Showing 141001 words to 144000 words out of 429394 words

Chapter 48 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1648

zamu kamo bakin zaren maganar nan"

"Kina ji Jalila ina son Umaimah kuma bani da wata matsala da ita, damuwata guda daya ce kawai yanayin aikina da bana zama guri daya a koda yaushe ana turani garuruwa nayi ayyuka kuma ina yin kwanaki wani lokacin ma satittika ni kuma ina da sha'awar duk ina zani na tafi da Matata, matsalar anan ita kuma Umaimah bata son tafiya.
Duk sanda wata tafiya ta taso se rayukan mu sun baci kafin ta bini, kinga last tafiyar da nayi Lagos har na gama zamana na dawo bataje ba acan nema na hadu da Hadiza dan a lokacin fushin da nake ciki na yanke shawarar aure kawai zan qara na auro wadda ko bangon duniya nace zanje zata bini"

Yaci gaba da bata labarin yanda ya hadu da Hadiza da irin soyayyar fa sukayi har zuwa matsayin da suke yanzu akai na zancen turowa da tayi masa. Ya rufe da cewa
"Banaso haqqinta ya kamani dan dagaske yarinyar tana so na ni kuma bansan ya zanyi ba yanzu.
Tun bayan dawowata na tuntubi Hajiya da maganar dan naji ta bakinta tayi futufutu tace babu wannan maganar ba yanzu ba har gaba babu ita.
Toh ni maganar Hajiya ma da sauqi nasan idan na lallabata tana iya yarda, Umaimah nada bala'in kishi irin wanda bakiyi tunani ba, idan zancen auran nan ya fito na tabbata babu sauran zaman lafiya tsakanin mu".

"Hmmmm" Jalila taja dogon numfashi tareda sauke taguminda tayi tana kallon Khalil tace
"Ni har na rasa ta ina zanfara ma, idan na fahimceka abinda yasa ka fara kula Sabuwarka saboda rashin Umaimah a kusa ne bari na fara da wannan bangaren in har kana ganin cewar Umaimah bazata haqura ta ringa binka duk inda zakaje ba kana da hujjar da zaka qara aure kuma duk wanda ka gayawa dalilinka baze hanaka ba kodan gudun fadawa halaka.
Amma idan shawara kake nema se nace maka qarin aure ba shine mafita ba ka zauna da ita kuyi magana ta fahimta ka nuna mata buqatarka da abinda bijirewa hakan ze iya janyowa idan har bata gyara ba daga nan kana iya daukar mataki na gaba sannan ita wannan Hadiza kace kowa sunanta ba son ta kakeyi ba, Umaimah ta riga ta siye filin a ganina ka saurareta ne kawai a lokacin saboda fushin Umaimah inda dagaske ka gantan kake sonta zuciyarka bazata kawo maka wani tunani ba balle har kaji shayin tunkarar kowa da maganar auranta.

Kuma koda ace ka aureta be zama lallai ka iyayin adalci a tsakaninsu ba, idan auran kake so dagaske ka bari ka samu wadda soyayyarta tayi takara data Umaimah a zuciyarka idan ba haka ba yanda kake Son matar nan kake tsoronta duk wadda ta shigo gidanka bayan ita wahala kawai zata sha".

"Kema bakya goyon bayan maganar kenan?" Khalil ya tambayeta fuska babu walwa kafin tayi magana yaci gaba da cewa
"Ni wallahi tsoron hakkinta ya kamani nakeyi na san soyayya nasan zafinta, bakiga irin Kukan da takeyimun ba jiya tana nanata tana sona naji tausayinta sosai"

"Tausayinta kakeyi ba Son ta ba Khalil, idan kuwa hakane ka barta kayi mata Addu'a Allah ya bata wanda ya fika dan bata da gurbi a zuciyarka Umaimah ta gine duka filayen sedai idan rusau za'ayi" Jalila ta fada cikin tsokana a zuciyarta tana sake auna maganar Khalil din, ita dai a iya tata Basirar abinda ta gani kenan, ba son hadiza yakeyi ba tausayinta yake kuma fushin Umaimah ne ya saka shi harya fara kulata, ko a yanzun bata raba daya biyu bata masa rai tayi shiyasa har yake tunanin yayi auran.

