Showing 138001 words to 141000 words out of 429394 words

Chapter 47 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

978

saka mata ciwo kenan ko, jiyan nan naji Salman yana maganar tsakar dare tayi masa magana akan yaje zata aike shi seda Safe yaga saqon ya duba lokaci yake cewa Ashe Umaimah bata dena kaiwa dare tana chatting ba toh Allah ya shirya" tayi masa fatan Alkhairi ya wuce Umaimah dai tunda ta shige daki tayi luf, da mama ta tashi yi mata tsiya wayar gaba daya ta kwace, Mu'ayyad daman suna shiga yara suka dauke shi dan haka tana cin abinci tasha magungunan tana nan zaune shiru Mama nata shige da ficenta kota kanta bata bi ba baccin dole ya dauketa saboda magungunan data sha.

Da suka koma gida kuwa yasha mita yayi mata banza dan kanta tayi shiru, doka ya kafa mata ta bacci qarfe goma kuma ta kashe wayarta ta bashi. Yanda ya hade fuska yana gaya mata dokar dole ta amsa a lokacin dan yanzu lallabashi takeyi bata so nan kusa ace an sake samun wata matsalar musamman da take da buqata a gurinsa so take a kwana biyu komai yayi daidai ta nemi abinda take so.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 37

Motar ya koma yana tunanin wanene wannan din kuma me yake dauka? Ganin bashi da me bashi amsa ya saka ya mayar da hankalinsa kan tuqin da yakeyi yana yi yana lallashin Hadiza dake kuka, har qofar gidansu ya kaita, be barta ta fita ba seda ya tabbatar ta sakko kuma ta dena kukan da takeyi ya lallabeta ya kuma tabbatar mata da In sha Allahu ze aureta amma tayi haquri ta bashi lokaci kuma ta ringa musu Addu'a.

"Ina son Matata sosai bansan ta yanda zan kalleta nace mata zan qara aure ba" ya fada yana kallon Hadizan ta buga masa wata harara tareda jan tsaki kafin ta kama murfin motar ta fice batareda ta tanka masa ba ya rakata da Murmushi, haega Allah yana son Hadiza kodan sanyin Halinta da kulawar da take bashi kuma tafi sonsa akan wanda yake mata yasan zata riritashi ta kiyaye bacin ransa to amma damuwar ta inda ze tunkari ita Uwargidan da wannan magana dan ta Hajiya da duk wani da ze iya kawo cikas me sauqi ne.

Gaba ya danyi ya bar qofar gidan nasu ya samu guri ya tsaya. Jalila ya kira ringing biyu ta daga tana cewa
"Aa Hussaina yau ka tuna dani kenan"
"Dama na taba cewa na manta dake ne?" Ya bata amsa se tayi yar dariya tace
"Toh ai muj sallamawa Maman Mu'ayyad kai, ta tsare gaba ta tsare baya Hajiya kadai ake bawa damar ganinka da magana dakai sanda taso mu kuwa idan mun gaji da neman ka sedai mu kirata mu bada saqo"

"Kina da Matsala Jalila yanzu duk meya kawo wannan qorafin" ya katseta, seta sake cewa
"Gaskiya ce kawai ba qorafi ba gaba daya ka maqalewa Mace baka da lokacin kowa yanzu se nata duk sunkasa fasa maka ne ni kasan bazanyi shiru ba"

Qaramin tsaki yaja yace
"Mutum na cikin wata damuwar zaki zo ki qara masa, kiranki nayi ki bani shawara amma zaki cikamun kunne da mita haba" yanda yayi maganar cikin alamun abu na damunsa ya sakata sassauta murya tace

"Yi haquri toh dan qanina meya faru, wace damuwa kake ciki kuma shawarar me zamuyi?"
"Aure nake so na qara Jalila" ya bata amsa kaitsaye dan bayaso aja maganar se tayi shiru kusan minti daya kafin ta numfasa tace
"Aure Khalil, ka gayawa Hajiya kuma ta yarda?"
"Ban gayawa kowa ba shawararki nake nema me kike gani akai nayi ko Aa?" Ya mayar mata da wata tambayar se Jalila ta ajiye numfashi tace

"Wannan ai ba maganar da kai tsaye zance maka yi ko karkayi bace. Qarin aure yana zuwa ne akan abu biyu, buqatuwar yin hakan ko kuma yazo maka baqatatan daga Allah dukda dukka biyun nufin Allah ne amma kashin farko da niyya kuma mutum yaso yin hakan kai wannene naka a ciki?"

