Showing 378001 words to 381000 words out of 429394 words

Chapter 127 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1054

suka tarar da Maman tayi mata magana amma babu komai zata dawo daga haka ta yi musu sallama Umaimah ta rakata bakin qofar shigowa kamar karta barta ta tafi yau din jinta tayi kamar sallah ta samu abokin hira.

Seda taji Ruman ta saki Get kafin ta dawo, gurin Mama ta wuce kanta a qasa tace ta kawo ta qarasa girkin
"Jeki abinki na gama kwashewa kawai zanyi" Maman ta fada jin haka seta wuce ta fito da kular da ake zubawa Maman ta sauke tukunyar Tuwon taja gabanta ta shiga kwashewa a leda ganin haka yasa Maman ta sakar mata ta wuce dakin Abba dan ta gyara Umaimah taci gaba da kwasar tuwon maganganun Ruma na dawo mata sedata gama ta tattara tukunyar da sauran kayan gurin kafin ta koma daki dan an kira sallar Isha. Tana nan zaune taji shigowar Abba ta miqe a hankali ta fita kamar munafuka ta rabe daga bakin qofa tayi masa sannu da zuwa worn nta na bugawa da tsoron meze biyo baya amma ga mamakin ta se ji tayi ya amsa fuska a sake har yana tambayarta gida kafin ya shige ciki abinsa.
Ta sauke ajiyar zuciye me nauyi ta koma ciki a ranta tana ayyana komai zezo da sauqi da yardar Allah.

Washe gari da wuri ta kama ayyukanta kamar yanda ya zame mata jiki qarfe bakwai ta gama komai saboda ranar makaranta ce ta shirya abin Karin Abba a Try yanda akeyi ta ajiye a bakin qofarsa dan kullum haka takeyi idan ya gama ma a nan za'a aje kwanukan ta dauko. Daki ta koma ganin Mama bata fito ba tayi wanka ta zura rigarta ba tareda ta shafa mai ba dan ya qare kuma wata beyi qarshe ba balle ta samu ta siya a pocket money ta. Seda taji motsin Mama suna gaisawa da Anty kafin ta fita, ta gaida Antyn da take mata wani gani gani yanzu a tata fahimtar tunda ta aurar da Ummu-Salma ta samu gidan daula ta ke wani buda hanci itama ta aurar da ya a ganin Umaimah fa. Seda ta jira Mama ta shiga falonta kafin ta bita jiki babu kwari a bakin qofa ta dakatar da ita ganin tana shirin shiga tace
"Lafiya?" Seta diririce, dakyar ta iya cewa
"Aa daman gaisheki zanyi" se maganar tata ma ta bawa Maman dariya ta murmusa tace
"Toh yau kuma ina a tsakar gida muka saba gaisawa yau ta musamman ce da se kin biyoni har daki?" Raurau tayi da ido hawaye na shirin kwace mata daman tasan fushin Abba me sauqi ne na Maman tafi tsoro, durqusawa tayi daga bakin qofar da take murya na rawa tace
"Dan girman Allah Mama kiyafe mun ki barni na ringa shigowa dakinki ina gaisheki" ta qarasa kuka na kwace mata Mama ta juya ciki abinta tana cewa

