Showing 93001 words to 96000 words out of 429394 words

Chapter 32 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1011

da magungunan matsalarta harma da wadanda bata nema ba.

Shawarwari ta bata akan yanda zata kula da kanta data tashi tafiya ta bata Hadin qasaitacciyar mace tace ta shanye ta bata robar, ingantacciyar zuma da akayita daga itatuwa masu amfani ga jiki da qara kuzari wanda basuda illah ko kadan sannan bazasu cutar da ita ko abinda yake jikinta ba take ta shanye ta bata wata jaka dake dauke da wasu sirrikan bata buqatar bayani dan kowanne akwai yanda zatayi amfani dashi a jiki, ranar tun a hanya Khalil ya fuskanci mutuniyar tasa akwai magana, seda ta kusan Kashewa Hajiya danta da soyayya dan duk kuzari da qoqarinsa ranar seda sukayi kankankan ta kusan qureshi.
Ya sakata gaba da tambayar yau ina raki Umaimah kuwa sedai ta sadda kai qasa tayi murmushi, tunda suka dawo kuwa sosai ta dage da amfani da sauran sirrikan da Anty Farida ta bata na *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS07031876677* da kanta taji chanji, koda yaushe cikin kuzari take ga Ni'ima da sam bata yanke mata ta saki jiki sosai suna tsinkar furan soyayya yanda ya kamata ta kuma sake samun kan Khalil din nata dan ji da ita yake yana lallabata kamar ya goyata, idan ya fita aiki kuwa suna manne a waya voice call da video call dole ta sake bude WhatsApp saboda shi.

A haka aka ci gaba da lallaba rayuwa tun sannan wani abu be qara tashi ba, yanzu baya buqatar yace ze tafi da ita wani guri duk inda zeje tana maqale dashi dukda cikinta ya fara nauyu dan yana wata na bakwai a sannan hakan babu abinda yake hanata, ta nutsu tsaf ta zama cikakkiyar matar aure data san kanta, tsakaninta da kowa yanzu lafiya lau koda yake ba'yi saurin yanke hukunci ba tunda babu wanda ya sake takalota.

Yanzu jefi jefi tana hulda da maqotan nata musamman Rufaida da Maman Hibban se wata Aisha da take bayan layinsu sun hadu a gidan Maman Hauwa gurin kitso daga nan suka qulla qawance da Umaiman, Maman Hauwa dai duk yanda taso ta shiga jikinta ta gagara bata fuska, sam matar batayi mata ba ita kuma kishiyar ta da jininsu yafi haduwa Maman Hauwan tayi kane kane ta hana huldarsu, dukda hakan Umaimah na kai mata wanke bayan da Zuwairan ta gaya mata tana wanki da guda, akan naira Hamsin takeyi amma ita Umaimah dari take bata duk saiti dan tana tausayin matar ta karanci irin zaman haquri da cin kashin da Maman Hauwa da yayanta sukeyi mata a gidan dukda kasancewar itace uwargida a dalilin bata haihuwa ya saka mijin qaro aure ya auro Sadiya da tazo ta gallabeta.

Tayiwa Khalil zancen chanzo dan kunnen da Mama tace zata cika a bata saiti gaba daya yace babu damuwa ai nata ne tayi duk yanda taso, da yana da kudi ma da kansa ze mayar ya chanzo matan dan haka ta gayawa Mama yanda sukayi da kanta taje Khalil ya basu Lambar Bashir sukaje shagon aka chanza mata wata seda Mama tayi mata cikon dubu dari hudu da sittin. A satin akayi bikin wata yar wan Babansu Khalil ranar yinin bikin ta Luncha sarqarta, tasha kwalliya da wani uban Lace ga zinare wuya da hannu duk inda ta gifta kallonta ake ana surutu qasa qasa masu fadin Khalil ya tare a qasanta yana bauta mata nayi masu ji mata dadi na dace da Miji me hidimtawa iyalinsa sunayi ita dai ko a jikinta aka gama Yinin biki suka wuce tare da Hajiya dan daman da ita suka tafi.

Da yamma bayan ta gama abinda takeyi ta kira Khalil da suka tafi gaya wata gaisuwa shida Hajiya tace zata shiga gidan Rufaida, harda ita ya kamata ayi tafiyar Hajiya ta hana a cewarta hanya bata da kyau zata jijjiga jikinta iya gaisuwar da tayi musu ta waya ma ta wadatar.

