Showing 303001 words to 306000 words out of 429394 words

Chapter 102 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1041

Datansa ya kalli inda Umaimah take yaga bata nan ta shiga daki kenan.

Dakyar yaja qafarsa yana cije baki zaman da yayi yasa ta qara yi masa nauyi ya isa qofar dakin nata ya kwankwasa.
"Come in" ta bashi amsa ya tura qofar da Sallama, tana kwance har taja bargo ta rufe jikinta saboda uban Ac data warewa dakin seya qarasa ya zauna gefen gadon yana cewa
"Idan bazan takura miki ba zan kwanta a nan qafata ta matsa mun bazan iya hawa sama ba"

"Mutum da gidansa se ya nemi izinin inda ze kwanta" ta bashi amsa tana gyra kwanciyarta, baya ta juya masa yayi murmushi kawai yana kallonta seya miqe dakyar ya wuce bandaki, alwala ya dauro ya dawo dakin, seda ya rage qarfin Ac kafin ya kwanta a gefenta yana sauke numfashi gaba daya qamshin turaren data saka ya dameshi ya nemi saka shi a wani hali. Kanta zuwa Bayanta ya shiga shafawa a hankali Umaimah dake jinsa tayi laqwam kamar me bacci, a hankali ya juyo da fuskarta, ta bude idonta cikin nasa da sukayi laushi, be bari tayi magana ba ya hade bakinsu ya shiga aika mata Kiss me zare lakar jiki. Yafi minti goma yana kissing nata tareda kai hannunsa jikinta yana ya mutsata, yayi mamakin yanda ta saki jiki sosai tana maida masa da martani da alama itama tayi missing dinsa, mantawa yayi da wani ciwo da qafarsa takeyi suka gurji junansu kamar babu gobe seda komai ya lafa munafukar ta juya baya tana wani muzurai.

Haushin kanta ya kamata wai ya akayi ma ta wani sakar masa fuska har haka shi kuwa Khalil kallonta kawai yake yana murmushin rigimar Umaimah darunta se Allah. Haka ya doddogara yayi wanka yana jin yanda riqewar qafar ta sake haurawa har kusan qugunsa daya fito daga wankan kasa kwanciya yayi haka ya zauna yana shafa qafar, Umaimah data fito daga wanka itama ta kalle shi ganin yanda yake cije baki tace masa
"Sannu, ko na dakko Aboniki na shafa maka?"
"Da zaki iya akwai magani a dakina na shafawa ki dakko mun".

Seda ta saka kaya ta tafi Saman ta dakko masa maganin ta bude hanci tana shaqar wani qauri da bata san kona menene ba kamar dai na magani. Baki ta tabe ta dauki abinda ya kaita ta kashe fitilun daya bari a kunne ta sauka qasan. Da kanta ta shafa masa, sun dade a zaune seda yace mata ta kwanta kafin ta kwanta dukda na bacci takeyi ba tana ta kallon yanda yake juya kai yana cije baki sosai tausayinsa ya kamata duk ita ta janyo masa wannan Azabar ai kuwa gobe dole Safina ta kira Malam ya karya abin nan ba zata jure har kwana uku tana kallonsa cikin wannan Azabar ba.

Washe gari babu yabo babu fallasa ta ringa ayyukanta, ita ta shirya musu abin karyawa, ragowar Kazar ta sake dumama masa ta dafa shayi ta gasa masa buredi ita kuma ta dumama tuwo ta dama Koko dan yanzu su take jin dadin kari dashi. Falon qasan ma Sammani ta kira ya shiga ya share ya goge dan ba zata iya ba, tana ganin ma sedai ta nemo wata me aikin kawai tunda bata san sanda Ruqayya zata dawo ba. A gida Khalil ya wuni, tunda ya fita sallar Asuba ya dan tsaya bangaren Hajiya suka tattauna bayan sunyi waya dasu Baba Abu da suka dauko hanya se gurin bakwai ya koma bangarensu tun sannan kuma be sake fita ba seda zasu tafi Masallaci da Khalifa. Yaji dadin qafarsa harma ya manta da batun komawa Asibiti daya dawo daga Masallcin ma kuma gida ya sake zama saboda yau har yar hira sukeyi jifa jifa data kwanta bacci ne ya koma bangaren Hajiya se kusan qarfe biyar na Yamma su Baba Abu suka sauka Jalingo, sun yi waya dasu Khalil din ya sanar masa sun basu masauki yanzu sunce su huta, se zuwa dare zasu zauna da Waliyyan Humairan suyi abinda ya kawo su washe gari kuma suyi Asubanci su juyo Kano.

