Showing 21001 words to 24000 words out of 429394 words

Chapter 8 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

925

shiga jikinta seya fito, Umaimah kuwa haka ta tsaya Mama ta shafa mata turaren dukda rashin dadinsa amma yata iya, gara a wuce wannan maganar adena qaqabamata iskokai babu gaira babu dalili a barta taji da damuwarta.

Karatu Malam din ya yafa yi mata, ya dauki tsahon lokaci yana yi amma ko gezau batayi ba harya gaji dan kansa ya dakata. Wayarsa ya dauka yayi kira, babu dadewa sega wata babbara Mace da zasuyi Sa'a da Maman ta shigo da kaskon wuta da garwashi, karba yayi zata tafi yace ta tsaya.

Wani turaren hayaqi ya debo ya zuba ya bata ta ajiye a gaban Umaiman data zura musu ido tana kallon ikon Allah jin hayaqin yasa ta kauda kai, matar ta janyo fuskarta ta dawo da ita saitin Hayaqin, Umaimah ta fara zuga Atishawa saboda sam bata shiri da hayaqi, Mama dake gefe ji tayi kanta ya fara mata wani Yuummm dan daman tunda ta shafa mata maganin nan warinsa yake damunta, miqewa tayi tace "Alhaji bari naje daga waje hayaqin nan ya dameni" ta fice baranda inda iska take kadawa ai kuwa Umaimah bata san sanda ta fashe da dariya ba har seda Abba yai saurin matsawa dan abin yazo masa a bazata.

A ranta tace "Allah shi qara, idanni baa tayar mun da Aljanu ba ai gashi nan zaa tsokalo miki naki"

"Allah gafarta Malam sunzo ko?" abba ya fada yana raba ido dan fa shi yana da tsoron Aljanu daman, murmushi Malam yayi yace
"Aa, shaqiyanci ne irin na dan yau baka gani ba da mahaifiyarta take saboda hayaqin ya koreta kar nata na gado su motsa"

"Allah ya rufa asiri" Abba ya fada ya sake rabewa gefe. Har hayaqi yaci ya cinye dai babu Aljanun Umaimah babu dalilinsu, Matar ya umarta da ta sakeyi mata karatun, ta zauna a gabanta ta kama babban dan yatsan hannunta kafin ta fara mata karatu a kunne nan ma dai shiru ba labari.

"Gaskiya Alhaji sabo duk wani ilimi da dabara da nake dashi akan al'amarin nan na gwada ka gani kuma, yarinyar nan bata da shafi ko rabar jinnu a tare da ita. Sedai idan wata matsala ta daban ce take damunta da tayi kamanceceniya da matsalar Iska" Malam ya fada yana duban Abba, shima ya gamsu da hakan dan haka ya gyara zama yana cewa

"Toh Allah gafarta malam, a yanda mahaifiyarta take fada abin nata yawanci yana tashi ne dalilin Kishi, tana da tsananin Kishi kaga karo uku kenan ana fasa auranta kuma duk ita take jawowa da baqin HALIN KISHIN ta, shin ko akwai wasu Aljanu da suke saka mutum ya zama me tsananin Kishi haka??"

"Murmushi Malam yayi kafin yace " Shi Kishi halittace Alhaji Sabo kuma ko wanne dan Adam yana dashi sedai na wani yafi na wani zafi, ko kuma wani yafi wani sanin yanda ze sarrafa kishin nasa. A yanayinta tana da zafin zuciya da saurin fushi, kuma kaga su wadannan siffofine da basu da kyau, sam fushi bashi da kyau. A duk sanda mutum yayi fushi, idan ba anyi dace ba yana iya aikata abinda daga baya zezo yana dana saninsa shi yasa da wani mutum ya taba zuwa gurin Manzon Allah SAW yace yayi masa Nasiha se Annabi yace masa 'kada kayi fushi' ya maimaita masa hakan har sau uku.

Bayan haka akwai hanyoyi da dama da mutum zebi gurin ganin ya kare kansa daga fadawa dana sani dalilin fushin zuciya shine ta hanyar lazimtar ambaton Allah, a duk sanda kaji zuciya ta yunquro maka tana raya maka aikata abinda yake ba daidai ba kayi qoqari gurin kama Ambaton Allah, kayi hailala kayi Istigfari kayi tayi har se kaji wannan Fushin ya sauka.

