Showing 351001 words to 354000 words out of 429394 words

Chapter 118 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1601

da fuskarta tayi mata kamar ta santa a wani guri amma ta manta ina ne dan haka ta juya ta fice karbo katin.

Wata mota ta gani me kyan gaske a qofar gidan, ta matsa jikinta tana kallonta seta bude hanci saboda qamshin da taji yana fitowa daga ciki amkar na Khalil, tsaki tayi ta matsa a ranta tana cewa
"Hasashe ne kawai me ze kawo Khalil nan kuma idan yazo ai ita ze nema" ta qarasa Shagon Ilu dake jikin gidan da yake kallon nasu ta karbi katin, fasa komawa gida tayi ta shige gidan Maman Nana. Babu inda take zuwa kullum tana gida idanta samuta fito siyan kati nema take leqawa gidan Maman Nana dukda babu wanda yace karta fita koda yake wa yake ta sabgarta ma balle ya sakata ko ya hanata? A canta shantake suka shiga hirar duniya, ganin biyar tayi yasa ta miqr tana mata sallama dan tasan Abbana dab da dawowa gida yanzu tana fitowa daga gidan Maman Nanan idonta yayi kyakykyawan gani. Khalil ta gani wanda badan sanin da tayi masa ha zata iya cewa me kama dashi ne saboda yanda ya canza yayi qiba, yana tsaye ya budewa yarinyar data gani tareda Anty yanzu qofar mota ta shiga ya ranqwafa ciki yana mata magana tana iya hango tsadaddan murmushin da yake kan fuskarsa.

KHALIL
Bayan fitar su Anty a hankali Mama ta bude baki tana kallonsa tace
"Khalil ina qara baka haquri akan abunda ya faru.."
"Haba Mama ni ya kamata na baku haquri na kuma nemi yafiyarku bisa cin fuskar danayi muku na saki yarku a gabanku amma Allah ya sani ba'a son raina ba amma haka Allah ya tsara, ina fatan hakan ya zame mana Alkhairi a rayuwar mu gaba daya" Khalil yayi saurin Katse Maman, kasa sake ce masa komai tayi a ranta tana sake takaicin rasa Miji Kamar Khalil da Umaimah tayi amma tana nan ko a jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta suna gaya mata qaryar ze dawo gareta wanda a yanzu ko Makaho ya shafashi yasan ya samu canjin rayuwa ya samu nutsuwa babu yanda za'ayi yana sane ya sake maida kansa cikin ramin daya fito dakyar.

Zaman shirun suka ci gaba dayi, shigowar Sharifa da sauran yaran ya katse musu shirun ta miqa Masa Iman dake ta yiwa yan uwanta dariya tamkar ta sansu. Fuskarta data sha kitso ya tsurawa ido yana sake ganin ainihin kamanninta da Umaimah tamkar an tsaga kara, besan irin kallon da yake mata ba seda yaji Mama tana cewa
"Kana mamakin kamanninta da Umaimah ko? Kowa ya ganta se yace kamar har tayi yawa" tana gama fada ta miqe tana sake cewa
"Bari nayiwa Saratu magana tasa a fitar da kayan nata ko zaku jira Abban naku ya dawo kafin ku wuce?"

Kansa ya shafa yace
"Zan samu lokaci in sha Allah na dawo na gaishe shi"
"Shikenan to bari nayi mata magana" ta fada ta fice ta barshi da Iman dan sauran yaran suna rakota daman suka juya sabgarsu. Rungume yarinyar yayi a jikinsa yana jin wani yanayi na taso masa. Salman ne ya shiga da Sallama, ya bashi hannu suka gaisa yana tambayarsa karatu da suke gangara dan Jarabawar qarshe sukeyi. Muqullin motar sa ya bashi saboda yace za'a saka kayan Iman ya gaya masa ya fito da kayan Booth din ya shigo dasu sey miqe da yarinyar a Jikinsa ya fito tsakar gidan, yana tsaye yaran suka fita da Akwatunan Iman harda Mota da Kekenta da sauran tarkacen kayan wasan da yake siya ana kawo mata seda suka gama saka kayan tsaf kafin Salmanya dawo masa da Key din, shiya shiga dakin Anty ya kira Humaira suka fito tareda Anty da seda ta sakata ta sake dan dole sukayi hira. Dakin Mama ta koma tayi mata sallama ta bata Leda Babba tana cewa
"Gashi babu yawa bamu samu munzo barka ba Allah ya raya yayi Albarka sannan ina fatan zaki qara haquri akan wanda kikeyi sabgar yara se an kai zuciya nesa musamman yanzu kin samu qarin wata Allah ya taya miki ya baki lada"

