Showing 327001 words to 330000 words out of 429394 words

Chapter 110 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1029

har sannan, a bakin Sammani da sukaje kai abincin dare yaji cewar Ankawo Amaryar. Seda Mama ta matsa masa kafin ya bisu gida suka koma tareda Khalifa da Sammani.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 72

Ko minti goma Khalil beyi da fita Abba da Anty suka isa Asibitin. Abban ya tsaya akanta yana kallo ta kafin juya yana tambayar Mama har yanzu bata farka ba Maman ta sauke numfashi tace
"Bata farka na Alhaji amma sunce da vi gaba tunda gashi numfashinta ya daidaita sun cire mata Oxygen bacci takeyi kowanne lokaci kuma zata iya farkawa"
"Toh Allah ya tashi kafadunta ya kuma sanyaya mata zuciyarta ta karbi qaddara a yanda tazo mata tunda me afkuwa ta rigada ta afku yanzu haka yarinyar ma tana cikin gidan, ni ina ganin koda ace an sallameta daga nanzamu wuce da ita can gidane zuwa wani lokaci seta koma, Allah dai ya qara rufa Asiri". Haka suka ci gaba da zama a Asibitin basu ankare da lokaci ba se gani sukayi sha biyu tayi, Abba da Anty suka tafi gida suka bar Mama da take kwana da ita kafin ya tafi seda ya sake magana da Likita ya tabbatar masa da komai lafiya sannan idan bata farka zuwa Safiya ba zasu farkar da ita da kansu.

A hankali ta sauke dogon numfashin data riqe tun zuwan su Abban ta farka daga baccin wahalar da take tayi tun jiya tana farkawa kuma duk abinda ua faru ya dawo mata a kwakwalwa tamkar a lokacin yake faruwa. Hirar da Abba da Maman sukayi kaf a kunnenta, sanda taji yana gaya mata Amarya ta tare seda tayi da gaske kafin ta hana kanta fasa Ihun da ze sa susan idonta biyu, taci gaba da kwanciya tana saqe saqen abinda ya kamata tayi a zuciyarta, a haka Nurse did da take dybata ta shiga ta sake mayar mata da ruwan da ta cire mata dazu ba tareda tayi aune ba bacci ya sake awon gaba da ita.

KHALIL
Cikin mutuwar jiki ya shiga bangarensu, Dakin Humaira ya fara shiga an guara shi tsaf dan tunda safe ya saka su Sammani suka gyara aka kwashe duk abinda ya lalace a ciki kijerunta kadai ta tsira dasu baya ga haka babu wani abu da ze moru a kayan falon sedai ko Carpet idan an wanke shi. Seda ya gama duba gurin kafin ya kulle ya wuce Dakinsa. Wanka ya shiga, ya dade yana wankan shikansa bazece ga dalilin wannan wankan da ya zauna ya ringa dirje jiki kamar wanda ya shekara beyi ba. Kansa ya kalla a Mudubi yaso ace yayi Aski jiya se kuma wannan tashin hankalin ya bullo.

Haka ya fito ya shafa mai da turaruka a jikinsa gaba daya a sanyaye yakeyin komai. A gurin zabar kayan da ze saka ma seda ya bata lokaci, Sky blue sabuwa ce be taba sakata ba ya zura kayan sun zauna masa a jikinsa irin dinkunan da Umaimah take so Abuja style Riga Jumper me gajeran hannu kayan sunyi matuqar yi masa kyau kamar a jikinsa aka dinka su. Seda ya sake feshe Jikinsa da turaruka ya dakko Hular data dace da kayan ya kafa ya daura Agogo, harya zura takalmi ze fita se kuma ya dawo da baya. Wardrobe ya bude ya dakko sabon Bedsheet babba dan Turkey, Umaimah ce ta siya masa da kudi bata taba shimfida musu ba ya cire wanda yake kan gadon ya mayar da sabon, seda ya sake bin dakin ya kawar da duk wani abu da ba'a muhallinsa yake ba dukda babu tarkace a dakin saboda shi baya ajiye kaya a ko ina duk abinda yayi amfani dashi ya gama ze mayar dashi gurin zamansa, ya jona Bunner ya zuba turaren wuta sannanya saisaita sanyin Ac daya kunna kafinya kashe fitila ya fice daga dakin.