"Nima ban sani ba" bata amsa kamar me shirin fasa kuka, baya so Hadiza ta zarge shi da laifin yaudara dukda wani mummunan abu be taba shiga tsakaninsu ba ze iya cewa ko hannunta be taba ba sedai bisa kuskure amma dukda haka bazeso haqqin Soyayyar da takeyi mishi ya kamashi ba kuma tsoron sa Allah tsoronsa yanda ze tunkari Umaimah musamman da yanzu suke zaune lafiya babu wata matsala a tsakaninsu. Dariyar Jalila ce ta dawo dashi hayyacinsa yaji tana cewa

"Dan qanina maganar nan bata waya bace, ka samu lokaci kazo mu tattauna in fahimceka kafin nasan abin da zan baka shawara akai"
Yayi Na'am da shawararta dan haka yace mata
"Shikenan zanzo, amma dan Allah kar wanda yasan wannan maganar ko da Hajiya ce na gaya miki ban sanar da kowa ba seke, ba kuma naso suji se na gama yanke shawarar yi ko akasin haka"

"Haba kaima kasan babu meji, ko mun taba kashewa mun rufe kaji wani ya tada maganar?"
"Naga kin koyi tsogumi ne yanzu shiyasa musamman tunda kun sakawa Matata ido qila ku kuke ta mata Addu'a har naji abin ya darsu a zuciyata" se Jalila ta saka dariya tana cewa
"Ai ko ace muna da wata matsala da Matarka bazamu goyi bayan haka kawai kayi mata kishiya ba indai ba da wani babban dalili ba ballantana ma babu, ka samu lokacin ka shigo se mutattauna kaji" daga haka sukayi sallama ya tada motar yaci gaba da tafiya.

Office ya koma amma gaba daya ranar be iya gane abinda yakeyi ba dan hankalinsa ya rabu da yawa.
Kwana biyu a tsakani cikin damuwa yayi su, tunanin yanda ze magance Matsalar Hadiza yakeyi gashi tayi fushi koya kirata a waya se taga dama zata dauka har tana cewa ashe yana da lokaci daman niyyar kiranta ne kawai bashi dashi se yanzu se ya ringaji toh kawai ya rabu da ita mana salin alin su rabu ga mafita ya samu amma yana tsoron haqqinta, yasan zafin soyayya tunda yanzu haka cikin karbar gashinta yake idan har haka Hadiza takeji a kansa idan ya barta beyi mata Adalci ba.

Umaimah kanta ta lura da rashin walwalarsa data tambaye shi yace mata bayajin dadi ne ga kuma ayyuka da suka yi masa yawa ta ringa mitar ai shi yake dorawa kansa me yasa duk Architects din da suke a kamfaninsu ace duk wani babban aiki shi ze ringa kula dashi ai se a bawa wasu dama. Sanda take maganar kallonta kawai yayi, shi kam Umaimah ta dena bashi mamaki yanzu dan duk abinda tayi yana tsammanin zatayi wanda ya fishi, yanzu ita ba Jin dadinta bane ace Allah ya daukaka shi cikin daruruwa shi aka zaba Aa mita takeyi akan me yasa akayi hakan toh Allah ya rufa Asiri, shidai Tsuntsun soyayyar sa beyi masa Adalci ba daya rasa inda ze sauka se akan wannan butsuwar yarinyar.

Be samu zama da Jalila ba se bayan sati daya ranar Weekend yacewa Umaimah ta shirya suje gidan dukda yasan ba zuwa zatayi ba latsine, ya rasa me yasa yanzu take ja baya da yan uwan nasa wanda sam farkon auransu ba haka bane sosai suke shiri take daukarsu tamkar su Yaya Naziyya amma tunda ta haihu abubuwa suka chanza, shi kansa gidan Hajiyar da take yawan zuwa ta rage sedai ta kirata a waya su gaisa wannan dai babu fashi kullum ta Allah seta kirata.

