Showing 243001 words to 246000 words out of 429394 words

Chapter 82 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1042

komo hayyacinta sannan ne zata tantance tana da buqatarta ko Aa.

Wayar ta kawo mata harda chaja ta koma cikin dakin ta jonata a chaji dan a kashe take, bayan ta kunnata ta fara dubawa, ta tarar da tarin missed calls na Jama'arta, Safinah ta kirata yafi sau a qirga ga Text messages tana tambayar lafiya idan ta kira bata dauka da alama duka kafin wayar ta mutu ne akayi ta kiran da messages din.

Maman ta fara kira, yanda ta amsa mata ya qara sanyaya mata jiki bata ma bata damar yin wata magana ba daga gaisuwa ta dakatar da ita tace se anjima. Seta maida kiran kan Abba, shikam ya amsa mata a dan sake har yana tambayarta Khalil tace ya fita. Nasiha ya qara dora mata kafin sukayi sallama yana saka mata Albarka wannan yadan sanyaya mata rai ta qudurce zatayi ta kiran Maman kulkum har se itama ta haqura ta sakko. Maman Asad ta kira, missed calls hudu tayi mata amma taqi dagawa na qarshe ma rejecting tayi hakamya tabbatar mata da tana kallo dagawar ne batayi niyya ba seta aje wayar kawai dan ta tabbata tunda Hajiyayye bata dauki wayarta ba to gaba daya sauran ma bazasu dauka ba alamar labari yaje musu kenan daman kuma har ta gama jinyarta babu wadda tazo gidan a cikinsu ai shikenan babu dai yanda suka iya da ita duk fushinsu dole suyi su gama su sakko.

Khalil dai dagaske yake shareta a gidan dan daya dawo da yamma ma tana zaune a falon saman tayi masa sannu da zuwa bata zaton ya amsa dan bataji ba ya wuce dakinsa ya bude ya shiga, data bishi ta kwankwasa kamar su da wani suke zaune a gidan yake tambayarta wai waye, abin ya qona mata rai amma ta daure tace Umaimah ce. Seda ta kwashi minti biyar a tsaye tana jira ya bude amma shiru, bata haqura ba ta sake kai hannu da niyyar bugawa se gashi ya bude yayi bake bake a bakin qofar tareda tsareta da ido. Duk seta duburburce ta kasa ce masa komai ganin tana bata masa lokaci yasa ya juya ciki ya sake rufe qofar tana ji ya murza muqulli wani abu ya tokare mata wuya, ta tsani wulaqanci a rayuwarta koda ace laifi ta masa ai be kamata yayi mata haka ba se ya bari ta shiga yaji abinda ya kawota ko yana nufin a bakin qofar zasuyi magana.

Komawa tayi ta zauna tana cika da batsewa, kusan minyi Ashirin ya fito ya sake wanka daidai nan kuma aka fara kiraye kirayen sallar Magriba.
A zatonta sallar zeje ya dawo, dakanta ta shirya masa abincin data saka Ruqayyan ta dafa anan falon sama ta koma dakinta bayan tayi sallah ta sake gyara fuskarta da tana nan har sannan da yatsun Baba Abdullahi duk sanda ta kalla seta masa Allah ya isa kuwa. Haka ta kasa ta tsare a falon tana jiran shigowarsa. A gurin tayi sallar Isha ta kunna Tv suna kallo da yaran da suka shigo shiru shiru har Tara tayi me aikin Hajiya Basira tazo kiran yaran suje su kwanta Khalil be shigo ba. A qasan carpet din da take zaune taja pillow ta kwanta saboda ta gaji da zaman, ga yunwa tana ji amma taqi cin abinci tana jiran Khalil, Fitsarin daya matseta nw ya farkar da ita daga baccin da bata san sanda ya dauketa ba.

Falon duhu dundum an kashe dukkan fitilu harda Tv data bari a kunne. Wayarta data san ta ajiye a kusa ta shiga lalube, Allah ya taimaketa ta samota ta kunna agogo ta fara kallo qarge biyu da minti Ashirin na dare setayi saurin kunna flash light ta miqe dakyar ta kunna fitulun falon. Kayan abincin data aje ta kalla suna nan inda suke babu alamar an taba kenan ya shigo gidan kuma shi ya kashe Tv da fitila amma saboda wulaqanci ya kasa tashinta dan tasan da Ruqayya ce dole zata tasheta kuma ta kwashe kwanukan bama zata hawo ba dan ta mata iyaka da hakan indai ba ita ta kirata ba, ai kuwa zega rashin mutunchi indai abinda haka yace zasu tafi to su zuba su gani.