Missed calls din Hajiya ya gani a wayarsa dana Anty Amina, qarfe goma da minti biyar ya ringa mamakin lokacin daya bata dan haka cikin hanzari ya tafi bangaren Hajiyar dan yaji kiran da take masa. A bakin qofa suka hadu da yan uwansa da alama tafiya zasuyi. Jalilah ta dauke kai tayi gaba Anty Amina ma fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar da yayi musu kafin tace
"Ai mun zata can zaka kwana tun dazu ake kiranka ga yarinyar mutane can ka barta ita kadai".

Kansa ya sosa ba tareda yace mata komai ba Jamila ce ta dan saki fuska tace
"Zaka sha rarrashi yau dan Amaryar nan taka da gani rigimammiya ce tana can ko ruwa taqi sha tunda aka kawota, na aiki Khalifa dai ya siyo muku dan abinda zaku buqata dan nasan dakyar in kayi tunanin nemo mata abinda zataci"

"Backs yar uwata you are the best" ya fada yana rungumeta ta gefe Jamila ta tureshi tana dariya tace
"Toh Allah bamu Alkhairi", a fusace Jalilah da har tayi nisa ta dawo tana kallon tace
"Idan ba zaki tafi bane muyi gaba kin zauna kina bata wa mutane lokaci da wanda basu san darajar kansu ba, be tanka mata ba kamar yanda itama Jamilan binta kawai tayi yasan jarabar Jalilah yanzu se a shekara tana wannan fushin to shi dan Allah meye laifin sa a nan? Idan bata tausaya masa ba ai be kamata ta qullaceshi ba.

Da sallama ya shiga falon Hajiyar suna zaune ita da qanwarta Hajiya Maimuna Mamansu Lubna suka amsa masa a tare ya samu guri a qasa ya zauna yana gaishe su suka amsa gaba daya tareda tambayarsa yame jiki se ga Khalifa ya shigo da manyan Ledoji guda biyu ya kalli Khalil yace
"Yaya gashi Anty Jamila tace na siyo"
Ba tareda ya kalli Khalifan ba yace
"Ka shiga dasu can gurin" se Khalifan ya juya ya fita.

Bayan yar gajeriyar Nasiha da Hajiya da yar uwarta suka sakeyi masa Hajiya Maimuna ta miqe tana cewa
"Yaya bari naje dare na qarayi"
"Mama ina kuma zakije a daren nan?" Khalil ya fada yana kallonta seta yafa mayafinta tace
"Gidan Alqasin zanje na gaji da ciwon bakin da yake muk akan duk sanda nazo Kano ina kwana gidan kowa banda nasa yau can zan kwana gobe in Allahya kaimu muyi Asubanci mu koma gida kuma mu huta haka"

"To bari nazo na kaiki" ya fada yana miqewa se tayo saurin dakatar dashi ta riqe baki tace
"Waya isa ya fitar da Ango a daren nan? Kaga tafi ka rarraso Amaryarka tana ciki tana kuka kaga ni Khalifa na can waje yana jirana shi ze saukeni daman su Lubna sunyi gaba tun dazu" daga haka tayi gaba Hajiya ta miqe danta rakata.

Har Hajiya ta dawo daga rakiyar yar uwarta Khalil na zaune inda yake, so yakeyi yaje yaga Humaira hankalinsa gaba daya ya koma kanta tun jiya rabon dayaji saga gareta gashi yanzu ance Kuka takeyi.
"Babana kana zaune ka tashi ka hau Saman ka sameta mana tana nan a dakina" Hajiya data dawo ta fada seya miqe yana sunkuyar da kai kamar wanda yake gaban surukai ya haye saman. A hankali ya tura qofar dakin Hajiya ya tsaya yana kallonta tana zaune a qasa ta sunkuyar da kai Habiba na tsugunne gabanta da Kofi fuskarta ta nuna damuwa yana jinta tana ce mata
"Dan Allah ki dena kukan haka kisha ko madarar nan ce tunda kinqi cin Abinci, kona kira miki Yaya?"

