Showing 255001 words to 258000 words out of 429394 words

Chapter 86 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

947

fada yana zaro wayarsa data sha jiki daga Aljihu. Bata fuska tayi kamar zatayi kuka Mama tace

"Sha kuruminki, kai kuma me son abin duniya baka isa ba. In kai na roqa ka rakata kaqi gara da baka je ba gashi nan rabo ne ya kirata. Maza karbi wayarki an gode masa Allah ya saka da Alkhairi daman yaushe muke zancen da Yayanku yace ze turo miki da wayar to ga dan uwansa ya hutashshe sa ya siya miki"

"Mama kinsan kudin wayar nan kuwa, Humairan za'a barwa ita lallai ma" Habibu ya sake fada Mama ta fizge kwalin wayar daga hannunsa tana cewa
"Ko Miliyan dubu ake saida ita haka zaka barta da abarta shi wanda ya siya beyi kyashi ba se kai dan hana ruwa gudu ko to ka canza hali. Maza ki kaita daki ki boye, Sumayya tace zata zo anjima naga hoton kamar irin tata da tazo seta saita miki ita kema ki samu ta daddannawa kinji Uwata Allah dai ya sakawa Khalil da Alkhairi" ta tattara mata wayar da ledar ta bata ta shige cikin daki Abinta. Tsalle ta ringa bugawa na murna tana kallon kwalin wayar.

Wai yau ita ma tayi wayar kanta kuma IPhone babba duk cikin yan qaryar Ajinsu masu zuwa da waya babu me irinta dole ranar Graduation kuwa ta wanke su sedai su ganta da waya tana daukar hotuna itama. Saboda zumudi bata iya jira Sumayyan tazo ba ta bude wayar ta jona chaji, Kati ta gani na dubu daya a ciki MTN, ta duba bataga Layi a ciki ba dan haka tana idar da Sallar Magriba tacewa Maman zata shagon Lawi ta siyo layi yayi mata Register Mama ta bata Dari biyar ta tafi, bata jima ba kuwa ta siyo ta dawo dan babu nisa daga gidansu tana dawowa ta tarar da Sumayyan tazo har Mama ta dakko mata wayar ta kunna Hotspot tana saita mata ita. Dakyar ta iya haqura ta bar Layin ya kai awannin da aka ce mata kafinta dora ta shiga WhatsApp da an rigada an mata downloading, number Noor data haddace tsaf ta loda tayi masa magana. Be yarda ita bace seda tayi masa voice yaji muryarta babu bata lokaci ya tura mata da hotunansa da tacs tana so, ya tafi Training din aikin Soja wanda shine karo na uku da yake zuwa biyun baya duk be samu ba amma haka ya sake nema ya tafi a karo na ukun dan ya dage shi idan ba Soja ba baya tunanin akwai aikin da ze iya yi.

A wayar Mama ta kwafi number Khalil layin na hawa kuwa ta rangada masa text na godiya kafin taci gaba da sabgoginta ta loda numbers din qawayenta da daman a wayar Mama take saving dinsu kafin ta shiga dora status din Haskenta kamar yanda take fata a kullum itama tayi waya ta ringa saka hotonsa a status kamar yanda yake saka nata.

KHALIL
Tun bayan maganar da sukayi da Anwar yake ta qoqarin ganin ya yakice Humaira da tunaninta daga zuciyarsa amma abun ya gagara. Tamkar yana jiran ayi masa fashin baqi akan abinda yake ji din akanta, maimakon ya cireta daga ransa kamar yanda yake niyya se abun ya faskara kullum qara samun guri takeyi tana narkewa a zuciyarsa idan kuwa ya ga tayi status na soyayya ji yakeyi kamar yayi bindiga amma a hakan kullum qaryata zuciyarsa yakeyi akan baya sonta.

A gari yaji za'a fara rubuta Jamb kwana biyu masu zuwa dan haka ranar ya shirya da Yamma tareda Mu'ayyad haka kawai suka tafi gidan Mama. Kewar Humairan yakeyi amma ya rasa ta inda ze jr gidan dan baya son Maman ta zargi wani abu yanzu daya samu zancen Jamb din seya fake dashi, kwalliya yasha da wata Danyar Shadda Cream color ya kafa hula. Yana cikin fesa turare Umaimah ta shiga dakin. Kallo daya ta masa ta dauke kai ba tace masa qala ba tabi lafiyar gado ta kwanta dan kwana biyun wani Mood swings take ji dashi kowa na gidan ma haushinsa take ji ko bangaren Hajiyan se a kwana a wuni bata leqa ba.