"Amin Mama babu komai in sha Allahu Da ai na kowa ne in sha Allah zanyi iyakar iya wata kuma ina fatan idan da rabon daidaito Allah ya shiga tsakani Mamansu ta dawo muci gaba da zaman mu" Humairan ta fada se Maman ta kasa amsa mata haka ta rakota har inda Khalil din yake jiranta da sauran yaran.
50k ya bawa Mama da Antyn yabi sauran yaran gida da 2k kowanne suka ringa saka masa Albarka suna tsaye tsakar gidan Anty na sake jaddadamasa zancen kawo yaran har ya hada kan iyalansa suka fice sauran yaran suka rakasu. A baya Mu'ayyad da Bibi suka zauna kafin ya zaunar da Iman itama dan se hanqoron shiga takeyi ganin su a ciki kamar ta sansu, da kansa ya budewa Humaira qofar gaba ta shiga ta zauna sannan ya karbi Aryaan daga hannun Salman suka sakeyin Musabaha ya miqa mata shi sannan ya sunkuya yana gyara mata mayafinta daya fito waje yana tsokanarta da cewa
"Qannenki sun qara yawa daga hudu kun zama ku biyar" ita kuma ta mayar masa da cewa
"Eh naji dai qannen nawa ne kai kuma Babanmu" ya saki murmushi saboda yanda tayi maganar, seda ya kulle mata qofar kafin ya juya zuwa bangarensa kamar ance ya kalli gefe karaf idonsa suka shiga cikin na Umaimah data qame a bakin qofar wani gida tana zare ido kamar wadda ta taka jelar Maciji.

Kallonta yayi na second biyu kafin ya dauke idonsa ya shiga motar zuciyarsa na bugawa, Tabbas So ba qarya ba, seda ya kwashi minti biyu yana qoqarin daidaita nutsuwarsa kafin ya iya kunna motar shima dalilin tambayarsa da Humaira takeyi lafiya taga yanayinsa ya canza lokaci daya seya dafa kansa ya kalleta yana yamutsa fuska yace
"Kaina ne ya sara"
"Sannu kona karbi Driving din?" Ta fada cikin nuna damuwa seya taka motar yana cewa
"Dadai ni dake ne kadai amma yanzu na debo gaba dayan Ahalina kice zaki jamu a Babban Titi Nooo" yayi maganar cikin zolaya seta zumburi baki tana cewa
"Allah yasa wata rana ka sake cewa ka gaji bazan kuma tuqaka ba" shidai yaci gaba da tuqinsa amma hoton ganin da yayiwa Umaimah ya gaza barin kwakwalwarsa.