Umaimah ko daya gaya mata zasuje din kaitsaye tace bazata ba saboda akwai sunan Mariya maqociyarsu da za'ayi a ranar Amaryace matar qanin Mijin Maman Hibban da sun fara zama a wata unguwa barayi suka damesu shine ya gina filin jikin gidan Maman Hibban din inda sukayi Suna suka tare a anan.
Ya gama shirinsa tsaf ze fita tana zaune a palour kanta ne yake sara mata haka a kwanakin take yawan fama da ciwon kai wani lokacin harda jiri ta gayawa Khalil yace yawan kallon waya da takeyi gashi bata samun isashshen bacci ta raba dare Online su suka saka shiko ya dena mata magana duk yanda tayi daidai ne tunda tana masa abinda yake so idan ta gama can taje ita ta sani.

"Baka bani kudin barka ba toh zaka fita" Umaimah ta fada jin yana mata sallama, se ya kalleta yace
"Kudin barka kuma? Ina kudin da kike kaiwa can gidan duk sati da kikace kuna tarawa ne saboda irin haka idan hidima ta tasowa wani se a bashi a madadin matan unguwa?"

Baki ta tura tace
"Toh ai wancan na gidauniya ne wannan kuma personal ne da zan bata"
"Ai Namiji kika ce ta haifa ki duba cikin rigunanku ki kai mata ko ki dauka a kudin dana baki jiya ni banda kudi yanzu" yana gama fada ya saka kai ya fita yana mamakinta. Jiyan nan dubu talatin ya bata wai zata siyi kayan gyara, sannan duk satin duniya se ya bata dubu biyu ta zubin gidauniya data ce banda idan ya samu kudi haka kawai ma bata yakeyi ko idan zata fita unguwa duk suna ina da seya bata kudin wata barka ai bashi ya aiketa ba.

Da dai Umaimah bazatace ya bata kudi ba duk abinda yaga dama ya bata zata karba tayi godiya wani lokacin har tace ya rage saboda tana tausayinsa amma yanzu ta zama yar fashi daga zaune. Bill ne take masa harda na banza, ana zaune lafiya zata qirqiro abu tace tana so idan yaqiyi kuma ta ringa fushi da baqin rai kenan da mita har se ya mata abinda take so yanzu a ritsin nan Iphone 13 ta saka seda ya siya mata shi yana fama da X tun kafin auransu be chanza ba ita kuwa 12 take riqewa rana daya tace duk qawayenta 13 ce dasu dole ya karbi ta hannunta ya cika aka bata wata.

Umaimah kuwa harara ta rakashi da ita babu arziqin a dawo lafiya tunda ya hanata kudin barka. Shifa yace dan ita yake nema a da tausaya masa takeyi ganin yana da dawainiya dayawa akan sa amma tunda Rufaida ta wayar mata dakai ta dena. Ita ta koya mata dabarun karbar kudi a hannunsa dukda kota karba ba wata tsiyar take dasu ba sedai rantawa qawaye da zubin Adashi se siyi banza siyi wofi abin kirki kadai da zata ce tana siya shine kayan gyaran jiki wannan ko bata wasa dasu dan da jikin take yaqarsa tayi iskancinta son rai kuma taci riba.

Kiran wayarta ne ya dakatar da ita ta janyota, Rufaida ce tana dagawa tace
"Madam kin shirya mu shiga gidan sunan kuwa?"
"Na dauka seda yamma ai" Umaimah ta bata amsa se tace mata
"Aa zamu shiga yanzu mana muga koda abinda zamu kama musu"

"Gaskiya sedai kije ni se zuwa yamma bana jin dadi kaina yana ciwo" Umaiman ta sake fada cikin jimami Rufaidan ta mata sannu tareda cewa bari ta shigo toh. Basufi minti goma da waya ba taji bugun qofa taje ta bude mata ta shigo ta zumbulo Hijabi da gani ko wanka ba tayi ba, seda suka zauna take tambayarta
"megidan baya nan naga babu motarsa".