Qarfe takwas bayan ya dawo daga Sallar Isha suna zaune a falon Hajiya shida Jalilah data zo gidan babu dadewa wai tazo jin yanda akayi a Jalingo Hajiya natayi mata fadan ta cika Azarbabi idan bata fita daga sabgar maganar auran nan ba ranta ze baci ita dai tayi shiru bata ce komai ba.
Wayar Khalil dake ajiye kusa da ita ce ta dauki qara ta miqa masa tana cewa "Mansur na kira" ta bashi wayar seta miqe jin Hajiya na kiranta daga daki
Khalil dake cin tuwo ya miqa mata hannu bayan yace ta daga masa, ya kara wayar a kunnensa yana cewa
"Allah ya taimaki babban Yaya yau ka sauka daga fushin da kakeyi damu kenan ka kirani?"

"Malam ba surutu na kira muyi ba number Matarka zaka tura mun yanzu dukda I'm not in support of abinda ya faru amma Alqawari nayi kuma ina so na sauke dan na gaya maka in Allah ya yarda duk randa ka qara aure ni zan fara breaking ma Umaimah labarin nan maza ka turo mun kafin wani ya rigani"

Dariya Khalil yayi yace
"Toh ai duk mugun halinka ka bari lokacin auran yazo ba ka kunnamun wuta tun yanzu ba daman cikinta nake na samu Allah ya kashe zaka sake tadota, har sun gama maganar kenan wata nawa aka saka Yayanmu?"
"Wata ubanka aka saka dan iska kawai badai ka rantse seka saka qanwata a tashin hankali ba to kafin ta shigo kai zaka fara tarbar rabonka ni dallah turo mun number na kirata na gaya mata tun maganar da zafinta in yaso ta mutu aure dai an rigada an daura" Mansur ya sake fada se Khalil yace

"Aiko bazan baka number ta na kuma san babu inda zaka samu dan ta canza layi ba kowa yake dashi ba, auran wa kuma aka dauka naji kana magana?"
Tsaki Mansur yayi yace
"Ko ban gaya mata ba zata ji ai nasan kuma ni zan fara fado mata a rai ko haka aka tsaya burina ya cika kai kuma Allah baka ikon yin Adalci dan idan kuka cutar mun qanwar kaida ita duk se naci ubanku" yana gama fada be jira Khalil yayi magana ba ya kashe wayar dan daman a fusace yake.

Guda yaji an rangada saman kansa ya dago yana toshe kunnen Jalilah dake tsaye ta sake rangada wata gudar tana cewa
"Alqawarin Allah ya cika aure kuma ya dauru yan baqin ciki sedai su mutu Humairah da Khalil Allah yayi mun nema kuma an bamu" yanda kasan wata maroqiya haka take maganar.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 68

JALINGO
Ana kiran Sallar Magriba su Baba Abu suka isa gidan Alhaji Muhammad Jibril wanda yake matsayin yaya ga Mahaifin Humaira Marigayi Malam Nura Jibril kuma qani ga Mama Hauwa. Sun rigada sun san da zuwansu dan haka sun tanadesu, a matuqar gajiye dattijan suka zauna a katafaren falonsa inda aka ajiye musu kayan abinci nau'ika kala kala, ruwa kadai suka sha suka fita zuwa Masallacin dake qofar gidan a can sukayi sallah kuma a sannan suka fahimci Ahalin gaba daya suna zaune a unguwa daya ne dan tun a Masallin Alhaji Muhammad ya fara gabatar musu da yan uwansa wanda kamannin da suke kadai ya isa ya gaya maka alaqarsu mutane masu karamci.