Qarasa shiga cikin dakin yayi da sallama qasa qasa Habiba ta amsa da sauri tana cewa
"Yawwa ga Yayan ma yazo" ta miqe tsaye tana gaishe shi ya amsa mata idanunsa akan Humaira data sake curewa guri daya saboda shigowar tasa. Habiba ta sake shagwabe fuska tace
"Yaya taqi cin abinci tunda aka kawota take kuka duk su Anty sunyi sunyi taqi haquri kuma komai aka bata taqi taci"

"Jeki abinki zataci" ya fada yana qarasawa inda take se Habiban ta ajiye kofin hannunta akan Bedside drawer ta fita daga dakin ta kulle musu qofa. Seda yaga fitar Habiban kafin ya qarasa a hankali ya durqusa a gabant, a sanyaye ya kira sunanta bata dago ba haka bata fasa kukan da takeyi ba sema qara masa qarfi da tayi. Khalil ya saki murmushi kafin ya janyota gaba daya ta fada jikinsa yana cewa
"Na sani nayi laifi amma ayi mun afuwa kiyi shiru yanzu i promise an jima zan rarrasheki har se kince kin haqura kinji".

Banza ta masa tana ci gaba da shashsheqar kukanta, ya janye mayafin data rufe fuskarta dashi kyakykyawar farar fuskarta me cike da quruciya ta bayyana, se yaga ta qara masa kyau ya saka hannu yana share mata hawaye yace
"Kin gani har idonki sun kumbura ki bari haka mana kuma kar kanki yazo yana ciwo". Rarrashinta ya ringayi ganin bata da alamar barin kukan dan idan tayi shiru kome take tunawa se ta sake fashewa da kukan dan haka ya miqe bayan ya maida ita kan Gadon Hajiya ta zauna yace yana zuwa. A qaramin falon dake sama ya samu Hajiya a zaune ta zabga tagumi, ta kalleshi tace
"Ya dai Babana"
"Hajiya taqi dena kukan" ya fada a hankali kamar shima zeyi kukan abin nasa ma ya bawa Hajiya dariya har seda ta murmusa kafin tace
"Toh ai se ka dauketa ku tafi can kayita rarrashi aiki ya sameka, Amina tace an gyara gurin nata ko dazu sun shiga se kayi qoqari a maida mata da abubuwan da suka baci kafin yan uwanta su fara zuwa ganin guri dukda dai dazu dasu Maimuna sukaje dakkota sun sanarwa da Hauwan komai kuma Alhamdulillahi ta fahimta daman kuma nasan ba za'a samu matsala da ita ba, ina fatan kuma Allah ya tsayar da rigimar haka. Allah yayi muku Albarka ya baku zaman lafiya kai kuma ina sakeyi maka addu'a Allah ya qara maka juriya ya kuma baka ikon yin Adalci a tsakaninsu, kuje ta samu ta huta nima magani na zansha na kwanta kaina yana ciwo"

"Hajiya ki cire duk wata damuwa daga ranki kodan saboda lafiyarki in sha Allahu babu abinda ze sake faruwa" Khalil ya fada a sanyaye se Hajiya ta sakeyi murmushi tace
"In sha Allah, ka kira ku tafi kar kazar tata tayi sanyi" sosa kansa yayi shima yana murmushi ya juya ya koma dakin. Tana nan inda ya barta ta dai yi shiru tana jan ajiyar zuciya ya qarasa ya kamo hannunta yana cewa
"Let's go wife"
"Ina?" Ta tambayeshi cikin muryar kuka seya miqar da ita tsaye yana cewa
"Gidanmu mana ko a nan kike so ki zauna?"
"Ni gidan Mama zan koma" ta sake fada tana shirin fashe masa da kuka yayi saurin cewa
"Muje na mayar dake shikenan" ta daga masa kai. Hannunsa cikin nata suka fita, a falon qasa suka tarar da Hajiya da Habiba harda Khalifa daya dawo daga kai Hajiya Maimuna dan babu nisa sosai.

