Showing 192001 words to 195000 words out of 429394 words

Chapter 65 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1038

shi se ya saki murmushi yana sake jinjinawa wauta irin tata yace
"To kin bawa kanki amsa baze ma yuwu ba se kiyi haquri kije kiyi Addu'a Allah ya sake baki wata ki saka sunan taki uwar bashi kenan ba?"
"Amma Abba..."
"Amma me Umaimah? Son zuciya qiriqiri? Kince idan taki uwar ya fara sakawa ya canza bazaki yarda ba sannan shi saboda besan dadin uwa ba se mu saka ya canza sunanta? Ban son shirmen banza tashi ki bani guri na zata maganar kirki ce ya kawoki ashe shirmenki da bashi da qarshe kikazo kiyi mun, tashi ki koma gurin yarki bana son wata magana a nan" Abban ya katseta cikin hade fuska dole ta miqe cikin qunquni tayi masa seda safe ya raka ta da ido a ransa yana mata Addu'ar Allah ya shiryeta, yarinya kamar wadda ke tunani a juye.

Da Mama ta shigo yake gaya mata yanda sukayi da Umaiman kai kawai ta girgiza tace Allah ya rufa Asiri, labarin baranbaramar da tayi gana qanwar Khalil ta bashi taci gaba da cewa
"Ni a cikin marasa hankali ma samun kamarki Umaimah se an tona, in ba haka ba mutum ya saka sunan uwarsa kice be miki ba se an canza ina aka tabayin haka fisabilillahi? Matar nan yanda take sonta koni uwarta ai se haka kaga fa irin hidimar da ta ringayi kullum wuni take a Asibiti har aka sallamo su bata gajiyawa ga waya akai kaia taji yaya suke duk wannan soyayyar bata sa ta raga mata ba se waye ze tsere daga Halin Umaimah?"
"Addu'a zamu cigaba da yi mata wata rana se kiga ya zama labari" Abban ya fada ganin ranta ya fara baci, ta miqe tana zuba masa abinci ba tareda tace komai ba amma a ranta tana ayyana yanda zataci Uban Umaimah tunda taga alamar duk Horon da akayi mata a baya be shiga kanta ba tana sane ta hana duk wata hanya da zata samu magana da Khalil din a zatonta zatayi laushi ta bada haquri ta kuna nemeshi amma taga alamar Umaimah bata tunani irin na mutane.

Anyi suna lafiya dukda ba'ayi wani taro ba Umaimah da Babynta sun sha gayu da hadaddun dinkunan da Ummu-Maheer tayi mata duk wanda yaga hotonta seya tambayi inda ta siyi kaya ta ringa yanga tana iyayi wai itama ta zama yar Unique collection, har kuma sannan bawai ta saki ranta akan sunan da aka sakawa Babyn da dasuka gaji da tambayarta me za'a ringa kiranta taqi fada ba suka fara kiranta da Bibi kamar yanda Mu'ayyad yake fada. A WhatsApp taga Hotunan da suka dauka ita da yaran Khalil ya dora, ta qulu iya quluwa, wato yana ganin status dinta ma ashe toshewa yayi yanda ba zata gani ba dan ko saqo ta tura masa baya nuna blue tick duk ita tayi zaton ma ko baya WhatsApp din dan tun da sukayi wayar nan be sake kiranta ba ita ce ma tayi masa magana a WhatsApp kuma be amsa ba to ashe yana gani wulaqanci ne ya hana ya amsa ta ze sani kuwa.

HALIN KISHI

48


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 48

Kamar wasa sukayi Arba'in, zuwa sannan Umaimah tayi laushi iya laushi ta kuma naba'a neman shiri take da Khalil ta kowacce shiga amma yaqi ya bata dama. Zaman ya ishe ta, wata kusan biyar ba wasa ba tana zaune ita ba me aure ita ba sakakiya ba kuma a gidan babu wanda ko a fuska ya nuna ya damu da zamanta sabgoginsu sukeyi kamar ma sun manta da wanzuwarta dan idan bata fito tsakar gida ba sedai taji suna hidimomi har wani lokacin ace mata ai an manta ma da tana gidan.