A gidan ta tarar da maman Hibban suka hadu suna hira Rufaida take cewa
"Wai ni kin dena WhatsApp ne bana ganinki online"
"Number chatting din na sake, ni yanzu Whatsapp idan bada Khalil ba se yan gidan mu kadai nake magana" Umaimah ta bata amsa se Maman Hibban tace

"Aiko kin huta dan nima inaga barin WhatsApp din nan zanyi na gaji haka ko na tafi hutu se an kwana biyu, keni ya a ka qare da rigimar su Aisha da Moon ne?" Tayi tambayar tana kallon Rufaidah, Rufaidan ta rushe da dariya tace

"Kai ai Anty Fati naga tashin hankali da ruwan bala'i kai kishi masifa ne, kinsan fa har gidan Eshan seda mukaje dan mu ganewa idonmu dagaske dai in gaya miki mijinta Moon ta aura nace Aminta tayi rana amma dani akayiwa wannan akuyancin wallahi dana koyawa yar iska hankali. Kiga fa irin qawancen da suke a group rimi rimi ashe binta take dan ta gama sanin sirrinta tayi wuf da mijinta Allah dai ya rufa asiri".

Baki Umaimah ta bude tana kallonta, a dan zaman da tayi a wancan group din kafin ta goge WhatsApp ta gane Esha da Moon din da suke magana akai qawaye ne na qut da qut dan Lovey ma suke kiran junansu dan ita yanda taga suna magana abin har haushi yake bata tace kamar wasu yan iska shine daya ta zagaye ta aure mijin daya tab ai Aminta tayi daidai.

"Toh yanzu me tayi ita wadda aka aurarwa Mijin" Umaimah ta fada se Rufaida ta gyara zama tace

"Me kuwa tayi, se fa da aka daura sannan tasan mijinta ne angon dan duk amintar nan ashe bata san wa zata aura ba kuma da ita akayi shirin biki tas in gaya miki. Yanzu dai ta gama tashin hankali da haukan shi kuma miji yace fa yayi mata babu abinda zesa ya rabu da Amaryarsa da gida daya ma ze hada su yanzu kuma ya fasa ya kamawa Moon din gida a wani gurin ita kuma ta tattara ta koma gidansu wai ta gama auransa nace kuji shirme, ta aurar miki miji ki bar mata gidan riba biyu kenan"

"Kan babban bala'i kenan, ai na rantse da Allah duk qawar da tayi mun wannan cin Amar ba ita kadai ba sena qarar da Ahalinta gaba daya kai Allah dai ya kauda abinqi amma tab" Umaimah ta fada tana girgiza qafa tsabar yanda abin yaci mata rai, ji take inama zataga Ita Amaryar da Mijin data taya Esha daukar fansar wannan qundumemiyar cin Amana.

Dariya Maman Hibban da ke kallon ta tayi tace
"Ke ko Amarya maida wuqar irin wannan huci haka kamar ke akayiwa kishiyar, aini banji haushin Mijin ba wallahi ita data jata a jikinta ta kaita gidanta bayan tasan ta fita komai da Namiji ze kalla yayi sha'awa itace me laifi. Babu dangin iya babu na Baba qawa har kwana takeyi a gidanki ta fito Mijinki ya fito su ringa cin karo qila da shigar da be dace ya ganta bama ai da sauqi tunda auren Sunna sukayi ba watsewar su sukaje sunayi a waje ba"

"Yo yanzun waya sani, ai daman maganar da akeyi kenan kamar sun dade tare dalilin auran ne yasa ta sani, ai bazaki san Esha daqiqiya bace se kinga yanda Moon din ta samu guri a gidan ta ta baje, Haihuwar da tayi ta qarshe kinsan naje suna lokacin ma farko farkon shigarmu group din ni na dauka ma yar uwarta ce saboda yanda ta zaqalqale tafi kowa yan uwanta ma gefe suka koma suna kallon ikon Allah se fa tayi sati a gidanta har fita Unguwa take ta barta jiran yara keko ta ina bazata san yanda ta shige wa Miji ba daman tana neman inda zata lafe ga Miji da abin hannunsa gida kamar Aljannar Duniya ni banga laifinta ba wallahi" Rufaida ta sake fada tana tabe hannu.

