Showing 168001 words to 171000 words out of 429394 words

Chapter 57 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1014

layin Umaimah ya kira, bata daga ba harta katse ya sake kira sannan ta daga ta bashi Uzurin Alwala takeyi Ankira sallah. Seda yayi namijin qoqari gurin danne bacin ransa ya saisaita muryarsa yace mata
"Kunyi maganar Hadiza da Khausar ne?"

UMAIMAH
Ranar da take jira ce tazo gashi ya kawo kansa da kansa dan haka yanzu za'ayi maganar, shigewa daki tayi ta zauna gefen gado wutar kishin daya qyastawa ashana ta shiga ruruwa a zuciyarta tace
"Daman ina jiran Allah ya kawo ranarda kai da kanka zakayi mun zancen yar iskar karuwar da kake nema a matsayin mata. Ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan ido na toh Asirinka ya tonu munafikin Allah dakai da yar iska ragowar Maza da Matan da kake nema. Wallahi kaji kunya Khalil, in ma mace zaka nema ka nemi me aji mana amma se yar Lesbian dabba me neman jinsinta"

"Ya isheki Umaimah" Khalil din ya daka mata razananniyar tsawar da seda taji dan cikinta ya juya kafin yaci gaba da cewa
"Tambayarki nayi kunyi magana da Khausar kuma naji amsata, sannan ina so ki sani ita Wadda kike kira Dabba karuwar tafi ki sau dubu a gurina, ban taba sanin wawiya ceke mara tunani ba se a wannan karon Umaimah, kinsan girman laifin da kuka aikata kuwa? Kinsan girman qazafi kuwa qazafi ma mafi muni saboda ke Mahaukaciya ce a hada kai dake a ruguza rayuwar yar uwarku mace, To ki shirya kin tayata kun lalata rayuwar wata a dalilina yanzu kece next target dinta, sannan ki shirya karbar sakamakon abinda kika aikata nan bada dadewa ba" yana kaiwa nan ya datse kiran wayarsa wata irin tsanar Umaimah nayi masa dirar mikiya.

Zare wayar tayi daga kunnenta tana so ta tabbatar da Khalil tayi magana ko kuwa wani ne yayi mata basaja. Ita Khalil yake kiran karuwarsa ragowar Mata ta fita daraja a gurinsa? Anya ma kuwa yana cikin hayyacinsa?
Neman guri tayi ta zauna saboda yanda taji kanta yana juya mata, ita Umaimah dai har tayi lalacewar da Khalil ya zabi karuwa akanta kuma yake iqirarin zeyi shari'a da ita saboda wata banza, ai kuwa seta tabbatar masa da be gama sanin wacece Umaimah ba, fili zata siya a gidan Radio da Jarida ta buga labarin idan yaso ya kaita Majalisar dinkin duniya ma qarewar Shari'a. Qwafa tayi tasaka Hijabi ta tayarda sallar da sam babu nutsuwa a cikinta saboda hankalinta gaba daya yana ga daukar fansa.

Tana idar da sallarta kira Rufaida, a taqaice tayi mata bayani Rufaida ta janyo Jimlar Ashar ta dire kafin tace
"An dira ki da ka Umaimah, kinfa san daman masu neman matan nan babu wanda ya kaisu bin Malamai da haka suke Asirce Yaran mutane suna lalata su toh Wallahi Khalil ma ta gama dashi dan dai kinsan da hankalinsa da mutunchinsa baze taba bari ko gaisuwa ta hadashi da irin matan nan ba. Se kin tashi tsaye kin rabasu in kuma ba haka ba kinaji kina gani za'a kwaso miki jangwangwama"

"Ai wallahi ko zan tafi tsirara Khalil be isa ya aureta ba, bama ita ba duk wata mace me daura zani da dankwali ita da Khalil sedai hange daga nesa dan nawa ne ni kadai ba Asiri ba ko tsafi Mace takeyi sedai ta gaji amma Khalil yafi qarfinta, ni kinga gobe inda ranka zan tafi na kai musu rahoto har address din unguwarsu dana inda take aiki duk zan hada na basu, badai Mahaukaciya ya cemun ba? Zega qarshen hauka kuwa" Umaimah ta fada se Rufaida tayi saurin tareta da cewa
"Aa karkiyi haka, wannan ma da mukayi ya isa. Ki ga ki bari gobe zanzo mu zauna se musan abinyi na gaba. Amma Su Mama basu san labarin nan ba ko naji baki ce komai ba?"

