Showing 342001 words to 345000 words out of 429394 words

Chapter 115 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1056

daki ta kwanta nan ta tashi can tunda hidimar yar ma Anty ce take yi mata ita dai a zuciyarta tana yi mata fatan shiriya idan tana da rabo dan babi wanda ze so yaga nasa ya halaka rana gobe qiyama. Haka rayuwa taci gaba da gungurawa sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da shudewa Umaimah na nan zaune gidansu ita da me zaman kanta marabarsu qalilan ce domin kuwa babu me sakata haka babu me hanata domin kwata kwata idan ka cire Anty a gidan ma babu me shiga shirginta se Yasir da lokaci lokaci takan aikeshi ya siyo mata kayan kwadayi duk ranar da aka girka abinda beyi mata ba tunda tana da uwar kudinta gashi duk watan duniya bayan kayan abinci Khalil din zo doro mata dubu Ashirin yasa take sharafinta son ranta kuka babu wanda ya daga kai ya kalleta kamar yanda Abba yace Duniya tafi bagaruwa iya jima tayi yanda take so ba ranar kuka tana gaba.

Tunda tayi tayi ta samu Khalil a waya abin ya faskara ta haqura ta watsar dashi, abu daya ta ajiye a ranta ze dawo gareta dan baze iya rayuwa babu ita ba. Maganar Humaira ko a ranta ma gani takeyi basa tare domin ta tabbatar ba zata zauna da Khalil din da lalurar data sameshi ba ko bata nemi rabuwa dashi ba yan uwanta ba zasu barta taci gaba da zaman ba shiyasa ta kwantar da hankalinta sosai kamar babu wani abu tana jiran lokaci kawai da Khalil din ze kawo kansa a sannan zatayi masa wankin babban bargo ta qarasa tashin hankalin da batayi a baya ba.

KHALIL

Sannu a hankali rayuwarsa ta daidaita bashida wata matsala da ze iya cewa gata idan bata lalular data sameshi ba. A bangaren zamansu da Humaira kuwa babu abinda ze ce sedai ya godewa Allah kamar yanda a koda yaushe bakinsa baya gajiyawa gurin godewa ni'imar da yayi masa. A cikin watanni shida da auransu ya samu nutsuwar da besan da ita ba a tsayin shekaru Bakwai daya shafe da Umaimah. A yanzu ne ya san yayi aure ya kuma san dadin aure, irin kulawar da Humairan tak bashi tana saka ya manta da duk wata damuwar duniya idan yana tareda ita baya tuna komai da kowa se ita dashi ta shayar dashi zallar madarar soyayyar da ya dade yana mafarkin samu shi yasa be tauye kansa ba ya ware ya ajiye komai ya rungumi Matarsa suke zuba qauna domin tayi masa halacci ita da iyayenta da har ya koma ga Allah baze biyasu ba.

Tun bayan fitowarsa daga Asibiti ya fito da qudurin cewar zamansa da ita bame yuwuwa bane domin ko a shari'an ce akwai cutarwa tunda har yasan bashida lafiyar da zero ci gaba da biya mata buqatarta dole ya sallamata ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ze rungumi qaddara ya cigaba da rayuwarsa harzuwa iyakar abinda Allah ya hukunta masa. Bayan komawarsa gida irin yanda take kula dashi take ririta shi ya karyar masa da zuciya, idan ya kalleta tausayin ta yakan narkar dashi ko kadan bata taba nuna alamar gajiyawa ko wata damuwa da abinda ya sameshi ba. A duk sanda taga yayi shiru ko yana tunani se tayi duk iya qoqarinta na ganin ta kore masa damuwa tareda qarfafa masa guiwa. Watansa biyu cikin wannan yanayin ya warke garas a zahiri tunda dama ba lalura bace da za'a gani a jikinsa har ya ci gaba da fita ayyukansa amma a cikin zuciyarsa rauninda Umaiman ta rigada tayi masa ya gaza warkewa. Duk sanda ya kalli dakinta se yaji wani abu ya dake shi ya kan zargeta da son rai da ace tayi haquri ta fawwalawa Allah lamuranta da yanzu suna zaune tare yaransu kullum cikin tambayarsa ina Momy take suke tun yana samun abin da ze gaya musu har suka haqura suka dena tambayarsa musamman saboda yanda Humairan take iya qoqarinta akan su, jansu takeyi kamar qannenta har wasan goyo da guje guje sukeyi abinda yake dauke musu kewa kenan har suka fara dena damuwa da neman uwarsu se lokaci lokaci.