Kenan bata damu da rabuwarsu ba dan babu alamar hakan a tattare da ita gani yayi ta qara kyau tayi qiba dukda Hijabi ne a jikinta ya tantance hakan koda yake me yasa zeyi tunanin zata damu dan ta rabu dashi ita da taso ta rabashi da duniyar ma gaba daya? Haka suka qarasa gida yayi qoqarin ganin ya kawar da komai daga ransa gudun kar wani ya zargi wani Abu, Humaira kuwa kallonsa kawai takeyi dan taga fitowar Umaiman kuma taga sanda Khalil din ya tsaya yana kallonta dan haka tasan damuwar daya shiga nada nasaba da ganin ta da yayi kuma bata ga laifinsa ha Matarsa ce da suka rayu tsahon shekara bakwai kuma yana sonta Qaddara ta rabasu dole zeji wani abu idan ya sake ganinta.
Da suka isa gida ma ganin yana buqatar fili yasa ta barshi ta shiga hidimar yaranta a Daren ta ware kayan Iman din tsaf ta shirya mata su a dakinsu na nan bangaren ta ware wasu ta kaiwa Hajiya aka saka mata a dakinsu na can tunda suma sauran haka kayansu suke, Ruqayya ta dawo dan haka bata samu wani qalubale ba ita take taimaka mata da hidimar Iman din ta bata abinci tayi mata wanka da shirin bacci ta goyata babu bata lokaci kuwa tayi bacci abinta daman Anty ta gaya mata bata farkawar dare indai taci ta qoshi haka kuwa sukayi baccinsu lafiya lau dan a dakinta ta kwana da ita da Aryaan ganin Khalil ya dage akan kan sa na ciwo yasa ta tafi dakinsa ta barshi yayi jinyar famin ciwon da ganin Umaimah yayi masa, washe gari kuwa da kansa ya bita ya lallabata bata ja magana ba dan daman ba fushi tayi ba suka ci gaba da rayuwarsu, Duk yanda ta tsara zata kula da yaran data haifa a cikinta haka take tafiyar da yaran a kullum kuma tana addu'ar ubangiji ya taya mata ya bata ikon kulawa dasu tsakani da Allah ba tareda ta cutar dasu cikin sani ko akasin haka ba.

UMAIMAH

Seda motar Khalil ta qurewa ganinta kafin ta farka daga suman tsayen da tayi, dakyar take jan numfashi saboda yanda zuciyarta tayi mata nauyi a hankali ta ringa tafiya tana dafa bango gudun karta fadi dan bata gani da kyau harta shiga gida, Mama da Anty na zaune tsakar gidan suna bude ledojin tsarabar da Khalil ya kai musu ta shigo Anty ta miqe ganin tana shirin fadowa kansu ta tareta tana tambayar lafiya? Cikin muryarta data shaqe saboda abinda take ji tace mata
"Khalil na gani shida wata mata ya bude mata mota har ya sun kunya yana mata dariya"
"Eh Matarsa ce daga nan suka fita ai yazo ya dauki yarsa" Mama ta fada cikin yanayin ko a jikinta se Umaimah ta bita da kallo kamar bata gane meta fada ba aranta tana maimaita kalmar Mataraa data fada, kenan tana Nufin Humaira ce wannan data gansu tare? Kuma ai itace ta gani da Anty se yanzu ta fahimci kallon sanin da tayi mata ashe ita ce.

Wasu hawaye masu tsananin zafi suka shiga tsere a fuskarta se kawai ta juya ta shige daki Anty ta saki baki ta bita da kallo tana cewa
"Toh kukan me takeyi kuma?"
"Na jin dadi mana" Mama ta bata amsa tana miqewa ta shige dakinta.

Umaimah kuwa zama tayi kan Gadon dakin tana hawayen da bata san dalilin yinsu ba. Wani radadi zuciyarta take mata kamar ana gasata idonta ya kasa dena ganin Khalil yanayiwa Humaira tsadadden murmushin da ita kadai take samunsa yanda yake kallonta kadai ya isa ya tabbatar maka da cewar soyayyarta ta huda Qashi da tsokarsa babu wata alama a tattare dashi da take nuna damuwa ko wani abu kenan ya manta da ita sannan yana nufin yayanta ma ya rabata dasu kenan duka ya mallakawa Matarsa ya dena sonta ya haqura da ita zeci gaba da rayuwa batareda ba? Tambayoyi ta jefawa kanta da bata da amsarsu haka bata da me bata amsar a kusa da ita

A sannu a hankali kwakwalwarta ta fara yarda da tabbacin cewar Khalil yana raye tareda wata Mace bayan ita ta kuma gasgata cewar a yanzun babu igiyar aure a tsakaninsu mafi munin abun ta haihu iddarta ta kammala tuntuni koda ace zasu sake komawa qarqashin inuwar aure dashi se bayan an sake daura musu aure wanda bata zaton iyayenta da a yanzu basu da abinda suka tsana sama da ita zasu yarda da hakan balle aje ga nasa yan uwan da bata matsayinta a gurinsu ba. Dagaske ta rasa Khalil ya zama mallakin wata daban ba ita ba. Zamewa tayi ta kwanta akan Gadon saboda ji da tayi dakin yana juya mata gaba daya a maimakon ta nemi taimakon Allah ya sauqaqa mata abinda take ji a ruhi da gangar jikinta se kawai ta bude baki ta ringa zunduma ihu tamkar ba diyar musulmi ba babu kiran Allah se maimaita Kalmar ta shiga uku ta lalace takeyi.

