Showing 291001 words to 294000 words out of 429394 words

Chapter 98 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

985

fushi dani ba"
"Ni ba fushi nakeyi dake ba tun jiyan nima bana jin dadi shiyasa ban kiraki ba ki dena kukan". Seda yayi aikin rarrashi kafin ta haqura, Humaira akwai shagwaba ya fahimci ma da gayya take masa dan ya rarrasheta shi kuma baya gajiya da lallashin nata dan abin nata burgeshi yakeyi.

"Kina ina naji surutan yara?" Ya tambayeta jin yara na hayaniya a kusa da ita se tace masa
"Ina gidan Anty Unaiza, jiya da daddare da taje Mama tace na bita wai na koma gidan da zama yanzu" ta bashi amsa, se ya bude ido yace
"Toh, me yasa?"
"Nima ban sani ba amma inaga saboda Noor ne dan jiya bayan ka tafi yazo yanata Hayaniya har seda ma sukayi fada da Yaya Habibu, ni tausayi ma ya bani wlh kamar nayi kuka kuma be samu Army dinma bafa wannan karon shiyasa abun yayi masa yawa".

Gimtse fuska Khalil yayi kamar yana gabanta yace
"Oh to tunda ya baki tausayi ai da se kicewa maman ta aura miki shi kawai a haka ko bashida abinyi zaki zauna dashi ko"
"Auw" Humaira ta fada tana riqe baki, Unaizatu data tarar da katobarar da takeyi ta dana mata duka a cinya ta shiga sosawa tana cewa
"Nifa ba haka nake nufi ba, bayan kazo kayi mun Asiri ka rabani da saurayina tun ina yar yarinya" tayi maganar tana zumbura baki se Khalil ya saki murmushin da be shirya ba yace
"Oh Asiri ma nayi miki lallai yarinyar nan wai yaushe bakinki ya bude kika fara magana haka?"

"Oho nima ban sani ba" ta bashi amsa cikin qunquni se ya saki qaramar dariya yace
"Idan na tashi zanzo na ganki, har yanzu a Gandu Unaizatu take ko sun chanza gida?"
"Eh sun chanza amma duk a unguwar ne amma ta layin bayan wancan gidan suka koma"
"Asalin gidan iyayen Mijinta kenan ko? Idan zan tuna sanda ta haifi Danta na farko a can ta zauna Mama tana aiken mu mu kai mata saqo"
"Eh nan" ta fada cikin tabbatarwa se yace mata
"Toh shikenan, zan zo idan nazo layin sena kiraki dan qila an chanzawa gidan fasali bazan gane ba"
"Toh shikenab se kazo"
"Alright babe" ya fada tareda yin shiru amma be kashe wayar ba, kamar daga sama yaji tace
"I love you take care" ko numfashi be aje ba ta kashe wayar shi kadai ya fashe da dariya a ransa ko yanda kasan ta wanke shi da Hypo, wayaga yaushe rabon duniya da Ayyaraye ace masa I Love you tun farkon tarewarsu a sabon gida.

Har Allah Allah ya ringayi lokacin tashi yayi ya tafi gurinya, yanayin sallar La'asar kuwa ya fita, seda ya tsaya yayiwa yaran Unaizatu tsarabar chocolate itama ya siya mata kalar wanda ya saba kai mata kafin ya kama hanya. Har cikin falo tayi masa iso wanda aka gyara tsaf ko ina se qamshi yakeyi, yaranta biyar duk suka shiga suka gaidashi ya basu tsarabar daya tafi da ita kafin Unaizan ta shiga itama. Har qasa ta tsugunna ta gaidashi ya amsa mata cikin kulawa a ransa yana mamakin yanda ta zama wata big madam kamar ba Unaiza Lilo sunan da suke tsokanarta dashi lokacin suna yara, ita take bin Mansur dan haka basa shiri a sanann Khalil ne abokinta komai da Yah Khalil ake qullashi danshi Mansur ya fiya tsokana shine ma ya saka mata sunan Lilon kuma har a makaranta haka yake kiranta kuma ya bita tayita kuka harta haqura take amsawa.

