Showing 51001 words to 54000 words out of 429394 words

Chapter 18 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

953

daya barta se tace zata kama yarinyar da kokawa kome? Anya ma Umaimah nada hankali kuwa?

Haka ya ringa tunani a zuciyarsa yana sharara gudu dasu a titi kamar masu tafiya Lagos Nuratu na baya tana zare ido da addu'ar Allah ya sauke su lafiya ita kuma hamshaqiyar ta hada kai da guiwa tana kukan baqin ciki biyu, maganar da yarinyar ta fada mata ga wanda akayi saboda shi ya banzatar da ita ko a kwalar rigarsa be nuna yasan tana kukan ba.

Yana tsaida Mota a qofar gidan su Nuratu ta kwashi komatsan ta tana hamdala tayi waje, Umaimah ta dago zata fara masa qorafi ya dakatar da ita da cewa
"Fita malama"
"Khalil ni kake kora daga motar ka?" Ta fada cikin mamaki tana nuna kanta, se ya kalle ta da idonsa da suka chanza kala saboda bacin rai yace

"Haka nace, Umaimah ba fita daga mota ta ba idan har bazaki dena wannan halin jahilcin ba zan fitar dake daga rayuwata ne gaba daya ba iya mota ba.
Yanzu ke abinda kike yi yayi kama da na me hankali wadda tasan me takeyi? Kishi hauka ne? Ko kuwa a zamanin Jahiliyya muke da zaki doshi wata a cikin mutane zakiyi dambe saboda bakida nutsuwa, waye ze kalli actions dinki yace kin taba zama a ajin koyar da karatu.

Toh wallahi bari kiji, ba jibi za'a daura mana aure ba ko a safiyar ranar ne kika kuskura kika maimaita something stupid as this maganar aurena dake ta tashi, kar kuma kiyi tunanin idan an daura mana aure kinci banza kenan, Umaimah idan baki shiga hankalinki ba you better get ready to deal with the othersidenof me da bazaki taba son na bayyana miki shi ba danba ke kadai ce saitin ki yake gocewa ba, idan kuma kika bari nawa saitin ya goce kece zaki sha wahala fitar mun daga mota".

Tunda ya fara magana ta daskare a gurin, Jahilci, rashin hankali, rashin nutsuwa duk ita kadai Khalil ya jefa da wadannan kalmomin saboda tayi kishi akan sa, saboda ta nunawa duniya muhimmancinsa a gurinta?

Dakyar ta iya bude baki saboda yanda kukan gaske ya taso mata dan ashe dazu na samun guri kawai tayi tana kallonsa tace
"Saboda ina kishinka kake kirana da Jahila Khalil?"

"To hell with the kishi fitar mun a mota Umaimah kafin kisa na aimata abinda ni dake zamu zo muna regretting, get out of my fucking car" ya fada cikin daga murya jikinsa na rawa jijiyoyin kansa sun fito rudu rudu ai bata jira komai ba ta fice a sittin dan ta tabbata ya kai matakin qarshe a fushi, yanda ya figi motarsa ya bar layin ya qara dugunzuma mata hankali idan wani abu ya same shi fa itace sila.

Wayarta ta fara lalubawa a jikinta taji babu se sannan ta tuna ta bar jakar a motar a garin sauri, jiki a sanyaye ta shige gida majalisar munafukan unguwarsu suka rakata da ido tana shiga suka fara tattara analysis na tunanin abinda ya faru dan basuji komai ba.

Can dakunan dake bayan gidan su ta nufa falle daddaya ne wanda sune dakunan gidan daga baya da Abban ya samu hali ya qaro wani fili shine yayi musu wani gini suka koma ciki wannan aka barshi a BQ saboda amfanin taro kamar yanzun, dakin da suka koma ciki ta bude ta shiga, babu kowa a ciki tasan Nuratu nacan tana bada kanun labarai seta maida qofar ta saka sakata ta haye kan katifa kawai ta saki Kuka, seda tayi iya yinta taji sanyi a zuciyarta kafin ta tashi ta shiga wanka ta wanke lallen da Allah ya sota garin ana iska sosai be jaguke ba.

