Showing 177001 words to 180000 words out of 429394 words

Chapter 60 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1025

yanzu da safe Umaimah ta saka jarabar se an dafa. Hira sukeyi abinsu a ranta tana lissafin zuwan Rufaida dan jiya dakyar tayi bacci saboda baqaqen maganganun da Khalil ya yaba mata kawai jira takeyi taji shawarar da zata bata akan yanda zata rama abinda yayi matan.

Salman suka samu a gofar gidan dawowarsa kenan daga Makaranta yaje rubuta jarabawar safe. A darare ya gaisa dasu dan ko hannu da suka bashi ne karba se kallonsu yakeyi yana jiran yaji abinda ya kawo su.
"Kayi mana sallama da me gidan nan mana" daya daga cikin su ya fada, Salman ya kalle shi daga sama har qasa kafin ya shiga cikin gidan, har yayi nisa ya tuna da ai Abban ma baya nan yaje daurin aure Qiru kuma yanzu dai beci ace sun dawo ba se ya juyo da baya daga jikin qofa ya daga murya yanda zasuji shi yace
"Wai baya nan yayi tafiya"

"Toh kayi mana magana da wani babbaa ciki naga alamar kamar kai ka tsorata da ganinmu" Mutumin ya sake fada se ya juya ba tareda yace musu komai ba ya shige gidan. Yanayin da yayi sallama ya saka suka bishi da kallo gaba daya, ya kalli Mama data fi kusa da qofar tsakiyar yace
"Mama wasu mutane sun zo neman Abba na gaya musu baya nan sunce wani babba yaje"

"Kamar Yaya wani babba? Kai din baka isa ka wakilce shi ba zaka taho wani zoqai zoqai dakai" Maman ta fada se yayi ciki yana cewa
"Jami'an tsaro ne, gara dai a cikinku wata ta leqa taji me yake faruwa"

"Ba shakka wato idan ma tafiya za suyi damu shikenan ba, baci gidanku kuwa kai zaka koma kaji abinda ya kawo su" Maman ta fada seya marairaice yana cewa
"Jiya fa na baku labarin case din wayar Hassan idan kuma sune suka biyo nifa dan Allah tunda dai su sukace na turo wani Mama ko Anty kuje, ga Yah Umaimah nan ma ai itama babbace"

Umaimah data bubbude qafafu ta aje ciki tsakiya ta galla masa harara harda murguda bakinta dayayi labcece dan wannan karon sosai ciki ya canza mata kamanni tana kallonsa tace
"Inda ace harkar samu ce ai da bazak shigo kace wani yaje ba ko" Sallamar da aka buga daga gareji ta saka su yin shiru. Mama ta maida Hijabin da tayi sallar Walha ta miqe tana cewa
"Bari na leqa karsu ce an barsu a tsaye".

Bayan sun gaisa ya zaro ID card ya nuna mata yana cewa
" Daga State CID muke, an bamu umarnin mu tafi da Umaimah Sabo".
Mama ta dafe qirji tana kiran sunayen Allah kafin tace
"Umaimah kuma? Ni Malika rigimar wa ta janyo mana"

"Idan munje can Zakuji koma menen Hajiya, ayi mata magana ta fito saboda ana jiran mune bamason bata lokaci" ya sake fada a qagare yana zazzare ido, badan doka ba da cikin gidan ze shiga dakansa ya fito da ita.

Jiki a sabule Mama ta koma ta tarar dasu cirko cirko dan tun Salatin da ta rafka suka jiyota, abinda yazo musu a rai su Abbane sukayi Hatsari amma yanayin data shigo beyi kama da na wadda aka fadawa zancen Mutuwa ba idonta akan Umaimah da ita kadai ce a zaune tace
"Tashi ki sako Hijabinki ana jiranki a waje"

"Ni kuma waye yake nemana?" Ta fada tana kallon Maman, tsawa ta buga mata da seda ta zabura ta miqe babu shiri kafin tace
"Ki wuce kiyi abinda nace, dukma wanda yake nemanki zaki gani tunda kinsan rigimar da kika siyowa kanki".