Dukda irin kwanciyar hankali fa nutsuwar da yake samu tattareda ita zuciyarsa taqi nutsuwa akan yaci gaba da zama da ita a yanda yake, baya so Allah ya kama shi da haqqinta Humaira yarinya ce qarama da bata gama sanin menene auren bama tukunna. A yanzu yasanbe zama lallai ta damuda halinda yake ciki ba amma ana tafe dole za'a kai lokacin da zata fara buqatuwa da Namiji shi kuma bashi da lafiyar da ze biya mata wannan buqatar daga nan fitina zata iya bullowa wadda baya fata, domin gujewa hakan tilas ya samar musu maslaha ta hanyar rabuwa da ita koda ace hakan zeyi sanadiyyar da shi ze qare rayuwarsa cikin qunci kamar yanda Umaiman take fata.
Yanke shawara yayi akan fara samun Hajiya da maganar kafin ya aiwatar dan haka ranar bayan ya dawo daga aiki kai tsaye ya wuce gurin Hajiyar.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 75

A falo ya tarar da Humairan da Habiba suna hira, yabita da wani malalacin kallo saboda yanda kwalliyarta ta dauke masa hankali yaji gaba daya ya rasa kwarin guiwar daya shigo da ita. Seda ta waiwaya ta kalli Bene kafin ta taso da sauri ta rungumeshi ya dagata sama dan tsahonta be kai kafadarsa ba yayi pecking lips dinta da suka sha Red lipstick kafin ya ajiyeta ya kalli inda Habiba take ya ga ta bar gurin kawai ya saki murmushi. Wannan yar babyn tana sakashi yin abin kunya a gaban Qannensa ta kama hannunsa tana murmushi tace
"Yau ka dawo da wuri, yanzu nan fa na shigo nace na rage lokaci kafin lokacin dawowarka yayi ka shiga can bana nan shiyasa ka taho nan?"

Hancinta ya dan ja yana qare mata kallo ta qara qiba da haske tayi kyau sosai ya zauna akan kujera ta zauna a gefensa yana ce mata
"Missing dinki nake tayi shiyasa na taho gida da wuri, ina Hajiya na ganku ku kadai?"
"Yanzun ta hau sama bari na gaya mata ka dawo" ta miqe sega hajiyar ta fito ta sakko qasan tana masa sannu da zuwa zame daga kan kujerar ya gaisheta ta amsa itama tana tambayarsa ya akayi yau ya dawo da wuri yace mata aikinr babu sosai. A kitchen din Hajiya ta dakko ruwa da Lemo ta kawo masa ya karba qasa qasa ya furta mata
"I love you" tayi qasa da kanta tana zuba masa ruwan Hajiya dake kallonsu tayi murmushi a ranta wani dadi yana qara mamayeta. Idan ta kalli Khalil da Humairan tana tsintar kanta cikin matsanancin farin ciki harta ce inama tun farko ita ya aura ba Umaimah ba? Ita ce irin matar data dade tana yiwa Khalil dinta addu'ar Samu a rayuwarsa se gashi al'amari mara dadi ya biyo bayan Gamuwarsu tana fatan hakanya zama wani Alkhairi a gabada basuyi tsammani ba.

Yana gama shan ruwan ya miqe yana cewa Hajiya bari yaje anjima ze shigo akwai maganar da zasuyi, suka fita tare ta daukar masa jakar sa. A bakin qofar ya fizge jakar ya ajiye ya dauketa kamar yar tsana ya haye sama da ita tana fizgewa da shagwabar ita ya sauketa be direta ba se akan Gadon dakinsa ya bita ya danneta ya sakar mata nauyi yanda yaga tana kokawa da numfashi ya sakashi saurin dagata yana cewa
"Yarinyar nan bakya motsa jikinki gashi nan qiba ta fara miki yawa har kina haki daga an dan wujijjigaki".