Randa zuka cika kwana Arba'in Hajiya ta aiko Habiba akan tana gayyatar su Maman gobe zasu tare a sabon gidansu. Mamaki fal ya cika Umaimah dan sam bata da labarin ginin daya fara lokacin ana dambaruwar zancen ciki an gama wannan kuma aka shiga ta Hadiza basu damu wani lokaci ba balle har ya gaya mata zancan. Su Mama sunje sundawo sunata santin gida. A bakinsu taji cewar itama yana mata ginin gida dayane tareda Hajiyar amma kowa Get dinsa daban dan har ciki aka kaisu suka gani Sunata saka albarka da fatan gamawa lafiya. Abin ya sake qule ta, wai me Khalil ya mayar da itane yazo ya jingineta ya kamata ayi wacce za'ayi tasan matsayi ta dan ta gaji da wannan wulaqancin nasa.

Seta kirashi sau nawa baze amsa ba idanma ya saga basa doguwar magana, data kawo qorafi ze ce mata yana abu ya kashe wayarsa WhatsApp kuwa tayi zuciya ta dena kulashi dan koya duba baya bata amsa dukda irin abunuwan da take aika masa dasu da atunaninta dole su saka hankalinsa ya tashi ya dawo gareta amma kamar me shuka dusa.
"Koda yake yanzu ai yasan nasan barikin da yakeyi shi yasa bazeji shayin yin komai ba, qila yana can ya sake samun wata yarinyar shiyasa yayi zamansa ya manta da ita idan ba haka badai Khalil din data sani bane ze kwashe tsahon wata biyar na tareda mace ba" abinda take rayawa a ranta kenan duk ranar da tayi wannan tunani kuwa kwanan kuka da baqin ciki takeyi, ta kuma qudure a ranta duk randa sukayi arangama da wadda ta janye mata hankalin Miji sedai uwarta ta haifi wata dan seta kasheta idan yaso ayi mata duk abinda za'ayi.

Kwanan su hamsin da biyar ta shirya da safe tace Salman yazo ya kaita gidan Hajiyar, Babu Wanda ya hanata suka kama hanya tinqis tinqis se gasu a gidan, mamaki ya kasheta ganin yanda gaba daya aka canza gidan, dan da sukaje seda sukayi gaba suka dawo, ta sake irga gidaje daga tsohon gidan Maman Asad da suka tashi tasan dai gida biyu ne tsakaninsu amma nasu Khalil din na daya bangaren. Ma'aikatan dake ta faman kwasar sumunti suna shiga dashi ciki suka tambaya ko Hajiya tana nan suka ce mata Eh, wani dan saurayi baqi da zeyi Sa'an Salman din ya taso ya bude musu qofa, qaton compound suka tarar ga qananun Get biyu dama da hagu, ya nuna musu na hagun yace nan ne gurin Hajiya Umaimah dai ta kasa dena kallon Hadadden ginin dake gabanta dukda bata shiga ciki ba gani takeyi yafi yanda su Anty suka ringa bada labarinsa haduwa.

A sabon qerarren palour Hajiya suka yada zango, Habiba ta fito daga kitchen da gudu ta rungume Umaiman da ta tafi duniyar kalle kalle da mamakin a yaushe duk Aka yi wannan aikin bata sani ba?

"Mamaki kikeyi ko Anty, ai se ma kin shiga naku kinga Aljannar duniyar da yaya yake qera miki zakiyi tsallen murna, nima dai Anty ki taimaka kiyiwa Yaya magana cikin Abokanan sa ya samo mun wani Architect yayi wuf dani, ko nima na samu a qera mun gida na haduwa irin naki" Habibata fada tana kallon Umaimah data kasa zama kamar wata yar qauye tana kalle kalle a parlour koda yake dole tayi kallo yanda a ka qalqalewa Hajiyar gida kamar na wata sabuwar Amarya, Khalil yayi nasa bangaren ya mata gini sauran yan uwansa suka qarasa qawata mata gida da kayan daki na alfarma, kujerun palour kansu saiti ne na Royal hade da gado da Dining Miliyan biyar cis suka siye shi a hakan ma Mijin Anty Amina ne yake kawo su yayi musu sauqi Hajiya ta ringa fada akan me zasu siya mata wadannan kaya suka cwme sun sanda Mahifinsu na raye na sama da haka ma ze siya ya zuba mata kuma yanzun suna dashi ne shiyasa sukayi. Ranar har kuka seda tayi, ta ringa saka musu albarka da addu'ar suma Allah ya kawo randa yayansu zasuyi musu haka.