Anty dake tsakar gida tana cigada ayyukanta dan ita ce da girki tana shirin dora abincin dare ta zabura tayi dakin dan ganin abinda ya saka Umaiman irin wannan ihun. Abba ya shigo gidan da Sallama dawowarsa kenan daga Kasuwa yaci burki a bakin qofa yana jiyo ihun Umaiman da muryar Anty dake qoqarin kwantar mata da hankali da nuna mata cewar Addu'a ya kamata ta ringayi ba iface iface ba.

Zuciyarsa tayi baqi ta kawo masa wuya, tun bayan Dawowarta gida be yarda sun hadu ido da ido ba saboda gujewa baqin cikin da yake tsintar kansa a ciki duk sanda ya tunata balle ace ya ganta a cikin gidansa. Tun sanda ya fahimci Anty da Maman ne suke hidimar Malika ransa ya qara baci wato Umaimah bataji maganarsa ba amma ya qyaleta kawai domin lokaci yake jira da duniya da kanta zatayi mata karatun da tilas ta fahimceshi yayi niyyar ya zuba mata ido ne yaga iyakar Hankalinta amma Ihun da take masa yanzu a cikin gida ya bata masa rai matuqa ya tunzura zuciyarsa, kasa dauke kai yayi dole ya koma waje, wani saurayi dan maqotansu ya kira yasa ya tsinko masa Bishiyar Dogon Yaro dake qofar gidan ya zuge masa guda uku Saurayin yanata mamakin abinda Abban zeyi dasu ya diba ya koma cikin gidan har sannan Umaimah bata bar ihun da takeyi ba a??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????bin baqin ciki daya shiga dakin a qasa ya tarar da ita tana birgima da ihu kamar wadda ta gamu da ciwon hauka, ba tareda bata lokaci ba ya shiga dukanta tamkar an aikoshi Anty batayi gigin shiga tsakani ba tayi gefe da sauri gudun kar ya hada da ita dan irin bacin ran data gani a idonsa tasan ya kai maqura yau kam. Jikinta ya dauki rawa saboda ganin irin dukan da yakeyiwa Umaiman da gushewar tunanin dan lokaci ta sameta saboda yanda dukan ya zo mata a bazata ta dena birgimar ta tsaya kawai kwakwalwarta na qoqarin gane abinda yake faruwa.

Wani gigitaccen ihu na gaske ta fasa sanda zafin dukan ya ratsa kwakwalwarta ta shiga neman ceto Abban kuwa be bata dama ba, a kwana ya sakata ya ringayi dukanta iya qarfinsa tamkar ya samu Jaka, tun tana ihu da guje gujen neman taimako harta haqura ta zauna guri daya ya ringa lafta mata bulalu seda duka ukun suka karye a jikinta kafin ya jefar da sauran yana haki ya kalli Anty da ta gama tsurewa a gefe ta gagara ko motsawa agurin da take saboda firgici yace
"Ki kawo mun ruwan zafi" ya fice fuu har yana shirin hardewa da babbar rigarsa.

Duk budurin da akayi Mama na zaune a falonta ko gezau batayi, ba qaramin dadin abinda Abban yayi taji ba dan ita kanta ta kusa tashi taje ta kwada mata mari seya fansheta yayiwa Umaiman dukan cire raini. Tana ganin wuce warsa ta tashi tabi bayansa da ruwa me sanyin gaske harda Zobo ta dora a Try ta kai masa dan tasan yanada buqatar abinda ze sanyaya masa zuciya yanzu.
Da kanta ta tsiyaya masa bayan tayi masa sannu da zuwa, be iya amsawa da baki ba se hannu ya daga mata ta miqa masa Cup cike da ruwa tana cewa
"Karbi kasha Alhaji akan me zaka bata ranka a banza akan wadda bata san ciwon kanta ba, Umaimah cefa haukarta ce ta tashi saboda Khalil yazo tareda matarsa ta ganshi cikin nutsuwarsa ba kamar yanda tayi fatan jefa rayuwarsa a cikin garari ba, ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba tasa ko dumi ba zatayi ba".