"Kekam idanunki basa ciwo kullum kuka kamar matar Mamaci? Gaki ga dakin ai bismillah ki shigo" ta wuce cikin daki ta barta a qofar falon tana kuka, ita kam tana rasa ajin da zata saka Umaimah lokuta da yawa ta rasa wauta ce ko gabunta suke damunta se Allah amma Al'amarinta bayan Iskanci na qashin kai harda rashin cikakken wayo ma duk ta hada.
Umaimah kuwa ta gama kukanta ta tashi ta koma daki ta dora, to ita tayaya zata nuna musu ta gane kurenta bayan babu fuska? Ai ya kamata koda sau daya ne su saurareta duk wanda ya kalleta ko bata fada ba ai yasan tana cike sa nadama da dana sanin abubuwan data aikata. Da zata gaida Abbanma dai kasa shiga falonsa tayi ta durqusa daga bakin qofa ya amsa mata faran faran kai ba zaka ce akwai wani grudges tsakaninsu ba. Haka ta wuni tana bare bare da Maman ta yunqura zatayi abu zata karba koda baya cikin ayyukan da take musu a gidan so takeyi tayi mata magana ta roqeta amma tsoron yanda zata karbeta takeji ita kuwa Maman tana ankare da ita tsaf sedai tayi murmushi a ranta da zahiri ko a kullum cikin nema mata shiriya a gurin ubangiji takeyi dan ta yarda fushi bazeyi mata magani ba. A haka suka sake kwashe sati biyu kuma Ruma bata sake zuwa ba damuwa ta sake mata rubdugu ta kasa sakin jiki kamar yanda Ruman ta gaya mata dukda tayi Namijin qoqarin ranar Juma'a dasu Nuratu sukaje gidan kamar yanda suka saba har bakin qofar Mama taje ta durqusa ta gaishe su ai kam seda sukayi Suman zaune na sakanni kafin suka hada baki gurin amsa mata kowacce cike da Mamakinta, yanda ta sunkuyar da kai tana hawaye kamar wadda tazo Maula ya taba su amma suka dake, jin daga gaisuwar bata qara cewa komai ba suma basu ce mata ba ta gaji da durquson ta tashi Anty Hafsa tace
"Allah ya yayewa yarinyar nan abinda yake damunta" Mama ta amsa da Amin kafin tace
"Haka take kullum zatazo bakin qofar nan tayi ta zubar da hawaye ni kuwa kanzil bana ce mata daga nan har randa qiyama zata tsaya muddin bata budi baki tayi magana ba mu zuba mu gani itace a wahale".

A haka rayuwa taci gaba da gara mata kullum kuma maimakon ta samu sauqin Al'amura qara tsananta sukeyi a cikin wannan yanayi Ummu-Salma diyar Anty da akayi aure wata goma kenan tadawo gida haihuwa. Nan dakin da take Abba yace Ummu-Salman ta zauna dake ita bata da Matsala kamar qanwarta lafiya lau suke zaune zuwan nata ma seya zamo mata wata sa'ida tubda ko babu komai ta samu abokiyar hira musamman da yanzu itama tayi aure ta fara sanin rayuwa da yanda take cikin hikima take nunarwa da Umaiman kurakuren daya kamata tasha kansu tamkar dai maganganun da Ruma ta gaya mata sedai tsoro yasa har sannan ta kasa tunkarar Maman ko Abban kai tsaye da magana se rara gefe takeyi da suke nuna tamkar basu san me take ciki ba.

Satin Salma daya da dawowa gida ta haihu, Umaimah ce ta zama yar saka ruwan wanka bisa Umarnin Abba ga damuna a lokacin wata rana haka take zama kamar zata zauce saboda hayaqi gana girki ga na ruwan wanka safe da yamma shikansa girkin ya qaru saboda yan zuwa barka haka yan uwan Anty zasuyita yada mata magana wasu a fakaice wasu kai tsaye yanda ta ringa musu a baya wai ta baro daula ta dawo Boyi boyi da zaman dabaro, ana gobe suna wata yar Yayar Anty da suke sa'anni zamanin yammatanci tare sukayi tana yawan zuwa gidan haka Umaimah zatayi ta gwaba mata magana wai tazo cin arziqi saboda gidansu Babu kullum tana tafe yawon kwadayi abun na bala'in yiwa Nabilan ciwo amma lokacin se Anty ta hanata mayar mata da martani. Ana gobe suna tazo barkar Ummu Salman itama da tsohon cikinta sukayi kicibus da Umaimah na kwashe ruwan wanka tayi yarkace yarkace dan ba qaramar wuya taci ba kafin itacen ya kama Nabilan ta kalleta cikin izgilanci ta kalli wadda suka shigo tare tace

"Kinga ma shikenan ina zancen neman me zaman dabaro ga wata bari mu shiga na tambayi Anty inda suka samota dan da gani zatayi aiki sosai sannu baiqar Allah" yanda tayi maganar seka rantse bata gane Umaiman ba nan kiwa tsabar wulaqanci ne daman Allah Allah take tazo ta ganewa idonta yanda akace Umaiman ta koma lokacin biki basu wani ganta ba daki ta ringa shiga tana kulle kanta har aka gama yanzu kuwa bbau dama tunda an dora mata Alhakin dora garwar wanka ya ta iya da ranta. Maganar Nabilan ta mata ciwo kwarai har seda ta zagaya bayan gida tayi kuka ta more ta yarda duk abinda ta gani ba komai bane akan irin tsiyatakun data shuka a baya.

