Showing 369001 words to 372000 words out of 429394 words

Chapter 124 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1050

gudu suka wuceta suna kiran sunayen yan gidan da alama suma cike suke da murnar zuwa gidan kakannin nasu.

Sakin tsintiyar tayi ta bisu da kallo, shekara uku kenan rabon da ta saka Mu'ayyad da Bibi a ido sunyi wani irin kyau da girma Musamman Mu'ayyad din ya zama sauriyi ga Iman ma da take shekara uku kenan yanzu tayi wayo sosai tana bin yayyenta tana maimaita sunayen da suke fada tunda ita dai bazata tuna yan gidan ba. Dakin Mama suka fada gaba dayansu, tana jiyo muryar Maman daga inda take cikin tsananin murna tana tambayarsu daga ina waya kawo su seta kasa ci gaba da sharar ta tsaya a gurin wasu hawayen tausayin kanta suna zubo mata wata qila sun manta da ita shiyasa babu wanda ya nemeta a cikinsu se su Yasir suke cigiya. Dakinta ta wuce ta fada kan gado ta fashe da kuka a hankali amma irin me cin ran nan, me tayiwa rayuwarta haka? Wace riba taci? Da ranta bata mutu ba yayan data haifa sun haqura da ita basa tunawa da ita anya idan mutu ba ta gyara alaqarta ba kuwa zata samu wanda ze ringa tunawa da ita kuwa yana mata addu'a?

"Momy" taji an kira ta se tayi saurin saka hannu ta share hawayen fuskarta ta juya Bibi na tsaye a bakin qofar ta tafi da gudu ta fada jikin Umaimah ga mamakinta se kawai yarinyar ta fashe da kuka tana cewa
"Momy dama kina nan gidan kullum na tambayi Dady ina kike se yace mun kinyi tafiya zaki dawo".
Rungume yarinyar tayi a jikinta wani irin kewarsu na sake shigarta a hankali tana shafa kanta tace
"To kukan menene kuma ba gani yanzu kin ganni ba" se yarinyar ta dago tana shafa fuskar Umaiman tace
"Momy kin rame baki da lafiya?" Se tayi saurin janye fuskarta saboda wani kuka daya sake taho mata dai dai nan mu'ayyad da Iman suka shiga shima da gudu ya fada jikinta yana cewa
"I miss you Momy ina kika tafi kika barmu kullum se Dady yace mana kinyi tafiya kinqi ki dawo?"

Ta kalli Iman data tsaya a bakin qofa wata sahihiyar qaunarta da bata tsaya ta tantance ba sanda ta haifeta ta shiga zuciyarta, seta miqa mata hannu alamar itana ta taho yar gasken ta maqe kafada ba zataje ba, Mu'ayyad ya tashi ya janyota yana cewa
"Kizo gurin Momy" kai tsaye ta fizge hannunta cikin muryarta da bata gama iya magana ba tace
"Ni ba Momy na bace, Mamah na tana gida da Aryaan".

Yanda kasan dukan guduma haka taji maganar har ranta, ta zubawa yarinyar ido yanda ta dauke kai ta cuna baki a dole ba zataje gurinta ba zuciyarta ta qara karaya, babu tantama haqqin banzatar da ita da tayi ne ya fara bibiyarta Mamanta da tace tana gida ta tabbata Matar Khalil take nufi tunda ita ta bude ido ta gani a matsayin mahaifiyarta batayi laifi dan tace ita ba Momynta bace.

Wunin ranar sir da yaranta tayi shi wani irin dadi mara misaltuwa ta ringaji suka ringa bata labarai na Hajiya Dadynsu, Mamah da Aryaan da ta kas gane wanene shi kp wata daga cikin su Jalilah ta sake haihuwa ne? A bakinsu taji cewar Habiba tayi aure harta haihu tun tuni sunanr Yarinyar Hajar. Har Magriba suna gidan suna kuma maqale da Momynsu dan da Abba ya dawo ma sukaje gurinsa basu dade ba suka gudo gurinta, Mu'ayyad da Bibi na lafe a jikinta Iman ce take ja baya da alama dan yan uwanta na gurin Umaiman nema yasa ta zauna da bazata tsaya ba su kuwa kewarta ce tasa suka kasa barin inda take dukda motsi kadan se sun tambayeta bata da lafiya ta rame se tace musu eh kawai se kuma suka kafa tambayar yaushe zata koma gidansu haka kawai taji bakinta ya furta
"Ku tambayi Dady, duk sanda yace na dawo zan dawo".