Bayan haka abu na biyu shine yin shiru a duk sanda kake cikin Fushin, idan kasan bude bakinka a lokacin fushi baze sa ka furta a khairi ba to kayi shiru ka kama salati

Na uku shine nisantar duk abinda ze jawo motsuwar Fushinka, idan gurine kake zuwa ake bata maka rai to ka nisance shi, idan wani mutum ne ko wasu mutane suke tunzura ka zuwa ga fushin toh ka rabu dasu hakan shi yafi zama Alkhairi a gare ka, idan ma wani abu ne kake yi duk ka dena se kaga mutum ya zauna lafiya a rayuwar sa.

Ke kuma yata maganar kishi kiyi qoqari ki sassautawa kanki, mace ce ke wata rana gidan wani zakije ba kuma ki da tabbacin ke kadai zaki zauna dashi a rayuwarki. Baya ga haka a koda yaushe ki tuna cewar Allah ne ya halastawa maza damar ajiye mace sama da daya dan haka ba wani abu bane ba kuma abin da zesa ki daga hankalinki bane kama ta yayi ki ringa Addu'ar koda Allah ze kawo miki abokiyar zama ya baki wadda zaku zauna lafiya, amma wannan mugun kishin baze haife miki Da me ido ba dan bama ko wanne Namiji ne zeyi sha'awar auranki ba saboda gudun abinda ka iya faruwa a gaba".

"Saboda kalamsa basuyi mata bama sam hana kanta fahimtarsu tayi ta hanyar tafiya dogon tunanin, seda Abba ya kira sunanta da qarfi kafin tayi firgigit ta farka, malam ya hada mata yan magunguna na tsari da baki ya bata itama Mama aka bata wasu kafin sukayiwa Malam sallama suka kama hanya.

"Yanzu Alhaji meyw abinyi, tubda matsalar nan bata Iska bace inaga fa toh sedai asibiti ko abin a kwakwalwarta yake" Mama ta fada cikin Jimami, Umaimah dake bayan mota ta tunzura baki, daga iskoki kuma yanzu Tabin hankali ake yayibo mata? To ai shikenan aje duk inda za'aje kudinsu ne zeyi ciwo tunda dai ita tasan lafiyarta qalau.

"Gaskiya Hajiya Babu inda zan sake zuwa kuma, kindai ji abinda Malam ya fada ita zatawa kanta fada ruwanta ta sakawa zuciyarta salama ruwanta taci gaba da abi da takeyi mudai Allah ya gani iyayi munyi namu zagi kuma da take jawo mana ita ta sani" Abban ya fada a fusace maganar Malam ta babu me auranta tana dawo masa, kwarai gaskiya ya fada dan duk wanda yayi aure yayi ne dan ya samu cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali, waye ze siyi tashin hankali da kudinsa ya kai gida? Duk ma wanda yazo yaga halinta doke ya gudu ai su kansu dan babu ya da suka iya da ita ne sun kuma karbi hakan a matsayin tasu Jarabawar.

"Haba Alhaji ka dena fadar haka, gatan da zamu mata kenan a yanzu mu tabbatar da lafiyarta saboda nidai wadannan abubuwan da takeyi ban dauke su a mutum me cikakken hankali ba, kaga yanzu idan Asibiti suka tabbatar da lafiyar kwakwalwarta daga nan zamu san matakin da zamu dauka akan ta tu da munsan zallar iskanci ne abinda takeyi" Mama ta sake fada cikin kwantar da murya.

Yi yai kamar bazeje ba sedai meya tuna ya zaro wayarsa ya kira wata lamba, bayan sun gaisa a taqaice ya tambayi mutumin yana gida ne ko Asibiti kamin ya kashe ya mayar da ita Aljihu. A lokacin har sun kusa isa gida ya karkata kan mota suka qara gaba, a zaton Mama zasuje Asibitin Malam ne ko Murtala se gani tayi Abban ya dauki hanyar Dawanau.