Washe gari ranar suna sega yaranta babu zato an Kawo su suka wuni tareda sauran cousins dinsu duk inda suka gifta se anyi maganarsu ta haka kuma za'a zageta wasu a fakaice wasu kai tsaye kamar yanda suke fada ai ba tsoronta sukeji ba, Mijin da take taqamar ya tsaya mata yanzu babu ita da banza duk daya suka a gurinsu da Magriba aka zo daukar yaran seda aka sha daga da Bibi kafin ymta yarda ta bisu tana kuka sosai Driver su daya kaisu ya dauke su haka rayuwa taci gaba yau baqi gobe tsumma.

GIDAN KHALIL
Washe gari hankalinsu be kwanta ba daga shi har Humaira seda sukaje Asibiti. Dr Mahmud likitan da yake dubashi ya kalleshi da murmushi bayan ya gama examining nashi ya kuma hada da bayanan da yayi masa akan abinda yaji a daren jiyaj fuskarsa dauke da murmushi yace
"Kaga abinda muka gaya maka ko? Dama na gaya maka bazamuce ka rasa lafiyarka gaba daya ba haka nan ba zamu baka tabbacin zaka warke ko kuma lokacin faruwar hakan ba amma gashi yanzu cikin yardar Allah alamun nasara sun fara bayyana. Abinda nake so dakai shine kayi qoqarin kiyayewa kar kace zaka takura kanka kamar yanda al'amarin jiya ya faru ba tareda ka shirya masa ba muna fatan hakan taci gaba da faruwa amma kayi haquri karkace zakayi gaggawa kabi komai a sannu ciwon kuma da kaji wannan dolene idan kayi la'akari da cewar ka kwashi shekaru ba tareda irin saqon nan yaje kwakwalwarka ba jijiyoyin da suke da alhakin hakan duk sun kwanta dole yanzu da aka motsa su za'a dan sha wahala kafin su daidaita su koma aiki yanda ya kamata shiyasa nace se kabi a sannu banda Garaje in Allah yayarda a dan lokaci komai ze daidaita dan Alamun nasarar da qafinsu sukazo tinda har kace kaji alamar kayi releasing sannan koda ace lafiyarka ta dawo zaka fuskanci wannan matsalar ta saurin Inzali amma kar hakan ya dameka da sannu komai ze daidaita".

Khalil dai baki kamar gonar auduga inda Humaira ta sunkuyar da kai qasa a ranta tana cewa wannan likitan bashi da kunya me makon yace ta fita. Seda ya canza masa magunguba kafin suka miqe zasu fita sukayi Musabaha da Khalil ya kalleta tana masa se anjima yace
"Madallah Amarya ina sakw tayaki murna, se a lallabamun patient dai kar ayi masa garaje".
Da kusan gudu ta fice daga office din suka rakata da dariya kafin Khalil yabi bayanta, a mota ma tasa ta yayi da tsokana ita dai ta kanne taqi kulashi, a gida Hajiya ta ringa tambayarsa meya faru saboda farincikin dake kan fuskarsa ya kasa boyuwa amma rashin kunyar tasa bata kai ya iya mata bayani ba balle Humaira se ta barsu akan kawai dadin zama ne domin ita shaida ce irin zaman da sukeyi me tsafta da girmama juna. A haka yaci gaba da lelen lafiyarsa kamar yanda likitan ya fada kuma beyi garaje ba dan be sake attempting tabata ba sedai suyi abinda suka sabayi wanda shima yanzu baya iya jurewa da yawa saboda jikinsa ya fara komawa daidai daya fara tabata zeji yana son kasancewa da ita sedai wani lokacin kafin yakai ga jikinta ma zeyi releasing daga nan komai ze sakeshi wannan al'amarin ya dameshi har yaso yafi sanda ya tabbatar da basho da lafiyar gaba daya shiga tashin hankali saboda a yanzu baya iyayi mata abubuwan daya saba a baya hakan kuma na damunta wanda ya fara fahimtar hakan a tareda ita. Walwalarta ta ragu, duk sanda ya jagwalgwalata ba tareda ta samu nutsuwa ba ranar wuni zasuyi babu dadi ita dai bata taba bude baki ta masa qorafi ba amma yasan abun yana damunta. Shi kuma ciwon da yake damunsa da mutuwar jikin da yake fuskanta da zarar ya fitar da abinda ya dameshi ne suke hanashi samar mata da nutsuwar, gashi daya fara tabata yanzu jikinsa ze amsa har ya fara jin dama ya zauna a yanda yake yafi samun kwanciyar hankali da iyalinsa dan yanzu wannan sabon Al'amarin na neman ya dagula musu lissafi.