Fitsarin ta fara zuwa tayi dole ta zuba abincin taci dan wata yunwa taji tana neman kada ita. A gurin ta bar kwanukan ta miqe tana shiga dakinta taji qarar bude qofa tasan kuma baze wuce shi ba, kamar ta fita taga meya fito dashi se kuma ta haye gado saboda baccindaya cika mata ido.
Tun daga ranar haka suka ci gaba da tafiya da safe kafin ta tashi ya fice daga gidan duk sammakon da zatayi kuwa ba zata ganshi ba haka da yamma idan ya shigo tana zaune wata rana ya amsa in ta gaishe shi wata ranaya shareta sannan idan ya fita sallar magriba baya dawowa se tayi bacci daman tuni ta sawwaqewa kanta jiransa dan sau uku tana kwanan falo kuma zezo ya kashe fitila da Tv amma baze tasheta ba sedai da Asuba ta tashi jikinta na ciwo saboda kwanciyar qasa haka kuma ko ta taki sa'a sun hadu idan zata kwana tana masa magana baze kulataba haka abinci bata san inda yake ci ba, dan gurin Hajiyar kanta idan ya shiga baya dadewa gaisheta kawai yake yayi ficewarsa.

Duk sanda ta shiga Hajiyar ta ringa tambayarta komai dai lafiya ko sedai tayi murmushi tace mata Eh,
"Ki qara haquri, Khalil nada sanyin hali amma idan wannan zuciyar tasa ta motsa kafin ya sakko daga fushi ana shan wahala amma kuma daya huce shikenan komai ya wuce a gurinsa dan yana da yafiya shi" Abinda Hajiyan take gaya mata kenan sedai tayi murmushi kawai.

BAYAN WATA DAYA
Daga yanda yake tuqin zaka san cewar a gajiye yake, seda ya tsaya a hanya ya siyo panadol night dan kansa ciwo yake masa ga gajiya, so yakeyi yayi bacci sosai musammanda yake gobe Juma'a bazasuyi aiki ba, Site zeje kuma se bayan an sakko sallah. Wayarsa dake qara ya kalla yaga Umaimah ce take kira, a fili yayi tsaki kafin ya daga ya sakata a speaker beyi magana ba ita ta fara cewa
"Ance se nayi scanning, kuma ga kudin test da akayi mun duka ba'a biya ba" ta fada a qufule, da irin muryar da tayi masa maganar ya mayar mata da tambayar nawane? Tace dubu goma,
"Ok" kawai yace mata ya katse kiran, yana tuqin yana mata transfer, dubu biyar ya tura mata, ai ya sani scanning dubu uku ne test din kuma da take magana yasan qarya takeyi idanma anyi ga 2k nan ai baze wuce haka ba shikansa scanning din ai a cikin Antinatal bill dinta duka ya biya dan dai zuwan nata na yau ba ranar awo bace haka kawai da safe ta tsareshi da cewar bata da lafiya wai Ruwane yake zubo mata, bashi da lokacin tsayawa ya bata shiyasa ya bata dubu goma yace taje Asibitin shine tun safen bataga dama taje ba se yanzu kusan Magriba zata sake ce masa ya tura mata wani kudin.

Tun bayan dawowar tata dai sauyi kadan aka samu a zaman nasu, yanzu yakan zauna a gidansa koda tana zaune a falon ze fito shima yayi sabgar sa dan yayi tunani babu dalilin da ze saka shida gidansa ta hana shi zama sedai ya fita yayi ta yawo a titi har lokacin kwanciya yayi kafin ya dawo dan haka ya canza, magana cedai har yanzu ba wata meyawa take shiga tsakaninsu ba se abinda ya zama dole ko kuma idan yaran suna tare dasu shine sukeyin magana kamar babu komai a tsakaninsu dan gudun karsu fahimci wani abu musamman Mu'ayyad da yake da shegen wayo ga tambaya.

Tun daga bakin layin yake hango kamar Mu'ayyad da wasu yara suna buga Ball a tsakiyar layin, ransa ya qara baci akan yanda yake, tunda Hajiya ta tafi Gaya yaja mata kunne akan barin yaran suna fita waje, ya gaya mata ko wasa zasuyi karsu wuce cikin compound din gidan amma bataji shine yanzu ta kama hanyar tayi tafiyarta ta bar masa yaro yana garari a cikin layi, kwafa yayi tareda yiwa yaron horn, yana ganin motar Dadyn sa ya saki kwallon dayake bugawa ya tafi da gudu ya bude masa ya shiga.