"Alhaji Dawanau zamu je ne?" Ta fada tana kallonsa, se ya juyo a fusace yace
"Can zamuje Malika, ko akwai inda suke da kwararrun likitocin manya da qananan mahaukata ne banda can din? Ki fa rabu dani idan ba haka ba tam" ya buga sitiyari, shiru Mama tayi dan da alama ran maza ya baci, shi kansa zafin ran na Umaimah ai daga gurinsa ta gado kawai dai nata ya zarce nasa ne amma shima ai ba baya bane a yanzu ne da shekaru suka ja ya rage wa kansa hayanjya da fada saboda hawan jini ammada akan qanqanin abu be qi ya wuni yana fada da mita ba.

Tsuru Umaimah tayi a bayan mota, Dawanau fa yanzu haka zaa kaita a daura mata injinan da ake saka mahaukata karfa a garin neman gira a lalubo mata haukan da bata dashi. Kamar tace kar aje amma tasan yanda Abban ya hasala beqi ya tsaida mota ya lallasa ta suji gaba da tafiya ba, tana ji tana gani suka isa Asibitin da tundaha haraba ha kalinta ya fara tashi ganin masu lalurar rangwamen Hankali kala kala an fito dasu suna ta hidimominsu. Harta hango kanta ance zaa ajiyeta anan, ai bata san sanda ta ruqunqumo mama ta baya ba ta zabura tace

"Subhanallahi jikin ne Alhaji kaga ni ko daga zuwa abu ze kuma rikicewa". Tsabatmr takaici ko kallonsu Abban beba har ya qarasa yayi parking motarsa a bakin Clinic din. A dardar suka fito suka bi bayanshi da alama yasan gurin suka ringa ratsa mutane suna wucewa abinda ya dan kwantarwa da Umaimah hankali kenan ganin mutane fes fes masu lafiya babu alamar wata lalurar hauka a taredasu, dagaske dai da akace ba Asibitin mahaukata bane, duk wani me lalura data shafi Kai ko kwakwalwa yana zuwa tana wannan tunanin har suka isa qofar wani office Abban ya kwankwasa.

Kamar ana jiransu daman aka bude, Babban Mutum dan kadan ne bazasuyi Sa'anni da Abbaba ya miqe ya tare shi ya bashi hannu da gani akwai kyakykyawar Alaqa a tsanin su.

"Mukhtar Mukhtar ashe ana ganin ku daman" Likitan ya sake fada fuska dauke da Murmushi bayan da suka gaisa da Mama, Mukhtar da taji ya kira ya tabbatar mata da Abokinsa na quruciya ne da sukayi makaranta tare ne.

"Wallahi fa Dr Kabiru haduwa tayi wuya, rabona da kai fa tun Daurin auran yar gidan Faruk Saleh daga nanaka ce ka bar qasar, se kwananan muka sake jiyo ka" Abban ya fada shima.

"Toh ya zaayi, rayuwar se a hankali, zumunchi yayi qaranci, amma lafiya kuwa na ganka tareda Madam da yarinyata, daka kirani fa na zata kawai tsohuwar Aminta ce ta motsa yau zaka kawo mun ziyara"

Umaimah Abban ya nuna masa lokaci daya bacin rai na taso masa yace"Ga tanan Dr, duk wani gwaji da akeyi a gane lafiyar kwakwalwar mutum ayi mata. Acaje ta tsaf ta yanda zan san abinyi a gaba".

"Subhanallahi ta samu Accident ne ko me" Dr ya fada yana miqewa tsaye, kan Umaimah ya dafa ya shiga duba kwayar idonta yana sake cewa

"Ina referral letter da file dinta muga menene matsalar?"

"Ba accident tayi ba, abubuwa take yi irin na masu tabin hankali kuma mun kaita Ruqiyya ance na Aljanu bane shiyasa nace bari na kawo ta nan".

Dariya Dr Kabiru yayi kafin ya koma kujerar sa yana cewa "Haba Mukhtar wani irin abu takeyi haka da har kake zaton tana da matsala a kwakwalwa?"

