuce su kuma suka juya ciki, Kitchen Yaya Naziyya ta fara shiga tana cewa

"Ke daga kasuwa nake na kwaso qishirwa bari na sha ruwa nayi alwala" se Umaimah ta shige palour idonta ya sauka akan sarqar da suka bari tayi saurin qarasawa gurinta kwashe su ta wuce dakin Khalil dan tasan Yaya Naziyya da saka ido,yanzu zata tasata gaba da tambayar ya akayi ya za'ayi.
Cikin safe dinsa da yake ajiyar muhimman abu?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? buwa ta bude ta saka, kallon sarqar tayi se taga tayi yellow sosai ba kamar tata ba ta tabe baki data tuna ance ai Gwal hawa uku ne qila wannan nw babban ko ta mayar ta rufe jin Yaya Naziyya na qwala mata kira.

"A ina kuma kika samo wannan tsohuwar guzuma?" Yaya Naziyyan dake nade abin sallah ta fada tana kallonta se Umaimah ta bata rai tace
"Daga ganin mace kawai kice mata tsohuwar guzuma tsabar daukan Alhaki toh qawata ce"

"Haka dai tun kina qawancen da sa'anninki har kin fara debo wanda suka kusa haifarki toh ki dai yi a hankali dan yanzu duniya babu gaskiya mata sun baci, ke kuwa ba wayo ne dake bare hankali sedai Allah ya kyauta kawai, duk wannan uban abubuwan ita kika kawowa kenanan?"

Harararta Umaimah tayi ba tareda ta bata amsa ba ta nemi guri ta zauna tana cewa
"Cikin mutum daya shine kika hado mata wannan kayayyakin saboda Khalil din tsinko kudi yake a bishiya ko?"

"To nima dan bakiga tarbar da tayi mun da naje gidanta ba, har shi seda yaci ragowar abinda aka hado mun na taho dasu" Umaimah data zauna a qasa ta fada tana tunzura baki, shi yasa basa shan inuwa daya da Yaya Naziyya dan ita ta fiya saka ido da fadan tsiya.

Shareta Naziyya tayi ta janyo kwanon Dambun nama ta shiga ci Umaimah ta kalleta tace
"Gashi nan kema ai kinci albarkacinta zaki zo kina cewa wani anyi almubazzaranci"
"Kafin nazo gidanki naci abinci kinje nawa kinci sau ba adadi kinga idan ma biyana nace kiyi be isa ba" Naziyyan ta fada a zafafe tana ture kwanon gabanta Umaimah data qunshe dariya ganin yanda ranta ya baci ta mayar mata tana cewa

"Allah ya baki haquri bari na kawo miki abinci shinkafa da wake nayi kina ci" bata kulata ba ta wuce kitchen ta zubo mata ta ringa damunta da magana har seda ta sauka daga fushin taci abincin suna yar hira.

"Wai ke bakiyi scanning bane an gaya miki me zaki haifaz kuma tanadin me kika fara kinja kinyi shiru shiyasa nace ni bari nazo naji ya ake ciki" Naziyyan ta fada tana kallonta, Umaimah ta shafa cikinta tana yatsina fuska tace

"Bansani ba wallahi nace su bari idan na haihu kawai na ga koma menene itama Hajiyar sa da yayyensa haka suka ringa tamabaya kwanaki, tanadi kuma kamar na me bangane b?"

"Uhm ke dai ai se addu'a kawai to Allah ya raba lafiya se mu ga abinda aka samu tanadi kuma na kayan haihuwa da abubuwan da ake buqata na tafiya Asibiti ko suma se kin hauhu sannan za'a nemo?"

"Lah ni wallahi nama manta tun kwanako fa aka bani wata takadda a Asibitin ta abubuwan da ake tafiya dasu ni ko nuna masa ma banyi ba, kayan baby ma duk nace ya bari se an haihu se a siya ko? Ni duk ba wannan ba na gama wani siye siye ma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login