Tattaunawa suka cigaba dayi akan Abubuwan da suka shafesu har suka gangara batun gidansu daze siya da yanda yake so yayi dashi, be bar gidan ba se gurin qarfe uku na rana shima saboda Mansur ya kirashi yana so su hadu ya tafi bayan ya cikata da Alkhairin dayaje mata dashi tanata godiya, suna son dan uwan nasu saboda yanda yake sonsu.

Maganar da sukayi da Jalila ta saka ya qara ja baya da Hadiza kuma ya yarda dagasken ba son ta yakeyi ba tausayine da kuma huce takaici da yaso yayi da ita amma dukda haka yana tausaya mata, kullum cikin rarrashinta yake da gaya mata cewar ta fawwalawa Allah idan hat ya qaddara zasuyi aure zasuyi a sanda yaso.

Data matsa masa akan Yayanta yace yana son ganinsa ranar ya haqura yaje, be boye masa komai ba ya gaya masa uzurinshi ya kuma fahimce shi yayi musu fatan Alkhairi idan Hadiza matarsa ce Allah ya tabbatar, bayan ya gama da Yayan ya turo masa ita sukayi magana, kamar ze zubda Hawayen tausayinta saboda yanda duk ta rame dalilin damuwar da ta saka kanta a ciki. Haquri ya bata tateda lallashi, yace mata baze ce ta jirashi ba, amma idan da rabon aure a tsakaninsu yana fatan Allah ya matso musu dashi kusa sannan ya roqeta da suci gaba da gaisawa idan tana ganin babu matsala tace zatayi tunani haka suka rabu rabuwar da yake ganin sunyi ta kenan shida ita.

Ciwon kai da jirin da suka matsawa Umaimah ya saka dole sukaje Asibiti wata ranar Litinin, bayan likitan yayi mata yan tambayoyi ya auna jininta ya rubuta mata magunguna akan taje tasha idan bata samu afuwa ba su sake komawa. A hanya Khalil ya ringa mata fadan rashin bacci da wuni da takeyi akan waya dan hatta idonta jini ya kwanta shiyasa likitan be kawo tunanin kowanne ciwo ba yace rashin bacci ne ta ringa samun isashshenhutu suna tafe ta tunzura baki gaba saboda fadan da yake mata kai tsaye gidan su ya kaita, idan da Umaimah tasan can ze ajiye ta yasan bazata yarda ba dan tunda ta gudo kamar yanda Anty ta fada bata sake komawa ba.

A tsaitsaye suka gaisa yayiwa Mama bayanin bata da lafiya daga Asibiti suke, ya qarasa da cewa
"Dan Allah Mama ki saka mata ido ta samu tayi bacci karta zauna danne dannen waya"
"Uhm abin nata har ya kai ya saka mata ciwo kenan ko, jiyan nan naji Salman yana maganar tsakar dare tayi masa magana akan yaje zata aike shi seda Safe yaga saqon ya duba lokaci yake cewa Ashe Umaimah bata dena kaiwa dare tana chatting ba toh Allah ya shirya" tayi masa fatan Alkhairi ya wuce Umaimah dai tunda ta shige daki tayi luf, da mama ta tashi yi mata tsiya wayar gaba daya ta kwace, Mu'ayyad daman suna shiga yara suka dauke shi dan haka tana cin abinci tasha magungunan tana nan zaune shiru Mama nata shige da ficenta kota kanta bata bi ba baccin dole ya dauketa saboda magungunan data sha.

Da suka koma gida kuwa yasha mita yayi mata banza dan kanta tayi shiru, doka ya kafa mata ta bacci qarfe goma kuma ta kashe wayarta ta bashi. Yanda ya hade fuska yana gaya mata dokar dole ta amsa a lokacin dan yanzu lallabashi takeyi bata so nan kusa ace an sake samun wata matsalar musamman da take da buqata a gurinsa so take a kwana biyu komai yayi daidai ta nemi abinda take so.
*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 38

Hotunane su fi guda Ashirin nashi da Hadiza a gurare daban daban da suke haduwa. Ba hotunan ne suka tayar masa da hankali ba, aa yanayin daukarsu ne da ko kusa ko alama besan a lokacin da akayi hakan ba dan yawancin hotunan sun nunashi ne rungume da Hadizan ko kuma tana kwance a jikinsa.
Video dayayi zargin an dauke su a ranar nan shine na qarshe, wata irin faduwar gaba ta ziyarceshi lokacin da ya kunna vice yana kallo, tabbas ya riqe Hadiza a jikinsa saboda gudun karta fadi ya sakata a mota sannan ya ranqwafa kanta yana mata magana amma a yaushe har ya sumbaceta dan shine abinda yake gani a video qarara gashinan yana Kissing Hadizan baki da baki.