Har qasa Humairan ta tsugunna tana yiwa Hajiya sallama ta dagota jikinta tana saka mata albarka tareda sake maimaita mata tayi haquri, Habiba ta rakasu har bakin qofar shigowa part din tana cewa Khalil
"Yaya bata ci abinci bafa"
"Kin fada mun Habiba zataci kinji" ya mayar mata yana murmushi itama tayi murmushi, sosai Humairan ta shiga ranta dukda ta dan girmeta amma ta samu qawa.

Humaira dai binsa takeyi ganin suna shirin shiga wani gidan a maimakon mota ta tirje ya juya ya kalleta ta fara qifta ido alamar zata ci gaba da kukan tana cewa
"Kace gida zaka mayar dani kuma naga zamu shiga wani gurin"
"To ai key din mota zan dakko ko a qafa kike so muje?" Ya bata amsa seta girgiza masa kai yace
"Good girl" kafin ya bude musu qofar falon suka shiga. Daga bakin qofar ta tsaya tana zare ido, Khalil ya kalleta yanda takeyi ya bashi dariya kamar wadda aka sato, ciki yayi ya barta tana rarraba ido se gani tayi hasken falonya dauke ba shiri ta fasa ihu tayi ciki da gudu inda taga yabi, Khalil daya kashe hasken yayi saurin kunna fitilar wayarsa yabi bayanta gudun karta bige da wani abun ta fadi tana ganinsa ta rungumeshi jikinta na rawa tace
"An dauke wuta"

"Anya kodai bulb din ne suka mutu kinga waje can da haske" wajen ta kalla kafin ta kalleshi ya saketa yana cewa
"Jirani Bari na dakko key din" bata ko kulashi ba yana daga qafa ta bishi, a tare suka hau saman tana riqe da hannunsa data qi saki suna shiga ya mayar da qofar falon Saman ya kulle ya murza key kafin ya zare ya jefa a aljihunsa seta saki hannunsa da sauri ta shiga buga qafa tana yarfe hannu, Khalil kuwa kasa riqe dariya yayi ganin abinda takeyi din ya wuce daki yana cewa
"Yarinya keda gidab Mama ai se dai idan gaisheta kika je yi".

Kuka riris ta zauna tanayi Khalil daya fito ya bude baki yana kallonta a ransa yace
"Ikon Allah" a fili kuwa ya qarasa kusada ita ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ya zauna tareda cire hularsa ya dagata cak ya dorata akan cinyarsa, qoqarin sauka ta shigayi ya saka hannu daya ya riqe fuskarta ta gane me yake sonyi dan haka tayi saurin damtse bakinta amma ina seda ya samu nasarar shigar da harshen sa cikin bakinta ya shiga nanata mata karatun data rigada ta haddace dan tun ranar da aka daura musu aure yake biya mata. Seda tayi laqwas daman tuni Kuka ya kama gabansa kafin ya saketa yana sauke numfashi a hankali kamar yanda ta lafe a jikinsa itama taana sauke numfashin.

Wayar sa tayi qara ya janyota ganin Khalifa ne yake kira ya amsa, da "ok" ya amsa abinda ya ce masa kafin ya maida wayar ya ajiye ya kalleta fuskarsa dauke murmushi yace
"Bari na dakko Miki Akwatinki a qasa se nazo na baki Abinci sabuwar qawarki nata nanata mun baki ci komai ba" ya sauketa ya miqe se itama ta miqe jikinta duk yayi sanyi tabi bayansa suka sauka qasan tare. Akwatunanta saiti daya ya gani a nan cikin falon ya dauki babbar ta kama qaramar ciki zata dauka yayi saurin tareta yana cewa
"Aa ban sakaki ba karki wahalar mun da jikinki" ya wuce sama ita kuma ta tsaya tana qarewa falon kallo yayi mata kyau sosai a ranta tana tunanin falon waye nan na sane kenan ko. Seda ya gama hawa da akwatunan kafin ya shiga kitchen ya dakko Abubuwan da zasuyi amfani dashi ta karbi wasu ta riqe masa suka hau Saman.