Cikin gidan suka koma bayan sunyi Sallah, Basa tare da yunwa sedai gajiya dan haka suka zauna a falon aka shiga sake gaggaisawa. Bayan gabatar da juna Alhaji Musa wanda shine babba a gidansu Maman gaba daya ya fara magana da cewa
"Hauwa ta rigada tayi mana bayani akan shi manemin Aisha da kuma zuwanku, bamu da buqatar sake yin wani bincike akansa saboda a duniya mu zamu fara bada shaidar irin tarin qaunar da Hauwa takeyiwa Aisha tun mun kuma san ba zata taba yi mata zabin Mijin da bana gari ba, amma dukda haka domin mu sauke haqqin da Allah dora mana mun sake bincika wanene Ibrahim is aka sake yin wani katari ashe na gida ne domin Abokin aikin dan uwan mune gashi nan" ya Nuna Alhaji Muhammad se Alhaji Muhammad din yaci gaba da magana yana murmushi yace

"Tabbas Khalil Abokina ne kuma qanina nafi shekaru biyar da saninsa mun hadu a qasar Africa ta Kudu lokacin da wani aiki ya kaimu daga nan alaqa me qarfi ta qullu tsakaninmu saboda kasantuwar harkar neman abincinmu daya, munyi kwangiloli da yawa tare kuma ya kasance mutum me Amana da kyakykyawar mu'amala shi yasa nayi matuqar farin ciki a lokacin dana fahimci shine manemin auran Yar dan uwana".

"Toh masha Allah haqiqa munji dadi kwarai da wannan shaida da kuka bayar akan Dan mu ina kuma me qara baku tabbacin yarku ba zatayi dana sanin auran Khalil ba domin mutumin kirki ne ku da kanku da sanin nesa kukayi masa kun shaida hakan, sedai muyi fatan Allah yasa su zama abokan arziqi na har abada Allah kuma ya hada kawunansu" Alhaji Garba ya fada kafin yaci gaba da cewa
"Ina ganin idan har babu damuwa zamu iya gabatar da abinda ya kawo mu saboda yanayin jiki da akwai gajiya tattare damu mu samu mu tafi masauki mu huta saboda Asubanci muke so gobe mu qarayi mu juya Kano, Alhaji Abubakar Bismillah".

Baba Abu ya zura hannu a Aljihu ya ciro kudi badir yan dubu guda uku ya ajiye gaban Alhaji Musa yana cewa
"A matsayina na waliyyin Ibrahim Khalil ina nema masa auran yarku Aisha wannan kudi Dubu Dari biyu kudin gaisuwar Iyayene dana na gani ina so, se wannan dubu dari kuma Sadaki ce kamar yanda waliyyinta Alhaji Muhammad ya yanka mana"
"Amma Alhaji mun rigada munyi magana da kai cewar mu a qa'idar gidan mu bama karban wani dukiyar aure Sadaki ne kawai kuma mun yanka muku" Alhaji Muhammad ya katse Baba Abu se Baba Imrana yayi saurin cewa

"Mun sani Alhaji amma muna neman alfarma tunda mun kawo ayi haquri a karba, Ya fa zaku bamu ina ganin ko Duk abinda muka mallaka muka kawo be kai mu biyaku karamcin da kukayi mana ba".

Bayan Alhaji Muhammad ya karbi kudin ne Alhaji Musa ya sakeyin gyaran murya yace
"Ba karambani ba duba da yanayin tazara dake tsakanin garuruwanmu da rashin tsaro da ake fama dashi ga kuma damar da tazo a kan gaba yasa nake tunanin tunda har mun samu daidaito kuma yarjejeniyar aure ta qullu a tsakani, me ze hana mu taqaita komai domin mu hutashshe ku dawainiya da sake dawowa harma da yin gayyar mutane zuwa daurin aure. Yanzu da yardar Allah idan an idar da Sallar Isha'i da akwai auren yar dan uwanmu da za'a maida a nan masallacin, ina ganin idan har babu damuwa daga gurinku dan mu a shirye muke in kun Amince a hada gaba daya ina nufin a daura auran ita Aisha da Ibrahim kaga mun sallameku Yarinya ta zama taku se ku koma can Kano ku yi shirinku duk sanda kuka so ku dauki Amaryarku a hannun Hauwa, muma daga nan sabga ta mata idan an tashi tariya suje suga mazauninta shi kenan ba se munyi rakiyar Kura ba kunzo kun koma ku sake dawowa sannan muma mu biku, zamu baku guri ku tattauna a tsakaninku yanda kukayi se muji".