Tasya shanye ruwanta sake qara masa yasha sannanya shiga sauke ajiyar zuciya a jere a jere tsahon lokaci kafinya bude baki yace
"Ina tsoron fushin zuciya ya saka na furtawa Yarinyar nan kalmar da ba zata zama Alkhairi a gareta ba". Cikin kulawa Maman tace
"Ka ci gaba da haquri Alhaji, shiyasa kaga nake nesanta kaina daga duk shirginta, banga abinda takeyi ballantana raina ya baci a banza tunda ita bata san daidai, kullum addu'ata Allah ya duba mata yasa ta gane abinda takeyi ba daidai bane tun tana da sauran damar gyarawa".

Jigum sukayi suna zaune aka kawo Nepa cikin dashewar murya yace ta kunna masa heater bandaki, ta shiga ta kunna tana fitowa Anty ta shigo da qaton Flask din ruwan zafi da ka ganta kasan a rikice take. Ita ta shiga ta hada masa ruwan kafin ta fito Maman ta koma dakinta Abba ya shiga wanka ita kuma ta koma kan aikinta tanayi har sannan zuciyarta bata bar tsinkewa ba. Ita dai wannan jaraba ta Umaimah daga tayi sauqi se wata ta bullo tana Addu'a Allah ya fito mata da Miji nan kusa ta daga su samu sa'ida dan idan taci gaba da zama itama seta dora mata hawan Jinin data sakawa uwarta da ubanta sunyi Anko, ina dalili wai gashi ita kamar Afi bata iya dauke kai taga abu ya samu Umaimar, sonta takeyi tsakani da Allah gashi babu abinda son yake tsinana mata se wahala.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 77


UMAIMAH

Daren Ranar bata iya bacci ba seda Anty ta kira wani me Chemist ya dubata yayi mata allurar rage zugi tasha magani sannan, washe gari da safe ta tashi da wani sabon tashin hankalin. Qarfe goma gaba daya yan gidan manya da yara suka hallara bisa umarnin kiran da Abban yayi musu tun daren jiya. Bata san kiran me ya musu ba tadai ga sun shige can bangarensa kuma sun dade suna magana dan har se gurin sha biyu sannan Salman yazo yayi kiranta.

Dakyar take tafiya saboda yanda jikinta yayi tsami, badan kar ta sake yin wani laifin ba daman da bazataje kiran ba. Irin yanda gaba daya suka dauke kai tamkar babu wanda yasan da tsiron halittarta a gurin ya mata ciwo daman tunda ta dawo gidan in ka cire Anty babu me shiga sabgarta Mama kuwa in zasu hadu sau dubu ta gaidata bazata amsa ba daman tun randa tadawo tayi mata iyaka da shiga dakinta tace bata buqatar ganinta a ciki. Tana zama kamar wata Mujiya a cikinsu suka fara darewa daya da daya duk suka fice daga dakin kowanne yazo giftata seya bugamata tsaki sannan su harareta, seda suka fice gaba daya kafin Mama ta kalleta rai babu dadi tace
"Matso ciki".
Gaba kadan ta muskuta amma bata yarda tayi kusa dasu da yawa ba cikin rawar Murya ta shiga gaishe su ta kalli Abba dake Kishingide da gani bashida lafiya, babu wanda ya amsa gaisuwar Tata har Antyn yau tana daga gefe idonta yayi jajir alamar Kuka tayi se Umaimah ta sunkuyar da kanta qasa, muryar Abban taji cikin dakiya yana cewa

"Ina so ku zama shaida tsakanina da Umaimah zan kafa mata sharudda da har idan tana neman zaman lafiya a cikin gidan nan dole ta bisu. Ban yarda Umaimah ta taka ko nan da qofar gida ba tareda izinina ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login