Showing 297001 words to 300000 words out of 429394 words

Chapter 100 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

957

ya tarar da qullin maganin Musa yaron maqocinsa ya kai mata ta ajiye masa.

Bayanya gaya mata yanda sukayi da Dattijon tace masa
"Ka gwada toh gashi nan kuwa dare daya ka rame dan jiya ba haka ka shigo ba duk idonka sun fada idan ka fita ka biya Asibiti a sake dubaka, na gaya maka ka cire komai daga zuciyarka kaqi bafa a fara ba Babana idan ka karaya tun yanzu ta yaya zaka tafiyar da zaman naku? In har kana ganin ba zaka iya jurwwa na lokaci be qure ba ka janye zama lafiya aka ce yafi zama dan sarki meye amfanin abinda za'ayi a maimakon ka samu nutsuwa da farin ciki ka sake gayyatowa kanki wata damuwar?"

"A can tsohon gidana nake so na ajiyeta, gyaransa kuma a qalla ze iya daukana wata shida Hajiya, idan kun sake yin magana da Baba Abu ki gaya masa se kuma maganar abinda za'a kai shima idan ya yanke se ki gaya mun na tura masa" ya bagarar da maganar da takeyi ya canza mata da wata, se taja numfashi tace
"Yace Alhaji Garba ya bada dubu dari biyu dukiyar aure shi kuma ze bada Dari Sadaki se kaji da biyan bashin da Hasanar ka ta tattago maka su"
"Allah ya saka musu da Alkairi" ya fada kafin ya kwance maganin yana kallonsa Hajiya tace
"Musa yace baya komai suma idan suna ciwon kai Kakan shi yake shaqa muba se ma daya gwadamun yanda akeyi bari ka gani" ta debi garin kadanta shaqa Khalil na kallonta haka ya diba shima ya shaqa da dan yawa ya qulle ledar.

Zama yayi yana jiran Habiba da take soya doya, kamar qura ta taso haka yaji kansa yayi dummm kafin kace me ya shiga jera Atishawa babu qaqqautawa. Tun Hajiya na daukar abun da sauqi harta tsorata ganin yanda yake yinta ya kasa zama akan kujera ya sauka qasa yana ci gaba da jera ta da qarfin gaske idonsa ya tara hawaye. Habiba ta kwalawa kira ta fito a rikice itama dan tana jiyo Atishawar tasa data zarce hankali.
"Kiyi maza ki shiga gidan Officer kice wa Musa yazo" Hajiya ta fada tana riqe Khalil dake Atishawa kamar wanda ya sauka daga iska, fitar Habiba babu dadewa se gata sun dawo tareda Baba Musa, Hajiya ta kalleta tace
"Musa qarami nake nufi ba kai ba Alhaji"
"Wannan kiran ai nawane Hajiya bana Takwara ba, ta gaya mun halin da ake ciki ne nace bari nazo da kaina na gani sannu Ibrahimu kaji Allah ya qara taqaitawa ai mantawa nayi daman ban gaya maka ba, idan da Sihiri ko sammu indai shaqarsa yayi da izinin Allah seya fitar da duk ma abinda ya shige masa kai wannan Atishawar da kika gani shaidanun da suka samu guri akan sa suke haddasa masa ciwon ne suka fita sannu kaji, da za'a samu tazargade se a sake turara masa babu komai in Allah ya yarda sannu" ya sake fada yana dafa Khalil dake zaune a qasa yana maida numfashi dan Atishawar ta lafa masa, kuma wani ikon Allah duk wannan nauyin da yake jin kansa ya masa ya sauka sakayau yake jinsa kamar wanda yayi sabon Aski.