Tilas babu shiri ya sake tafiya India ganin likita, suka gama masa duk gwaje gwajen daya kamata suka qara masa magunguna tareda kalaman ban haquri akan komai zeyi daidai with time haka ya tattaro ya dawo cike da fargabar yanda zamansu zeci gaba da kasancewa sedai be yanke qauna ba Allahn daya farfado dashi shi ze bashi isashshiyar lafiyar daze cigaba da kulawa da ita.

Wata uku cikin wannan yanayi Humaira ta fara zazzabi me zafi da Amai suna zuwa Asibiti gwajin farko aka tabbatar masa da tana da shigar ciki bayan an mata scanning suka sanar masa da watannin cikin uku da kwanaki.
Seda numfashinaa ya tsaya na wani lokaci kafin ya dawo hayyacinsa ya rasa gane yanayin da yake ciki, tambayar kansa ya ringayi tayaya hakan zata kasance Humaira da ciki to yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da ita har da zata iya daukar ciki?
Salati kawai ya ringayi a zuciyarsa da a'uziyya bisa ga tunanin da shaidan yake so ya darsa masa wanda ko kusa baya so ya samu gurbi a ransa yana kyautata mata zato kuma koda gaya masa akayi baze yarda ba dan haka baze taba bari tunanin yayi tasiri a ransa ba. Ita kanta bayan data farka daga bacci saboda ruwa da aka sakata sosai ta tsorata dajin wai ciki ne da ita, yanayin yanda ta firgice din ya sake darsa masa wani abu a ransa seya sulale ya fice daga dakin ba tareda yace mata komai ba zuciyarsa ta ringa bugawa kamar zata fito daga qirjinsa wani bangare kuma yana qoqarin kareta ta hanyar nuna masa ba laifinta bane, shiya kasance me son zuciya daya tilasta mata zama dashi alhalin bashida Lafiya tsayin shekara kusan hudu da yarinytarta tabbas dole cutarwa ta shigo ciki.

Can ya samu waje ya zauna ya rasa kalar tunanin daya kamata yayi, yana zaune a gurin yaji an dafashi ya daga kai suka hada ido da Dr Mahmud daya dade tun daga nesa ya hangoshi ya ringa masa magana amma be amsa ba dalilin daya sa ya qarasa kusa dashi kenan. Cikin kulawa da tausayawa yake kallonsa dan a zatonsa matsalar dake damunsa ce ta sakashi zama haka ko gurinsa yazo baya nan tunda shigowarsa kenan shi dan haka yace masa suje office.
"Khalil na sani akwai damuwa ga mutum lafiyayye ya gamu da ibtila'i irin wannan dole abin ze dameka sosai amma abinda nake so ka gane yawan damuwar kansa matsala ne domin yana iya kawo cikas gurin samun abinda ake buqata" Dr Mahmud ya fada bayanda suka zauna a office din se Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace

"Dr samba wannan ne ya dameni baai tun farko na gaya maka na karbi qaddarata a yanda tazo mun, wannan wani al'amari me me daure kai ya sameni daban, yanzu haka maganar da nakeyi maka Matata tana cikin Asibitin nan munzo bata da lafiya kuma an tabbatar mana tana da shigar ciki har wata uku na kasa gane yanda hakan zata yuwu Dr nida bani da lafiya tsahon shekara uku da wani abu yanzu".