"Oho in ma sun sani banji kowa yayi zancen ba, jiya nema da Maman Asad tazo take maganar wai ta gani a Facebook suka taru sunata surutansu wai wadda ta yada bata kyauta ba wanda ya rufawa wani Asiri shima Allah ze rufa masa a raina nace kanku akeji na shige daki, duk tsiya dai zasu sani idan ta fashe kowa zeji ai" Umaiman ta sake fada daga nan suka qarasa shiryawa akan Gobe Rufaida zata zo dan haka ta dakata karta dauki wani mataki har se sun tattauna sannan.

Khalil

Be taba zaton rashin tunaninta yakai haka ba, koda ace Khausar ce ta shirya komai Umaimah tafi kowa laifi tunda ai ba mahaukaciya bace ita ko qaramar yarinya da bata san me takeyi ba, tayi amfani da wauta da rashin tunaninta ta sakata a matsala dan yanzu duk inda akaje aka dawo Umaimah ce a ciki ita za'a kama da laifi ba Khausar ba.
Tunanin kiran Khausar din yazo masa har yayi dialing number ya katse saboda yanzu idab har tasan yasan da hannunta a ciki zata nemi hanyar kare kanta ne, gara ya rabu da ita ta yanda z samu dama ya kanata a hannu cikin sauqi.

A daren ya hada dan abinda zeyi amfani dashi, yasan akwai jirgin Nigeria gobe dan a cikin wadanda suke aiki akwai wanda zasu taho goben take shima ya yanki ticketz ya rubuta uzurin cewar buqatar gaggawa ta same shi ta zuwa gida washe gari kuwa qarfe sha biyu na rana tayi masa a Kano bayan ya sake hawowa jirgi daga Lagos inda suka sauka. Already Jalilah daya gayawa dawowar tasa tana jiransa a Aipirt, ita ta dauke shi kai tsaye yace mata Na'ibawa zasuje yana mata kwatance har suka isa qofar gidan su Hadiza.


Kasancewar rana ta kwalle babu yaro ko daya a layin dan haka ya rasa wanda ze aika yayiwo masa sallama da ita seya koma yacewa Jalilan ta shiga ita ciki haka kuwa akayi ta shiga gidan da sallama aka amsa mata daga cikin daki ta qarasa qofar inda taga takalma a zube ta shiga.
Maman Hadiza na kwance akan Qaramar Katifa da aka shimfida mata a tsakiyar palour, idan ka santa a da ka ganta a tsakanin kwanaki biyu da faruwar abin bazaka gane ta ba. Ta zabge lokaci daya tayi wata irin rama idanunta sun koma ciki zagayensu yayi baqi saboda tsabar Kuka da damuwar data saka kanta a ciki.

A lokacin da Jalilah ta shiga ta tarar da Manyan Mata guda biyu tareda ita se Matashiya da zasuyi Sa'anni a gefe tana ballo magunguna. Maganar daya daga cikinsu ta tsinta tana cewa
"Se kace ba Musulma ba Karimatu ace kin kasayin tawakkalli ki karbi qaddarar da ubangiji ya dora miki, wannan wane irin abu ne, bafa kanki aka fara ba. Jarabawar ubangiji babu ta inda bata riskar bawa se ke ce zaki kasa karbar taki kiyi haquri yanzu ance ba'asan inda yarinya take ba kin kadata duniya me kikayi kenan ina kikeso taje kinga yanzu duk abinda ta aikata idan ma da gaske ne kinada kamasho a ciki" se dayar tayi saurin cafewa da cewa