A tarkace Hajiya ta binciko Tazargadenta dade da wata Qanwarta ta kawo mata tace ta ringa turarawa itama amma ko sau daya bata taba gwadawa ba nan Habiba ta kunna coal ta zuba, ba iya Khalil ba duka gidan suka bi suka turare Hajiya na cewa
"Ni Aishatu Babana a ina ka shaqo wannan jaraba kuma koma ina ne dai an auna arziqi tunda mun samu makarin abun da wuri kai Allah kayi mana maganin abinda ya dame mu"

"Nifa Hajiya ban yarda da wani Asiri ko menene ba kawai ciwon kaine kuma stress ya kawo shi, me nayiwa wani da zeyimun Asiri nida hayaqi in ba akan titi ba na motoci a ina nake ganinsa ma ko turaren wuta za'a saka a gidan nan kin sani kafin nadawo an saka dan bana son na ringa shaqar qaurin" Khalil ya fada se Hajiya tace
"Ai shikenan, Allah yaci gaba da karewa ka tashi kaci abincin idan babu hali ka haqura da zuwa aikin ma kawai yau daya dai ka huta" .

Hakan kuwa akayi Anwar ya kira ya bashi uzurin bashi da lafiya yayi duk abinda ya kamata, a nan bangaren Hajiya ya wuni daman Itama Umaimah tara bata cika ba ta bar gidan. Sanda Jalilah tazo haka ta sakashi gaba seda suka bude kayan, ya ringa mamakin yanda ta zabo kaya haka kuma Undies da dogayen riguna duk yana tunanin zasuyiwa Humairan se ya kalleta yace
"Wai ya akayi kika san size din yarinyar ne?"
"Kai dai ka zauna anan ai wlh tunda na saka raina akan se kayi auran nan babu abinda bazanyi akai ba, ni yanzu muyi maganar kudi itace a gabana na samu na sallami masu kaya"
"Ai tunda kika siyo bakiyi shawara dani ba se kiyita Addu'a har sanda zan samu kudi na biyaki dan ni banyi lissafin wani lefe a yanzu ba.

Se bayan Isha Umaimah ta dawo gidan yana zaune a compound yana waya da Humaira ta wuce shi ba tareda tayi masa kallo biyu ba. Seda ya gama wayarsa tsaf sannan ya shiga gidan, haka nan yake ji shakkarta ta ragu a zuciyarsa tana zaune a falo tana waya ya haye sama warin Tazargaden da Jalilah ta saka masa duk ya cika gurin dole ya sake bude windows ya kunna Ac. Tunda Hajiya ta labar ta mata abinda ya faru da safen tayi tsalle ta dire akan Umaimah ce
"Toh Hajiya a ina zeje ya shaqo wani abu in ba a gidan sa ba wannan matar tasa fa ta zarce duk yanda kike tunaninta a banza zata dauke wuta haka kema kinsan canza salo tayi ta koma yaqin ta qarqashin qasa kuma ta Allah ba tata ba, ina kowa zan gayawa Abban Sadiq ya hada masa magungunan karya sammu dana tsarin jiki daman ya fara hada naki in Allah ya yarda duk mugun abunta sedai ya koma kanta" haka ta kwashi tazargaden taje ta turara Hajiya na hanata amma taqi ji sa'a daya Umaiman bata nan da Allah kadai yasan yanda za'a kwashe.

Seda ya feffesa freshener kafin ya sake sauka qasan, bata falon ya zauna dan yasan zata fito so yakeyi ya gaya mata zancen tafiyarsa jibi yana nan zauna ta fito tana tura ciki se yamutsa fuska takeyi bata ko kalli inda yake ba ta zauna a qasa tana kiran Ruqayya.
"Idan Allah ya kaimu ranar Friday zamuyi tafiya dasu Baba Abu zamu iya dawowa Saturday ko Sunday ya danganta da yanda muka gama abinda ya kaimu" ya fada a sanyaye qirjinsa na bugawa. Be zata zata kula shi ba se kuma yaji tace