"Ikon Allah Unaiza, ashe zakiyi qiba" Khalil daya kasa shiru ya fada se ta fashe da dariya ita kanta abin mamaki yake bata tace
"Wlh Yah Khalil gashi kuwa kuma qibar ta lokaci daya abin mamaki"
"Shine nima na gani ai, yaushe na ganki na qarshe ai baki kai haka ba yanzu nasan ko Sumayya ai seta buda miki"
"Kai rabani da kamo Sumayya qiba Yah Khalil wannan Mata kamar Bijimar Sa kuma a qaryarta Najib din ne yake son qibar shi yasa taqi ta rage" Unaizan ta fada tana riqe baki, hirar baya suka dakko ana tuna yanda kowa yake da yanda ya zama yanzu Humaira ta shigo da Try data doro kayan ciye ciye Khalil ya kalleta yace
"Kice wannan ma wata rana zata zama giwa kenan" seta waiwaya ta kalleta tana yar dariya tace
"Wannan kuma kiwonka ne ze tabbatar" daga haka ta miqe ta basu guri.

Beyi niyyar jimawa ba amma hirarta me cike da quruciya da labarai da basa qarewa yasa ya shantake se ji sukayi ana magriba. Seda yayi salla a masallacin layin kafin ya koma yayi mata sallama, sun fito ta rakoshi yake sanar mata da zancen zuwansu Jalingo ranar Juma'a se tayi shiru tana juya zoben hannunta.
"Ya naga kinyi shiru, ko bakiyi farin ciki da magana bane?" Ya fada yana kallonta, ba tareda ta dago kanta ba tace
"Amma Yaya cewa kayi fa se na fara makaranta"
"Maganar makaranta Humaira ni nayi miki Alqawari indai karatune zakiyi harse kince kin gaji, nida zaki zama business partner ta, idan na ginawa mutane gida ke kuma kiyi musu furnishing da kayayyaki na yan gayu ko kin fasa bude Interior design company din?" Ya fada cikin lallashi, nan sabuwar hira ta balle, burinta kenan ita a ringa bata kwangilar gidaje tana saka kaya a ciki ta zabi fenti da duk kalar abinda ze dace da gida.

"Karki damu ni zan fara employing naki da na gama miki gidanki zan baki dama ki shiryashi mu gani, kinga idan yayi kyau daga nan zan fara recommending ma abokan kasuwanci na ke amma tare zamu ringa raba ribar fa kin yarda" Khalil ya fada ganin Isha na neman yi suna tsaye seta daga masa kai alamar ta yarda tana murmushi daga nan ya shiga mota yana ce mata
"Karki manta ki gayawa Mama dukda nasan zasuyi magana da Hajiya amma dai ki gaya mata dan ta san da yardarki za'aje" daga haka yaja mota tana daga masa hannu ya bar gurin. Ciki ta koma tana shiga ta gayaqa Unaizatu yanda sukayi dashi.

"Wallahi Humaira kinyi dacen Miji matsala daya ce matarsa amma itan ma Allah ya fita in sha Allahu zakuyi auranku ku zauna lafiya" Unaiza ta fada, Humaira ta rafka tagumi tace
"Nima wlh Anty ita nake tsoro, kinsan fa ranar nan tazo gida, nan ta bata labarin zuwan Umaimah Unaiza ta bude baki tana jinta harta gama tana cewa
"Amma fa karki gayawa kowa dan Mama tace karna fada koshi Yayan be sani ba. Kuma kinga Yaya Mansur ma baya so, kwanaki kirana yayi yana tamun fada akan nacewa Mama banason Yah Khalil ita kuma ta kirashi tayi masa fada shine fa har yanzu yake fushi dani shima Yah Khalil din yace koya kirashi baya dauka to kinga ai shi yasan halin matar abokinsa toh ita Mama taqi ganewa"

"Toh ke kina son Khalil din?" Unaiza ta tambayeta tana kallonta, seta rufe fuska da hannunta tace
"Kai Anty baki san Yah Khalil bane indai kuka fara magana dole ka fara sonsa baka sani ba"
'Toh ai shikenan se kiyita addu'a in sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi. Yanzu dai ki ajiye shirme ki maida hankali dan kinsan abinda ya kawoki gidan nan, gobe zaki fara zuwa gidan Maman Ayman inaga sau hudu tace a sati zaku ringa Classes din, nasan kin iya girki se ki qara maida hankali ki gane dabarunda zata qara miki sannan akwai saqon da za'a kawo gobe suma ki fara amfanj dasu, bari ma kiga na tashi na hada Miki TULA-TULA ki fara sha wannan qirjin dake nan kamar na yara a samu su taso dan matarsa idan kikaji ana Figure 8 toh itace gara kema kidan qara auki yawwa".

