Showing 90001 words to 93000 words out of 429394 words

Chapter 31 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

995

da sukayi a company Umaimah kuwa ta saka a ranta saboda gudun jidalinta ya saka shi qin komawa gidan da wuri.

Tana zaune a palour ya shiga da sallama ta amsa ciki ciki tareda yi masa sannu da zuwa ya amsa yana qarawa inda take bayan ya ajiye ledojin daya shiga dasu yana tambayarta ya jikinta, fuska ta yamutsa batace komai ba, ya wuce dakinsa yayi wanka dan ya rigada yayi Magriba kafin ya shigo ya dawo palour ya zauna yana janta da hira gimbiyar se cika take tana batsewa Ledojin daya ajiye ma suna nan babu wanda ta taba se shine ya janyo su ya fitar dana abinci ya ajiye a gabanta ya dauki nasa ya bude ya fara ci.

"Ki duba waccen Ledar wasu dogayen riguna ne aka kawo talla Office dinmu na daukar miki naga yanzu kinfi jin dadinsu" ya fada yana nuna mata wata leda me dan girma, a ciki tace masa ta gode bata tashi ta dauki kayan ba se yaji ba dadi dan ya saba idan ya siyo mata abu komai qanqantarsa zata karba tayi murna tareda godiya, be sake magana ba yaci gana da cin abincinsa yana gamawa aka kira Isha ya tashi ya fita.

Janyo ledar tayi ta bude, irin Egyptian silk gowns din nan ne masu aiki a jiki guda hudu kowacce kalarta daban ta tabe baki ta mayar cikin ledar dan sam ita basu burgeta ba, asalima da irin rigunan baccin yan saudiyyan nan sukayi mata kama na gumama ta miqe da ledar ta shige daki ta watsa ta cikin wardrobe dan bata jin zata saka su ma seta wuce ta dauro alwala itama ta tayar da sallah.

Be gaji ba bayan ya dawo haka ya ringa janta da hira yana lallaba abarsa dan shiya kaita aka daketa yasan yayi laifi dole ya nemi shiri tana ta basarwa hardai ta fara sakkowa tana amsa masa hirar kadan kadan, wani abokinsa ya kirashi a waya bayan sun gaisa yake gaya masa Gwal ya sauka dan tun farkon auransu yayi masa maganar yana so ya siyawa Umaiman Sarqa yace ya bari Dala ta dan sakko tunda ana saka ran saukarta, farashin ya tambaye shi ya gaya masa yace ya hau whatsapp suyi magana.

Designs yace ya turo masa na sarqa da dan kunne da zobe da suka kai nauyin Gram Ashirin zuwa da biyar haka, ya turo masa su masu kyau seya miqawa Umaimah wayar yace

"Duba mun wacce tafi kyau a nan" ta karba ta shiga dubawa, wata ta zaba ta miqa masa tana cewa
"Idan ni zaka siyawa ma karka wahalar da kanka dan wadanda nake dasu ma ba sakawa nake ba bana son sarqa qara dan kunne da zobe da awarwaro sarqa damuna takeyi kuma ni wannan Indian design din ma ba wani burgeni suke ba".

Wani iri yaji toh wai duk cikin fushin da takeyi ne ya saka take gwasale duk abinda yayi mata ko kuwa daman haka halinta yake? Amma da ai ba haka take ba kai shifa lamarin Umaimah yana cakar masa da kai wani lokacin.

Badan ya rigada yayi niyya ba da fasawa zeyi dan bega alamar idan ya siya din ma zata yaba ba amma badan halinta zeyi ba dan idan yace ze biyewa halin Umaimah abinci baze bata a gidannan ba dan ko tayi masa abin arziqi yaji dadi ya bata tukuici seta zobe ladanta dana tsiya harda qari. Wayar ya karba ya cewa Abokin nasa ya fasa sarqa ya samo masa dan kunne me kyau kawai babba da awarwaro da zobe, sukayi lissafi aka hada masa seda ya kai Gram Talatin akan dubu talatin da uku take yayi transfer kudinsa 1M yace ya siyawa yara alawa da dubu goman da safw zeje ya karba, daya tambayeshi sunan da ze rubuta a Receipt yace ya saka Umaimah Sabo dan kyautace ya siya mata halak malaj nata ne tayi duk yanda taso dashi.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 26


Zama yayi dadi tsakanin Mutuniyar ta sakko shi kuwa yana ta faman hidima da ita, kwana biyu? tsakani ya karbo mata dan kunnen daya siya.
"Wato abokina kana ji da Amaryar nan taka gaskiya a zamanin nan ka zare Miliyan a tashi daya ka se mata Dan kunne, koda yake qila kaja kaya da yawa ka samu wata kwangila me zafi ne ko" Abokin nasa ya fada yana miqa masa Dan Akwatin da suke ciki.