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 79

Seda akayi sallar Magriba akazo daukarsu dan daman sun fada musu ba kwana zasuyi ba. Wata Farar mace kyakykyawa ajin farko tayi sallama riqe da yaro kalarta Umaiman na tsaye bakin qofar shigowa tana jiran yaron data aika ya siyowa Mu'ayyad Awara wai zeci matar ta shigo qamshinta me sanyi da Aji ya kai mata ziyara ta shaqa tana ware ido akanta saboda akwai hasken nefa a gurin ta ga fuskarta tar seta zuba mata ido tana so ta gano inda ta santa. Humaira ta fadada murmushin ta cikin ladabin data ke gaida duk wanda ya girmeta ta dan rankwafawa Umaiman tana cewa
"Ina wuni"
"Lafiya lau" ta amsa ba tareda ta gano inda ta santa din ba seta raya qila baquwar Anty ce dan da ta bangarensu ce zata santa. Qara gyara tsayuwa Humaira tayi tana kallon Umaiman tace
"Mama fa tana ciki?" Seta nuna mata qofar Maman kawai ba tareda ta sake cewa komai ba dan haka siddan taji tsanar matar ta dirar mata dukda bata da tabbacin wani abu ya taba hada, murmushi ta sakeyi mata kafin ta shige cikin gidan Umaimah ta bita da wani siririn tsaki daidai nan yaron data aika ya dawo ta karba ta wuce dakinta inda yaran suke jiranta.

A plate ta juye musu sun fara ci kenan ta Mama ta kwala mata kira seta miqe bayan ta mayar da Hijabinta ta fita. Tare ta tarar dasu da matar dazun tana zaune a qasa yaronta na kan cinyar Mama se wani sunne kai takeyi Umaimah ta tabe baki qila cikin surukanta ne yaran yan uwanta tunda anyi bukunkuna da yawa a shekarun duk bata je ba tana zaune kamar Prisoner Mama ta nuna mata Humaira tana cewa
"Mamansu ce tazo daukarsu" set kalli Maman kafin tace
"Maman suwa?"
"Su Malika, su fito su tafi kar su bata mata lokaci dare yanayi" Maman ta bata amsa tana harararta Umaimah kuwa daskarewa tayi a inda take kamar wadda ta samu cutar mantau kusan minti biyar kafin ta dawo hayyacinta sanadin tsawar da Maman tayi mata akan ta wuce ta turo yaran ta tsaya musu aka kamar wata kurma seta juya jiki a matuqar sabule tana jefa qafafunta kawai badan tasan ina ta nufa ba, a qofar dakin ta kifa kanta ta fashe da kukan data kasa riqewa wanda ta rasa ma na menene, ta tabbata dai waccen Matar ana nufinitace Matar da Khalil ya aura wadda tayi sanadin barinta dakinta ta rabata da yaranta har Iman take fadin ita ba Mamanta bace to idan haka ne shi kuma yaron hannu ta na waye dandai tafi kowa sanin cewar Khalil ya rasa lafiyar da ze iya yiwa Mace ciki ta haihu?