A taqaice Abban yayi masa bayani, Dr yayi shiru yana saurarensa yana kallonta, yes she looks depressed kana ganinta kasan akwai abinda yake damunta. Seda Abbanya gama tsaf kafin ya kalle shi yace

"Ko zaku bamu some minutes nayi magana da daughter may be ni zata gaya mun abinda yake damunta daku ta kasa gaya muku" Miqewa sukayi suka koma wajen office din inda akwai kujeru se a sannan Mama take qorafin Yunwa takeji dan basu karya ba suka fito dan Haka Abbanya fita dubawa ko ze samo musu wani abinda zasu ci.

A ciki kuwa cikin lallami da dabara Dr Kabir ya samu Umaimah da yana fara mata tambayoyi ta saka kuka ta fara bashi amsa. Tambayarta yake akanme yake damunta? Wane yanayi take ji a jikinta da sauran abubuwa daya kamata likitan kwakwalwa kamar sa ya tambayi mara lafiyarsa.

Sosai mamaki ya qulle masa kai yanda take masa bayanin abinda takeji dangane da kishi akan wanda take so.

"Idanna ganshi da wata ko naji yayi maganar mace ji nake kamar zuciyata tana ci da wuta, kawai rayawa nake a raina zan iya kashe ko wacece ta shiga rayuwarsa kuma kome za'ayi mun bazan damu ba indai akan sa ne" Umaimah ta fada hankali kwance ba tareda shakku ko dar a zuciyarta.

"Uhm lallai kam akwai matsala" Dr kabir ya fada kafin yayi rubutu a wata takadda ya miqe tsaye yace mata yana zuwa.

Waje ya fita inda su Abba suke, a taqaice ya masa bayanin akwai gwajin da zasu mata guda uku, biyu zasuyi mata yanzu dayan kuma sedau suje Aminu Kano dan Injinsu na nan ya samu matsala. Abban yace ya bashi yaje ya biya kudin amma yaqi yace dai su bata abinci taci bari yaje ya gani idan gurin suna aiki.

Wasa wasa sega Umaimah a dakin gwajin kwakwalwa, gajin farko general check up ne na kwakwalwa dan a ga ko akwai wani ciwo data samu dalilin buguwa ko faduwa ko kuma an haifeta dashi ba'a sani ba se yanzu yake bayyana. Daga nan kuma akayi mata gwajin tunani.

Basu suka bar Dawanau ba se kusan la'asar, har suka isa gida jin kanta take wani gingirin kai yaji inji, dan dayan gwajin se wani satin ma sannan zasu samu saboda se da appointment. Wani lallaba ta Mama harma da sauran yan gidan suka shigayi kafin fitowar sakamakon gwaji tasan matsayinta.

Bayan sallar Magriba tana zaune ta jona wayarta da se lokacin ta tuna ashe tun jiyan a kashe take chaji, ta manta shaf data kashe ta jiyan qila shiyasa Khalil be kirata ba ya aiko yaro. Tuno sunansa da tayi nan da nan abinda take ji ya nemi dawo mata sabo, qoqarin kiran sunayen Allah ta shigayi kamar yanda Malam ya gaya mata amma shedan da ya rigada ya samu gurin zama me kyau a zuciyarya ya shiga bijiro mata da wasu tunanikan na banza raya mata yake yanzu fa jiya yaje neman aure gidan su wata qila ma an bashi ita, kai an bashi ma inane Khalil zeje neman aure ace za'a hana shi kawai seta shiga rera kuka mara sauti.

Qarar da wayar ta tayi ce ta sakata dagowa, sunan Khalil ta gani yana yawo akai, meya kira kuma ya gaya mata yanzu idan baso yake ya qarasa ta ba?
Da so samu ne bazata amsa wayar ba amma ina zuciyarta bazata iya ba, ta rigada ta yarda zuciyarta ta kamu da mummunan Son Khalil, So me tsanani irin wanda ka iya saka me yinsa ya zauce.

Tana can tana tunani bata san wayar ta katse ba sega wani kiran ya sake shigowa, ta miqa hannu ta dakkota ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba.