Shiru sukayi ganin waliyyan Humairan na shirin miqewa Alhaji Garba ya numfasa yace
"Idan akayi hakan Alhaji zamu fi kowa murna to sedai wani hanzari ba gudu ba, bamu san shirin ma'aurin ba ina nufin ta bangaren gurin zaman ita yarinyar da sauran abubuwan buqata bamu da tabbacin ya tanade su amma hakan baze zama wata damuwa ba da yardar Allah, Abubakar seka kirashi ka sanar dashi halin da ake ciki Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" gaba daya suka Amsa da Amin.
"Ai maganar muhallima nasan wannan ba matsala bace Lefe kuwa ya gama danma sunce kar azo dashi ne kaga babu wani abu da yayi masa saura inaga se zuwan Amarya kawai" Baba Abu ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? fada cikin raha kafin ya shiga kira wayar Khalil sau biyu be dauka ba, jin fara kiran Sallah yasa suka fita. Masallacin ya cika danqam ciki da waje ba kamar yanda sukayi sallar Magriba ba Baba Abu ya kalli Angon da za'a maidawa aure da zugar abokansa ya cewa Baba Imrana
"Kaga shirin Allah, qila da munzo dashi yayi mana taurin kai shiyasa can qafarsa ta riqe muka zo babu shi, Allah ya sanya Alkhairi yasa mutuwa zata raba.

Bayan an daura auren suka niyyatu wucewa Hotel inda zasu kwana amma iyayen Humairan suka hanasu dan tuni an tanadar musu makwanci Abincin da basu ci bama can aka kai musu, duk wani abu da zasu buqata an tanada bayan sun dan sake taba hira suka barsu saboda su huta se a sannan Baba Abu ya kira Hajiya ya shaida mata, kasa magana tayi seda ya sake cewa
"Hajiya ko bakya Ji nane" kafin ta aje numfashi saboda kaduwar da tayi da zancen daurin auran tace
"Ina jinka Abubakar labarin ne yazo mun a bazata har na rasa abinda zance akai"
"Me kuwa zakice muma duk haka abinya shammace mu kuma su da zasu bamu suka yanke haka kinga babu damar muce Aa se ya zama kamar ba dagaske muke neman ba fatanmu dai Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi kawai amma yanzu kuyi shiru da maganar karta fasu a Dangi tukunna har se mun dawo"
"Toh ubangiji yasa hakan ya zama Alkhairi Allah ya basu zaman lafiya kuma yasa matarsa ce har gidan Aljanna" Hajiya ta fada daga nan sukayi sallama.

Gaba daya rasa ta inda zata fara tunani ma tayi, an daura auran Khalil daga zuwa tambaya ta ina zasu fara fitar da wannan Labari har ya isa kunnen Matarsa a wane matsayi zata karbi abun?
Jalilah ta kwalawa kira dan tanada buqatar wanda zasu shawarta tunda wuri, seda ta sauke tagumin data rafka saboda Jimami Umaimah kawai take tunowa a duk cikin al'amarin dalilin daya hanata yin murna da daurin auran gaba daya kenan. Bude baki tayi da kyar ta gayawa Jalilan yanda sukayi da Baba Abu, sak tayi da farko kamar bata gane abinda Hajiyar take fada ba kafin ta saki Kabbara ta waiwaya gabas ta tsugunna tareda kai goshinta qasa tayi Sujudushshukur seta miqe tana kallon Hajiyar bakinta kamar ze tsage tace
"Kin gani ko Hajiya Allah kadai yasan sirrin daya boye cikin wannan auran Allah yasa silar fitar Khalil daga qangin rayuwar da yake ciki kenan" seta juya da sauri ta koma falo, a kan Khalil ta tsaya ta rangada masa guda tayi ta qarayi yanda kasan wadda ta kawo Amarya.