Baki ta tura masa tana qunquni ya kuma kama bakin nata ya shiga kissing nata passionately badan yana jin komai ba. Seda yayi sosai kafin ya cire bakinsa daga naya ya kalli fuskarta ganin ta rufe idonta yanayinta ya nuna tana jin dadin abinda yayi mata, a hankali ya saketa ya shiga qoqarin miqewa still idonta a rufe ta sake shigewa jikinsa be gama mamakin abinda tayi ba se ji yayi ta sake maida bakinta cikin nasa tana biya masa haddar abinda ya koya mata. Kasa yin komai yayi kawai ya bude ido ya kallon yanda takeyi cike da mamakinta. Har sannan idonta a kulle ta kama Hannunsa ta ta dora akan qirjinta da suka qara cika gabansa ya yanke ya fadi abinda yake gudu har yazo kenan, seda ya hadiye wani yawu kafin ya tattaro duka nutsuwarsa ya shiga yi mata abubuwan da yasan zasu bata nutsuwa dukda bayajin komai a tattare da abinda sukeyi din. Tausayinta ya kama shi ganin yanda jakinta yake rawa, yayi iya yinsa gurin ganin ya gamsar da ita ta hanyar amfani da hannayensa da kuma bakinsa har seda ta samu gamsashshiyar nutsuwa se kuma ta kife a jikinsa ta fasa masa kukan da kana jinsa kasan na zallar shagwaba ne yayi yayi ta dagashi taqi ita a dole kunyar sa takeji abinma ya bashi dariya dakyar ya rabata da jikinsa ya shige bandaki jin ana kiran sallar Magriba.

Seda yayi wanka tareda Alwala zuciyarsa cike da zullumin abinda ya faru. Qirjinsa ya ringa bugawa duk yanda yake da jaraba ace yau gashi ga mace a cikin irin yanayin da yake so amma ace beji komai a kanta ba. Hawaye ya digo masa me zafi daga ido daya ya share yana jin wata tsanar Umaimah da be taba zaton zeyi mata irinta ba ta taso masa ita ce sila ita ta janyo masa ya zama mara amfani dashi da dutse yanzu marabarsu kadance tabbas Umaimah ta zalunce shi kuma ta zalunci Humaira yanzu ta yaya zama ze yuwu a tsakaninsu bama ita ba da duk wata lafiyayyar mace da ze aura ko ita kanta Umaiman a yanzu yasan babu abinda zatayida shi tunda ta rigada ta kassara abinda takewa wasu baqin cikin samu a gurinsa.

Qofar da Humairan ta buga masa ta sakashi qarasa wankan ya fito fuska babu walwala ya wuceta ta bishi da kallo jiki a sanyaye kafin ta shiga wankan itama tana mamakin meya bata masa rai? Haka tayi wankanta ta fito tana shafa mai tana tuna abubuwan da yayi mata. Da hannu biyu ta rufe fuskarta saboda kunyar yanda ta sako jiki harda fa wani kuka ta ringayi ita wlh bata ma san meya shiga kanta ba da har ta shishshige masa.
"Amma fa akwai dadi na yau daman ya iya irin haka shine yayi mun na mugunta kwanaki?" Ta fada a fili kamar me magana da wani. Tana saka kaya tana tunanin ya warke kenan ma tunda takamaimai fa ita daman ba wai ta san meye ciwon da yake damunsa bane qarancin shekarunta be barta ta fahimci illar da ake iqirarin Umaiman tayi masa ba ita dai tasan ta buga masa abu a ciki shikenan. Tsaf ta shirya cikin qananan kaya ta kalli kanta ita kanta ta lura da qibar data yi sosai fa abin ya mata dadi tunda daman ai shi so yakeyi tayi qibar seda ta gama shiryawa kafin ta zura dogon Hijab akan kayanta tayi sallah. A gurin ta zauna har akayi isha tayi tareda shafa'i da wutri kafin ta cire Hijabin ta sake gyara jikinta ta wuce bangarenta ta dakko Baqar Abaya ta dora akan kayan jikinta kafin ta sauka qasa. Ta rigada tayi girki tun tuni, qara gyara kwanukan tayi ta ciro Jug din Zobon data hada daga Fridge da ruwa ta ajiye komai ta koma cikin falon ta zauna tana kallon Tv a ranta tana tunanin to se yaushe kenan Umaimah zata kwashe kayanta tunda an saketa gashi kusan wata nawa har yanzu kuma ba' acire komai ba.