Turare ya dauka yana qara fesawa a jikinsa dukda ya saka amma ji yayi be ishe shi ba. Ya gama fesa turare ya sake daukar comb yana taje Gemu daga nan ya koma gyaran hula. Umaimah dake kwance abin ya isheta, yanda yake ta wani faman qalqale qalqale kamar sabon Ango yasa ta miqe zaune murya a cukule tace
"Wai ina zakaje kake ta wani faman kwalliya kana gyara fuska?"

Waigawa yayi ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
"Inda kika aikeni" dan shima yanzu gasa mata magana yake a tsaye yanda take masa. Aiko ta harareshi ta koma tayi kwanciyarta yana jinta cikin qunquni tana cewa
"Duk abinda mutum yakeyi dan kansa ni dai idan anci Amanata ba yafewa zanyi ba".

Murmushi kawai yayi be tankata ba ya fice daga dakin, a bangaren Hajiya ya dauki Mu'ayyad bayan ya gaya mata zasu fita tayi masa a dawo lafiya kafin suka kama hanya.
Seda ya tsaya a hanya yauma yayi wa Maman cefanen kayan miya masu kyau daya gani ya biya gurin da ake siyar da Kaji ya siya Frozen kafin suka kama hanya. Seda sukaje qofar gidan zuciyarsa ta raya masa cewar ya kamata ace ya zowa da Humaira da tsaraba, wa yaga azarbabi.

A cikin Get din gidan yayi mugun gani, Humaira na tsaye ta saka dogon Hijabi kamar kullum har qasa tajawoshi ta refe fuska ta kamar mejin kunya. Ya maida kallonsa kan Dogo siririn Saurayin dake tsaye kusa da ita yana mata magana dukda be jiyo abinda yake fada ba da alama shi ya bata kunyar.

Wani abu me daci yaji ya taso masa, kamar ya juya amma Mu'ayyad daya dakko ledar Tumatir ya rigada ya shige ciki dan shi ya tsaya hado kan ragowar Ledojin, haka ya ratsa su ya wuce. Yana jin tana masa sannu da zuwa harda shima saurayin nata amma yayi kamar beji su ba ya shige ciki.

Mama nata yiwa Mu'ayyad sannu da zuwa ya shiga, ta juyo kansa tana cewa
"Gaskiya ka kyauta, yau zuwan naka yafi na kullum tunda ka taho mun da Megida harda Cefanensa"
Seda yayi da gaske kafin ya iya danne abinda ke taso masa ya shiga gaisheta, ta amsa tana tambayarsa gida tareda godiyar Wayar daya bawa Humairan.
Shiru yayi kawai ya zubawa qofa ido yana jiran yaga sanda zata shigo Mama data tafi kawo musu ruwa ta dawo da babban Try data doro ruwan da Lemo. Ta ajiye wani kwano gaban Mu'ayyad tana cewa
"Wannan na megida ne".

Alkaki ne a ciki nan take kuwa ya hau ci ta shiga tsokanarsa da cewa Shazumamu shidai Khalil ya gaza shan koda muqurwar ruwa daya dan ya tabbatar bazasu iya wucewa ta maqoshinsa ba. Hira Mama take masa ganin ya maida hankali yana ta danna waya yasa tayi shiru ta mayarda hirar tata kan Mu'ayyad.

Seda suka ahafe kusan minti Ashirin a zaune kafin ta shigo da sallama cikin siririyar muryarta.
"Oh ni Hauwa'u, wallahi na manta shaf da batun bakya gidan nan Humaira se kace wadda ta tafi rubuta jarabawar gaba daya kusan awa nawa keda kika ce ba zaki dade ba" Mama ta fada tana riqe baki dan da gaske ta manta da Humairan ta fita.