Ita dai Umaimah ta rafka tagumi, hasaso kanta kawai take ace ita akayiqa qila da yanzu a Police station za'a maida Statement din nan ba'a gida ba, Ajiyar numfashi tayi tace da Rufaida
"Ki maidani group din dan Allah",seRufaida tace
"Wane group ai tuni kowa yayi takansa aka rufe group, ke bakisan gurmin da aka sha bako ai tuni Admins suka sallami kowa ina zasu iya wannan tashin hankali, sedai in kaiki wani sabo da na samu shima yana kawo haske dan har yafi wancan hada yan gwarama"

"Kedai Allah ya shiryeki ya kiyaye randa rigimar zata hado dake tunda bakida aiki se shige shigen groups din yan rigima" Maman Hibban ta fada Rufaida ta tura dankwali gaba tace
"Ai mu duk inda gwarama take muna nan muna daga gefe muna iza wuta muna watsa mata fetur"

"Allah ya shirye ki toh" Maman Hibban ta fada suka ci gaba da hira, se dab da magriba suka fita daga gidan bayan data bawa Rufaida sabuwar lambarta da za'a? sakata a group, a qofar gidan Umaiman suka tsaya Maman Hibban ta kalleta tace

"Amarya karki biyewa Maman Anam dan wannan turbar da ta ke kai bame bullewa bace wallahi kullum kuma ina nuna mata amma taqi ji, bance karki shiga group ba dan ana samun qaruwa da ilimin rayuwa sosai a ciki amma kisan irin wanda zata saka ki a ciki ki kuma lura da irin mutanen da zakiyi mu'amala dasu danni kin ganni tsakanina da yan group din WhatsApp mu hadu a can mu rabu a can, kadan daga ciki ne muka samu fahimtar da har muna chatting ta pc wasu ma mun zama qawaye mun hadu a zahiri muna zumunchi dan haka ki kula, mutane yanzu babu Allah a ransu, baki san mutum ba be sanki ba babu dalili ya jefaka a bala'i"

"Hakane Maman Hibban in sha Allah zan kiyaye" Umaimah ta fada sukayi sallama kowata shiga gidanta.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 27


Bayan tayi sallar Magriba ta miqe a gurin ta bude WhatsApp din dan taga ko an sakata dan daman duk a takure take tsahon lokacin nan na rashin groups din dan taji dadin su wancan karon. Halima dai tayi rantsuwar bazata qara sakata a WhatsApp group ba tunda bata da mutunchi dan kona class dinsu ma na secondary s zuwan da tayi Dutse Ruma ta saka aka maida ita dana Poly.

Cikin sa'a tana shiga WhatsApp din ta ga an sakata a groups hudu harda na girki, tsaki tayi ganin na girkin da sauran biyun a rufe suke iya Admin ne suke magana ta tsani irin groups din nan da ba'a sharing idea to ko meye amfanin hakan oho sedai ayi ta turo muku abu ku bazakuyi magana ba gara gara ma na girkin tunda shi Recipes ne ake turowa amma in kana da tambaya sedai ka bi Admin pc kenan ta tabe baki shiga wanda yake a bude daga sakata zuwa lokacin ta tararda messages sama da dari.

Info din group din ta fara dubawa taga mata sun kusa dubu a ciki a fili tace
"Tab kace a kwai gwarama dan nasan nan ba mutane kadai ba harda Aljanu se an samu" ta rubuta sallama ta tura ba a dauki lokaci ba aka shiga amsa mata wata azakwai tace

"Ban taba ganin wannan sunan ba a gidan nan da gani sabuwar zuwa ce se ki gabatar da kanki ki turo hoto da voice note".
"wani sabuwar dokar groups ce haka da za'ace dole seka tura hoto da voice" ta fada a ranta, a taqaice tayi bayanin kanta da voice message ta tura kafin ta shiga laluben hoton da zata tura, daga cikin hotunan datayi ranar da sukaje Yinin cousin din Khalil ta zabi wani da tayi a gaban Mudubi yayi kyau sosai ta tura aka ringa mata sannu da zuwa anata yaba hoton ta da zuzu tawa suna cikin haka Adminta rufe group akan za'a fara gudanar da Program na ranar,a tsarinsu kullum suna da abinda suke gabatarwa na qaruwa na dan wasu mintina idan an gama se abude group aci gaba da sharholiya.

Fita tayi ta ci gaba da bude status da duba massages din mutane kafin a gama program din da akace za'ayi ranar zasuyi ne akan Ado da kwalliya. Wata number taga tayi mata magana kamar ta share se kuma ta bude

"Assalamu alaikum Asiya dama rai kanga rai" aka rubuta, seta bude info din number, Zee Ladan sunan me lambar ga hotonta nan akan Dp tayi zooming ita dai ko a irin fuskokin da bata gama tantancewa babu wannan sannan sunan data kirata Asiya ba sunanta bane kuma gashi suna cikin group daya sabon da aka sakata dazu dan haka ta rubuta mata
"Wrong number" kawai ta tura.