KHALIL
Kallon bakin Jalilah kawai yakeyi yana so ya tantance abinda take fada, wai shi Khalil take nufi an daura masa aure kowa? Maganar da sukayi da Mansur ta fado masa take ya hadasu da maganganun Jalilar lissafin ya bashi daidai da gaske kenan aurensa aka daura amma ya akayi hakan ta faru?
Wayarsa ce ta sake daukar qara ya daga ganin Baba Abu ne kafinma yayi magana yace masa
"Kai ina ka shige ina ta kiranka baka dauki waya ba ina fatan da kaji abinda ya faru ko? Toh daman kira nayi in ja kunnenka ko zaka fadawa matarka ka bari seda safe dan wlh babu ruwana ga Hajiya nan ka tambayeta sanda Nayiwa Zinatu Kishiya lokacin kana Ingila seda nayi sati daya a gidanku Hajiya ta bani Maboya kafin su Alhajin Gabas Allah yajiqan rai suka shiga suka sasantamu dan haka kabi a hankali"

A hankali yace
"Toh Kawu, nagode kwarai Allah ya qara girma Allah kuma ya dawo daku lafiya"
"Ai dole ka gode mun mana dan qusa irin wannan cin bagas da kayi koda yake cikin iyayen yarinyar akwai Abokinka MJ yace sunan daka sanshi dashi seda safe ka dai ji abinda na gaya maka idan kuma kaudi ya kaika ka gaya mata shikenan".
Mamakin MJ da Baba Abu ya kira ya kamashi tabbas MJ constructions dan Jalingo ne ashe sirikinsa nema be sani ba. Komawa yayi cikin kujera ya kwanta yana jin karadin Jalilah dake buge bugen waya lokaci daya yaji zuciyarsa ta washe wani farin ciki ya lullubeta, a fili ya yi Hamdala har sau uku seya sake daukar wayarsa daya ajiye ya shiga kiran layin Humaira amma harta katse bata dauka ba, ya sake kira karo na biyu bata dauka ba seya shiga rubuta mata saqo kamar haka
"Nayi alqawarin zama mutum na farko da zanyi miki albishir din kin zamo tawa, dukda nasan kin rigani ji saboda abun ya shammacemu duka nida ke bazan haqura ba ina farin cikin sanar dake cewa kin zama matar Khalil, tun sanda nafara ganinki naji a jikina kedin Alkhairi ce a rayuwata. Ina roqon Allah daya sanya Alkhairi da Albarka a cikin tarayyata dake ina Alfahari da kasancewarki Mata a gare ni Humairata I love you moreee" ya hada da Emojis na heart da kiss ya aika mata.

"Babana" Muryar Hajiya ta fito dashi daga shauqin daya tafi, jinsa yakeyi kamar bashi da sauran wata damuwa a duniya. Hasaso kansa kawai yake rungume da yar babyn tasa da ta zama halaliyarsa a sanda be taba zato ba duda yasan ze sha daru qarshema kacokan ta dora masa laifin cewar shiya saka a daura musu aure amma wannan duk me sauqi ne, burinsa shine auranta kuma Allah ya cika maaa sedai yayi fatan ta zamo Alkhairi a rayuwarsa.
"Babana kaji lamarin ubangiji ko? ashe auran a kurkusa yake irin wannan rabon ne fa idan kayi ja'inja dashi se ayi babu kai? Hajiya ta sake fada se ya shiga shafa kansa ya kasa ma hada ido da ita wata kunyarta taji ta kamasa yanda kasan wanda ya kwana dakin Amarya kansa na qasa yace
"Wlh Hajiya har yanzu mamaki nakeyi abin kamar wasa, Mansur ne ya fara kirana duk banma gane abinda yake cewa ba ashe ma Baba Abun ya kirani se yanzu muka sake yin waya dashi"
"Haka yace toh ubangiji ya sanya Albarka Allah kuma ya kade fitina sedai ni yanzu babban tashin hankalina yanzu Khalil matarka ce ta yaya zata fahimci wannan al'amari?" Hajiya ta qarasa maganar cikin muryar damuwa.

Kallonta Khalil yayi, tunda ya darsa qarin aure a zuciyarsa yana yawan Hasaso a yanda irin wannan rana zata riskeshi da kuma yanda Umaimah

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login