A mugun fusace ya taka burki daidai Qofar gidan, kallon Bibi dakw zaunw dare dare a cinyar Sammani yayi tana shan raken da shi da sauranmasu gadin gidajen da suka mayar masa da qofar gida Majalisarsu ta zama. Qarar taka birkinsa ce ta ankarar dasu dan sam basu ga zuwan motar ba suna kyalkyala dariyar labarin da Muttaqa yake basu. Ajiye yarinyar Sammani yayi jiki na rawa ya fara bude Get din Khalil ya fito daga cikin motar a fusace ya dauke Bibi da itama ta nufoshi ya koma motar yana ballawa Sammani da Abokanansa hararar da suka rasa ta mecece.
"Karka kuskura na fito na tarar da kowa a qofar gidan nan, kaima idan ba zakayi aikin ba ka kama gabanka" Khalil ya gaya masa sanda yake qoqarin shigar da motar ciki.

Yarsa a tsakiyar maza akan cinyar me Gadi, lallai Umaimah kuwa zata gane kurenta, besan ma for how long take sakar masa yarinya tana shiga cikin qarti ba, ita rashin sanin daidanta a komai ma gwada shi takeyi.
Beko amsa sannu da zuwan da Ruqayya take masa ba ya rufeta da masifar akan me tabar yaran suka fita, kasa magana tayi har ya gama bambaminsa ya haye sama da yaran, tare suka sake sakkowa, tana rabe a gefe dan fadandaya shigo dashi yau dinya bata tsoro. Kallonta yayi yana sakin hannun Bibi yace
"Gata nan, saura ki barta ta sake fita dake da Ita yau duk se kun gane kurenku a gidan nan useess kawai" ya finciki Mu'ayyad suka fita masallaci.

Ita dai Ruqayya da ido ta rakashi tana tunanin ita dawa zasu gane kuren nasu, Bibin ko Uwar Bibin??

A compound suka ci karo da Umaimah tana fitowa daga mota, wani banzan kallo ya aika mata kafin ya miqa mata hannu yana cewa
"Da izinin wa kika daukar mun mota, kinga Umaimah ki shiga hankalinki wallahi. Karki dauka sako sakon dana farayi miki na manta abinda kika mun ne a cike nakw dake kuma har yanzu ina kan duba abinda zanyi miki na rama karki dauka na manta" ya fada yana fincike muqullin hannunta.

Kallonsa tayi ta riqe baki tace
"Ikon Allah" kafin ta shige ciki ranta a dagule. Zuwan data shiryi yi Asibiti saboda ta samu kudi a hannunsa ne dan tunda ta dawo koma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????i ya canza. Yar dubu dayar da yake bata ta cefane a kullum ta Allah dukda babu abinda take siya dan komai na amfani siyowa yake ya ajiye wanda ze ajiyu a Fidge ko Freezer ta saka wanda baya buqatar haka ta barshi a waje amma dukda hakan seya bata wai koda zata nemi wani abun girki da babu a gidan. Lokacin da suka tsohuwar unguwarsu Zubin Adashi take dasu, Adashin da bata tsinana komai dashi ba dana rance yake qarewa saboda sun rainata sun kuma maidata saniyar tatsa haka ta qaraci zubin sau daya ta taba dauka itama seda suka ringa bi me rantar dubu biyu dubu uku suka kashe.

Bayan dawowarsu nan ne tayi hankalin adana kudin idan zataje gida ta siyi wani abu ta kai musu na neman Albarka ko ta basu kudin dan ada duk lissafinta be taba gaya mata tayi hakan ba a ganinta basu da buqatar komai, zata iya cewa wannan ce kadai dabi'a me kyau data koya gurin Safinah dan ita taga tana siyan abubuwa takai gidansu duk kuwa da cewar masu wadata ne sosai dan sunfi iyayen Umaiman ma to yanzu ko tunda ta dawo se a hankali kayan cefanen ma duk abinda be zama dole ba da ya qare be siyo ba. Shekaran jiya data ce masa Madara ta qare ce mata yayi su sha baqin Tea bashi da kudi, se dazu da safe ne da Bibi tasa rigimar zata sha madara ya bawa Sammani ya siyo mata Peak ta Sachet, abinda ba'a taba siya a gidan ba dan madara kafin Gwangwani yayi rabi ya kawo wata.

Tana shiga Ruqayya ta shiga wassafa mata a yanda Khalil din ya shigo da abibda ya gaya mata, se a sannanta gane fushin da yake na an bar yara sun fita ne toh canya gane goya su yake so a ringayi ko yaya ita yanzu ya barta da tunanin yanda zata hado kudinda Safinah tace ta kawo.

*TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*.
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY* .

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 57

Khalil kuwa be shigo gidan ba se bayan da suka idar da Sallar Isha. Bamgaren Hajiya ya wuce, Suna shiga palour kiran Mansur ya shigo wayarsa seda ya zauna kan kujera kafin ya daga wayar.