Tunanin halin da Khalil yake ciki takeyi, ina ya tafi? Me yake yi yanzu gashi babu waya bare ta kirashi ta bashi haquri kuna bata so ta shiga cikin gidan yanzu tasan se sun cinyeta a danya. Bubbuga qofa taji anayi da kiran sunanta, seda ta kasa kunne kafin ta gane muryar Rumasa'u ce da Halima se wasu da bata tantance su waye ba.

Bude qofar tayi suka shigo kusan su biyar kaya kaya suka fara mata cari
"Amma Umaimah baki da kirki, yanzu ace sedai muji labarin auranki a gari? Toh gani tunda bani da zuciya na taso gari ya gari tundaga Maiduguri nazo" Fannah da sam Umaimah batayi tsammanin ganinta ba ta fada, qarin mamakin ta qaton cikin da ta gani a jikin Fannah haihuwa ko yaushe amma ta iya yiwo wannan takakkiyar. Halima tace ta sauke goyon yarinyarta Umaiman ta karbe ta tace

"Ki rabu da ita ni ban taba ganin inda laifin wani ya shafi wani ba a rayuwa, saboda kin samu matsala Nabila da Fauziyya shikenan se ki dauki gaba damu, mu menene namu a ciki? Mutanen nan fa ke kika kwaso mana su kika kawo su group dinmu amma da taku ta hado ku se kika mana kudin goro duk kina toshe lambarmu. Ni wallahi naji dadin abinda ya faru sosai ko babu komai mun rabu da alaqaqai dan duk wani abu mara kyau su suke qara saka mu a ciki musamman ke da kike daukar shawararsu kamar me gashi da Allah yaso ki da rahma kun rabu kin samu miji zakiyi aure na tabbatar da ace har yanzu kuna tare wallahi bazasu barki ba, se sun san yanda sukayi suka lalata maganar kamar yanda suka saba tunzuraki kina lalata auranki".

Yanzu dai komai ya wuce ayi haquri, sannan ke kuma Katinan da kika bani sunyi kadan akwai wadanda sukace zasu zo dan haka seki qaro wasu na gaya musu mu hadu a gurin kawai goben" Ruma ta katse musu cece kucen.

Umaimah da duk jiki yayi la'asar, tunaninta yana can kan sanin halin da Khalil yake ciki tayi murmushin yaqe kawai, se kuma ta miqe ta ajiye Baby Ayra tana kallon Ruman tace "Dan aramun wayarki nayi kira"
"Gaskiya bazaki cinye mun kati ba dan ke kina da me saka miki ki kirashi yanzu ya turo na samu nima kimun transfer" Ruman ta fada tana miqa mata wayar.

Fita tayi tacan gefe inda babu hayaniyar mutane ta shiga kiran layin Khalil, seda tayi kira uku ba'a daga ba, harta haqura se dabara ta fado mata. Text ta rubuta masa ta tura

"Rumasa'u ce Aminiyar Umaimah, daman ta bani number kane tace muyi magana akan motocin da zaka turo mana gobe na tafiya gurin Kamu" tana turawa ta dakata, ba'afi minti biyu ba kuqa se gashi ya biyo bayan kiran tana dagawa ta fashe masa kuka ba tareda tayi magana ba.



PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 16

Khalil

Bayan daya bar qofar gidan rasa inda ze nufa yayi haka yayita yawo a titi dan baya so ya koma gida a yanayin da yake ciki, tambaya ce ze shata a gurin Hajiya ga gidan kuma ya fara cika da yan uwa da sukazo se kace wani bikin mace a fadar sa zasu taho tun ana sauran kwana uku bayan babu abinda za'ayi.