"Ballantana ma wallahi Innani ko Qur'ani aka bani zan iya rantsewa da qaryane ba halin Hadiza bane. A wannan zamanin irin wannan sharrin ai ya zama ruwan dare. Babu damar aga mace ta kama kanta bata kula kulen maza Allah ya rufa mata asiri se magauta sun sakata a gaba sun bibiyi rayuwarta da sharri. Nan kullum idan ta gayamun abinda qawarta take zuwa tana fada akan ta me nake cewa? Ce mata nakeyi idan har Gaskiya ne abinda take fada akan Hadizan to itama halinta ne tunda tare suke komai duk inda zasuje tare suke zuwa, sannan har ta zagayo ta kawo mata gulma da munafunci kuma ta hau kai ta kasa yarda da yar data haifa ta raina ta yarda da maganar wata maqaryaciya me suffar munafukai. Bana raba daya biyu ma ko wannan abun da saka hannunta ciki dan ai babu dadewa Akayiwa Hadizan qarin matsayi kuma ance wannan din ita taso ta samu. Sannan an dade ana yamadidi a unguwar nan akan tana zargin Hadizan na mata kwacen samari duk wanda suka hadu daya ganta se ya koma kanta toh ba dole ba tana yawo da fuska kamar duwawu ga fara kyakykyawa ko wannan qyashi da hassadar ma yasa ta iya aikata mata komai wallahi"

"Kuma fa Barira kinyi tunani me kyau, to wai duk wannan abin ma an tsaya anyi bincike an tabbatar da sahihancin maganar an ji daga inda labarin ya bulla kuwa se neman kashe kanki kika zauna kinayi?" Wadda aka kira da Innani ta sake fada, ganin da Jalilah tayi kamar sun manta da shigarta itama kuma ta samu labari tayi shiru se tayi gyaran murya suka kalketa gaba daya Barira tace
"Sannu baiwar Allah, ke kuma wacece daga ina? Jajen gaskiya kikazo ko kuwa kuwa kema gulmar ce ta kawoki ku taru ku sake turata daman ga alama nan kin shigo kinyi muqus kina kwasar zance to ta Allah bata ku ba, kuma duk me yunqurin ganin bayan Hadiza sedai yaga bayan kansa wallahi"

"Haba Barira me yayi zafi haka" Innani ta fada kafin ta juya kan Jalilah data sadda kai qasa tace
"Yi haquri baiwar Allah waceceke kuma meya kawoki?"

Kallon Maman Hadiza Jalilah tayi cike da tausayi tace
"Sunana Jalilah, munzo gurin Hadiza ne tareda dan uwana Khalil yana waje ko zamu iya ganinta dan Allah?"
Daga kwancen da Maman Hadiza take ta daga kai dakyar tana kallonta tace

"Bata nan, kuma ki gaya masa karya sake zuwa nemanta gidan nan ko kuwa beji abinda take aikatawa bane?"
"Wallahi Karima kika sake wata magana mara dadi a nan sena saba miki" Innani ta fada cikin bacin rai, seta juya tana kallon Jalilah tace
"Wanene Khalil?"
"Shine saurayin daya gama bata mata lokaci har nake gaya muku ta samu Miji se daga baya yace baze aureta ba. Waya sani ko tun a sannan shi ya gano mugun halinta mune bamu sani ba" Maman Hadizan ta sake fada nan kuwa daga Innani har Barira sukayi kanta kamar zasu daketa ta fasa musu kuka tana kiranta su qyaleta taji da baqin cikin da take ciki a qyaleta duk saboda ba yar suce ta jawo musu wannan tashin hankalin a shi yasa suke cewa tayi shiru

Jalilah ganin abin nasu yana neman ya zama rigima ya saka ta sulale ta fice daga dakin zuciyarta na tsinkewa, a yanda Khalil yayi mata bayani Umaimah da wata wadda bata sani ba sune silar komai yanzu ina zasu kai haqqin wannan yarinyar? Ko iya munanan kalaman da Mahaifiyarta tayi akanta sun isheta banda tarin ala tsine datake sha a bakunan mutanen gari dukda da yawan wadanda suka santa suke mu'amala da ita sun qaryata amma kamar yanda aka fada ne laifi bashida kama dan haka duk wanda yaji labari seya gasgata alhalil qaryace. Hassada ce ta qawa da baqin Kishi na matar Saurayinta suka jefa rayuwarta cikin gararin da Allah kadai ze iya fiddata. Yau koda ace gaskiya ta bayyana ba kowane ze yarda cewar sharri aka mata ba, tabbas wata shari'ar se a lahira.