Sum sum Umaimah ta shige daki ta sako Hijabi, silifas ta zura bata iya tsayawa daukan wayarta ba saboda Tsawar da Mama ta sake buga mata ta fice tana waiwayensu, a garejin taga Mutane sunsha baqar Suit su hudu suna jiranta girjinta ya bada qara Dumm, badai Khalil ne ya turo a tafi da ita ba?
Anty data biyo bayanta ganin qatti har hudu ta kwalawa Mama kira tana cewa
"Na shiga uku ina zasu tafi da ita? Haka kawai kince yarinya ta fita Kallarau fa mutane babu alamar Rahama a fuskarsu su waye wadannan?"

Shiru Mama dake tsaye a bakin qofa tayi mata seta koma ciki da gudu ta sako Hijabi tabi bayansu tuni sun tasa qeyar Umaimah a mota Anty ta sako kwasowa da gudu ta shigo gidan tana cewa
"Sunfa tafi da ita, a zamanin nan Idan wani abu ya samu yarinyar nan me zamu cewa Mijinta"

"Sunce daga CID suke kuma laifi tayi aka turo su tafi da ita" Maman ta fada tamkar ta rusa ihu saboda abinda takeji, Salman ya dora hannu biyu a kai yace
"Mama kika bari suka tafi da ita? Kin tabbatar daga can suke innalillahi, se ya zabura yayi waje yana cewa
"Ku kira Yaya Aminu ku gaya masa bari nabi bayansu naga inda zasuje" ya burga Mashin dinsa ya bisu da gudun tsiya dan har sun fice daga layin. Seda Salman din yayi magana kuma taji wani tsoro ya dirar mata, meyasa ba tayi tunanin kiran Aminun ba kafin su tafi da ita kai ita kam ta shiga boni.

Maganar Anty ta jiyo tana waya da alama da Aminun ne dan taji tace Yayansu seta nemi guri ta zauna kawai a zuciyarta tana Addu'ar Allah ya tsare mata Umaiman yasa tana hannu na gari. Kusan minti goma sha biyar sega Aminun ya shigo daga bakin qofa yace su fito, Anty da Maman suka runtuma har suna ture juna Salma da Yasir zasu bisu ya daka musu tsawa dole suka koma suna hawaye. Har suka isa tambayar junansu suke akan me yake faruwa?
A can suka hadu da Mijin Rufaida da Mamanta wadda Mama ta ganeta saboda sunzo sunan Nuratu da akayi Sati biyu da suka wuce tareda Rufaidan nan suka shiga tambayar juna ba'asi babu me amsar bawa dan uwansa se suka samu guri suka zauna jiran Aminu da aka barshi ya shiga Albarkacin kasancewarsa Jami'in tsaro.

Sanda Khalil ya iso a sannan Aminu yakeyi musu bayanin tuhumar da akeyiwa su Umaiman, Mama dake zaune akan Benci tace
"Yanzu meya hada yaran nan da wata hukumar kare haqqin Mata da har suka kawo su qara kai lamarin Umaimah baze kashe taba.

Umaimah
Tana fitowa daga mota idonta ya sauka akan Isma'il da suka fito daga sallar Azahar. Wani mugun kallon tsana ta bishi dashi ta tuna Marin da yayi mata amma in ta tuno da abinda ta aikata musu se taji ranta yayi sanyi, haka aka tasa qeyarta shi be ma ganta ba suna magana da Barr Kallah tana shiga ta ga Rufaidah a rabe a wani guri tana aikin Kuka fuskarta tayi qozai qozai duk kwalliyar nan ta kama gabanta dan dankwalin dashi take faman goge hawaye tana ganin Umaimah ta miqe tana cewa

"Gata nan wallahi, dan Girman Allah ku sallameni na tafi tunda tazo. Wallahi bani da hannu a ciki ita ta shirya abinta kawai gani nayi ta tura mana".
Turus Umaimah tayi tana kallonta wata mata ta bugawa Rufaidan tsawa tana cewa idan bata rufe mata baki ba zata jefata a Cell saboda ma taga an barta a waje ne take musu surutu criminal din banza kawai seta koma ta zauna jiki na bari tana ci gaba da share hawaye.

