Showing 108001 words to 111000 words out of 429394 words

Chapter 37 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

986

kallonta kawai takeyi a ranta tana tuna irin qarairayinda Maman Nihal ta ringayi mata.

"Hajiya ku qaraso mana" muryar Abu ta dawo da ita daga tunanin data tafi se Mama tayi saurin tareta da cewa
"Me qaraso ina malama karki bata mana lokaci ki shiga ki dakko mana abinda ya kawo mu ba surutu muka zo yi ba"

"Yi haquri Hajiya kinga yau ruwa ya saka dambun be sauka da wuri ba" Abu ta fada Mama tayi saurin tareta da cewa
"Ke ki fita a ido na, idan baki sanni ba ita ma wannan zaki ce zakice baki santa ba ko kuwa wani wasan kwaikwayon zaki sake yi mana a nan? To tun wuri ki shiga hankalinki idan ba do kike na tara miki gajiya ba a nan barauniyar banza kawai".

"Haba Hajiya ya daga magana zaki nemi kici mun mutunci har cikin gidana meye hadina dake a ina na san ku da zaki zo kina kirana da barauniya yanzu idan na kai zancen nan gurin hukuma ai s an bimun haqqina" Abu ta fada taba bata fuska tana rufe baki kuwa Mama ta kwashe ta da mari tana cewa

"Idan baki kai mu gurin hukuma ba baki qaunar Allah, ke kuma da kika tsaya a nan zaki matso ne ko kuwa sena ci ubanki kema, a shegen kwashe kwashenki ai yau ga abinda kika dauko barauniya har cikin gida"

"Wallahi bazan yarda ba se an bi mun kadin marina da kirana da barauniya da kikeyi haka kawai ban san ku ba kuzo daga sama daga abin Arziqi ki hau dukana, Salisu bazaka fito ba kana kallo anzo har gida ana cimun mutunchi" Abu ta fada tana kururuwa se Umaimah ta kalleta tace

"Amma Maman Nihal kinji kunya wallahi ban taba zatonki da qarya ba ashe daman kin shiga jikinane saboda ki damfareni da a zatonki kinci banza kenan kin gudar mun da sarqa sedai kinyi batan basira da kika kaini inda aka sanki, yanzun ma can mukaje kuma Matar da kike qarya da sunanta ta saka aka rako mu har nan".

Tsilli tsilli tayi da ido jin magnganun Umaimah amma saboda iya bariki seta kwasa tayi dakinta tana kwalawa Mijinta me suna Salisu kira tace
"Salisu ka fito kana ina kana ji matan nan sunzo zasu daura mun sharrin sata wallahi bazan yarda ba ka fito ka kirawo mun yan sanda a bimun kadin sharrin da suka mun"

"Idan ke baki kira yan sanda ba ni yanzu zan kira su tunda bazaki fito da ita ta laluma ba" Mama ta fada tana danna wayarta, Aminu ta kira a taqaice tace ya turo mata yan sanda ya kira Salman ze bashi Address din gidan da take, yana tambayarta meya faru ta kashe tana jaddada masa ya turo su ba'a wuci minti sha biyar ba kuwa sega jiniyar yan sanda ta karade unguwar Abu ta dafe qirji amma qi fadi ya hanata cewa komai se Mijinta ne ya fito yana tambayar Maman ya akayi tace idan sunje can yaji komai.

Matan yan sanda biyu ne suka shiga gidan da sallam Mama ta nuna musu Abu dake shirin fadawa daki data gansu tace gata nan suka cafketa kuwa suka tasata a gaba haka suka sakata a mota su Mama suka bisu a baya tareda mijin Abun. A station Sanda Yaya Aminu ya isa station din aka shigar dasu office din DPO fafur taqi yarda da tuhumar da ake mata ta kafe akan ita bata sansu ba sharri suke mata.

Umaimah ta bada wayarta duk wani hirar su da Maman Nihal din tana ciki ga hotunanta nan da voice messages muryarta ce amma dukda haka ta musanta ita ba ita bace, ran DPO ya baci ya saka mata nan su jefata a Cell, su tuhumeta seta fadi gaskiya haka kuwa suka sameta suka ringa jibgarta musamman suna jin haushin zaginsu data ringayi a hanyar tahowa, seda taga suna neman hallakata da duka kafin tace zata fadi gaskiya aka fito da ita fuskarta tasha maruka ta kumbura suka koma Office din DPO, Mama ta maka mata harara Umaimah dai na gefe kanta a qasa dan itama ba tsira tayi a gurin Maman ba masifa take mata tana zaginta.

