Showing 216001 words to 219000 words out of 429394 words

Chapter 73 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

959

makaranta kafin itama ya sauketa gidan Maman Asad data haihu jiya da daddare se ya wuce gurin aiki. Ba yanda beyi da ita ba akan ta bari gari ya qara waye wa sannan ta tafi amma qarfe bakwai tajewa mutane gida kaman tashin hankali amma tayi biris, baya son jan magana ya sa ya rabu da ita, Bibi ko wanka batayi mata ba ta tasata a gaba bayan ta dibar mata kaya suka fice daga gidan, seda aka fara aje Mu'ayyad kafin ya dauki hanyar gidan Maman Asad din da su yanata Mita ita dai bata tanka shi ba kuma tunda ta niyyata se taje.

A waje ya tsaya, Bibi ta sauka da Jakar goyonta da aka zubo mata kaya Umaimah na mayar da takalmanta data cire saboda qafarta da ta dan tasa wayar Khalil dake tsakiyarsu ta shiga qara. 'Zahra S' ta gani, ta dago ta kalle shi yanda ya zabura ya dauke wayar ya qara qona mata rai me ze boye to bayan ta gani? A fusace ta bude murfin motar ta fice ko jakarta bata tsaya dauka ba ya bita a bayabda jakar wani yaro ya bawa yace ya kai mata kafin ya koma mota yana jin wayarsa daya saka a Aljihu nata faman qara.

Seda yaci rabin tafiya office kafin ya tsaya ya dauki wayar da kamar mayya har sannan bata gaji ta dena kira ba. A fusace yace
"Wai Zahra wace irin yarinya ce ke me nacin bala'i, da kika kira sau daya ban dauka ba base ki haqura ba ai kinsan idan na gani zan biyo ki ko? Wai ma akan me zaki kirana da safiyar nan bayan kinsan ta yuwu matata tana kusa dani?"

Daga can bangaren Zahra cikin ko in kula da banbamin da yakeyi tace
"Tun jiya kace zaka kirani har nayi bacci baka kiraba, da Asuba na kiraka wayarka a kashe ni kuma na kasa samun nutsuwa banji muryarka ba shi yasa nake ta kira"

"To ai seki zuba ruwa a qasa kisha hankalinki ya kwanta kin hadamun rigima a gida, ke bari kiji daga yau ma karki Sake kirana idan ni naga dama zan kiraki haba duk kibi ki addabi mutum ba dare babu rana ke ko dan jan ajin nan na mata ma baki dashi haba, nin yanzu na fita aiki, karki sake kirana ki bari idan na samu free time zan kiraki dan Allah" Khalil ya katseta yana gama fadar haka ya kashe wayar yana sauke numfashi, wannan kwarzaba ta Zahra ta ishe shi Allah ya kawo masa lokaci Contract din nan ta tabbata kowa ya kama gabansa dan wallahi babu yanda ze iya da wannan yarinya me shegen nacin jaraba sedai Dr Sabitu yayi haquri.

Motarsa ya tayar yaci gaba da tafiya, ba'a ko ci minti biyar tsakanin wayarsu da Zahra ba wani kiran ya shigo masa, gabansa ya fadi ganin Me kiran, Dr Sabitu Bashir seya gangara gefe ya kashe motar jikinsa har rawa yake ya daga wayar cikin ladabi yana cewa
"Barka da Asuba Dady"
"Riqe gaisuwarka Injiniya, wato har kayi kaurin wuyan da zaka saka mun yarinya kuka da safiyar nan ko? To bari kaji wallahi ko ka kira Zahra ka bata haquri ka lallabata ko yanzun nan kira saya zanyi a kwace kwangilar nan daga hannunka a bawa wasu. Kasan dai akwai wadanda suka fika cancanta na shiga na fita aka baka saboda to karka manta da yarjejeniyar da take tsakanin mu kuma duk wani shirme da zakayi ka tabbatar kana rage chances na tabbatuwar kwangikar ka ne, foolish boy kawai" Dr Sabitu ya fada cikin saurin bakin sa wanda a maganganun gaba daya kwangila da Zahra kaai Khalil ya iya tattarawa ya fahimci abinda yake nufi.