"Ina zaku je?"
"Jalingo" ya bata amsa zuciyarsa kamar ana kodan kwarya dan seda ya fada yayi dana sanin fadar idan kuma tasan garinsu Humairan fa ya sake kunno wata wutar da ze kasa kashewa. Zaman jiran yaji ko zata sake magana yayi amma har Ruqayya ta kawo mata abinci ta shiga cin abinta bata kulashi ba se ya miqe yana sauke ajiyar zuciya yace
"Zan tura miki da saqo ta account" kamar da dutse yake magana haka ta masa banza, ya wuce sama yana sauke Ajiyar zuciya, Umaimah ta bishi da wani matsiyacin kallo kafin taja tsaki a fili tace
"Se inga da qafar da zakaje Jalingon ai Mtsw" ta sake jan tsaki taci gaba da cin abincinta. Seda ta gama tsaf kafin ta koma dakin ta dakko yar robar da Malam ya sake aiko mata da ita bayan ya kira shida kansa ya sanarwa da Safina zancen tafiya neman auran dasu Khalik din zasuyi. A corridor ta tsaya inda yake ajiye takalmin da yake zuwa sallar asuba dashi ta saka leda a hannunta ta debi man dake cikin robar zuciyarta ta rigada ta qeqashe biyan buqata kawai take nema babu bata lokaci ta shafe duka takalman qafa biyu da yake zuwa salla dasu tunda bata san wanda ze saka ba. A sharar waje taje ta yarda ledar da robar maganin ta wanke hannunta tasa kafin ta koma daki ta kwanta, seda ta turawa da Safina saqo a WhatsApp cewar tayi seta maido mata da cewa

"Yawwa qawata, kedai ki ci gaba da jurewa ranar biyan buqata ai rai ba a bakin komai yake ba in Allah ya yarda mune da nasara.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 67

KHALIL
Cikin ikon Allah a daren yayi bacci me dadi wanda har ya iya tashi yayi sallah raka'a hudu kamar yanda ya sabayi a kowanne dare, da yake dab da Asuba ya farka bayan ya idar da sallar be koma bacci ba, Lazumi ya ci gaba dayi har akayi kiran farko kafin ya tashi ya shiga wanka yayi shirin masallaci bayan ya cire kayan da ze saka da sauran abinda zeyi amfani dasu saboda da wuri yake so ya fita, jiya beje office ba kuma akwai abubuwan daya kamata ace yayi dukda Anwar yana nan. A masallaci Baba Musa daya ganshi yake cewa

"Madallah kace jiki yayi kyau gashi yau ka fito da wuri yanda ka saba, toh Allah ya qara kikayewa. Ka nemi ganyan magarya masu kyau ka zuba a ruwa ka tofa Ayoyin nan na karya sihiri kayita sha kana shafe jinka sannan koda yaushe bakinka karya yi shiru daga ambaton Allah duk abinda kake yi ka ringa Istigfari kana hailala kaga Istigfari waraka ne daga duk wata damuwa sannan karka ringa rabo da Karanta Lahaula, ka kuma ringa tofata qafa dari a ruwa kullum kaida Yayanka da Iyalinka kusha ku shafe jikinku duk abin maqiyi sedai yayi amma baze same ku ba da yardar Allah".
Godiya yayiwa Baban suka rabu bayan an idar da sallah ya shiga gida.

Yana tsaye yana saka kaya haka kawai yaji qafarsa ta sage kamar wanda ya taka qanqara, zama yayi akan gado yana duba qafar, shidai baya tunanin yaji ciwo ko ya buge da wani abu a kwanakin nan kuma ko dogon tuqi beyi ba qarqarinsa daga gida ne yaje office idan ma zasu fita site yawanci Anwar ne yake tuqasu. Haka ya qarasa shirin ya fito, dakyar ya iya sauka daga benen ya zauna a falon qasan yana maida numfashi. Takalmin daya saka ya cire hada da safar yana sake duba qafar. Yafi minti goma a zaunen, jin an bude qofa ya sakashi daga kai ya kalli gurin, Umaimah ce tayi masa kallo daya ta nufi hanyar kitchen bata dade ba ta fito da cup a hannunta ta sake wuce shi ta shiga daki.