Baki ta tura cikin shagwaba tace
"Kai Mama ko fa awqa biyu banyi da fita ba kuma ni na dade da dawowa muna tsaye da Noor a Get, sanda su Yah Khalil ma suka zo muna nan fa" kallonta yayi, yanda ta ambaci Khalil din ka rantse ita ta saka masa sunan yanda ta fada yayi mugun masa dadi amma haushin maimaita cewar tana tsaye da koma waye yazo yasa ya galla mata wata harara.

"Ai fa Allah ya dawo da Nura se kuma abinda aka gani. Yanzu dai makaranta zaki fara dole ki tsayar da hankalinki idan ba haka ba kuma ya fito kawai a hada a kaiki ku qarata can, wannan soyayya taku se kace kanku a ka fara. Yanzu ina takaddar ranar yaushe zakiyi?" Mama ta tambayeta,, seta miqa mata takaddun dake hannunta tana cewa
"Jibin zanyi, mune farkon yi ma" Mama ta karba ta duba tana cewa
"Toh Allah ya bada sa'a. Se ki maida hankali kiyi karatu dan ka ganta nan tunda ta samu wayar nan babu sakat, aikin gida ma se anyi da gaske take tashi tayi bini bini suna hira da wannan yaron Nura daman abinda yasa Mansur yaqi bari a bata waya kenan toh kuwa inaga kwace ta zanyi har se sun gama jarabawar".

Shidai Khalil shiru kawai yayi yana hadiyar zuciya, Humairah ta wuce dakinta tareda Mu'ayyad shi kuwa Mama na tayi masa hira amma sam hankalinsa baya kanta tunanin waye wannan Nuran yakeyi ya dai gane shine yaron daya gansu tsaye to kuwa dole yayi maganinsa.
"Bari muje Mama, Magriba ta kawo kai zan tsaya kuma wani guri bayan nan" Khalil ya fada yana miqewa, se Mama ta kwalawa Humairah kira suka fito tana riqe da hannun Mu'ayyad kamar Yaya da qaninta, Mama tace
"Megida kazo ku tafi, ko zaka kwana anan"

Mu'ayyad dake shan chocolate ya maqe kafada alamar baze kwana ba Humaira tace
"Kai ba yanzu kace mun zaka zauna ka kwana ba tunda babu School?"
"Aa ni bazan kwana ba, sedai kizo mu tafi gidan mu".
Dariya Mama tayi tana cewa
"Ja'iri, wato sedai ta bika naku gidan ko ai shikenan, laifinka ne da baka kawo mana shi daya saba damu ai" ta maida maganar kan Khalil, yaqe kawai yayi dan tsayuwarsu a kusa ma damunsa take dan haka yayi gaba daya yiwa Maman Sallama. Humaira ta koma daki da sauri ta hado Alawoyi da biscuit wanda Noor ya kawo mata ta biyo su dashi. A bakin mota ta same su, ta miqawa Mu'ayyad tana murmushi tace
"Yah Khalil me yasa baku zo da qanwarsa ba? Yace su biyu ne ni ban santa ba".

Yanda take maganar fuskarta dauke da murmushi yasa ya zuba mata ido kawai yana kallonta wani abu na sake fizgarsa akanta, ganin yana nema ya shagala yasa ya bude motar ya shiga yana kallonta yace
"Qarfe nawa ne Exam din naki?"
"7am suka rubuta" ta bashi amsa seya gyada kao yace
"Zanzo na kaiki".

Baki ta bude kamar zatayi magana kuma se ta fasa tace
"Toh Allah ya kaimu ku gaida gida, Mu'ayyad bye" ta daga masa hannu kafinta juya ya bita da kallo saboda yanayin da tayi maganar ya nuna kamar bataji dadin cewar da yayi ze kaita ba.