Murmushi Khalil yayi ya karba ya na dubawa yace
"Toh Bashir meye amfanin arziqi idan bazaka wadata iyakinka ba? Nifa ka ganni bazan sha wahala na nemi kudi dan na tarasu ba ba gara mu kashe su muji dadi dan idan ka tara ka mutu be zama lallai iyalan naka ma su mora ba. Kana kallo dai mu da aka mutu aka bar mana tarin dukiyar wasu suka danne suka cinye komai amma kaga ko a jikin mu dan tun yana raye babu abinda muka nema muka rasa yayi mana duk abinda ya kamata yanzu kuma da baya nan mun tashi muna neman Rabon mu shine shari'ar gaskiya ka mori arziqinka kaji dadi"

"Gaskiya ne mutumina toh Allah ya qara rufa mana Asiri duniya da lahira" Bashir ya fada Khalil ya amsa da Amin kafin ya nuna masa wasu zobuna yace ya miqa masa. Guda biyu ya cira yace
"Zasuyi kyau a hannun Hajiyata nawa suke ko bashi ne na karba"

"Kai Alajin Allah" Bashir ya fada yana dora su a abin awo, ya auna ya buga lissafin ya nuna masa, bashida isassun kudin da zasu kai ya karbi biyun seya ajiye qaramin ciki yana cewa
"Kudi bazasu isa ba bari na dauki wannan idan an kwana biyu na samu sarari sena qara mata"

"Ka dauka kawai babu damuwa duk sanda Allah ya hore seka bani ai ana tare" Bashir ya fada yana saka masa su a mazubi se Khalil yace

"Aa bana son bashi ka sani idan ina dashi zanyi abu idan babu a haqura kuma na san sana'ar ku babu bashi kaga bazan saka kayi abinda baka yi ba"
"Haba Bayero yanzu ko kyauta na baka ai ban fadi ba dan Alkhairin da kayi mun a rayuwa bazan taba biyanka ba, kaje dasu duk sanda ka samu ka bani" da haka ya saka shi dole ya karbi zobunan ya hada dana Umaimah ya wuce gidan Hajiyarsa.

Bayan sun gaisa ya ajiye mata kayan a gabanta ta bude tana cewa
"Wai wai zankadi Babana wadannan fa?"

"Kudin aikin da nayi a Kaduna kwanaki ne aka biyani, kin tuna daman nace miki idan na samu sarari zan siyawa Umaimah sarqa shine naga wadannan zobunan zasuyi miki kyau na taho miki dasu" ya qarasa yana ware mata natan. Seta dauka ta zura a hannunta tana cewa

"Kai amma mungode kwarai Allah ya qara budi na Alkhairi amma biyu sunyi yawa Babana ina laifin daya ni yanzu ma da tsufa ya kamani kwalliyar ma bayi nakeyi ba kana kallo nawa duk su Jalila sun are amma wannan dai zan barshi a hannuna wannan kuma ka qarawa Umaiman tayi ta cancada maka kwalliya"

"Aa Hajiya ke na siyawa itama ai ga nata nan"
"Hajiya idan bakya so ni ki bani dan Allah" Habiba da ta fito daga kitchen tayi caraf ta fada, Khalil ya maka mata harara yace
"Seki kwata ai"
"Kai Yaya Khalil dan Allah" Habiban ta marairaice fuska, seya dauke kai bece mata komai ba Hajiya tace

"Kyaleshi kinji auta zan ringa baki aro" seta taho da sauri tana cewa
"Yawwa bari na gwada yanzu ma Hajiya" ta karba ta saka a hannunta tana juyawa Hajiyan na mata dariya, sama tayi da gudu wai zata dakko wayarta ta dauki Hoto se Hajiya ta mayar da hankalinta kan Khalil dake dannan waya tace

"Amma Babana dawainiyar nan batayi yawa ba kuwa? Kaga yanzu akwai nauyin iyali a kanka dole seka daidaita abubuwa fa da yanda kake kashe Kudi, jiya Jamila take gaya mun ka tura mata da kudi tayi jari, ba'ayi sati ba ka biya kudin makarantar Khalifa ba yanda Kawunku beyi ba akan ka bari kaqi yanzu kuma yau ga zobuna har biyu ya kamata a rage kashe kashen kudin nan a fara tanadi, yanzu nan da yan watanni za'a samu qaruwa ya kamata ace ka fara himmar ginin filinka saboda can din dan lokaci kadan zeyi muku kadan ya kamata ku samu inda ya fishi wadata"