Mansur ne ya fado masa a rai, da safe sunyi waya ya gaya masa yana off se da dare ze shiga Asibiti dan haka ya karkata kan motar ya nufi gidan su Mansur.

A tsakar gida ya tarar da Mamansu tana aikace aikave suka gaisa a mutunce dan tamkar Hajiyar sa haka ya dauketa saboda Amincinsu da Mansur tun Primary gashi yanzu sun wuce Aminai ma sedai a kirasu yan uwa.

"Ango Ango, ya shirye shirye? Bamu dade dayin waya da Hajiyan ba ai nake tambayarta ko akwai abinda za'ayi tace Aa se gobe ne za'a rage girkin daurin aure, gashi dai abin Allah nan Dan uwanka kullum yake tasaka gaba a gidan nan ashe ma seka rigashi yin auran Allah dai ya sanya Alkhairi yasa mutuwa ce zata raba" Hajiyar su Mansur ta fada, Khalil dake ta faman sunkuyar da kai dan karta ga idon sa da yayi ja ya amsa qasaqasa kafin ya wuce can inda dakin Mansur yake.

Buga qofar ya shigayi Mansur dake bacci ya farka yana tambayar waye
"Malam zoka bude mun qofa" Ya fada muryarsa a cunkushe, Mansur din na jin shine ya taso ya bude yana cewa

"Me kuma ya kawo ka? Dan Allah ku barni na huta. Kana kallo kwana biyu na jera straight ina call morning to Evening saboda na samu off muyi hidimar biki shine yanzu zaka biyo ni ka hanani bacci me zan maka" Mansur ya shiga Mita shidai Khalil be kula shi ba kai tsaye toilet ya nufa ya kunna famfo ya ringa zuba ruwa akansa seda yaji ya samu nutsuwa kafin ya dauro Alwala ya fito lokacin Mansur harya koma baccinsa.

Kan kujerar dake dakin ya samu ya zauna yai shiru lokaci lokaci ya buga tsaki, ji yake yi zuciyar sa na zugashi akan ya fasa auran nan. Wannan yarinyar babu alamar samun zaman lafiya da nutsuwa a tattare da ita gara tun yana da sauaran dama ya raba kansa da alaqaqai ya huta saboda idab ya rigada ya aureta Saki is the last thing da ze iya aikatawa.

Bashi da burin ya auri mace ya saki kai duk girman laifin da zata masa sedai ya nemi wata hanyar ya hukuntata amma banda saki saboda shi ya saka a ransa idan yayi aure to se dai idan shi ya mutu ko matar ta mutu amma babu rabuwa shi yasa ya dade yana laluben wadda halinsu ze zo daya su zauna suyi haquri da junansu amma qarshe ga inda ya qare.

Tsaki me qarfi ya qaraja Mansur ya miqe zaune tareda jifansa da Pillown daya tashi saga kai yace

"Dallah Malam tashi ka fita, kaje palour Mama ka zauna kazo se uban tsaki kake wa mutane ka duk ka cika mun kunne na kasa bacci".

Shiru Khalil yayi masa ya gyara zaman sa akan kujerar ya harde qafa yana girgizasu, se Mansur ya dawo gefen gadon yana kallonsa yace
"Talk to me Man me yake damunka why are you upset?"

"Mansur waccen yarinyar ce gaba daya so nake nima nayi going crazy kamarta. Shikenan abinta ya zama kamar wani season film ko da yaushe i should be anticipating new episode kullum da kalar sabon haukan da zatayimun display" Khalil ya fada cikin bacin rai.

Dafa kafadar sa Mansur yayi yana bubbugawa ba tareda yayi magana ba se Khalil din yaci gaba da cewa
"Daga na kirata tana Salon lafiya lau muka gama magana the next thing naje daukan su kawai ta hau kaina da bala'i sannan saboda bata da hankali zata cakumi wata yarinya da dambe a gaban mutane kawai dan yarinyar ta kalle ni"

"Dambe?" Mansur ya fada yana bude ido dariya nason kufce masa ya danne se Khalil ya maka masa harara yace
"Na zama laughing stuff kenan, ina gaya maka matsala kana neman kayi mun dariya ko bayan duk kai ka qara jefani a halin da nake ciki, sanda na nemi shawarar ka daka qarfafamun guiwa ai da yanzu ba wannan maganar akeyi ba".