Gurinta Umaimah ta nufa wanda ya shigo da ita ya dakatar da ita ya nuna mata wata qofa, batayi musu ba ta tura ta shiga. Dakine babu komai ciki se Table da kujeru guda biyu daya na kallon daya ta nemi guri ta zauna tana kalle kalle. Mutumin da ya tambayi Rufaida ne ya dawo ya qara tamke fuskar nan ta kalleshi take itama ta sake hade tata fuskar ta na muzurai se kawai ya tsaya yana kallonta tsabar mamaki. Ba Mace ba ko Maza manyan Criminals sukayi Arba da fuskarsa shiga taitayinsu suke ballantana wannan da tsaf ze iya hadiyeta tazo tana masa muzurai seya buga takaddun da ya shigo dasu akan Table din Umaimah ta daga kai ta harareshi a fakaice ta kalli qasa.

Hotuna ya watsa mata yana kallonta da jajayen idonsa yace
"Wacece wannan?"
Ta debesu tana dubawa, baki ta tabe irin ko a jikin nan nata kafinta maidasu ta ajiye tana cewa
"Wai sunanta Hadiza kowa"
"Ki shiga taitayinki nan ba gurin wasa bane" Mutum ya fada cikin tsawa yanabuga bencin gabansa. Umaimah ta gyara zama har ranta taji tsoron tsawar daya mata amma ta dake. Kallonsa tayi tace
"To wai ma nan din ina ne kuma menayi da zaka zo ka sani a gaba kana mun Ihu? Nidai karka firgitamun Da a ciki, idan tambayata zakayi salin alin base kayimun hargagi ba".

Dukda dokar da aka bashi ta karya taba lafiyarta besan sanda ya kwasa mata mari da lafcecen hannunsa ba ta fasa ihu tayi baya qiris ya rage ita da kujerar su fadi yayi saurin tareta yana sake buga mata tsawa yace
"Naga alamar bakida kunya kuma baki san a inda kike ba, to ki tattara hankalinki guri guda ki amsamun tambayoyina mu rabu lafiya idan haka ba sena saba miki kamanni kafin ki fita daga nan".

Magana akayi masa ta cikin abinda ya maqala a kunnensa cikin girmamawa yace
"Sorry Sir, yarinyarce bakinta bashi da saiti amma za'a kiyaye" seya juya kan Umaimah shatato hawaye kamar lalataccen famfo ta toshe bakinta da hannu daya tana shafa inda ya mareta da dayan. Murmushin mugunta yayi ya sake tura mata hotunan yana cewa
"Wacece wannan, kuma menene alaqarki da ita?"

Cikin kuka tace masa
"Sunanta Hadiza kuma budurwar Mijina ce"
"Budurwar Mijinki?" Ya maimaita ta daga masa kai ba tareda tayi magana ba se ya sake bude wani envelope dinya zaro hotunan da take yadawa ya ajiye mata yana cewa
"Me kika sani akan wadannan hotunan?"

Kallonsu tayi ta kalleshi kafin ta juyar da kai gefe tace
"Wata ce ta turamun dasu, tace ita Aminiyar Hadiza ce sannan itace ta gaya mun abinda yake tsakaninta da Mijina da duk irin Badalar da suke aikatawa a bayan idona ta turamun da shaidar hotuna da videos ta kuma hado mun da wannan tace mun daman Hadizan yar Leabian ce, kuma Mijina ya sani yace a hakan ze aureta, shine ni kuma na turawa da yan uwansa dan su gani su san irin matar da yake so ya auro kuma na watsa a media saboda na tona mata Asiri kowa yasan abinda take aikatawa".

Kallonta ya ringayi yana nadar abinda take fada har ta kai aya, a ransa ya jinjina mata wannan ita Gaba gadin ai babu Tsoro ko shakkar komai a ranta kuma da alama iyakar gaskiyar abinda ya faru ta fada. Jin tayi shiru ya sakashi ya sake tamke fuska ya kalleta yace
"Kecw kika yada hotunanta a Media kenan kikayi mata qazafi saboda kawai Mijinki yana nemanta koh?"