"In sha Allahu hajiya hidimomi kuma ai haqqinane dukka gaba daya babu wanda be zama dole ba tunda Allah ya hore za'ayi kedai kici gaba dayi mana addu'a kawai amma akwai haske sosai abubuwan Alkhairi suna ta samuwa dan yanzu haka akwai kwangilar da muke nema A Abuja, idan ta tabbata abubuwa zasu qara chanzawa in sha Allah" Khalil ya fada, se Hajiya tace

"Toh Allah ya qara rufa asiri ya tsareka daga sharrin mahassada, na saka Malam Babba ma yayo maka rubutun tsari da baki dan dole kana buqatar dafa'i"

"Ga babban dafa'i nan addu'ar da kike mun ba dare babu rana ai kici gaba dayi kawai Hajiyata itace fitila duk tsananin duhu tana haska mun na samu hanya" ya fada a fili a zuciyarsa yace
"Ga kuma dayan hasken tawa yar rigima, tunda na hadu da ita nake ganin nasara a rayuwata, Allah ya bar min ita ya chanza mun halinta". Hira suka ci gaba dayi ta tambayi shi watan haihuwar Umaiman ya gaya mata zuwa wani lokaci yayi mata sallama ya tafi gida.

Be bawa Umaimah nata a ranar ba se bayan kwana biyu da daddare suna zaune ya gaya mata inda ya ajiye yace ta dakko masa, seda ta bude akwatin taga meye a cikin kafin ta kai masan, receipt din da ta gani ta duba ta fasa ihu ganin kudin jiki ga kuma sunanta se a sannan ta fahimci gold ne na gaske ba Indian design yanda tayi tunani ba sanda yace ta zabi wadancan, data sani me sarqar ta dauka amma wannan dinma sunyi kyau sosai tayi murna dan ta dade tana son a siya mata zinare ko iya zobe ne amma Mama taqi kuma duk yayyenta babu wanda Maman bata siyawa masa ba lokacin auransa dan har harda Nuratu akace wai ba'a zata tare za'a hada auransu ba shiyasa kuma dai tasan kawai da ke ita ba'a sonta ne shiyasa ba'a sai mata ba.

Washe garin daya bata kuwa da sassafe ze fita aiki ta bishi ya sauketa a gida dan ta nuna musu.
"Nima dai nayi Zinare irin na mata, me sona na gaske ya siyamun kuma dukda bansan kudinsa ba nasan duk yafi na sauran" ta fada tana juya ido, Mama ta kalleta ta girgiza kai kawai tana murmushi tace

"Toh ai shikenan kinga kudina ya huta dan daman inata Adashe inaso kafin Allah ya saukeki lafiya Abban ku ya cika a siya miki sarqar toh Khalil ya fanshenu se na qara jari da kudina kawai" Maman ta bata amsa tana moqawa Anty da tayi dariya tace

"A haba dai ai haqqin tane idan ma baza'a siya ba se a bata kudinta gara ma dai a siya miki ki qara kadara ce bata yawa, Ina kwadon sarqar, ko kon baro shi gida a garin zumudi?"

"Abinda nake shirin fada kenan ko kuma ta yar ba da shegen rawar kanta, ni ai tuntuni tsoron Asara yake daqileni da siyawa Umaimah Zinare, tana iya zuwa ta yardashi ko ta kyautar tunda ba hankali ta cika ba" Mama ta fada se Umaimah ta yatsina fuska tace

"Ni ba yarwa nayi ba ni nace bana son sarqa cimun wuya takeyi"
"Allah ya yaye miki wauta dai Umaimah, kuma a gidan ubanwa sarqa take ci miki wuya" Mama ta fada se Anty tayi dariya tace

"Umaimah rikici ai kuwa kwalliya bata cika idan babu sarqa musamman irin wuyanki Masha Allah baki ga yanda take miki kyau ba amma ace irin wannan saiti har saiti babu sarqa ai kinyi wauta".

Zumbura baki tayi tana hararar Antyn a fakaice jin tana cewa
"Badan ba ai seki koma ki lashe Amanki kice masa kinason sarqar"

"Tab saboda zubar da kai wannan din ma ai ba roqarsa nayi ba" ta bata amsa tana juya ido Mama ta kai mata duka da mafici tana cewa
"Laure (qanwar Maman ce) kika juyawa ido ba ita ba mara kunyar banza kawai" Umaimah ta goce tana cewa

"Haba Mama nifa yanzu na wuce duka bakuga abinda yake jikina bane? Haka fa Yaya Aminu daga zuwa gidansa ya rufeni da duka kamar..." Seta rufe baki jin tayi subul kalam, Mama ta kalleta tace
"Uhm kamar me, Me ma kikayi da Aminu ze dakeki halan wata ta'asar kikayiwa Khalil din ya kai masa qararki ko?"