Hannunta da Khalil ya kama ne yasa ta gane ta fito daga gidan,
"Naga kin dade, ina Hadizan?" Ya fada cikin qaguwa seta bude baki zatayi magana daidai nan Anty Bilkisu da tunda ta shiga bataji tace komai ba ta qaraso gurin, takadda ta miqa mata tana cewa
"Gashi tana wannan Asibitin kuje zaku sameta" ta juta dasauri saboda bata so wani ya ganta.

Kwatancen Asibitin sukabi Khalil ne yake tuqi kamar ze tashi sama saboda sauri. Harda room number a jiki shiyasa basu sha wahalar gane dakin ba, tundaga waje yake jiyo kukan Hadiza da maganganunta da yake jinsu tamkar zubar ruwan zafi a zuciyarsa. Umaimah ta cuceta bata kyauta mata ba, idan Hadiza bata yafe mata be san yanda zata qare da haqqinta ba. Tura qifardakin yayi daidai sanda take cewa
"Waye ze wankeni? Na tabbata rayuwata tazo qarshe Umma saboda banida sauran wanda ya yarda dani. Uwar data haifeni ta kasa shaidata, mutanen da nake tare dasu sun kasa shaidata me yayi mun saura?

Wallahi dana san abinda duniya take kallona dashi kenan da tunda na fita bazan dawo gida ba, gara na hau Titi na tsaya mota ta taka ni na mutu dana ci gaba da rayuwa mutane suna kallona a matsayin me aikata mugun fasadi. Lesbian fa Umma Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ta qarasa tana girgiza kanta da take jinsa kamar ze rabe biyu saboda ciwon da yake mata. Malama Lawisa ta riqota tana zubda hawayen tausayin Hadizan hatta da Khalil da Jalila dasuka shiga kasa riqe hawayensu sukayi. Dakyar ya iya qarasawa jikin gadon cikin dakiyar daya aro dakyar ya sakawa ransa yace

"Ki dena fadar haka Hadiza kin sani ko duniya zata taru akanki ni zan tsaya miki. Idan kowa ya yarda kin aikata ni nace qaryane qazafi akayi miki kuma bazan bar duk Wanda yake da saka hannu a ciki ba sena bi miki haqqinki. Ki dena kuka kina Asarar hawayenki na rantse da Allah sunanki baze baci a banza ba nine sila kuma zan share miki hawayenki". Kasa dagowa tayi ta kalleshi ta kife kanta jikin Malama Lawisa tana kuka me karyar da zuciya, Jalilah ta qarasa ta dafa bayanta cikin muryar kuka tace

"Kiyi haquri kinji Allah yana tareda me gaskiya". Seda sukayi dagaske kafin ta tsagaita da Kukanta, kallonta Khalil yakeyi wani tausayinta yana narka zuciyarsa shidai soyayyarsa bata qareta da komai ba se wahala da tashin hankali. Shi bata samu biyan buqata daga gareshi ba sannan ana bibiyar rayuwarta da sharri duk a sanadiyyarsa.

Kallon Malama Lawisa yayi se a sannan suka gaisa yake tambayarta game da jikin nata tace masa da sauqi, tsagewar qashin data samu ce kadai yanzu ta jininta da bugun zuciyarta sun daidaita sedai Likitan yana ta jaddada mata akan a kula da duk abinda ze bata mata rai. Kai ya daga alamar ya gane ya sakawa Hadiza ido ta sauke kanta qasa har dannan hawaye basu bar digar mata ba. Se Malama Lawisa ta miqe tana cewa
"Bari nayi alwala naji ana kiran Sallah Jalilah ma ta bita suka fita daga dakin ya rage daga ita se shi.

"Kiyi haquri Hadiza nasan nine silar komai daya sameki" ya sake fada yana zama a inda Malama ta tashi, Hadiza ta kalle shi da idanunta da basa buduwa dakyau ba tareda tace komai ba

"Ki kwantar da hankalinki nayi miki alqawarin bazan zauna ba sena gurfanar da duk wanda yayi miki sharri sun wanke ki da bakinsu sun fadi cewar sharri sukayi miki" Khalil ya sake fada, seta bude baki dakyar tace