"Lallai Asy, daman ance kin zama big girl yanzu kin yada duka yan GGC amma ban zata nima zaki ce kin manta dani ba duk irin zaman mutu chin da mukayi daga yin Candy kikayi batan dabo akace kun koma garinku Zamfara se yau Allah yasa naganki a group ina ganin hotonki na gane ki" matar ta sake turo mata da dogon rubutu, se Umainah taja tsaki a fili tace

"Baiwar Allah inaga kinyi kuskuren lamba dan ni ba Asiya sunana ba Umaimah nake kuma ni ba yar Zamfara bace a Kano nake"
Se matar ta turo mata sticker irin ta mamakin nan tareda voice note tace
"Kai amma wannan kama da yawa take, dan Allah bakuda yan uwa a Zamfara? Kamar ku daya da wata qawata da mukayi Secondary Asiya Sani ina ganin hotonki bakiji yanda nayi murna ba dan nafi shekara goma ina nemanta"

Umaimah na shirin bata amsa tajiyo horn din Khalil dan haka ta kashe datar ta ajiye wayar ta miqe dakyar dan cikinta yayi nauyi, daga bakin qofa ta jirashi ya shigo da mota ya kulke gidan, hannunsa dauke da manyan ledoji ya ajiye su aqofar kitchen seta qarasa tana masa sannu da zuwa ya amsa yana cewa

"Zabi ne Kawu Labaran ya saka aka yanka mana an gyara su se ki saka a Frizeer" ta amsa ta toh ta shiga kitchen din dasu shi kuma ya shige daki.
Seda ta kai masa ruwan sanyi da Lemon Tamarin da tayi tun da ran???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a ta barshi ya shiga wanka ta koma kitchen din ta kunna Gas ta shiga dumama miyar zogale da yake tuwo tayi ta cire zabin ta sake wanke su dakyau ta saka a Freezer sannan ta shiga hada kayan abincin tana kaiwa kan Dining tana gamawa Khalil ya fito da shirin fita masallaci.

Sannu yayi mata yace bari yaje yayi salla tunda an kira se itama ta wuce ciki ta sake Alwala ta dawo palour tayi sallar ta, tana idarwa ta sake zarar waya, Khalil ya shigo ta tashi ta koma kan Dining din ta zuba masa abinci ya fara ci yana kallonta ganin ta maida hankali tana kallon waya tana zuba murmushi,

"Me kike kallo a wayar haka da kike murmushi" ya fada yana kallonta, seta dago tace
"Babu komai nida Maman Asad ne wai jiya ashe Nuratu tayi naqudar qarya har Asibiti aka kaita sun zata haihuwa ce akace da saura bakaga yanda ta gigice ba wai tana ta sambatu"

"Uhm daman ana naqudar qarya ne qila dai ita tasan abinda take ji a jikinta" ya bata amsa yana ci gaba da aikawa cikinsa tuwo Umaimah ko ta maida kai taci gaba da danna wayarta.
"Ke bazaki ci ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar ta daga masa kai kawai alamar eh se ya saka hannu ba tareda ta ankare ba ya zare wayar daga hannunta ta dago tana marairaice fuska yace

"Uhm kice kin koma sana'ar taki ta chatting ko" ya fada yana bin chats din group din dan tana ciki lokacin.
"Wato abinda kukeyi kaiwa daren kenan ku zauna kuna qare mana zagi da sharri kala kala ko?" Ya fada yana yamutsa fuska saboda ganin wata mata data ke cewa 'ai duk maza tsinannune, idan ba ana cin kutumar ubansu ba ba'a daidaitawa dasu' ya miqa mata wayar yana cewa

"Ita wannan harda uban ta a ciki kenan ko? Allahya rufa asiri"
"Bafa kasan me akayi mata da take fadar haka ba" Umaimah tayi saurin katse shi seya tareta shima yace
"Duk ma me akayi mata ya kamata tayi jam'u ta tsinewa mazan duniya duka? Daga jin kalamanta kinsan ba matar arziqi bace bana so ki fita daga wannan group din idan ba haka ba ranki ze baci Umaimah, na fuskanci a nan kike kwasu duk baqin halayen da kike zuwa dasu toh ki fita idan ba haka ba zan karbe wayar gaba daya ki rasa" ya qarasa yana miqewa tsaye dan gaba daya abincin ya fita a ransa.

Cikin palour ya koma ya kunna labarai Umaimah ta bishi da kallo kafinta miqe itama ta koma kusa dashi tana cewa
"Honey bafa wani abu bane ba kuma ni banma san wacece ba kawai magana akeyi ta sako baki kagani ma Admin seda tayi mata magana tace be kamata ba abinda ta fada"

"Nidai na gaya miki ki fita, ba kijw kin shiga cikin marasa hankali bama ya aka qare" ya fada ba tareda ya kalleta ba, seta zumbura baki tace
"Me kake nufi"
"Duk

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login