Baki Umaimah ta tabe tace
"Ya tafi gidan Anty Jalila"
"Kice yau seta Allah ko ba ita ce tazo kwanaki da qanwar Mijinta ba?" Rufaida ta fada tana gyara zama Umaimah ta girgiza kai alamar Aa kafin tace
"Ba ita ba wannan Yan biyunsa ce ba Anty Amina ba ita ce babbarsu"
"Au wai yan biyune, toh Allah ya fishsheki dan kinsan idan ka hadu da yayyen Miji mata se a hankali musamman keda ake ganin kina ciki daula yanzu se kiji zantuka kala kala".

"Uhm" kawai Umaimah tace tayi shiru, hudubar Rufaida ta rigada ta gama tasiri a zuciyarta ita ta nuna mata tunda yayyen Khalil matane bazasu sota tsakani da Allah ba zasu ringa kishi da ita suna ganin Dan uwansu na bauta mata yana mata abinda su basa samu a gidan auransu dalilin da ya saka taja baya dasu dukda ko kallon banza babu wadda ta tabayi mata a cikinsu, yanzu hatta da Habiba da take yar gidanta ta rage kiranta tazo gidan acewar Rufaida zata ringa kwashe sirrinta tana kaiwa gida ita kuma taga hakan ze yuwu.

Nan suka zauna basu shiga gidan sunan ba se bayan la'asar Rufaida ta koma tayo wanka itama ta shirya bayan Hauwa ta dauki Mu'ayyad ta tafi dashi gidansu seda aka yi Isha'i suka baro gidan sunan ta shiga gida har sannan kuma Khalil be dawo ba.

Khalil
Seda ya fara biyawa gidan Abokinsa Mukhtar da yake shirin angwancewa nan da sati uku, fenti akeyi, ya duba masa aikin suka dan taba hira kafin ya wuce gidan Jalila.
Cikin murna ta tareshi dan ya dade rabonsa da gidan nata, ita kadai ya tarar se Almajirinta yana mata wanki a tsakar gida suka shiga ciki ta kawo masa ruwan Lipton da Dumamen tuwo miyar Kuka yaji man shanu.

"Kai amma Allah ya tsundumaki a Aljanna kamar kinsan na kwana biyu banci tuwo ba" ya fada sanda ya bude kwanon.
"Ai tun da kace mun yau da safe zakazo, banyi niyyar tuwo ba jiya saboda kai nayi nace dan qanina nasan ba lallai Maman Mu'ayyad nayin tuwo ba balle ka samu dumame".

Hannunsa ya wanko a Kitchen ya saka tuwon a bowl hade yake da miyar ta dumama irin yanda yake so yayi bismillah ya fara ci ita kuma ta tsiyaya masa baqin shayin daya sha kayan qamshi a kofi.
Seda ya cinye tas yasha shayin yayi hamdala, shi ya kai mata kwanukan kitchen ta rigada tayi wanke wanke dan haka ya dauraye wanda ya bata ya kife mata su a kwandon daya gani cikin sink ya futo da gorar ruwa a hannunsa.

"Ashe dai har yanzu kana aikin gida" ta fada cikin tsokana ya zauna yana murmushi yace
"Nasan mitarki idan na ajiye ban wanke ba har na tafi kina mun surutu"
"Kasan haka muke da Abbansu tun be iya wanke wanke har seda ya saba yanzu da sun bata kwanuka zece a wanke se kaji Zee tana ayi wanke wanke kafin Mama ta fara mita" suka saka dariya gaba daya.

"Ina yaran nema naji gidan shiru" ya tambayeta bayan daya zauna tace
"Kamal da Asiya sun tafi Tahfiz, Nuradden kuma yana Jalingo kasan Hajiya da Didi kuma qanwarsa ta kai su gidan kitso jiya wai sunyi dare suka kwana a gidanta inaga se anjima zata dawo dasu"

"Wai har yanzu Nuraddeen be dawo ku haqura da yaron nan kawai ku bar musu shi mana" Khalil ya fada tayi murmushi tace
"nima haka nace jiya da yake zancen ze kira Hajiyar ya gaya mata an dade da komawa makaranta nace ai sun sani ka barshi kawai yayi zamansa nan da can ai duk daya ne toh kasan shi da qulafucin Yaya bedai ce komai ba kuma be kirata ba yana dai mitar wai Nura nada wasa baya sonkaratu idan ba an takura masa ba acan in ya samu sake sangarcewa zeyi"

"Haka dai ze haqura ya barshi da ya samu kakannin ma masu so su riqe jikan, nan Hajiya data dauko Inteen kina ganin yanda suka qare" Khalil ya fada suka fashe da dariya gaba daya. Seda suka lafa Jalila ta kalle shi tace
"Toh ya ake ciki ranar mun fara magana a waya?"