Kuka takr haiqan, Mu'ayyad daya fito da plate ya ganta yayi saurin ajiyewa ya matsa kusa da ita fusakarsa ta nuna damuwa yace
"Momy me akayi miki kike kuka?" Se a sannan ta tuna a inda take tayi saurin daga kanta ta shiga share hawayen amma sun gagara tsayawa se ta juya tana tafiya tace masa
"Anzo daukarku kira qannenka ku tafi" tayi can hanyar tsofaffin dakunan su na baya da se ana wani sha'ani ake amfani dasu. Guri ta samu ta cigada da rera kukanta da takeyi tundaga can qasan zuciyarta. Kishin matar da ke amsa sunan ta Khalil a yanzu ya cikata, yanzu duk wata soyayya da tarairaya da yakeyi mata ita take samunta kenan, Khalil ya iya mallakawa wata mace bayanta kansa abinda bata taba tsammatar ze iya faruwa ba. A zatonta irin tarin qaunar da Khalil yake mata ko a Aljanna da da hali ze iya haqura da Kyautar Hurul ayni ya zauna da ita kadai suci gaba da cin soyayyarsu amma se gashi tun a duniya tana raye ya manta da ita ya juya mata baya ya sadaukarwa da wata kansa ba tareda ya dubi halin da take ciki ba wanda shine sila shiya jefata shiya janyo ta aikata koma menene Soyayyar sa ce sila.

Tana nan zaune tana kukan suka fito Mama ta rakosu har bakin qofa tana musu Addu'a ga qatuwar leda a hannun Mu'ayyad da bata san ko menene a ciki ba haka suka fice daga gidan tana jin Bibi na cewa
"Ina momy? Bamuyi sallama da ita ba fa" tayi maganar cikin son fasa musu kukan rigima ta jiyo tashin muryar Humairan dukda bata ji abinda take fada ba amma tasan lallashin tayi suka tafi seta sske kecewa da wani kukan dana sani da nadamar ayyukanta suka ringa taso mata, me yasa ta biyewa zuciya ta gazayin aiki da kwakwalwarta? Me yasa bata saurari yanuwa da abokan arziqi da suka ringa qoqarin nusar da ita ha ya ta kwarai ba a lokacin bata yi tunanin makomarta ba ta biyewa hudubar shaidar da son zuciyarta kawai gashi Khalil din da tayi danshi ya barta harya samu lafiyarsa yaci gaba da mu'amalantar watanta tubda ga shaida ta gani da idonta wanda kadai ya isa ya tabbatar mata da cewar yayi gaba a rayuwarsa ba kuma zai waiwayeta ba.

Bata san lokacin data bata a gurin tana kuka da dana sani mara amfani ba kafin daga qarshe ta haqura ta tashi daga gurin tana jin kanta tamkar ya tsage saboda ciwo. Ragowar awarar da suka bari taci ta kwanta kawai amma bacci ya qauracewa idonta, duk inta motsa Khalil take gani a idonta da Humairan yana gwada mata kalar soyayyarsa me tsayawa a zuciya ta dora pillow akanta ta fasa qara kamar zata tsaga dakin, a fusace Mama ta shiga ta saiti bayanta ta watsa mata Carbin dake hannunta Umaiman ta zabura ta sake zuba mata shi yanda ta bude baki ta fara kuka me hade da ihu ya sake tunzura Maman ta ringa caula mata carbi ta ko ina seda ya tsinke kafin ta rabu da ita tana haki tace

"Ke dan ubanki baki san ki ambaci Allah ba a duk sanda kike cikin tsanani se ihu da kwaroroto kamar diyar Arna? Ihun ne ze miki maganin damuwarki ko me, se yaushe zakiyi hankali Umaimah ki maida Al'amuranki zuwa ga Allah sannan ki ringa neman agajinsa akan duk abinda ya dameki? Kullum cikin yi miki tunatarwa nake akan duk a abinda ya sameki ki nemi taimakon Allah ki lazumci karanta Hasbunallahu wani'imal wakeel da sannu Allah ze kawo miki rangwame da salama cikin lamuranki, sannan ki riqe 'La'ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin' duk tsanani da yardar Allah zaki samu mafita amma inase ihu da kururuwa kadai kika sani babu Istigfari babu hailala babu salatin Annabi babu karatun Alqur'ani se Kuka da tagumi kika qulla aure dasu tayaya zakiga daidai a sha'ani ki Umaimah? Tun lokaci be qure miki ba ki gyara badan wani ba sedan ke a karan kanki kodan kiji dadin sauran rayuwar data rage miki Umaimah ki kama Allah" daga haka ta juya ta bar mata dakin Umaimah da tayi luqus jikinta gaba daya radadin dukan carbin data sha yakeyi amma maganganun Maman tabbas sun shigeta matuqa.