"Innalillahi wa'innq ilaihi raji'un" ya fada a fili yana miqewa tsaye, wacece ko wanene wannan? Me suke nema a gurinsa da suke neman wargaza masa rayuwa tayi masa sharri ta zubar masa da mutunchi a idon masu ganin girmansa dan wannan ya zarce yaji tsoron Umaimah ta gani, idan duniya taga wadannan hotunan me zatayi tunani akansa saboda dukkansu an daukesu ne a cikin mutane kuma yake aikata hakan me za'ayi zargin yana yi idan ya kebe inda babu me ganinsa se Allah?.

Qarar wayarsa ce alamar shigowar saqo ta katseshi ya zabura ya duba,
"Nasan zuwa yanzu kaga saqona, shin ka shirya magana dani ko kuwa na turasu inda dolenka ka magantu idan sun isa?" Abinda aka rubuta a saqon kenan yana gama karantawa be jira komai ba ya dannan kiran layin.
Qofar Office dinsa yaje ya rufe dan a halin da yake ciki yana da buqatar kadaici ko ze samu ya warware abinda yake ciki.

"Nasan dole zaka kira ai dan bazaka so Matarka tayi katari da wadannan Hotunan ba, Uhm Hajiya Umaimah iyayen kishi, ko yaya zata kaya idan tasan mijinta yana neman mata a waje?"? Aka fada bayan da aka daga wayar kafin yayi magana taci gaba da cewa

"Malam Khalil, buqatata ba wata me wahala bace amincewarka kawai nake nema amma fa idan ka sauqaqawa kanka"

"Khausar" ya fada cikin wani sauti me nuna bacin rai da kuma tashin hankalin da yake ciki seta kwashe da dariya tace
"Ya akayi kayi saurin gane nice? Koda yake wannan bashi da amfani, yanzu ka shirya muyi magana ko na qara maka lokaci ka sake kallon hotunan da kyau kayi tunanin abinda zan iya aikatawa dasu?"

"Khausar mekike tunanin kinyi? Meye wannan me kike nema a gurina da har zakiyi mun irin haka?" Khalil ya fada cikin tsawa kamar yana gabanta se tace
"Aa fa ka denayi mun tsawa Malam me nayi maka?"

"Me kikayi mun kike tambaya na ma? Wadannan hotunan a ina kika same su yaushe aka dauke su?" Khalil ya sake jefa mata wata tambayar, Khausar taja qaramin tsaki tace
"Lokacin da kuke fita yawon shaqatawarku da Hadiza ni kuma na saka wanda yake bibiyar mun dukka sahunku yana daukar mun hotunana" se yayi saurin katseta da cewa

"Qarya kikeyi wadannan hotunan ba gaskiya bane, babu ko guda daya da yake ainihin yanda aka dauke shi dan ban taba riqe Hadiza kona taba jikinta cikin sanayya ta ba"

"Wannan kuma matarka da sauran mutane zakayiwa bayani idan na watsasu bani ba, ni daman abinda yasa na kiraka na zata zamu samu fahimta ne cikin sauqi amma naga alamar cikamun kunne da ihu kawai zakayi dan haka na barka lafiya ka kuma kuka da kanka duk abinda ya biyo baya" Khausar ta fada tana qoqarin kashe wayar ya dakatar da ita cikin wata murya yace

"Me kike da buqata?"
"Yawwa now you are talking like a smart Man amma da se wani surutu kawai kakeyi" Khausar ta fada kafin taci gaba da cewa

"Da farko inabuqatar ka turamin da 1M a account dina kudin bata lokacina da kudin aikin yaron da na saka yake daukan mun hotunanku, sannan idan kayi wannan se muyi magana kuma akan buqata ta ta gaba" tana gama fadin????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? haka ta kashe wayar ba tareda ta jira amsarsa ba, qarar shigowar Message ya sakashi rufe bakinsa daya bude tsabar mamakin Khausar, account number ta turo masa kuwa tana sake jaddada masa ya tura sannan ya kirata su qarasa magana.