Bayan sun gaisa Mansur yake ce masa
"Abokina dan Allah idan babu takura akwai saqon da zan aiko dashi ta gurin wani abokin aikina da ze taho Nigeria zuwa wani satin, Magungunan Mama ne, kullum tasha na nan din cewa take ciwo babu sauqi shiyasa na aiko mata dasu ta gwada ta gani ko za'a dace da irin na nan din toh Habibu kuma yana Dutsin Ma sun kona makaranta ko zaka taimaka ka karba mata idanya iso danshi ba dan Kano bane besan gurare ba"

"Babu damuwa, ka turamun da number sa idanya zo se na karba mata. Gaskiyar Mama ai dan nidai paracetamol kadai nasha na saudi na fahimci da banbancin ingancin magunguna tsakanin mu dasu, Allah dai ya kawo mana sauqi Nigeria amma komai namu se anyi ha'inci a cikinsa kana shan magani dan neman lafiya qarshe ya janyo maka wata lalurar".
Hira suka dantaba kafin sukayi sallama yana kashewa kuwa lambar mutumin daya turo masa ta shigo. Da Yake ya sanar dashi be rigada ya iso Nigeria ba dan haka yayi saving zuwa randa ze iso din se ya kirashi kafin na ze masa magana a WhatsApp yaji ina ne masaukin sa idan ya iso Kanon.

Yana ajiye wayar Hajiya ta sakko daga sama, fuska babu cikakkiyar walwala kamar yanda ya koma a gidan ya shiga gaisheta Dan Sosai Hajiyan ke takura masa da maganar Umaimah wanda shi kumabaya soshiyasa yanzu baya wani jimawa a bangaren nata yake fita ya gwammace yayi zamansa a palour Sama yayi kallo dan tuni ya saba da zaman kadaici ya dena Hira da Umaiman.
Tuwo Hajiyar ta saka aka kawo masa, sanin babu lallai ya samu abinci a nasa gidan yasa sukaci shida Mu'ayyad yana ci Hajiyar na masa hira shidai Eh da Aa ne amsar sa harya gama yayi mata sallama ya fita dan Mu'ayyad ya wuce Habiba zatayi masa wanka ya kwanta.

Da mamaki ya ringa kallon falon daya sha gyara se tashin qamshi yake, dukda dai Ruqayya na qoqari gurin gyaran gidan amma na yanzun daya gani na daban ne dan dazu daya fita sallah babu wannan qamshin ko kuma be lura bane oho. Tabe baki yayi ya haura saman, Mamaki ya sake kashe shi dan gyaran da akayiwa falon saman har yafi na qasa ga kalar turare me sanyi da qamshin da aka saka yana shaqarsa yaji gabbansa sun fara sanyi gajiyar daya kwaso ta hauro masa so kawai yake ya kwanta a kan kujera yayita shaqar daddadan qamshin.

Qarasa shiga ciki yayi, yabi Kwanukan abincin da aka jera akan Table mat a qasa da kallo harda Jug din Zobo me shegen sanyi dan se diga yakeyi ya gani ga fruit salad a bowl an rufe da Clingfilm ya hadiye yawu qut saboda yanda ransa ya biya Sanyin zobon amma ya hadiye kwalamarsa ya wuce dakinsa yana mamakin yau kuma meya hau kanta ya sakata wannan aiki ita da tace bata da lafiya?

Shi kansa gadon a lailaye ya tarar dashi an chanza masa Bedsheet se kawai ya wuce bandaki yana mamakin wannan sabon salo kuma na Umaimah. Matar da tunda tayi ta shige masa yana shareta na dan lokaci ta yakice shi itama ta watsar hidimar gabanta kawai takeyi ita ce yau harda gyara masa daki abinda rabon da tayi tun kafin tasan alaqarsa da Zahra. Da ruwandaya tarar ta tara masa ya sheqa wankansa me kyauya fito. Tsaf ya shirya cikin kayan bacci Farare Cotton marasa nauyi ya dauki wayarsa ya dawo falon dan yana so ya kalli labarai.

Umaimah na zaune tasha kwalliya da doguwar rigar Material Light Pink me santsi dan haka rigar tabi jikinta ta lafe cikinta ya fito sosai a gaba ya mata kyau dan shi bema taba lura da yanda ciki ke mata kyau ba se yau din ko kuma wannan din ne dai oho.
Fuskarta ya kalla data sha joda da Lip balm pink bakinta se qyalli yakeyi, wani abu yaji ya tsarga masa wanda rabon da yaji makamancinsa tun kafin ta janyo masa Asara se yayi saurin dauke kai daga kallonta ya wuce can kujerar gefenta ya samu guri ya zauna.

"Sannu da dawowa, ashe ka shigo ina ciki banji shigowarka ba" Umaiman ta fada tana masa murmushi. Seya bita da kallo. Mamakinta ya sake kamashi amma seya kanne shima ya maida mata da murmushin yace
"Yauwa, ai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login