Dariya ta shiga kyalkyalawa jij wani suna wai TULA-TULA, Unaiza ta dawo Salalan ta ajiye mata da madara ta dauka tana cewa
"Wai Anty shine TULA TULAN? ina jira naga wata balloon ni ashe ma kunu ne"
"Ba zaki gane ba yarinya kedai dauki kisha a jikinki zakiga tula tulan da ake magana nan duk da kika ganmu shi yake taimakar mu gamun mun haihu nawa amma Qirji na nan a cike" se ta rufe fuska kuma wai kunya Unaizatu tace
"Kyaji da munafuncinki Malam ni maza ki shanye ki bani kofina.
(Domin mallakar naki ki tuntubi Maman Ilham mai Tula Tula akan 08135613021 tana Kaduna tana aikawa da kaya ko ina a fadin Nigeria).
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 66

UMAIMAH

Kasa zama tayi ta jira Safina ta gwammace ita ta tafi gidanta, a Get suka hadu da Jalilah zata shigo ita kuma zata fita suka jefi juna da kallon Banza motar Jalilah na shiga ta Anty Amina ta biyo baya dole Umaimah ta jira suka shige dan a jere suke se hararar su take tamkar idanunta zasu fado. Jalilah ce ta kwalawa Sammani kira ya bar bakin Get da gudu ya shiga cuki, ta bude masa boot ya dakko wani kwali da Umaimah ke da tabbacin na akwati ne gasu nan guda biyu ya dauki daya ya shige bangaren Hajiya ita kuma Jalilan ta fara fito da kayayyaki daga back sit dinta Haka ma Anty Amina cikinsu babu wanda ya sakw kallon koda inda motarta take. Kwafa taja kafin ta taka motar da qarfi ta bar gidan, a falon Safina ta baje bayan ta soya musu kwai da dankali sunci Wanda turawa kawai Umaimah take amma komai daci yake mata a baki.

"Qawata ki kwantar da hankalinki na kira Malam tun jiya kuma yace kwana zeyi yana aikinki, yace in tambayeki hayaqin daya baki yace kiyi a tsakar gida kinyi kuwa?" Safina ta fada se Umaiman ta tabe baki tace
"Ni hayaqi daya na gani wanda yace na ringayi a dakinsa kuma nayi"
"Sun dauke abinsu kenan" Safinan ta fada kafin taci gaba da cewa
"Haka fa suke wlh se Malam ya baka abu me ci subi dare su dauke abinsu, bari toh na gaya masa ya sake hado miki dashi se kiyi Azama da an kawo ki turara dan alamu sun nuna Faka faka ne" haka tayi ta subadadi ita dai Umaimah jinta takeyi har aka kira Safinan a waya ta fita se gata tareda wnai saurayi se bayan ya zauna Umaimah ta ganeshi Almajirin Malam din da sukaje gurinsa ne.

Wasu sababbin tarkace ya kawo mata harda layu ya bata wasu qananu da yace a abinci zata sakawa Khalil din ta tabbatar da ya hafiye se wata lafceciya da zata tsaga pillow ta saka a ciki, se Rubutu irin na farko yace ta qara ruwa ta bashi dana Abincin shima harda qarin na Nama kamar yaji yake amma shi da gasashshen nama za'aci yaron ya miqa mata yana cewa
"Dandanonsa kamar yaji yake amma fa ki kula koke karki dandana kuma kar ki bashi yaci sama da sau dan qarfi ne dashi wlh, yace wancan turarenya qare amma idan an hada wani za'a kawo miki kuma wai ki ringa haquri kina danne zuciyarki dan kinada saurin fushi da hasala ga qawa zuci shi yasa aikinki baze ci da sauri ba". Daze tafi wasu uban nin kudin Safina ta debo ta bashiya kaiwa Malam sannan ta bashi ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na mota ya wuce yana musu godiya.