"Ni ba qazafi nayi mata ba, na ma santa ne ballantana nayi mata qazafi? Na gaya maka Aminiyarta ce ina zaman zamana ta kirani a waya ni badan ta gaya mun ba babu ta yanda za'ayi nasan tana tare da Mijina kuma ita ta gaya mun Halinta ni kuma na tonata a duniya saboda wanda basu sani ba su sani ni meye nawa a ciki?" Umaimah tayi saurin katse shi seya miqe tsaye yana zaro mata ido yace

"Bazaji gyara bakinki ba ko? Naga alamar se jikinki ya gaya miki sannan zaki fahimci a inda kike, wato ke ga Fitsararriya kin aikata laifi sannan har kinada bakin kare kanki. To ki adana duk wasu surutanki zasuyi miki amfani a gaban Alqali, idan kinje can se kiyi muau bayanin dalilin daya saka kika Lalata Rayuwar Baiwar Allah ta hanyar yi mata mugun qazafi" ya shiga tattara takaddun daya barbaza a gurin. Kotun da taji ya ambata ta saka ta qarasa shigewa cikin nutsuwarta murya na rawar Kuka tace
"Yanzu kuma me nayi dan girman Allah, kai fa kace na fadi gaskiyar abinda na sani kuma na fada. Wallahi banida laifi nima fada mun akayi ba Sharri nayi mata ba. Idan ma kuma baka yarda ba aje a duba wayata lambar qawartata tana nan da duk maganar da mukayi da ita zaku gani wallahi bani na qirqiri maganar ba".

Banza yayi mata ya juya ya fice daga dak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in, hankalin Umaimah ya dugunzuma, ita bata ma san ina suka kawota ba tadai san office din Jami'an tsaro ne amma bata san wadanne iri ba shikenan daga zuwa se yace ze kaita Kotu? In ma kullewar Za'ayi ai qawar Hadiza zasu nemo su kulle tunda ita ta fada mata ai.
Sake bude qofar akayi mutumin ya dawo yana kallonta yace

"Wacece wadda kika ce ta tura miki kuma ina wayar taki take?"
"Nima bansanta ba kawai a waya muke magana, amma ka bani aron wayarka na kira gida se su kawo wayar tawa daga nan ma seka fada musu inda nake dan nasan yanzu suna can hankalinsu a tashe yake basu san inda nake ba" Umaimah tayi caraf ta fada se ya tsaya yana kallonta wannan yarinya lamarinta da ban mamaki yake, da alama ta dauka shirin film sukeyi ko amma zata gane kurenta. Fita ya sakeyi daga dakin babu jimawa wata mace ta shigo itama fuskar dai kamar Hadiri tace mata ta taso. A gaba ta tasata a zatonta gida zasu maida ita se gani tayi sun sake shigewa can cikin gurin, birki taci ta shiga zare idanu ganin inda ta kawota, Cell ne Matan dake ciki suka zuro musu ido kamat Kura taga Nama Umaimah ta hadiye yawu dakyar ta kalli mayar tace

"Dan girman kuyi haquri ku maidani gida wallahi iyakar gaskiyata na gaya muku, in baku yarda ba muje tare na baku wayata se ku nemota nidai ku qyaleni" bata kulata ba ta iza qeyarta har zuwa gaban wani Cell da babu kowa Se Rufaida tana can qurya ta hade kai da Guiwa itama Umaiman saboda kayan jikinta ta gane ta.
"Shiga ciki Malama idan ba so kike jikinki ya yagaya miki ba" Matar ta fada tana turata, Umaimah ta maqale a bakin qofar tana cewa
"Fitsari nake ji toh" banza ta mata taja qofa ta mayar ta kulle ta juya kan sauran Matan dakw cikin dakunan tace

"Saura naji wani surutu" ta fice daga gurin tana fita kuwa wata me suffar Yan daba ta matsi jikin qofar su Umaiman harda zura hannu ta jikin qarfe zata tabata tayi saurin yin baya suka kwashe da dariya kamar wasu mahaukata matar tace
"Daga yanayinki dai nasan qaramar kwaruwa ce baze wuce ashe Kishiya kima yiwa wani abun ba aka kawoki nan ko?"

Murguda mata baki Umaimah tayi tana hararta tace
"Aa Uwar kishiya ba kishiya ba, dallah malama kiyi takanki ina ruwanki da ni da abinda ya kawo ni? Naji ni kalar qananan qwari ke ai ana ganinki anga anga Tsohuwar yar ta'addah".