Wallahi bada ban wuyar daya sha gurin tsara paper work da sauran abubuwan da yayi akan aikin nan ba da saki zeyi ya haqura, ina dalili? Shin tun farko ma waya kaishi shiga wannan bala'in da yayi haquri idan rabonsa ce kwangikar nan yana kwance zata same shi. Gaba daya Anwar Saleh ne yaja masa, Abokinsa ne tare sukayi karatu kuma yanzu yana aiki a Companynsa shi ya fara kwadaita masa Zancen kwangilar wanda tunda ya gaya masa a lokacin yace baze iya shiga ba dan Kwangila ce ta dubunnan miliyoyin kudi yasan babu yanda za'ayi ma ayi considering qaramin company irin nasu. Anwar ne ya ringa pushing akan suje su nema ai abin na Allah ne baya ga haka ai shima yayi ayyuka da yawa manya a Company daya bari kuma mutane da yawa sun sanshi dan haka kar yaji komai suje suyi Addu'a qila sa'ar tasu ce haka ko akayi suka shirya takaddun tsare tsare da budget da komai Anwar yaje yayi submitting se gashi cikin ikon Allah an kirasu cikin Kamfani goma na sama da a ciki za'a zabi wanda zaayi awarding aikin.

Anwar be haqura ba seda ya binciko masu fada aji a Ministry da za'ayi aikin a ciki ya gano Dr Sabitu Bashir daya daga cikin Directors din gurin yace ya sanshi abokin Uncle dinsa ne ze roqi Uncle din ya hadasu dashi haka kuwa akayi cikin Sa'a se gashi sun samu appointment da Dr Sabitu ya basu lokaci yace suje gida su same shi.
Sun samu Dr Sabitu a gida ya tarbe su da fara'a saboda akwai kyakykywar alaqa tsakaninsa da Uncle din Anwar. Sun gabatar masa da abinda ya kaisu ya karbi Blueprint din da sukaje dashi ya duba kai tsaye babu kwana kwana ya gaya musu suyi haquri bazasu samu wannan kwangila ba dan akwai manya manyan kamfanunuwa da suka shafe su yamayi mamakin yanda akayi suka fito a Top Ten dan kamfanin nasu dako cikakkiyar shekara beyi da kafuwa ba amma hakan na nuni da idan an samu kwangila daidai dasu za'a neme su kenan haka suka tattara suka tafi gida jiki a sanyaye.

Sati daya tsakani Anwar ya same akan Dr Sabitu ya kira shi yace yana son ganinsu haka suka dunguma suka tafu bayan sunje suka same shi yasa aka kira masa yarsa suna zaune wata zuqeqiyar yarinya me kyan sura dukda ba fara bace tas ta shigo palour, jikin Dr ta tafi ta lafe kamar mage ba tareda ta ko kalli bangaren da suke zaune ba.
"Kalle su ki gani Daughter wanne ne a cikinsu?" Dr ya fada yana shafa kanta seta dago da sauri ta kalli inda baban nata yake nuna mata dan sam bata ma lura da mutane a gurin ba karaf idonta ya sauka cikin na Khalil, baki ta washe kamar wata wawuya ta nuna shi tana cewa
"Wannan ne Daddy".

Khalil da Anwar suka kalli juna cikin rashin fahimtar abinda yake faruwa. Dr dake dariya shima kamar yar tasa ya shafa kanta yana cewa
"Oh My daughter Allah ya shiryaki, to tashi ki koma ciki kinji" seta noqe kafada kamar wata yarinya Dr ko ya sake washe baki yana cewa
"Idan mun gama zan saka a kiraki kinji maza kije kiyi wanka kiyi kwalliya kafin nan" se a sannan ta miqe ta fice fuskarta kamar gonar Auduga tana aikawa da Khalil wani kallo da ya kasa tantance na menene.

"Zahra baby kenan, tun ranar da kuka zo gidannan yarinyar nan ta shiga wani hali bata da aiki se kuka da damuwa qarshe ko abinci se munyi dagaske take iya ci kuma taqi fada mana damuwarta sam se jiya dana matsa mata sannan take sanar mun da a cikin baqin da suka zo gidannan ne ta kamu da son wani, bayan ta fada mun ranar ne nayi tunanin wadanda na gana dasu ya zama ku biyu nan ne ze Aminina Alhaji Zakari dalilin daya saka na kirawo ku kenan dan ta tantance wannan ne ne a cikinku kuma kunji, kai Khalil kaine kayi mun fashin zuciyar yarinya daga zuwa neman kwangila" ya qarasa cikin barkwanci.