Khalil kuwa seda yayi sallar isha'i kafinya koma bangaren Hajiya, tayi masa tayin abinci ya girgiza kai yana sosa qeya, Hajiya tayi murmushi ba tareda tace komai ba. Qara gyara zama yayi fuskarsa na qara bayyanar da damuwar da yake ciki yace
"Hajiya daman maganar da nace zamuyi akan Humaira ne"
"Toh me kuma ya sameta?" Hajiyar ta fada tana gyara zama se yayi qasa da kansa saboda nauyin maganar da ze fada din kafin ya fara magana cikin sanyin murya yace

"Hajiya nayi la'akari ne da halin da nake ciki ina ganin kamar akwai cutarwa a zaman mu da ita tunda bani da lafiya ita kuma dole tana da buqatun da bazan iya biya masa su ba. Tun ina Asibiti nayi tunanin na sawwaqe mata kamar hakan zefi mana sauqi dani da ita sedai kuma banyi hakan ba. Hajiya kullum qara sonta nakeyi harta kai yanzu ina jin bazan iya rayuwa babu ita ba amma kuma bana so Allah ya kamani da haqqinta shiyasa nake so nayi yaqi da zuciyata na rabu da ita taje ta auri wani me lafiya ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Ubangiji yaso ya ganni" ya qarasa maganar cikin rawar murya saboda abu biyu da suka shaqe masa zuciya, baqin cikin abinda Umaima tayi masa ga kuma fargabar rabuwa da Humaira da yake jinta har cikin jini da tsokarsa.

Jin Hajiyar tayi shiru bata ce komai ba ya dago ya kalleta, a rikice ya sauka daga kan kujerar da yake ya durqusa a gabanta yana cewa
"Kiyi mun afuwa Hajiya idan a cikin maganata da akwai wadda ta bata miki rai har tasa kike zubar da hawayenki ki yafe mun zubar kwallar ki ba Alkhairi bace a gareni".

Ganin yanda ya rikice din jikinsa har yana rawa ya saka Hajiya qoqarin tsaida hawayen nata tana cewa
"Bakayi mun komai ba Babana ba kuma kaine silar zubar kwallata ba. Ina tuna irin Halaccin da mukayiwa yarinyar nan a rayuwa amma ka dubi da abinda ta saka mana. Umaimah ta cutar damu sedai mu barta da Allah ya bi mana haqqin abinda tayi mana" Hajiyar ta fada tana sake rushewa da kukan daya fi na farko, dakyar Khalil ya lallabata tayi shiru cikin yanayi na rashin dadi tace
"Maganarka gaskiya ce Babana tabbas zamanka da Humaira a halin da ake ciki da akwai cutarwa amma ai bama fatan ka dawwama a haka, ba zama zamuyi ba zaka ci gaba da neman magani har Allah yasa a dace saboda bazan so ace ka rasa nagartacciyar yarinya kamar Humaira ba ka rabu da waccen alaqaqai sharrinta be rabu damu ba yana nema ya sake rabaka da Alkhairin da a kullum nake roqa maka gurin Allah nayi imani da cewar Allah ze karbamin ya maida maka da madadin Alkhairi. Kar kayi gaggawar yanke hukunci ka fara tuntubarta kuyi magana duk abinda ta zaba se muyi fatan ya zama mafi Alkhairi dukda in har rabuwar ku ce ta kasance wadda bana fatan toh tabbas bazan yarda nayi Asarar suruka kamarta ba, zan umarci Khalifa ya nemi auranta qila abinda Allah ya...."