"Nifa bazanyi amfani dasu ba ingaya miki wanda ya banin ma me suka mun balle na qara wasu, tashi zanyi ma na tafi yanzu naje naci kutumar ubansu gaba daya dan nasam sun hadu a gidanda zan fito yar iskar Jalilan nan da Amina sunzo nasan Jamilan ma tana tafe duk zan hada naci uwarsu la'ada waje" Umaimah ta fada Safina dake hade mata kan tarkacenta tace
"Umaimah ikon Allah, na roqeki sau daya a rayuwa ki gwada juriya ki dauke kai ki bawa aikin nan sati daya kedai ki tabbata kinyi komai yanda Malam yace se ki koma gefe ki zubawa sarautar Allah ido wlh na tabbata se kin sha Mamaki"

"Uhm, kanki ake ji" Umaiman ta fada tana tura qeya Safina tayi dariya tace
"Ohni Allah Kiga yanda kishi ya fitar dake daga hayyacinki a dan lokaci Allah dai ya kiyaye bacin rana amma in aka samu kuskure auran nan ya yuwu kice zaucewa kawai zakiyi dukda ma bame yuwu ba bane in sha Allahu" Safina ta sake fada, Umaimah tayi mata banza tana danna waya Safina ta sake cewa
"Nifa idan nice Mijina yake sona kamar ke din nan wlh ko zeyi auran ba wani damuwa zanyi ba, kwantar da hankali zanyi tazo na mayar da shegiya yar aiki se yanda nayi da ita kuma Miji nawane, koni da kikaga ina tsoron amun ai saboda a dofane nake gurin Mijin Uwarsa da danginsa kaf ba sona suke ba da banida Malam Sha yanzu ai bansan ya rayuwata zata kasance ba wlh". Ita dai Umaimah bata kulata ba haka ta gaji tayi shiru, bayan Azahar tace zata tafi, Safina ta rakata har gurin Mota tana sake jaddada mata da dan Allah ta dauke kai kome za'ayi karta kula su.

"Ke ni ban tambayeki ba ya kukayi zancen mota ne?" Safina ta fada se Umaimah ta juya tace
"Bece komai ba, to ya mayi maganar na rotsa masa kai shima ai yasanhaukata shi yasa baya tanka mun in ina sama"
"Toh Allah ya sakko dake amma fa kinyi ganganci kuma ko dan gaba ki ringa sanin abinda zakiyi. Banda shirmen ki da haquri kikayi idan ya tashi ma kice ita kike so a matsayin kayan fadar kishiya tunda zaman lafiya yake nema mu samu ta yawo muyita zaga gari muna hura hanci amma kika mata rotse ke shi be mora ba ke baki mora ba wannan ai mugunta ce"
Motarta taja ta fice Safina ta koma ciki tana mita.

Sanda ta isa gida cike ta tarar da Compound din da motoci kamar ana wani biki a gidan dan motarta ma a waje ta ajiyeta, har ta niyyaci ta shiga bangaren Hajiyar tayi tijara tace se fita da motocin zata aje tata kuma ta fasa, bata san su waye a ciki ba karta taroqa kanta abinda ba zata iya ba. Ruqayya ta gyara falon tas ta kwashe duk abinda ta lalata jiya ta kai store, tana aje mayafinta taji sallamar Nuratu a bakin qofar tana kwankwasawa seta koma ta bude Nuratunta shigo tana cewa
"Inata kiran sunanki kamar wadda ta toshe kunne bakiji ba".

Zama Umaiman tayi tana cewa
"Banji ba wlh, kamar tare muke nima shigowata kenan gyalena kawai na ajiye naji knocking"
"Ai taren ma muke ina ta binki a baya tun daga babban Titi"
"Au wai kece daman kinsan na kusa tsayawa naji waye yake bina haka kamar jela sedai na fasa mota kika canza kenan?" Umaimah ta sake fada, se Nuratu ta gyara zama tana cewa
"Ba tawa bane, ta Yah Hajiyayye ce Baban Asad ya gwangwajeta da dalleliyar mota cikin kayan fadar kishiya".