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 81

"Calm down Khalil calm down" Dr Mahmud ya fada kafin yaci gaba da cewa
"kar ka bari shaidan ya jefa maka mummunan zato a zuciya shin baka yarda da matarka ba?" ya fada yana kallonsa cikin nutsuwa, se Khalil ya gyara zama yace
"Dr na yarda da ita ba kuma na kawo tunanin cewar Humaira zata ci Amana ta ba amma yanda abun ya zo nake tunani taya ya haka zata faru Dr?"
Se Dr Mahmud ya janyo system din gabansa ya kunna, File din Khalil ya binciko yayi shiru yana dubawa zuwa wani lokaci kafin ya daga kai yana kallonsa yace

"Idan zan iya tunawa, ranar da kace kaji wani abu akan matarka kamar kace har releasing kayi ko?"
Shiru Khalil yayi kafin a sanyaye yace
"Hakane Dr amma bana tunanin wannan ya isa ace an samu ciki, na gaya maka duka faruwar abun ne wuce minti daya ba, ban samimu dama na shiga jikinta ba and before i know komai ya faru ya tsaya kuma bayan hakan ma ya sake faruwa kuma ko yaushe dai kamar yanda na maka complain wani lokacin sena fara qoqarin yi wani ma kafin nayi attempting nakejin ya fita daga nan kuma zanyi loosing interest da strength dina bana ko iya satisfying nata da romance din yanzu" yanda yayi maganar zaka karanci tsantsar damuwa da fargabar da yake ciki Dr Mahmud ya fadada murmushinsa yana cewa

"To ina so ka yarda abinda ya faru a wancan lokacin dalilin samuwar wannan rabon ne har Allah ya baka qarfin yin abinda kayi. Kuma shi sperm da kake gani yana da matuqar sauri, inhar ya samu hanyar shiga jikin mace ko yaya take shikenan kuma kaga se akayi sa'a ita matar a lokacin a shirye kwanta yake koda yake daman Allah ya shirya faruwar hakan kaga wannan yana maka nuni da kaida Amarya duka sharp shooters ne, kaga Dayan Babyn ma kace sau daya akayi aka dace to ga wani ma idan lafiya ta samu se anyi taka tsan tsan idan ba haka ba Amarya zatayi ta jera babys ne duk shekara" ya qarasa maganar cikin zolaya kuma yayi nasarar saka Khalil din murmushi ya dauke kansa gefe Dr yaci gaba da cewa

"Ka kwantar da hankalinka in sha Allahu waraka zata samu baby kuma naka ne karka kuskura shaidan yasa kayi kokonto akansa kaji ko?" Seya daga masa kai alamar yaji ya kuma samu nutsuwa a zuciyarsa dukda cewar daman baya zarginta da cin Amana amma abin ne yazo masa da rudani sannan kukan da takeyi sanda ya gaya mata tana da cikin ya qara dagula masa lissafi to kenan meye dalilin kukanta ita? Abinda ya kamata ya sani yanzu kenan. Sallama yayi wa Dr Mahmud ya fita, dakin da take ya koma ya tarar da it har sannan tana kukan seya nemi guri kusada ita ya zauna cikin nutsuwa yajata jikinsa yana cewa

"Wai kukan me kikeyi haka ne kuma?"
Lafe masa tayi ta rage kukan tana cewa
"Habibi ciki fa, ni wlh tsoro nakeji baka san wahalar dana sha a haihuwar Aryaan ba ko shekara uku beyi ba na sake haihuwa" ta sake fashewa da wani kukan. Ajiyar zuciya me qarfi ya sauke jin dalilin kukan nata daya fi kama da shirme yana shafa bayanta yace
"Shine kike kuka haka baki san haihuwa baiwa bace ba mutane da yawa nema sukeyi basu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login