"Yanzun ma Khalil lokaci be qure ba you can call the wedding off na tabbata kuma babu me ganin laifinka tunda kowa yasan halinta. Bari na saka rigata ma ba se nayi wanka ba kawai ka tashi kawai muje mu gaya musu ka fasa, su riqe komai mun bar musu ma Allah ze bamu kudin da zamu hada wasu dan gaskiya nima na fara tsorata da halinta, dambe fa? Ni rabonda naga Mata na dambe tun zamanin muna zuwa Ma'ahad Islamiyya" Mansur ya qarasa yana yar dariya ganin yanda Khalil ya zaro masa idanu se kace bashi ne ya tayar da maganar ya fasa din ba.

"You must be mad Mansur, jibi fa ne daurin auranmukake cewa na fasa so kake na bata mata suna ko yaya? Sannan duk wadannan mutanen daka je kayo gayyar daurin aure me zaka koma ka gaya musu?"

"To Khalil me kake so ayi, kasan ni me sonka da Alkhairi ne. Bazan so ka auri matar da zata ringa saka ka a damuwa ba kullum shiyasa kuma da tun wancan lokacin kayi mun bayani sosai qila dana fahimceka nayi supporting abinda kazo dashi amma yanzun ma lokaci be qure ba, zamu iya fasawa kawai kowa ya huta" Mansur dinya sake fada kamar gaske, se Khalil ya juya kai yayi shiru kamar baze ce komai ba can kuma ya juya ya kalle shi yace

"I love her Mansur, i just hate thia bad side of her. Da zata zauna a yanda na fara ganinta har na fada sonta we would be the happiest couples because we are madw for each other"

"Toh Romeo ai shikenan kana sonta tana sonka the soyayya will hold the bond karka damu she will change for better data shiga gidanka" Mansur ya fada kafin ya komawarsa kan gadon ya kwanta daidai nan aka buga qofar dakin Mansur din ya bada damar shigowa wata yar farar yarinya ta shiga da sallama ta gaishe su kafin ta ajiye Try din da aka doro kayan abinci akai tana cewa

"Gashi Mama tace a kawowa Yaya Khalil"
"Lallai Mama wato Khalil ta aikowa abinci bayan ni ina zaune nan ko abincin safe baa kawo mun ba" Mansur ya fada yana jan kwanukan gabansa, se yarinyar tayi yar dariya tace

"Lah Yaya ai bamu san kana nan bane ni ta tambaya ma nace baka dawo ba shi yasa amma bari na koma na qaro muku toh idan wannan baze isa ba" ta juya zata fita Khalil ya dakatar da ita dacewa

"Barshi duk cinsa wannanya ishe mu danni bada yawa zanci ba"
"Toh Yaya" ta fada kafin ta juya ta fita.

"A ina Mama ta samo yarinya" Khalil ya fada yana gutsirar Funkason da aka kawo musu.

"Yar gidan Kawu Sani ce na Jama'are, kasan Mamansu ta sake aure yayarta Muhsina ma anyi mata aure se ita kadai tana hannun Inna Sadiya to ruqon Tsofaffin nan babu wani da ze ringa sakawa yaro ido ba dadi shiyasa Mama ta dakkota tunda nan din ita kadai ce yanzu ta samu yar tayin zama" Mansur ya fada yana cin abincinsa. Se Khalil ya gyada kai yace

"Oh rayuwar fa kenan duk ka gama haqilonka ma akan macen ka mutu watanni kadan ta auri wani su cinye abinda ka tara tare, jifa gaba daya Kawu banjin ya shekara biyu da rasuwa duk Kururuwar nan data ringayi ranar jana'iza wai har ta sake wani auran".