Wayar da Umaimah ke dannawa ce ta subuce daga hannunta ta fadi qasa kafin ta zubawa Nuratu ido yanda kasanbata fahimci yaren da tayi mata ba ita kuwa ko a jikinta taci gaba da cewe
"Kinga danqareren gidan dayake gina musu? Ko ita bata sani ba se a satin nan Qanwarsa ta fesa mata gulmar bangaren Maman Asad hawa biyu ya mata yace ta sakata ta wala ita da yayanta Amaryar kuma yayi mata hawa daya sannan a bangaren kowacce yana da nasa part din kinga babu abinda ze hadasu se idan su suka so haduwar kuma ma Allah ya taimaketa yanda take babu ruwanta haka Allah ya dubi zuciyarta ya sakashi nemo yarinyar itama an shedeta bata da matsala sedai fatan su zauna lafiya idan an hadu".

Har Nuratu ta gama surutu Umaimah ba zatace ta fahimci wani abu ba tun bayan zancen kayan fadar kishiya da taji, Bandaki ta wuce ta bar Nuratu na gaisawa da Ruqayya data kawowa Nuratun ruwa da snacks zuciyarta ta ringa bugawa yanda kasan ita aka ce an kaiwa kayan fadar kishiyar wato da gaske kenan yarinyar data gani gidan Maman Asad din budurwar Mijinta ce amma kuwa Hajiyayye ta cika Jakar mata mara zuciya (in ji Umaimah fa). doguwar rigar Atamfar jikinta ta cire ta watsa ruwa kafin ta dauro Towel ta fito, Nuratu ta kalleta ta zaro ido tace
"Kai Umaimah kin ganki kuwa anya cikin nan be wuce lokacin sa ba kuwa yaushe suka ce miki EDD?"

"Ai ke bazaki taba ganin abu kiyi shiru ba se kinyi magana tunda dai bake kike dubani ba se ki saka ido in lokacin haifarsa yayi ai ze fito" ta fada cike da fitsara tana kallon Nuratun se ta maida mata da cewa
"Ke ai baki gama sanin ciwon kanki ba daman har yanzu shi yasa, ni ba zuwa nayi muyi rigima ba, zuwa nayi na gaya miki gaskiya a matsayina na yar uwarki tunda mun zura miki ido gaba daya munga ke baki san zuru ba. Naje gida yanzu duk na tarar dasu har Yah Naziyya tazo tun shekaran jiya tana Kano ke kadai ce babu kuma daman wannan bashi ne karo na farko da za'ayi wani taro a gida kike qin zuwa ba shiyasa yanzun ma sukace bazasu gaya miki ba kowa a cike yake dake.

Yanzu Umaimah tsakaninki da Allah yaushe rabon da ki daga waya ki kira wata daga cikinmu da sunan ayi zumunchi ballantana ki taka kije gidajenmu? Ni daman na cire kaina a lissafi amma ko Maman Asad ban zata harda ita kika watsar ba duba da kunfi shiri da ita duk a cikinmu. Yanzu Naziyya da ba'a gari take ba waya yar mecece da bazaki daga ki kirata ba ashe har tayi rashin lafiya ta kwanta a Asibiti baki dubata ba kuma Mama ta gaya miki kika share. Su kansu can gidan ba zuwa kike ba se idan taki ce ta kaiki anya kuwa Umaimah rayuwa zata yuwu a haka?

Ke idan kin nemi mutum to matsala ce amma in kina zaune lafiya babu ruwanki da kowa se yawon bin gidajen qawayen ba babu abinda kike amfana dasu duk qawayenki na kirki wanda kuka tashi tare kin watsar dasu saboda suna gaya miki gaskiya kuma suna hanaki abinda be kamata kin gwammace kiyita bin irinki babu meyiwa wani fadan be kyauta ba a cikinku. Yanzu wace qawa kika samu a unguwar su Anty Hafsa da kullum kina hanyar gidanta kuma saboda tsabar baki da mutunchi wani lokacin ma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login