Tana shiga gida ta zube akan kujera Mama ta kalleta ganin fuskarta ba kamar yanda ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta fita ba tace
"Ke kuma lafiya kike hada fuska?"
"Mama wai Yah Khalil ne yace ze zo ya kaini rubuta Jamb, kuma ni munyi magama da Noor tare zamuje" ta yi maganar cikin shagwaba. Mama ta kama haba a ranta tana mamakin jin Khalil ze kaita a fili kuma tace
"To menene abin bacin rai dan yace z kaiki? A dadinki ai"

"Mama da Noor fa zamuje na gaya miki" ta sake fada se Maman tace
"Se ki gaya masa Yayanki ne ze kaiki ai".
Bubbuga qafa ta shigayi zatayiwa Maman shagawaba tace ta tashi ta bata guri. Tana shiga daki ta kira Noor ta sanar masa da abinda aka ce
"I'm sorry My Humy nima ina shigowa gida yanzun Hajiya take gaya mun zan kaita Gabasawa Ranar kuma da wuri zamu tafi, daman anjima nake shirin idan nazo na gaya miki" Noor din ya fada seta sake bata fuska amma bata ce komai ba. Lallashinta ya shigayi har seda ta sauko suka shiga hira kiran Dallar Magriba ne ya katse su daga nan ya gaya mata yana idar da sallar Isha ze zo sukayi sallama.

Humairan Noor kenan, kusan yan unguwar kaf da haka suke kiranta saboda irin so da shaquwar dake tsakaninsu babu wanda be sani ba. Noor Matashi ne dan kimanin shrkaru Ashirin da hudu, gidajr uku ne tsakanin gidan su dana su Noor din haka zalika tun suna Makarantar Primary suke tare dukda ba ajinsu saya ba soyayya ce tunta quruciya akeyinta har zuwa yanzu da suka kawo hankalin kansu dukda mutane da yawa suna ganin soyayyar tasu bata da matsaya da yawa suna ganin Humairan tayi masa girma a irin matakin da yake a yanzu da ko Makarantar gaba da Secondary be kai ga shiga ba dan ya dage akan aikin soja yake so yayi. Baya ga haka baya wata sana'a da za'ayi tunanin zata iya riqeshi har yayi aure kuma be fito daga wani babban gida ba da zasuyi masa auran gata iyayensa masu rufin Asiri ne kawai amma dashi da Humairan tasa sun yarda cewar suna son junansu a hakan kuma zasu jira har zuwa lokacin da burikansu zasu cika suyi aure akan hakan suke yanzu musamman da suka samu goyon baya daga Iyayensu Mata, Mama da Hajiya Asabe mahaifiyar Noor din sunyi Na'am da hadin dan qawayene sudin wasu daga cikin yayyensa da nata ne dai suke ganin batawa kansu lokaci kawai sukeyim dan yayyensa sun sha nuna masa akan ya rage irin zafin son da yake mata dan sun tabbata wata rana zata shammaceshi ta tafi ta auri wani, Macece ita babu yanda za'ayi ace ta jira Namiji amma yaceshi ba haka ba yasan ko nan da shekara dubu Humaira tasa ce kuma bazata iya barinsa ta auri wani ba abinda take fada mas akenan lullum.

Kamar yanda yayi alqawari ranar da zata rubuta Jamb qarfe shida da yan mintina a qofar gidansu Mansur tayi masa, be shiga ba a waya ya kirata kawai yace ta fito. Tana zaune gaban Mama tana shan shayin data takurata seta sha kafin ta tafin tana ganin kirankuwa ta miqe, Hijabinta ta zura dogo ta dauki qaramar Jakar data zuba abubuwan da za'a buqata tayiwa Mama sallama dake mata fatan nasara ta fita. Seda ta zauna cikin motar kafinta gaida shi ya amsa mata suka fara tafiya. Har suka isa inda zatayi jarabawar babu wanda yayi magana a cikinsu se sautin karatun daya kunna ne kadai ya karade motar. Seda ya tabbatar ayi mata screening ta hau layi kafin ya koma inda ya ajiye motarsa.

Ciki ya shiga ya kwantar da kujerar saboda yaji dadin hutawa kafin ta gama. Jakarta data bari a motar ya janyo ya ciro wayarta dake ciki. Hotonta dake kan screen dinya kalla tayi kyau tana sanye da Uniform din Islamiyya fuskarta dauke da murmushi. Bude wayar yayi yaga da key akai, zuciyarsa ta raya masa ya gwada sunan Saurayin nan nata da take sakawa a status yana rubuta Haskena kuwa wayar ta bude, yaja kwafa kai tsaye WhatsApp ya shiga amma ta rufe da Fingerprint seya ja tsaki rufe. Messages ya koma wannan Hasken ne kadai yaga suna musayar kalamai dashi daman babu wasu numbobi da yawa akan wayar duk na yan gidansu ne se qawayenta.