Dukan wasa ta kaiwa Habiban tana cewa
"Lallai ma yarinyar nan kin riqa, a fakaice dai gayamun kike aure kikeso ko? To bari Hajiya ta fito in gaya mata musamu mu tattaraki mu miqawa me rabo" suka saka dariya gaba daya daidai nan Hajya ta sakko daga sama cikinshigar Alfarma harda Mayafi a jikinta da alama fita zasuyi Mu'ayyad na binta a baya yana mata surutu, hango Mamansa da yayi ya sakashi kwasowa da gudu ya sakko yana kiran Mama ya dane ta, dagashi sama tayi suna dariya Hajiya ta qaraso itama cikin dariyar take cewa
"Ikon Allah, sakkowar nan tamu gurinku zamuje ashe kuna tafe? Idonki kenan yau a gidan nan Umaimah" Ta qarasa tana karbar Bibi daga hannun Habiba.

Umaimah ta zube a qasa tareda Mu'ayyad dake ta tsallen murna a jikinta ta shiga gaishe da Hajiyar ta amsa tana tambayarta mutanen gida da yanda suka koma tace duk suna lafiya kafin suka gaisa da Salman shima

"Kasa gane gidan mukayi Hajiya har seda mukayi tambaya" Umaimah ta fada Hajiya tayi dariya tace

"Ai daman ba zaku gane ba, yaushe rabonki da gidan nan? Inaga tunda aka fara aikin ma baki zo ba?"
"Munzo lokacin da kuke shirin komawa daya part din lokacin nema yayi mun zancan za'a fara aikin daga nan be sake cemun komai ba" Umaiman ta fada tana shan lemon da Habiba ta kawo musu. Hajiya ta kama baki tace

"Tab kice kusan shekara guda kenan, gashi nan har an gama an tare, nakun ma qarashe yarage, da da aka gama nan yace ze dakata kuma bansan ya akayi ba mukaga an ci gaba da aiki, a yanda yake so ma kafin ya dawo an gama yanda kawai tarewa zakuyi"
"Uhm" kawai Umainah tace ta ci gaba da cin abinda aka ajiye musu Hajiya kuma nata yiwa Bibi wasa ga Mu'ayyad daya hanata sakat wai se ta bashi ita.

Hira suka ringayi Hajiyan nata mata labarin ginin, tace ta tashi ta zaga ko ina ta gani Habiba ta rakata suka shiga kurya da saqon gidan se santi takeyi a ranta ko tattara irin rashin M din da zatayiwa Khalil take, yanzu ace bata da darajar daze gaya mata yana gini kenan, qila da se rana daya zece zasu tashi ko kuwa da a nan din yayi niyyar ajiye Hadizan tasa.

"Guri yayi kyau Hajiya Allah yasa raida lafiya akayiwa, su kuma Allah ya saka musu da Alkhairi ya cigaba da buda musu" Umaimah ta fada bayan sun dawo palour se Hajiya ta amsa da Amin cikin jin dadin Addu'oin Umaiman, abinda yasa take matuqar sonta kenan saboda hankalinta da sanin ya kamata ga kyauta da fara'a babu wanda zeje gidan nan ya dawo be yaba kirkinta ba in banda bangaren su Gwaggo Zara'u da tasan da biyu suka tsani Umaiman, saboda yaqi auran yarsu ya aureta ne.
(Aa dai Hajiya ke da masu sa'a ne zasu bada wannan sheda akan Umai)

Murmushi tayi tace
"Ai ni banma so ya barnatar da kudi yayi wannan gini haka ba, ina laifin a mun dan daki biyu na da palour Flat nida ba yara ba nan da kwanaki idan Habiba ta daga gidan ai ya mun girma daga ni se Khaleefa, koda yake kinga an huta yayiwa dan uwansa tanadi se kuyi zamanku tare idan ya tashi aure ni se na koma inda zaku baro ko ya kika ce?"

"Haba dai, Allah ze hore ayi masa nasa Wanda yafi wannan, kullum qara samun sababbin qere qere ake hajiya musammansu Yaya Khalil da harkar su kenan kar kiyi mamaki shekara iyanzu yace za'a rushe gidannan a sake wani" Habiba ta fada Hajiya ta kwalo ido kamar anzo rushe gidan tace
"Saboda yace miki shima kwarkwarne irinki ba, Allah na tuba wannan gida ko a Aljanna ka samu kamarsa ai ka more wallahi menene babu a ciki? Har gurin wankan nan da Garden naji yana za'ayi idan masu filin bayan mu sun yarda sun siyar masa, nidai nace yajashi can cikin gidanku ku qarata wane gurin wanka ne ana zaune lafiya yan ruwa suzo su tare mana a gida".