"Aa fa Mama mantawa nayi ba haka zan ce ba" Umaimah ta marairaice dukda ta rigada ta kwafsa yanzu se Mama tabi diddigin abinda ya faru idan ya gaya mata kuwa ai ta shiga uku da fada da mita ita wane shegen surutu nema ya kaita taso da maganar?
"Kyaci ubanki kuwa Aminun ze zo zanji koma menene ya faru" Mama ta sake fada daga nan suka ci gaba da hirarsu, se yamma lis Khalil ya dauketa bayan da yaci abinci Anty ta juye mata tuwon Masara da miyar busashshiyar kubewar da tace tana so ta tafi dashi gida sun rabu da Mama tace mata ta tambaye shi idan ya yarda zata cika a canzo mata saiti me sarqa gaba daya.

A hanya yake gaya zeje Dutse gobe amma tare zasu tafi.
"Yanzu kwana biyun kawai kaje ka dawo shine se mun tafi tare, nifa kasan bana son tafiya a mota wallahi" Umaimah ta fada cikin shagwaba, hancinta yaja yace

"Ba kwana biyu zanyi qila mu iya kaiwa sati daya ma saboda ayyukan da zanyi da yawa kuma kinsan dai bazan iya yin sati ba tareda ke ba gashi babu Jirgi Kano to Jigawa da se mu hau tunda bakya son tafiyar mota Ajebo" ya qarasa maganar cikin sigar tsokana seta harareshi tace

"Nifa ba mota ba gaba daya tafiya ce bana so, nifa a rayuwata ko garin su Abba zan iya irga sau nawa na taba zuwa saboda bana son tafiya, nifa Makkah kadai nake qulafucin zuwa a rayuwata bayan nan ni ko wata Dubai da Paris da akw zuwa ba burgeni sukeyi ba"

"Toh kuwa gara ki mayar da Travelling one of your hobbies dan kin auri matafiyi kuma duk inda zanje ina maqale dake kamar handbag kinsan dai dakyar nake iya kwana biyu banji duminki ba ko" yayi maganar yana shafar qirjinta ta doke masa hannu a zuciyarta tace
"Jarababbe kawai" a fili kuma tace

"Toh idan yanzu bana komai zan ringa binka ko ina idan muka fara tara yara fa suka shiga school?"
"Kina tunanin yara zasu hanani jin dadin rayuwata ne ni babu ruwana suyi sabgarsu nayi tawa, nan da shekara saba'in idan muna raye babu abinda ze chanza na soyaya da tarairayar da nake yi miki sedai idan kuma kinyi sadaka dani kin barwa qanwarki da zata zo" kallon data watsa masa ya sakashi tuntsurewa da dariya ai kuwa ta hade rai har sukaje gida bata sake ce masa komai ba.

Kamar yanda ya fada kuwa washe gari da yamma suka wuce Dutse, dukda taso tayi masa gardama akan bazataje ba yayi mata jan ido dole ta bishi tana fushi tana komai shidai be kulata ba dan tasan lalurar sa, babu kuma yanda za'ayi ace zeyi tafiyar sati yana da mata ya tafi shi kadai bayan babu wani uzuri da ze hanata zuwa.

Sun cinye sati a Dutse lami lafiya babu tashin hankali dan se ya zaman Umaimah tafishi jin dadin tafiyar dan se bayan sunje tayi waya da Rumasa'u take ce mata itama tana Dutsen, akayi sa'a unguwar da take tana kan hanyar Site din da yake zuwa dan haka kusan kullum ze fita seya ajiyeta a gidan su Ruman idan ya tashi ya dauketa ita kuma tayi amfani da damar gurin koyon abubuwa a gurin yayar ruma data kasance hadaddiyar mace yar gayu ta gaske.

Kwararriya ce ta fannin girke girke da ado da kwalliya, a sati dayan da Umaimah tayi ta mayar da hankali ta koyi ire iren girke girken da Khalil din yake so dan ta taki sa'a a lokacin Anty Farida tana practical class na girki se Umaimah ta shige ciki aka ringa yi da ita. Da suka tashi tafiya ta hada mata tsaraba ta gaske da Umaimah ta gode mata saubabu Adadi bayan tayi amfani da kayan tsarabar.

Ingantattun kayan gyara ne gangariya da Anty Faridan take siya a gurin *SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS? 07031876677* Ruma ce tayi mata zancen qorafin da Umaimah tayi mata akan damunta da Khalil yakeyi, washe gari ana gobe zasu koma Kank da taje gidan ta kirata dakinta ta tambayeta, Umaimah ta sunkuyar da kai qasa a ranta tana ayyana yanda zata ci uban Ruma tunda dai ita ba terere tace taje tayi mata ba kawai ta nemi shawararta ne a matsinya na aminiyarta banda abin Umaimah ina Ruma taga abin cewa ita da ba aure ba shiyasa ta kai maganar ga Anty Farida se gashi ta gwangwajeta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login