Haka ya ringa takawa dakyar ya fice daga gidan ya shiga bangaren Hajiya.
"Babana lafiya kake dogara qafa kamar me karaya?" Hajiya ta fada tana kallonsa ganin yanda yake tafiya kamar wani Saqago. Seda ya zauna yana cije baki saboda yanda yake jin qafafun nasa kafin ya shiga gaisheta ta amsa tana cewa
"Me kuma ya samu qafar?"
"Nima ban sani ba Hajiya, ina dawowa daga Masallaci naji ta riqe mun kuma abin qaruwa yakeyi, ba ciwo take mun kawai qashin ya riqe tun daga guiwata har zuwa tafin qafar" ya bawa Hajiyar amsa seta matsa kusa dashi tana duba qafar tace

"Ikon Allah sanyi ne toh, shiyasa nake yawan maka maganar Ac da baka rabo da ita gida da Office irin wannan sanyin qashin nake gudar maka wani baya tashi tambayarka se girma yazo musamman ku da daman kuna da Gadonsa kana kallo Mahaifinku harya rasu yana yana fama da ciwon qafa toh Allah ya taqaita, bari na dakko man zafi na shafa maka ko zata saki in yaso kaje Asibiti su baka magani daga baya".

Sama ta wuce ta dawo da qananan robobi na Man Mainasara da kuma kwalbar Aboniki, da kanta ta shafe???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? masa qafafun tun daga guiwar har tafin qafa. Seda ya karya a bangaren Hajiyar kafin ya fita zuwa sannan qafar ta saki dukda ba gaba daya ba haka ya wuce office. A can dinma aikin yana yi yana hutawa saboda yanda qafar take riqewa se kuma ta saki. Rigima Humaira ta saka masa akan tanason ta ganshi kamar ba jiya yaje gurinta ba, babu yanda ya iya haka ya biya Gidan Unaizatu bayan ya tashi aiki. Be shiga ciki ba a qofar gida suka tsaya. Cikin kulawa Humaira ta kalleshi ganin yanda yake cije baki yana canza tsayuwa tace

"Yah Khalil meya sami qafarka naga ka kasa tsayuwa da kyau?"
"Babu komai dan ciwo takeyi mun amma yanzu idan na tafi daga nan zan biya naga Likita inaga nayi over working kaina ne shi yasa nake ta jin babu dadi a jikina" ya bata amsa seta sake narke fuska kamar zatayi masa kuka tace
"Wayyo sannu Allah ya baka lafiya, ciwon qafa babu dadin ina gani idanya tasarwa Mama ko bacci bata iyayi amma idan na tofa mata Fatiha se kaga ta dan samu sauqin ciwon kaima idan kaje gida kacewa Anty Umaimah ta tofa maka".

Kallon ta yakeyi har ta kai qarshe yayi dan murmushi yace
"Ashe kin san sunan matata amma shine kullum kika tashi magana sedai naji kince Matarka?"
Tura baki tayi ta kalli gefe ba tareda ta tanka masa ba ya sakeyin murmushin qarfin hali dan sosai qafar ta matsa masa ya ce mata
"Bari naje Baby, zamuyi waya idan na isa gida kinji" seta daga masa kai tace
"Toh, Allah ya qara sauqi yanzu a haka kuma gobe zakayi doguwar tafiya?"

Shaf ya manta ma da wai gobe zasuyi tafiya, se ya sake yi mata murmushi yace
"Eh mana ko bakya so naje?"
"Aa kaga fa qafarka na ciwo ka bari kawai se next week se kuje saboda zaman mota fa da wahala ko baka ciwon qafa daga nan zuwa Jalingo se kaji jiki ballantana kuma kana fama da qafa"

Bude ido yayi yana kallonta yace
"Dan Allah fa? Kinsan ni ban taba zuwa Taraba ba nadai je Yola shima a jirgi so ban san nisan tafiyar ba"
"Aiko da nisa ga hanya bashi da kyau shine ma abinda yake qarawa tafiyar nisa" ta bashi amsa. Se ya bude motar ya shiga, Carton din Madarar waken suya ta kwalba daya tsaya ya siya a hanya ya miqa mata yana cewa
"Gashi, kwanaki naga Anwar ya siyawa Matarsa wai yana saka qiba ki gwada sha mu gani ko ze karbeki kinsan Matata qatuwa ce kar kuzo dakuwa tafi qarfinki".