"Gyara kintsi yarinya idan ba haka yanzun nan nayi miki balli balli, naga alamar kanki yana hayaqi to kibi a sannu baki san inda kika shigo ba. Ni in fardeki in miki tiyata a nan gurin qaramin abu ne a gurina nan da kike ganinmu mun ci dubu se ceto" Daya daga cikin Matan ta zaburowa Umaimah ganin tana neman ta zagi shugabarsu. Umaimah tayi ciki can kusada Rufaida a tsorace jin za'ayi mata Tiyata da alama wadannan manyan yan tasha ne.

"Rufaidah ya akayi kika zo nan kema?" Umaimah ta fada tana dafata kamar tana jira kuwa ta dago cikin bacin tace
"Tambayata ma kikeyi ya akayi nazo bayan kece sila haka nan ina zaman zaman kin jefani a masifa daga taimako to wallahi idan Allah yasa muka fita daga nan kowa yayi takansa babu ni babu ke ballantana ki ringa janyo magana kina sako ni a ciki a ringa kulleni a Cell"

"Lallaima to daman gayyatar ki nayi ko kuwa ni bace kije ki dora a Facebook ni bance kin jawo mun ba tunda nasan ai ta silarki har aka bincikoni se kece zaki ce wani waye waye aikin banza kawai duk kinbi kin wani rikice kamar wadda akace tayi kisan kai" Umaiman ta hayayyaqo mata itama se kuwa Rufaida ta miqe tana cewa

"Ai da banyi kisan kai ba gashi nan an sakani cikin Yan ta'addah, wallahi Allah ya isa tsakanina dake Umaimah idan har naje Prison ta dalilinki bazan taba yafe miki ba" ta qarasa tana sake fashewa da kuka wiwi kamar yarinya. Hasko kanta kawai takeyi a prison yanda take jin labarin irin gwale gwalen da ake sha ina zata iya, da ace tasan yarinyar nada daurin gindi da bata saka kanta a sabgar Umaimah ba, yanzu gashinan daga solidarityn qawance se ta zurme da gidan yari gaskiya Umaimah ta cuceta.

A can waje kuwa bayan dogon cuku cuku da Yaya Aminu yayi dakyar ya samu jin bayanin tuhumar da akeyiwa su Umaiman, kansa ya dafe yana kallon Detective Adnan dake kora masa jawabi ya qarasa yana cewa
"Yanzu abinda ya rage mu samu ita wadda tace ta tura mata hotunan a farko daga nan zamu tattara dukka shaidun da muke dasu mu turasu koto ta yanke musu hukuncin daya kamata dan haka muna buqatar wayarta tace komai yana ciki".
Jiki a sabule ya koma ya shaidawa su Mama abinda aka gaya masa daidai lokacin Khalil ya dawo daga Sallar Azahar din da beyi ba, ya kalli Mama dake hawaye tana cewa
"Yanzu daman Umaimah ce? Itace ta tozarta yarinyar nan haka duniya gaba daya take mata tofin ala tsine amma shine a gabanta muke maida zancan yarinyar nan tayi funfurus bata ce komai ba yanzu ina zata kai haqqin wannan baiwar Allah? Me yake damun Umaimah anya Umaimah naso ta gama da duniya lafiya kuwa?"

"Aa Mama ki dena fadar haka, addu'a dai zaki ci gaba dayi mata kina nema mata shiriya a gurin Allah shine kadai mafita" Anty da gaba daya itama jikinta yayi sanyi ta fada. Mama ta goge hawaye da gefen Hijabinta tace
"Tunda na haifi Umaimah ban huta ba Saratu ke shaida ce babu ta inda na banbanta tarbiyyarta data sauran yan uwanta amma ta fita zakka a cikinsu. A kullum abinda yake faranta mata rai shine ta dakko mana magana, duk wani abin tsiya Umaimah ce daga yari tarta har girmanta bata barmu mun huta ba se yaushe zamu rabu da Jidalin Umaimah?
Wallahi da nasan fitinar da zata zamar mun kenan dana zubar da cikinta na huta tun tuni qila da Rayukan kowa ya zauna qalaubarshi ya shiga" ta qarasa tana rushewa da sabon Kuka wani Dattijo dake tsaye gefensu shima tasa ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login