"Khausar ce ko?"
"Ba ita bace, amma ita ce sila, Ita ta shiryawa Umaimah komai ita kuma ta aiwatar" Khalil ya fada ba tareda ya bari sun hada ido ba, besanya zata dauki abun ba idan taji cewar matarsa ce silar shiga damuwarta. Ga mamakinsa se ji yayi tayi murmushin daya tabbatar na baqin ciki ne tace

"Tazo gidan mu amma bamu hadu ba"
"Ita ce ta watsa hotunan a social media, zan bi miki haqqinki gaba dayansu se sun fuskanci shari'a dole a kwatar miki haqqinki" Khalil ya sake fada, seta zame ta kwanta tana cewa
"Na yafe musu, kai su gaban shari'a ko akasin haka babu abinda ze chanza, shi mutunchi tamkar madara ne sun rigada sun bararmun da nawa ba kuma zan qullace su ba dan dukkanninsu suna da dalilinsu na aikata hakan".

Kallonta kawai Khalil yakeyi saboda Mamaki ya kasa ce mata komai, ta yaya zata yafewa wanda yayi mata wannan mummunan qazafin?
"Amma Hadiza..."
"Ni sukayiwa kuma nace na yafe, Allah ya yafe mana gaba daya" ta sake katse shi sannan ta juya masa baya saboda wani Kuka daya taho mata ba kuma tason ya gani. Sam bata ji haushin Umaimah da yace ba, bata santa ba tasan haka kawai bazata qirqiri abu ta liqa mata ba Khausar ce silar komai daya faru.
Tunda take da ita koda wasa bata taba sanar da wani irin rayuwar da takeyi ba saboda roqonta da tayi akan ta rufa mata asiri kuma ta tayata da Addu'a saboda ta dena, ta riqe mata amana haka zalika bata taba yin sallah ta tashi ba tareda ta roqar mata yafiyar ubangiji tareda shiriya ba amma shine ta rasa abinda zata saka mata dashi seta bibiyeta da sharrin abinda ita take aikatawa? Amma ba laifinta bane, laifin kanta ne data ci gaba da Mu'amula da ita har bayan tasan zahirin wacece ita, gashi yanzu ta shafa mata baqin fentin da har abada baze taba gogewa gaba daya ba amma yaqinin daya take dashi Allah yana madakata yana jiran kowa da komai.

Gajiya Khalil yayi dayi mata magana tayi shiru kamar me bacci, yana kallonta yace
Zanje gida na huta dan dawowata kenan daga SA ko gida banje ba na wuto nan, zan tafi amma ki sani koda kince kin yafe ni bazan haqura ba dole na dauki mataki akai"
"Kaje amma karkace zakayi rigima da matarka saboda ni, Sonka da kishinka ne suka saka ta aikata komai da taimakon wasu kaga laifi bana ta bane ita kadai" Hadizan ta sake fada ba tareda ta kalleshi ba dole ya juya ya fita daga dakin, a waje ya tarar da Malama Lawisa da Jalilah suna magana yayi mata sallama yayi gaba Jalilah ta bishi.

"Wai ta yafe musu tace" ya fada yana kallon Jalilah dake tambayarsa yanda sukayi da Hadizan, bude ido tayi tana kallonsa kafin cikin wani yanayi tace
"Allah sarki anyi mata mummuna ta saka fa Kyakykyawa ubangiji ya saka mata da mafiyin haka. Anyi amfani da kyakykyawar zuciyarta an cutar da ita. Na tabbata irin wannan halayyar tata ce har ta bawa qawar tata damar cutar da ita ba tareda ta sani ba ita Kuma Umaimah bata kyautawa kanta ba, ban taba zaton koda wasa zata iya aikata kwatankwacin sakarci irin wannan ba ita yanzu koda ace dagaske ne ya kamata ka yayata irin wannan abin a duniya? Idan baka rufawa dan uwanka Musulmi Asiri ba ai baka kuma bankadashi kowa ya sani ba"

"Hmmm kawai Khalil yace dan idan ita tace ta haqura shi be haqura ba, Umaimah ta dade tana abubuwa yana shanyewa, idan har zata iya yiwa Mace sharri irin wannan ba tareda tana da hujjaba gaba besan me zata aikata ba. Dole ya taka wa abin burki ya kuma dauki mataki daidai wanda ya dace da laifinta, A hanya suka rabu da Jalilah tasauka ta bar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login