Dariya sosai suka ringayiwa Hajiyan, wai yan ruwa kamar wanda ze gina wani Teku. Umaimah da taje da niyyar qulla Sharrin da ze saka Hajiya ta kirawo Khalil ko be shirya ba ya dawo se gashi ta buge da hira, a gidan suka wuni sur se bayan la'asar suka fita tareda Hajiyan suka shiga wani gida da ake suna yarinyar gidan ta haihu. Basu fito ba se ana kiran Magriba dan haka suna idar da Sallah Umaimah ta hau shiri Hajiya na kallonta tace
"Nadai gayawa Babana wannan zaman ya isa haka tunda dai Allah yasa kin haihu lafiya se ya zaba ko ya dawo ki koma dakinki ko ya shirya miki ki bishi can, ai su Malikan ko basuyi magana ba abin ze damesu a ajiye maka Ya sama da wata biyar ai babu dadi, gara ki tattara ki koma dakinki in yaso ki nemi me tayaki zama kafin ya gama walagigin nasa ya yanke shawara dan ya fara cewa wai gurin zama waye waye dinsa dai".

Wani sanyi taji ya ratsa ranta, tun dazu shirya abinda zata fadawa Hajiyan takeyi ta rasa se gashi ta rage nata aiki dan haka ta marairaice fuska tace
"Wallahi ko Hajiya, kinsan mutane da surutu, wasu ma cewa sukeyi akan abinda ya faru kwanaki ai sakina yayi muke boyewa"
"Subhanallahi innalillahi wa'inna ilahi rajiun inji wane me mugun bakin? Kai mutane mutane Allah ya shiryi mutum. Baka da gadon mutum amma yana da na maganar ka ta kuwa zanyiwa tufkar hanci tun kafin abu yayi yawa ya kai inda ba'a zato.
Nan ma fa seda nasha fama da munafukai wasu kigansu da shegen tsugudidi sun kawo mun video se in sage musu guiwa nace a gaba akayi, daman ina so naja kunnenki kema kiyi ta kanki ki fita sabgar duk wasu masu jefa mutum a masifa.

Yanzu fa duniya ta baci, wani ma dariya kuke dashi amma neman damar da ze cuceka yake dan haka ki kiyaye duk wata harkar qawaye balle azo ana gaya miki abinda ze daga miki hankali har ki aikata abinda be kamata ba. Duk wadda ta kawo miki wata gulma da baki da tabbaci kiyi watsi da ita kin daiga izina haka kawai yarinya taso ta sakaki a bala'i badan Allah ya tsare ba yanda yayan yarinyar nan yake zare zaren ido ai beqi a tafi gaban Alqali ba. Kedai babu ruwanki ki ci gaba da kula da kanki kina kula da Mijinki shikenan zaman aure daman dan haquri ne, duk namiji bakya raba shi da kule kulen yammata dan haka Allah ya halicci zukatansu dan haka ki saki ranki koda ace Allah ya qaddara wata rana ze kawo miki abokiyar zama idan ya zamana kin kama kanki duk wadda zatazo sedai ta biki, ballantana nasan Idan Babana gadon Marigayi yayi ke din dai kece babu qari, So dayan nan ne tak sukeyi ba kuma sa iya rabashi biyu. Ko Mahaifiyar Jamila daya auro gaba dayan mu munsan rabonta ne ya saka tunda kinga wata tara da auran ta haifeta kuma Allah ya karbi ranta sanadin haka to wani abun baka kaucewa qaddararsa dan haka dai ina nanata miki ki qara haquri".

Yanda kasan me daukar karatu a gaban Malam haka ta nutsu ta duqar dakai har Hajiya ta kai aya kafin ta dago tace
"In sha Allahu Hajiya wani abu makamancin haka baze sake faruwa ba, wancan dinma sharrin shaidan ne ni kaona daga baya na ringa tunanin meya shiga kaina harna aikata hakan amma qaddara ta riga fata kuma na miki alqawarin haka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login