Cikin tattali da kulawa ya ringa ciyar da ita wani hadadden dankali da Khalifan ya siyo bayan ya dumama mata a microwave dake nan saman kazar kadan taci, seda ya tabbatar ta qoshi kafin ya cika mata Cup da tatacciyar madara me sanyi yace tasha sannan ya fara ciyar da nasa cikin seda ya qoshi shima kafin suka tattara komai suka sake sauka qasa dashi a sannan ta shiga kitchen din tabi ko ina da kallo dukda komai a tsaftace yake amma ta gane ba nata bane tunda beyi kala da sabo ba kenan nan kitchen din matarsa ne gabata ya yanke ya fadi data tuna Umaimah da kashedinta se ta matsa kusa dashi qasa qasa muryar ta na nuna alamun tsorata tace
"Tana ina?"
"Wa?" Ya waiwaya ya kalleta se tayi farfar da ido tace
"Matarka mana"
"Yanzu saboda matar tawa duk kika firgice haka kina shirin yin kuka toh tana dakinta yanzu zamu shiga ku gaisa".

Gwalo ido tayi Khalil ya fashe da dariya kafin yaja hancinta yace
"Matsoraciya kwantar da hankalinki bata nan tana Asibiti CS za'ayi mata gobe"
"Wayyo daman ciki ne da ita Allah ya raba lafiya toh" ta fada cikin jimami a ranta tana mamakinsa, yanzu matarsa na Asibiti zata haihu amma shi yana gida da wata matar lallai Namiji. Seda ya kashe fitulun kitchen din dana falon gaba daya kafin suka haye saman tana sake ce masa
"Ita a qasa take zama kenan?"
"Eh duka qasa da nan saman nata ne, ke ga bangarenki can" ya nuna mata qofarta tana cewa
"Key din ne ya fadi se gobe da safe zan saka a yanko wani".

Seda suka shiga falon ya lura da yanda tayi kicin kicin da fuska kamar zata fasa ihu ya janyota jikinsa yana cewa
"Meya faru kuma?"
Se hawaye sha ta shiga cewa
"Shine zaka kawoni dakin matarka da kasan ka yarda key din da ba seka bari se gobe idan an bude qofar a kawoni ba kawai dan ka nuna mun iyakata zaka kawoni dakin wata"

"Haba mana Baby meye abun nuna iyaka anan? Kema kinsan bazan iya qara wani kwana ba tareda ke ba you have no idea irin wahalar dana sha daga sanda nasan kin zama mallakina kullum na kwanta se nayi mafarkinki kuma ai dazu key din ya fadi fa bayan ma an kawoki ne inaga and nan ai daman falona ne ga Master Bedroom nan wancan ne dakinta kema ga extra room nan seki dauka shikenan kowa tana da daki a bangarena ko" Khalil ya fada yana goge mata hawayen seta saka kanta a qirjinsa tana cewa
"Ni bana so ai kai kace duka saman nan nata ne kuma ni gaskiya a fitar mun da staircase ta wani gurin yanda ba se na ringa shigo mata falo ba idan zan hau sama"
"An gama ranki ya dade ai bama dadewa zakiyi a nan ba da an gama gyara miki gidanki zaki koma can ki zuba iko son ranki Madam Kishi" Khalil ya fada yana jan hancinta, qara boye fuskarta tayi tana murmushi, tafiya ya shigayi da ita a jikinsa har suka shiga MasterBedroom din, qamshi da sanyin dakin suka sakata sakin Ajiyar zuciya kafin ta daga kanta tana kallon dakin, da zuciya daya tace
"Gidan nan yana da kyau and komai na ciki ya dace dashi"
"Nasan naki se yafi wannan ma haduwa" ya bata amsa yana sakinta daga jikinsa.

Agogonsa yaje ya cire akan mirrow ya kalleta yace
"Kije kiyi wanka ki kwanta dare yayi fa it's almost twelve" yana gama fada ya wuce cikin closet dinsa ya bude wata drawer ya ciro sabon towel fari ya miqa mata ta karbi kafin ta wuce inda ya aje mata akwatunanta ta dauki qaramar ciki ta kwantar da ita akan gadon ta bude. Ita kadai tasan yanda qirjinta yake lugude daurwa kawai takeyi saboda hudubar su Anty Unaiza da suka ce ta daure duk abinda zezo mata dashi kartaqi, a irin wannan ranar mace take qara kafa kanta azuciyar Mijinta haka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login