Tissue yaja ya goge zufar data tsatstsafo masa a goshi gaba daya ma ya rasa tunanin me zeyi yanzu kenan Khausar Blackmailing nasa take so tayi ta ringa tatsar sa kudi akan laifin da ne aikata ba amma me yasa zatayi masa haka? A zatonsa Aminiyar Hadiza ce me yasa zatayi musu haka dan wannan abin bashi kadai ta shafa ba harda Hadizan wannan tunanin da yayi ya sakashi saurin daukar wayar ya shiga kiran Hadiza sedai tun daga yanayin muryarta jikinsa ya qarasa yin sanyi.

"Ta turamun nima ta kuma fada mun wasu banzayen sharudanta idan ba haka ba zata turawa Mama da Yaya hotunan" Hadiza ta fada lokacin da ya gaya mata saqon Khausar daya samu.
"Amma me yasa zatayi haka Hadiza daman Khausar ba Aminiyarki bace me yasa zata ci amanarki ta nemi saka mu a tashin hankali?" Khalil ya fada murya a sanyaye se Hadiza ta saki kukan da take riqewa tana cewa

"Daman Mama tace tana zargin ka gama dani shiyasa ka gudu kaqi aurena. Bansan waya dasawa Mama zargina a zuciyarta ba ada duk inda zanje Mama bata damuwa ta yarda dani ita da kanta tana fada amma haka kawai komai ya chanza. Ta kai ta kawo har tana fada mun da bakinta cewar tasan duk Barikin da nakeyi nake fakewa da sunan aiki, tun abin yana damuna nayi kuka har ya zaman mun jiki sedai kullum ina addu'a Allah ya wanke ni ya kuma kawo min Miji nayi aure sannan ina Addu'ar Allah ya tonawa duk wanda ya shiga tsakanina da mahaifiyata Asiri se yanzu na gane Ashe Khausar ce, me nayi mata? Yanzu idan ta fitar da hotunan nan da sauran da tace tana dasu da wane baki zan kare kaina a gurin Mama?" Hadiza ta qarasa tana fashewa da wani kuka me tsuma rai.

Gaba daya kansa ya qara zafi ga damuwar da yake ciki ga kukan Hadizan, cikin muryar rarrashi yake mata magana
"Kiyi shiru Allah shine shaidar mu bamuyi duk abinda yake a cikin hoton ba, kuma qarya takeyi da tace miki tana da wasu kawai so takeyi ta firgitaki. Ki kwantar da hankalinki yanzu zan kai report gurin yan sanda akan tana so ta bata mana suna idan anje can ta fadi gaskiyar yanda ta hada hotunan qarya".

"Aa Khalil ni nasan wacece Khausar hatsabibiyace ta gaske duk abinda tace zatayi zatayin, kuma ba ita kadai ta shirya wannan abin ba, ko da ace ka saka an kama ta ragowar Abokananta zasu iya aikata abinda bamuyi tsammani ba. Ta taba bani labarin wani abokinta da yake aikin computer, a lokacin wata yarinya aka saka yayiwa sharri ya dora fuskarta akan wani nude video suka turawa Mijin da zata aura qarshe haka suka lalata auran ita kuma suka kassara mata rayuwa" Hadiza ta sake fada cikin kuka kafin taci gaba da cewa

"Dan Allah Khalil ka bita a hankali, duk abinda tace kayi idan da hali kayi mata mu samu mu tsira da Mutunchinmu daga ni har kai"

"Miliyan daya fa tace na tura mata yanzu" Khalil ya katseta se tayi saurin cewa
"Miliyan daya, Anya Khausar tana da hankali?"

"Koma menene idan na tura mata yanzu kinsan gaba abinda zata nema a gurina? Zata ci gaba da blackmailing nawane kuma hakan bashine yake bada tabbacin bazata fitar da hotunan ba kamar yanda tace. Nidai bazanyi falling ma tricks finta ba, inada Aboki DSS ne zan kirashi na gaya masa su zasu san abinda zasuyi akan maganar"

"Aa Khalil dan Allah kabi a hankali bana son abinda ze janyo daga ni har kai mu shiga matsala" Hadiza ta sake fada cikin kuka da tsoron abinda ze iya biyo baya. Tayi kuka tayi nadamar sanin Khausar a rayuwarta. Tsakaninta da ita Alkhairi ne bata san me ya saka ta aikata mata ahakan ba.

"Ki dena kuka kuma ki kwanatar da hankalinki in sha Allahu babu abinda ze faru kinji" Khalil ya fada cikin rarrashi, dakyar ya samu ta yi shiru da kukan, ya kuma tabbatar mata duk abinda ake ciki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login