Kallonsa ta tsayayi se kuma ta zumburi baki ta harareshi qasa qasa tace
"Allah ya sauwaqe nayi dambe da Kishiya"
"Me kika ce?" Ya fada yana kallonta seta dauki Carton din ba tareda ta bashi amsa ba ta wuce seda taje Get ta waiwayo ta murguda masa baki irin yanda yara sukeyi tace
"Da zakace matarka qatuwa zata dakeni ai abun ba a qarfin jiki bane kuma ai a qauye ne ake kishin hauka ana doke doke" tayi saurin shigewa ciki Khalil daya saki baki yana kallonta yace
"Ikon Allah" lallai ya yarda da Jamila da tace ba'a raina mace komai qanqantarta gashi kuwa ya gani, in har zata iya maida masa da Magana to Umaiman me?

Tashin motar yayi ya wuce, yanda yake jin qafarsa dole ya wuce Asibiti tun kafin ya isa ya kira Dr Al'amin likitan da Umaimah take gani a yanda ya fada masa yayi sa'a Physiotherapists dinsu is on Sit dan haka zeyi masa booking kafin ya qaraso. Sanda yaje be jima ba ya samu ganin likitan, bayan duk bincike da tambayoyin daya kamata yayi masa akan musabbabin ciwon qafar tasa ya rubuta masa magani nasha dana shafawa da zasu rage masa Ciwon qafar sannan ya gaya masa ya daure dukda yanda yakeji ya ringa motsa qafafun kafin ya bashi X-ray dan su duba da kyau suga ko wata matsala ce ta ciki dukda Khalil din ya tabbatar masa da wayonsa be taba faduwa ko wata buguwa da zata janyo ciwon ya tasar masa yanzu ba kamar yanda Likitan yake tunani. Seda ya koma gurin Dr Al'amin ya gaya masa yanda sukayi ya karbi takaddar X-ray din yace masa ya dawo da safe sannan yayi masa fatan samun lafiya.

Har Khalil ya kai bakin qofa Dr Al'amin ya tsayar dashi yana cewa
"Yauwa kaga na sha'afa, Madam bata zo Antinatal ba jiya ina taso na kiraka wlh aiki ya dauke mun hankali. Daman tun last week na gaya mata ban sani ba ko kunyi maganae idan har ta wuce satinnan bata haihu ba to gaskiya sedai Muyi mata CS kawai a cire abinda yake cikinta dan tun farko data bamu hadinkai ma da yanzu anyi amma ta nuna bata so ita amma kai ina so ka fahimci halin da take ciki da complications din da cikin nan ya samu CS din is the best option dan haka ka lallasheta, if possible within the weekend kuzo kawai a cire Babyn".

Ajiyar zuciya Khalil dake sauraronsa yayi kafin ya tabbatar masa idan ya koma zeyi magana da ita duk kuma yanda sukayi ze kira Dr a waya ya gaya masa, suka sakeyin Musabaha ya fita yana tafiya a hankali saboda duk in ya motsa qafar shi kadai yasan abinda yakeji. Dakyar ya iya kai kansa gida saboda mommotsa qafar da akayi tamkar an qaro masa ciwon da takeyi ne, seda ya dafa Khalifa sannan suka iya shiga gida. Saboda yanda yake be iya hawa Sama ba anan falon qasa yace ya ajiye shi kafin ta lafa masa se ya hau saman, Khalifa ya ringa kallonsa da tausayawa se yake tuna Lokacin da Mahaifinsu ya ringa fama da qafa dukda yana qarami a sannan amma be manta ba kamar haka wata rana idan ta tasar masa sedai Khalil din da Me Gadinsu su kama shi su shigo dashi cikin gida gashi yanzu Yah Khalil ma yayi Gado.

Shi yaje ya gayawa Hajiya a yanda Khalil din yake, yana zaune kan carpet bayan ya samu dakyar yayi alwala a bandakin dake falon yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya a zaune yana Azkar Hajiyar ta shiga da sallama ta zauna kan kujerar da yake jingine tanacewa
"Babana qafar ce yanzu Khalifa yake gaya mun se shi ya kamak kuka shigo kaje Asibitin kuwa daka fita"
"Naje Hajiya sun bani magani na sha dana shafawa sannan gobe zan koma ayi hoto" ya bata amsa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login