Kallon Anwar Khalil yayi lokaci daya yaji ransa ya baci, daya ce Dr Sabitu na neman su ya dauka wata kwangilar ce ta samu a she wani zancen shashanci ne kawai ya saka ya kirasu, to shi yayi me da wannan sangartacciyar yarinyar da kana ganinta kasan bata qoshi da tarbiyya ba? Taba shi Anwar yayi ganin yayi nisa a tunani dan sam be ma san Dr na magana ba
"Yanzu dai kunji dalilin kiran, zaku iya tafiya idan yaso ka jirata a waje tazo ku gaisa daga nan se ku musayar lamba ko amma kafin nan zan ja maka kunne, kaga Zahra ita kadaice yata mace.

Ina bala'in sonta yanda baka tsammani kuma zan iyayin komai akanta dan haka ka lallabamun ita dan badan ita tace tana sonka bama kai baka kai ajin da zan baka auran Zahra ba".

Wani kallo Khalil ya ringa bin Dr dashi har ya disa wa maganar sa aya, ransa ya kai qololuwar baci, ya hasaso yar tasa da yake magana a idonsa bata kai macen da ze kalla ba balle har azo ana gaya masa maganganu irin haka akanta, seya miqe tsaye yana kallon Dr yace
"Ai ranka ya dade ina ganin a cigaba da duba mata daidai da ita Wanda zasu dace danni already I'm happily married with the love of my life, qila ko sedai Anwar shine single idan sun daidaita shikenan" yana gama fadar haka ya juya ya fice dan rainin wayon mutumin ya ishe shi. A Compound din gidan suka ci karo ta fito daga wani part taci uban gayu da wani shegen Lace dinkin fitted gown ganinsa yasa ta nufe shi tana karairaya haushi ya qara kamashi wai wannan abun ake cewa bekai matsayin da ze aureta 'Mtsw' yaja tsaki ya fice daga gidan yana ji tana tsayar dashi.

Besan yanda suka qare da Anwar ba dan be jirashi ba ya tafi, kwana biyu a tsakani ya sake samunsa akan Dr na neman sa urgently ya rantse ba zashi ba Anwar da baqin naci seda ya shawo kansa sukaje can suka tarar da Dr Sabitu da Zahra tsakanin su kasa gane Wanda yafi wani fita hayyacinsa sukayi abinma ya basu dariya ya basu takaici. Wai ashe bayan ya fita binsa tayi da gudu tana ganin ya wuce da mota ta zauna nan bakin get ta ringa birgima tana ihu dakyar aka shiga da ita gida tsabar kuka tana a kira mata Khalil seda aka nemo likita yayi mata allurar bacci. Mamanta daman bata shiga sabgar iskancinta shiyasa koda taga ta fara tayi hayewarta sama ta barta da Uban, hankalin Dr ya tashi abu dai ba kan gado haka ta ringayinsa har tana zata kashe kanta idan be aura mata Khalil ba dalilin daya saka ya sake kiran Anwar kenan dukda haushin abinda Khalil din yayi masa ya fita suna magana amma farin cikin yarsa yafiye masa komai.

Babu wani kwana kwana Khalil ya sake jaddada masa shi yana da matarsa ba kuma ya buqatar wani qarin aure a yanzu, Zahra ta fasa ihun da kusa toshe musu dodon kunne Dr ya qara gigicewa kamar zeyi kukan shima ya shiga roqon Khalil akan ya amshi tayin Zahran amma ya sunkuyar da kai yaqi ce masa komai

"Ka auri yata, ni kuma nayi maka alqawarin zan shige maka gaba ku samu wannan kwangilar" Dr Sabitu ya fada ganin bashi da wata sauran mafita dan roqo ba kalar wanda beyiwa Khalil ba amma yayi biris. Kallon kallo Khalil da Anwar sukayi, A zuciyar Khalil ya raya wasa kawai zeyi da hankalinsa bayan shi da kansa yace bazasu samu ba dan akwai sharadan da basu cika ba sannan yanzu saboda yana so ya yaudare shi zece zasu samu.

"Ranka ya dade kamar yanda na gaya maka ne ina da mata kuma ina sonta dan haka koda kwangila ko babu bazan yi mata kishiya ba, kayi qoqari ka fahimtar da yarka tayi haquri kawai" Khalil ya fada. Dr Sabitu yace

"I'm serious Khalil, nasan dai duk son da kake yiwa matarka ba zaka qi damar mallakar wannan kwangilar ba saboda ita, dan haka na baka kwana biyu kaje kayi tunani dan muna kan tattara alqaluma ne domin fitar da wanda za'a bawa, idan har ka amince da buqata ta to ni kuma zan cika alqawarin da nayi maka" akan haka suka rabu tun a hanyar su ta komawa Anwar yake ce masa

"Khalil tunanin me zakayi? This is what you have been dreaming for ka kuma samu dama a sama ka na neman kayi wasa da ita? Please mu koma just tell him ka amince, gafa kwangila ga bonus na mata me kuma kake nema?"