Gaskiya Mama ta fada a duk lokacin da taji wani al'amari me nauyi ya taso mata a zuciya a maimakon ta miqa komai ga Allah seta zabi tayi ta zunduma ihu irin yanda take karantawa a littattafan turawa da gani a finafinan su idan abu ya samesu sukayi irin wannan ihun me qarfi kamar yana tafiya ne da dukkan damuwarsu ta dauki hakan kuma ta gwada taga yayi mata tun daga nan ta mayar dashi dabi'a da wata damuwa ta sameta zata taqarqare tayi ta zunduma ihu har ada suke tunanin tana da shafar Jinnu bata mantawa kullum Maman cikin nuna mata falalar addu'a takeyi amma ta gagara riqewa, ko Malamin da aka taba kaita ruqiyya gurinsa seda ya jaddada mata yin addu'a a duk sanda zuciya ta bijiro mata da abinda yake harqitsa mata tunani.

Haka a islamiyya Ya sayyadin su kullum seya karanta musu falalar Hasbunallahu da sauran lazumai da suke sanya nutsuwar zuciya kuma idan yanayi yawanci ita yake kallo alamar in directly da ita yake dan ita ce majanuniyar ajin tayi shura kaf makara tar babu Wanda besan Tijararta ba, Headmaster idan aka fita sallar la'asar takanas yake sakawa a kirata bayan yayi alwala ya bata butar yace tasha ragowar ruwan ciki akan wannan abun har dena zuwa Islamiyyar tayi wai ya raina mata hankali yana sakata shan ruwan buta idan suka tafi gaba daya se ta zame tayi wani wajen tayi zamantahar se an tashi sannan zata biyosu su dawo gida seda Mama taci Ubanta bayan da su Nuratu suka ce basa ganinta idan anfito sallah tunda kowa ajinsa daban se an tashi suke haduwa a get sannan fa ta nutsu ta koma zuwa Islamiyyar amma bata yarda ta sake shan ragowar ruwan Alwalar Uztaz Muslim ba.

Ta muskuta ta gyara kwanciyarta ta sake fadawa kogin tunani, ita da kanta ta yarda da cewar rayuwarta akwai dazgado a cikinta. Tana salloli biyar na farilla tana Azumin Ramadana baya ga haka babu wata Ibadah ta neman lada da takeyi ta bari sharholiyar duniya da abinda yake cikinta yayi tasiri a zuciyarta. Idan da ace mutum yana haifar Da ya haifi halinsa tabbas data kasance daga cikin mutane masu kyawawan dabi'u da ake misali dasu domin ba fariya ba Mahaifiyarta maceceta gari me matuqar kirki da riqo da Addini kuma tayi iyakar qoqarinta gurin basu tarbiyya kuma duk cikinsu kowanne yana kamantawa daidai misali banda ita data fita zakkah. Ta tashi a gidansu taga Mahaifiyarta ta kasance me yawan ibadah tasha ji a bakin Abba yana fada yana nanatawa Maman ita ta koya masa tsayuwar dare da Azumin litinin da Alhamis kuma tunda ya kamasu yake ganin haske a Kasuwancinsa da rayuwarsa gaba daya shiyasa a kullum yake qara godewa ubangiji akan hadin da yayi musu domin Malika ta zama haske a rayuwarsa. Tun suna qanana sanda suke kwana a dakinta tasan tana tashi kullum dare tayi sallah koda raka'a biyu ce haka nan koda ace tana fashin sallah wannan abin ya zame mata jiki seta tashi tayi addu'a tayi musu idan suna bacci haka zat???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a shiga dakinsu ta tsaya akansu ta ringa tofa musu addu'oi yawanci tanayin hakan akan idonta saboda bata da nauyin bacci koya akayi motsi seta farka amma bata mori wannan baiwa da Allah yayi mata ba gurin ringa tashi tana bauta masa cikin dare sanda sauran jama'a suke bacci tana kallo su Nuratu zasu tashi subi Maman suyi sallar koda ba kullum sukeyi ba amma banda ita tun suna ganin yarintarta su barta har ya zamana suna tashinta wani lokacin tayi wani lokacin ta tsaya daga bayansu suna sallah tayi kwanciyarta bawai sallar dare ba har lokutan Azumi idan anje Tarawi haka takeyi tasha baccinta ta dawo gida ayi fadan a daka duk a banza har suka haqura suka zubamata ido randa Allah yaci da ita tanada rabon samun ladan tayi randabata dashi taqiyia haka ta tashi ta girma ta auri Khalil ta same shi shima me tsayuwar darene a farko farko tana binsa suyi daga baya ta saki tana kallo ze tashi yayi sallolinsa ita ko ta shanya baki tana bacci wani lokacinma idonta biyu sedai ta dauki waya tayi ta danne dannenda bazasu amfaneta da komai ba idan ya matsa mata tace da wanne zata ji gajiyar daya tara mata ko kuwa ya barta tayi baccinta tunda ba farilla ta tsallake ba bare yace ta sabawa Allah seya rabu da ita kawai taci gaba da rayuwarta a yanda ta zabar ma kanta babu Allah a ciki waddaga sakamakonta ta fara girba tun BA's ko ina ba duniyar ta nuna mata cewa ita ba koman kowa bace ba a dan qaramin lokaci ta zama abar tausayi.
Daren ranar kwana tayi cikin jimami da tunanin neman mafita da hanyar da zata bi ta gyara kura kurenta, tana da buqatar wanda ze saurareta ya kuma nuna mata hanya domin kwakwalwarta ta rufe ruf bata tunanin gaba baya kawai take hasko mata tana tariyo irin mugayen abubuwan data aikata a rayuwarta da tun a nan duniya sun fara farautarta sun hana mata nutsuwa.