"Hmmm ka bari kawai Abokina abin takaicin ma a cikin gidan fa take zaune anyi magana wai ai rabonta ana yayanta ne kuma ze ringa biyan haya shine saboda dan Akuya ne wai baze riqe mata Yarinyar nan guda daya ba ita kuma inaga Asirce ta yayi ko yaya ta tattarata ta mayarwa da Inna Sadiyan, toh muna dai zuba ido kowa dai yasan abinda yasa ya aureta kudin kuma na qarewa gayyar zata watse, yanzu ma shirin shiga Kotu suje da Kawu Labaran akan ta dawo da komai na yaran tunda tayi aure"

"Allah ya rufa Asiri" Khalil ya fada yana rufe baki wayarsa ta fara qara ganin besan number ba yasa ya shareta suka ci gaba da cin abincin suna yan hirarrakinsu.

Ganin ana ta kira anqi haqura ya saka Mansur cewa
"Ka daga mana ka sani ko cikin mutanen mu ne wani yake kira"
"Kyale su kawai ko waye ya yi text in na gane na kira ko kai ka daga kaji waye".

Jan wayar Mansur yayi yana dannawa kuwa sega Text ya shigo ya bude ya karanta yace wa Khalil
"Ka gani ba Aminiyar Amaryace, se taje ta gaya mata ka mata wulaqanci ka qara wani laifin tukunna"

Tsaki Khalil yayi yace
"Seka kira kaji me suke so, in kudi ne wallahi sisi bazan bayar ba dan na bata komai dama muna yar dadi ne sena qara mata amma yanzu kuwa tayiwa kanta"

"Allah ya taimaki Angon Umaimah" Mansur ya fada cikin shaqiyanci kafin ya danna kiran layin.
Kukan da Umaimah ta fasa tana daga wayar ya saka shi kallon Khalil kafin ya janye wayar daga kunnensa ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ua sakata a speaker ya ajiye a gaban Khalil.

Kuka take bilhaqqi harda sheshsheqa, Khalil ya daya tsame hannu daga cikin abincin ya dafe kansa saboda yanda yake jin sautin kukan nata, tabashi Mansur yayi yana masa alamar ya daga, ya cije baki kamar baya so ya dauki wayar ya cire ta daga speaker ya saka a kunne

"Wai bakya gajiya da kuka ne" ya fada murya a cukule, Umaimah taja doguwar sheshsheqa kamarme shirin shidewa tace

"Ba kaine kayi fushi dani ba, dan Allah kayi haquri bazan sake ba. Wallahi kasa controlling kaina nayi shiyasa amma na gane nayi kuskure bazan kuma maimaitawa ba" ta fada tana shirin cigaba da kukan.

"Kullum haka kike cewa ai amma idan kika tashi se kinyi abinda yafi na baya. Dambe fa kikayi niyyar yi a cikin mutane, kina zaton da kunyi da yanzu video ki be gama zagaye Social media ba yanda qiris mutane yanzu suke jira su fara recording abu wane irin kallo kike so mutane suyi mun ace matar da zan aura aka gani a titi tana dambe? Saboda kinga ina kyaleki ne yasa kike abinda kika ga dama ko? Shi kenan zan dauki mataki" Khalil ya fada a hankali amma a muryarsa zaka karanci bacin rai.

Marairaicewa tayi sosai tace "Ai bamuyi ba ma zan tabayi ba in sha Allah kayi haquri, na yarda in dai na sake yin wani abu irin wannan ka dauki kowanne mataki na yarda"

"Haka kikace ko? Kinsan irin matakin da zan dauka ne?"
"Koma wanne irine na tabbata ma bazan sake ba balle kayi wani abun" ta tareshi a shagwabe kafin ta sake cewa

"Ka haqura toh?"
"Da ban haqura ba bazan amsa wayar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login