Tattara hankalinsa yayi akanta yace
"Wato wata yarinya ce muka hadu da ita kin gane, harga Allah tana burgeni kuma ina sonta amma kuma ni banyi tunanin nan kusa zata kawo maganar muyi aure ko wani abu ba kuma ita bala'in sona takeyi, nidai in taqaice miki magana yanzu kinsan dai matsayin da nake ciki a yanzu bazance zanyi aure ba saboda kowa seya tambayeni dalili idan kika duba aurena shekara biyu kwata kwata ni kuma bani da wani dalili me qarfi dazance gashi ya saka zanyi aure".

Shiru Jalila tayi tana kallonsa har ya kai aya kafin taja numfashi tace
"Ita yarinyar yaushe kuka hadu, kuma tsahon wane lokaci kuke tare?"
"Bamu wani dade ba wata uku zuwa hudu kenan da haduwarmu lokacin da naje aiki Lagos din nan, dukda dai mun taba haduwa a nan Kano amma dai Officially mu fara magana da ita yanzu za'ayi 3 months" Khalil ya bata amsa tayi shiru tana kallonsa, so takeyi tace masa lokacin da Umaimah taqi binsa Lagos kenan kuma ta tambayeshi wace irin alaqa ce tsakaninsu dukda bata zargin qanin nata amma tasan abinda Umaiman tayi masa yana iya sakawa shedan ya zugashi ya fada abinda ba halinsa ba. Itama ta samu labarin ne a bakin Khalifa kuma ya roqeta akan dan Allah karta gayawa Kowa dan Yaya Khalil yaja masa kunne kawai ya kasa hadiye maganar ne yasa ya gaya mata dan ita ana sirri da ita ba irin su Yaya Jamila faransai bace.

"Kinyi shiru kina kallona kamar wanda nayi miki qarya" Khalil ya fada se tayi murmushi tace
"So nake na auna soyayyar da kakeyi mata da irin wadda na gani a idonka sanda kake gaya mun ka hadu da Umaimah"

"Babu hadi Jalila babu macen da zata kamo qafar Umaimah a zuciyata" Khalil yayi saurin tareta a zuciyarta tace
"Ta gano lagon ka shiyasa take garaka kamar kwallo a fili kuwa seta gyara zamanta tace
"Toh tanada wannan matsayin ya akayi har idonka ya iya hange hange ka samo wata ka fara so, kuma a yanda kake jaddada soyayyar nan tata ace a ayan shekarun nan zaka mata kishiya Khalil?
Idan har da gaske ka daukeni yar uwar da zamu kashe mu rufe ka gaya mun gaskiyar meye damuwarka, meye dalilinka na son qara aure? Ni kuma zanyi maka hukunci bisa adalci in sha Allah dan bazan so ka tauye kanka ba haka itama Umaimah bazan bi bayanka kayi mata rashin Adalci idan har ya zamana son ranka ne kawai".

Shiru Khalil yayi yana nanawa maganarta a zuciyarsa, yanada yaqinin Jalila zata riqe masa sirri idan ya gaya mata amma yana tsoron ta farayiwa Umaimah wani kallo na daban a matsayin me musgunawa dan uwanta, yasan zata qullaceta dan Jalilan nason duk abinda yake so tana kuma qin abinda yake bata masa.

"Kayi shiru dan qanina ko da akwai matsala ne" ta fada cikin tsokana ya dago ya harareta tayi dariya tace
"Sarkin son girma duk tsiyarka dai minti biyar ba wasa bace" dole yayi murmushin shima ta sake cewa
"Yawwa ina jinka kayi magana mu samu mu san ta inda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login