Qarar wayarsa ce ta tsayar dashi daga binciken da yake mata, ya janyo wayar daga Aljihunsa Umaimah ce. Bayan ya daga take tambayarsa ina ya tafi da sassafe ta farka baya nan,
"Wata Jana'iza na tafi, Baban wani Ma'aikacinmu ne ya rasu yanzu ana shirye shiryen kaishi ne da an gama zan dawo" Khalil ya shiryo mata qaryar dashi kansa besan sanda Idea tazo masa ba. Jajantawa tayi da Addu'ar Allah ya jiqan wanda ya mutu kafin sukayi sallama seya kashe wayar gaba daya ya ajiyeta. Kwanciyarsa ya gyara ya rufe idanunsa yana tunanin abinda zuciyarsa take ayyana masa yayi ko kar yayi yana cikin haka bacci ya daukeshi.

Besan iya Adadin lokacin daya kwashe yana baccin ba kwankwasa Glass din da akeyi ya farkar dashi. Humaira ce, ya cire lock din motar kafin ya gyara kujerar da yake kai ya tashi zaune. Bakinta a washe ta shigo motar ya kalleta yace
"Har kun gama kenan"
"Mun gama kuma tayi sauqi sosai wlh" ta bashi amsa tana duba jakarta.
"Allah ya bada sa'a" ya fada kafin ya tada motar seta kalle shi ganin bata ga wayarta a jakar ba, shima kallonta yayi yace
"Yaya dai?"
"Waya ta ce bangani ba kuma na taho da ita" ta bashi amsa. Da ido ya nuna mata Aljihun motar taja ta bude sega wayar ta dakko, satar kallonsa tayi dan tana budewa a kan Gallery ta tarar. Hotunanta na shirme ta shiga dubawa a ranta tana addu'ar Allah yasa be bude ba da kuwa tasha kunya Khalil dake ankare da ita yayi murmushi a zuciyarsa kawai.

Wani gurin cin abinci taga ya tsaya, ya kalleta bayan ya kashe motar yace
"Muje kiyi breakfast"
"Na qoshi, seda na sha Tea kafin na fito daga gida" ta bashi amsa. Fita yayi ya barta be jima ba ya dawo da Ledoji masu tambarin gurin a jiki ya saka a bayan motar kafin ya shiga suka ci gana da tafiya.
"Wanene Noor?" Ya jefa mata tambayar dake ta cin zuciyarsa. Humaira dake danna waya ta dago da sauri ta kalleshi ganin shima itan yake kallo yasa ta sadda kai kamar munafuka qirjinta na bugawa saboda wani abu da taji ya tsarga mata saboda irin kallon fa yayi mata.

"Uhm na tambayeki kinyi shiru" ya sake mata magana seta qara sunkuyar da kai tace
"Abokinane" dan haka kawai taji ba zata iya ce masa saurayinta bane, karya mammaketa irin na Yaya Mansur da yace tayi qanqanta da fara kula samari shekara sha bakwai.
"Aboki, shine naga kina saka hotunansa kullum kina rubuta haskenki?" Ya sake jefa mata wata tambayar seta kalleshi kamar zatayi kuka tace
"Toh ai fassarar sunansa ce haka, Noor ba Haskenan ba?" Ta qarasa da sigar Tambaya.

Yanda tayi maganar cikin sangarta da quruciya ya sakashi sakin murmushi. Rage gudun da yakeyi yayi, so yake yayi amfani da wannan damar yasan wasu abubuwa akanta dan haka ya sassauta muryarsa cikin lallami yace
"Toh amma naga harda waqoqin soyayya kike sakawa duk saboda shi sannan kuma kince Abokinki ne. Ki fada mun gaskiya daman wani ne ya ganki yave mun yana Sonki ni kuma naga kinada saurayi shiyasa bana so na hada ku kice bakya sonsa bazanji dadi ba dan dan uwanane".

Kallonsa ta ringayi harya yi shiru, ta tuna qawarta Mimi da tace mata ita banza ce da takr kula saurayi guda daya saurayin ma yaro duk ga mutane masu sonta nan da yawa amma tana musu wulaqanci gara ta qara samun ko mutum biyu ne da zata ringa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login