"Anwar bazaka gane ba. Yes maganar gaskiya zanso ace mu samu abun nan amma sharudan ciki kuma fa akan me zece sedai na auri yarsa kai baka ga yarinyar ba tayi maka kalar matar da ni zamu zauna lafiya da ita? Beside i love my wife ka sani, and bringing any issue like adding another wife is like sending an invitation for word war 3, baka san Umaimah bako? To kai kanka idan ta samu labarin da kai aka hada wallahi ba zaka zauna lafiya ba. I know my wife's capabilities, yar bala'i ce ta kaiwa BBC dan haka na haqura Allah ya bani rabo na a gaba".

Anwar be haqura ba, mutum ne me dan banzan naci tsiya ga iya tsara mutum, haka ya ringayi har seda ya samu ya rinjayi ra'ayin Khalil din.
"Ni bance ka aureta dole ba, amma zamu iya using opportunity din muma muyi wasa da hankalinsa, da zarar buqata ta biya se musan ta yanda zamu zame ai dai baze iya kwacewa ba bayan an rigada an bamu mun fara aikin ko?" Anwar ya fada cikin rarrashi, da haka ya samu ya shawo kan Khalil din dan gaskiya baze bari suyi asarar aikin nan ba dan ba qaramin kaya zasu ja, shi me yasa ma batace shi take so ba, duda shidin ma.tarbiyyarta batayi masa ba amma da ze iya maneji da ita, shiyasa yake ganin baiken Khalil din ba seya aureta ba taje ta qaraci shirmenta tunda shi yanada wata matar a gefe.

Dukda tsoron abinda ze iya biyo baya Haka Khalil ya koma ya sanarwa Dr cewar ya amince da sharadinsa, sedai shima da nasa. Dole yana buqatar lokaci su fahimci juna da Zahran har zuwa bayan tabbatauwar kwangilar danshi a halin yanzu ma bashi da kudin da zeyi aure dan haka a qalla yana buqatar shekara Daya ya gama duk shirinsa ya kuma lallaba matarsa ta gida kafin sannan kuma sun samu fahimtar juna da Zahran itama ya gayawa Dr.

Dukda maganar ta zowa Dr Sabitu kamar wani rainin wayo ma amma se yayi murmushi yace masa babu komai, idan shi yaro ne me wayo shi kuma ze nuna masa tun kafin a haifeshi yasan takan duniya dan haka babu yanda za'ayi ya yaudareshi, kuma kamar yanda yayi alqawari ya cika, ya shiga ya fita ya samo musu kwangilar dukda tarin qalubale daya fuskanta amma akan farin cikin Zahra ze iyayin komai.

A bangaren Khalil kuwa ba qaramin qoqari yakeyi gurin tolerating Zahran ba, sangartacciyar yarinya ce ta ajin qarshe da sam bata san daidai ba haka take rayuwa sakaka babu kwaba babu gyara gata da nacin tsiya, son sa take kamar tayi me sam bata da aji idanta ganshi jikinta har rawa yakeyi waya kuwa idan ta dosa kiransa se duk abibda yakeyi seya bari ya daga sannan yake samun lafiya a cikin haka yake matuqar taka tsan tsan dan kar Umaimah ta fahimci halin da ake ciki shiyasa a kullum daya fito daga office zeyi blocking number Zahran ya kuma goge duk ubannin messages din sa take cika masa waya dasu kamar zararriya.

Ranar data dauki wayarsa ya tabbatar bataga komai ba dan da babu yanda za'ayi tayi saurin sakkowa har ta bashi haquri yanzun kuwa ya tabbatar wannan kiran ya gayyato masa yaqi. Tsoronsa Allah yanzu tsoron Umaimah tayi wani sakarci da ze janyo masa matsala dan ya rigada ya gama paper work dinsa tsaf a satin nan ze kammala yayi submitting daga saka hannun Dr Sabitu kawai yake buqata a sakar masa kudin aikin, dukda yayi mamakin yanda akayi ya zama Signatory din amma yasan duk cikin shirin daurin talalar da yake masa ne na ya auri yarsa, shi kuwa ya qudurce dayaji Dirim kudin aiki sun sauka magana ta qare zeyi ta kansa ne dan be gama da ta gidan ba ballantana ya dakko wadda tafita cin kai ya hadasu.
[8/13, 7:46 AM] Maman Aslam: *KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login