"Hankalina ya tashi Umaimah, tun jiya nake kiran wayarki a kashe, dazu da safe nazo akace kun tafi Asibiti meya same ki daman baki da Lafiya ne?" Khalil ya jero mata tambayoyin ba tareda tsayawa ba. A maimakon ta bashi amsa sw kawai ta sakar masa sabon kuka me tafe da sheshsheqa,

"Yah salam Umaimah ki dena Kuka dan Allah kiyi mun magana ko jikin ne?" Ya fada yanda kasan shima ze fashe da kukan. Lallashinta ya ringayi amma kamar wanda yake qarawa wuta fetur haka ta ringa rusa masa kuka, bata san tsahon lokacin data dauka tana qona masa credit ba dan ta zata ma ya gaji ne ya ajiye wayar ba tareda ya kashe ba se ji tayi yace
"Zaki iya fitowa gani a qofar gida".

Da mamaki ta cire wayar ta duba, minti Arba'in da hudu ta kwashe tana masa kukan banza ashe tahowa yayi, seta miqe da zumbulelen Hijabin jikinta ta fito ta gani da gaske yake ko wasa ai kuwa ta hango shi a durqushe a qofar gidan suna gaisawa da Abba.

Rabewa tayi ta qi qarasawa har seda Abban yazo ze shiga gidan yace mata
"Ki bude masa sitting room ku zauna acan" zeta gyada kai ta juya ta dakko muqullin gurin ta bude kafinta leqa tayi masa iso.

Kallonta kawai yake kamar wanda ya samu Tv ita ko ta samu guri ta kame fuskar nan a hade kai kace wani mugun saqo ya kawo mata, sallamar Imran dan Anty Saratu ta katse musu shirun da sukayi, ya ajiye Try me daukeda ruwan roba da zobo se gireba a cikin wani dan bowl me kyau.

"Sannu nagode yaya sunanka?" Ya fada yana kama hannun yaron, Imran ya bashi amsa kafin ya zura hannu a aljihu ya zaro Yan dari biyar guda hudu ya bashi yace
"Maza jeka kasha sweet kaji" yaronya fita da gudunsa yana murna Umaimah ta raka shi da harara.

"Umaimah!!!" Ya kira sunanta da wani sauti da ya saka tsigar jiki ta zuba saboda yanda kiran ya shigeta, bata iya amsawa ba illah kyawawan idanunta data dagota zuba masa tana qare masa kallo. Khalil Kyakykyawa ne, irin kyan da kana kallonsa zaka ce wannan yanada kyau. Dukda baqi ne amma hakanbe boye kyansa ba, yana da hanci, ga bakinsa leben qasan yayi ja na saman baqi abinda yake qara matar da yammata akan sa kenan ga kuma wasu irin idanu da Allah yayi masa, koda yaushe ka kalli idonsa kamar mejin bacci, idan kuwa akayi sa'a ya budesu gaba daya akan ka mace ko namiji duk dakiyar ka se kaji wani abu me kama da tsoro ko kwarjininsa ya tsirga maka.

"Karki saka na komawa Hajiyata a rabi irin wannan kallo haka" ya fada yana waving hannayensa a gaban fuskarta ganin kamar ma bata gurin tsabar nisan da tayi a tunani.

"Oya tell me, meya sameki jiya gaba daya kin???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? daga mun hankali gashi na kasa samunki a waya bare naji ya kike"

Kunya ce ta kamata amma ta kanne ta jefeshi da hararar wasa tace
"Wayace maka kallonka nakeyi? Me zan kalla mani itama wadda kaje gurin nata rufa ido kawai kayi mata tace tana sonka bawai dan ka hadu ba" ta fada cikin matuqar qarfin danne abinda take ji, so take ta bugi cikinsa taji ya ake ciki sannan taji view dinsa akanta dan bazata zauna a banza da wofi son sa ya kashe ta ba.

"Na hadu ko? Thank you for the complement, itama danaje jiya haka ta fada"
Yanda tayi da fuska dole ya fashe da dariyar dabe shirya ba, ya fuskanci yarinyar ta folla masa kamar yanda ya fada sonta ba tareda ya sani ba, yana kuma iya karantar tsananin kishinsa a kwayar idanunsa.

Dariyar da yayi ta qara qonawa Umaimah rai se kawai ta bude baki ta saka kuka,

"Allah ya baki haquri, waike baki san wasa ba komai kuka kamar wata Doll baby" ya fada yana zamowa gabanta. Hijab tasa ta rufe fuska taci gaba da shaqar kukanta, ta tabbata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login