"Haba Hajiya wace irin magana kikeyi haka a gabana kike kiran Khalifa ya auri matar dana tara da ita da raina ban mutu ba haba Hajiya" Khalil ya katseta cikin wani irin sauti da ya sakata yin shiru babu shiri sannan ta fuskanci katobarar da tayi. Idanunsa suka kada sukayi jajir ya sunkuyar da kansa qasa a hankali ya sake cewa
"Kiyi haquri na daga miki murya amma Hajiya dan Allah karki qara kawo wannan tunanin bazan jure ba zuciya zata iya yin bundiga na mutu kawai kowa ya huta" ya fada tamkar ze rushe mata da kuka.

"In sha Allahu ba zaka mutu yanzu ba Babana yanda ka fara dandana rayuwar farin ciki da Izinin Allah haka zaka qare rayuwarka cikin farin ciki da annushuwa. Kaje ka samu matarka kuyi magana ta fahimta nima zan samu Mariqiyarta domin babu abinda zamu boye musu sannan muci gaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkhairi"
"Amin Hajiya" ya amsa se ya miqe da shirin tafiya maganarta ta dakatar dashi ya kasa gaba ya kasa baya jin tace

"Babana naji kace ka tara da ita kana nufin ka dora mata iddarka kenan?"
Dakyar ya iya daga mata kai saboda bala'in kunyar daya lullube shi Hajiya ta zabga tagumi tace
"Allah ina roqonka kasa da dogon zama tsakanin wadannan yara, Babana bansan da idon da zamu kalli iyayen yarinyar nan ba idan rabuwa ta gifta tsakaninku bayan ka maida musu da yarinya bazawara, ashe hasashena ba qarya bane da nake ganin kamar tana da Shigar ciki"

Wani quum yaji a kansa kamar ta buga masa guduma Jin wai kamar Humaira nada ciki, a hankali ya furta 'Hasbunallahu wani'imal wakeel' idan kuwa har ya zamo gaskiya Umaimah ta cutar dasu da abinda Humaira zata haifa tayi sanadiyyar da ze rayu ba a tsakanin iyayensa ba kamar yanda ta janyo wa nata yaran. Haka ya fita daga bangaren Hajiya a salube kamar mara lafiya ita kanta Humaira ganin yanayinsa ya jefata a damuwa ta shiga tambayarsa ko bashi da lafiya ne amma yace mata qalau yake. Abincin ma kadan yaci yace suje su kwanta ta kalli agogo tara ma sannan tayi hakan ya qara tabbatar mata da tabbas bashida lafiya to ko abinda tasa yayi dazu ne ya tayar masa da ciwon sa gashi ita kuma ji takeyi kafin su kwanta ma da ze qara da taji dadi haka ta bishi suka kwanta ya sakata a jikinsa sosai ya rungumeta gaba daya ya rasa ta ina ze fara tambayarta tana so taci gaba da zama dashi ko yaya, idan kuma ya tuna furucin Hajiya na cewar zata nemawa Khalifa auranta se yaji kamar ya hadici zuciya ya mutu wata zuciya ta hakaito masa kenan abinda Umaimah take ji game dashi kenan? tabbas Abune me matuqar nauyi a zuciya amma be kai ta aikata abubuwanda tayi ba inda tana da Iklasi a zuciyarta.

A haka bacci ya fara fizgarsa yana ta tunane tunane ya kasa yi mata maganar, qirjinsa da yaji tana shafawa ya sakashi bude ido ya kalleta base ta gaya masa abinda take buqata ba yanayinta kadai ya fahimtar dashi gabansa ya fadi to me yake faruwa kuma, wace jarabawar ce ta sake tun karo shi? Wata uku kenan yanzu duk idanba shi ya jata jikinsa ba kunya da tsoron ya tabata takeji har seda ta tabbatar da ba abinda take wa tsoron zeyi mata ba kafin ta sake dashi sosai amma a yau tazo da wani sabon Al'amari da yake rikitashi, babu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login