KHALIL
Kallon qofar gidan ya ringayi abubuwa da yawa suna bijiro masa tun daga farkon fara zuwansa gidan har kawo yau din nan dayazo daukar yaran. Jiya suka hadu da Abba a wajen wani daurin aure, ba qaramin kunyarsa yaji ba harya kasa hada ido dashi shi kuwa Abban ko a jikinsa suka gaisa ya tambayeshi iyali har yake ce masa
"Malam Khalil mun tuba kar laifin Umaimah ya shafe mu a taimaka a ringa kawo mana yara muna ganinsu ko da a wuni ne, kaga Amaren nan nawa biyu ba qaramar kewarsu nake yi ba a dubamun na dan samu na gansu ko naji sanyi a raina" Abban ya fada cikin raha abinda ya sake jefa Khalil cikin matsananciyar kunya kenan dan haka da yamma yana komawa gida yace musu washe gari da sun taso daga Boko zasuje unguwa dama kuma Alhamis ce babu islamiyya ya sanarwa da Sabon Driver daya daukar musu saboda makaranta da sun taso ya jira su shirya ze kaisu wani guri. Seda sukaje kwanciya yake gayawa Humairan gobe za'a kaisu gurin Mamansu tayi masa murmushi me kyau tana lafe a qirjinsa tace

"Ko kaifa Habibi amma ace tsahon lokaci ka raba yara da mahaifiyarsu Alhalin tana raye kasan kuwa zafin rashin uwa?"
"Shiiii" ya dakatar da ita ganin tana so ta tado da wani abu kuma kafin yaci gana da cewa
"Basu rasa uwa ba tunda suna dake kuma ai gashi nace gobe zasuje wajenta shikenan se ki dena yi mun mita"
"Toh kwana nawa zasuyi? Kaga daman gobe da Monday babu makaranta se su zauna kawai zuwa Sunday se a dakko su ko ba haka ba?" Ta sake fada seya zuba mata ido kawai ba tareda yace komai ba.

A tsahon shekara ukun nan babu abinda ta rageshi dashi da yaransa, ta karbesu da hidimarsu gaba daya a hannunta take tamkar yadda uwa zata tarbiyyantar da yaranta haka take musu babu mugunta bare qyashi ko hassada ya gamsu da cewar tsakani da Allah take riqe masa yara amma dukda hakan a kullum cikin haqurtar dashi take akan ya bari su ringa zuwa gurin Mahaifiyarsu ko Yayane.
"Ita kadai ce Alfarmar da zaka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login