Khalil daya je gida da safen aka ce sun fita ne ya qaraso dan ya kirata ta gaya masa inda suke bayan ya zo Yaya Aminu ya fita ya shigo dashi office din. Abu na sheshsheqar kuka ta zayyana musu yanda suka hadu da Umaimah da duk abinda ya faru tsakaninsu, ta qarasa da cewa
"Kiyi haquri wallahi sharrin shaidan ne, kuma ni banyi niyyar guduwar miki da abu ba tsautsayine ya fada akai na rasa ta yanda zan gaya miki shiyasa amma wallahi ba gudu nayi ba"

Tsaki Mama tayi tace
"Can ke kika san tsautsayi ni sarqa kawai na sani ki fadi inda take salin alin kowa ya kama gabansa".
Rantse rantse ta ringayi akan ita ba satar sarqar tayi ba, takamaimai kuma taqi fadan inda take da DPO ya gaji yace ze cike mata FIR a tura su kotu can Alqali ya san yanda zeyi dasu nan idonta ya sake raina fata jin zancen kotu, ta riqe qafar Umaimah tana roqonta Mama ta hadasu su dukata qunduma musu zagi tace

"Babu kotun da zamuje anan zata fito da ita dan ko munjr qarshe gidan yari za'a turata sarqa kuwa seta Allah yanzun ma bata daku bane idan kuka lallasata zata fadi inda ta kaita ko ni ku bani kulkin na daka yar banza".

Murmushi DPO yayi yace
"Ayi haquri Hajiya, Officer kuje ku cike mata takaddar kawai ku turasu kotun zefi sauqi" kuka Abu ta fasa ganin dagaske fa kotu za'a kaita tasan kuma daga nan se gidan yari, Salisu Mijinta ne ya kalleta yace

"Yanzu Abu bazaki fadi inda kika kai musu abinsu ba kinfi so a kaiki kotun da kudin su zakiji koda na tara ga zaman gidan yari? Ina jiya naji kina zancen da kudinki a hannun Alhaji Auwalu yana juya miki ga daukar Adashin da aka kawo miki dazu da safe idan kin hada ko basu isa ba ai zaki rage wani abun".

Wata uwar harara ta galla masa kamar idonta ze fado tace
"Salisu kaji tsoron Allah daman ashe labe kake mun a gidan uwar wa kaji nace inada kudi ana juyamun saboda kawai ka sakani a wata masifar ko bayan wadda nake ciki"

"Shikenan kiyi yanda kike so amma nidai babu ruwana daga nan gida zanyi su kaiki ko ina ne sedai ki rube a can amma babu wanda zan gayawa ballantana a fito dake tunda haka kika zaba" ya fada yana miqewa tsaye, se kuma tayi qasa da kai, muryarta na rawar kuka tace
"Ranka ya dade a bani wayata toh na danyi kiraye kiraye ko zan samu na hado kudin"

"Ranka ya dade wannan matar bata da mutunchi wallahi kana ji mijinta ya fada tana da kudi tunda babu sarqa seta bada kudinta dan wallahi seta biya kudin nan" Mama ta fada se DPO ya kalli Matan yan sanda yace su maida ita, suyi ta dukanta har seta magantu kar su saurara mata Abu na ganin sunyo kanta ta fasa kuka tana roqon su tsaya, daya daga ciki ta kai mata mangari, ta dafe haqarqarinta jij Azabar zafi na ratsata suka fara janta tace a tsaya zata fadi inda kudin suke.

A wayarta Salisu ya kira Alhaji Auwalu kamar yanda ta bashi umarni tana kuka ya shaida masa Abun tana cikin wani hali aba buqatar kudi da za'ayi belinta, Alhajin ya jajanta musu yace kudinta dubu dari bakwai da Hamsin ne a hannunsa amma yanzu bazasu samu duka ba dan yayi sari, sedai akwai kudin da aka kawo masa yanzu na wasu dubu dari biyar, ze bayar idan yaso saga baya idan dari biyu da hamsin din ta hadu seya ciko musu ya gaya masa inda zeje ya same shi ya karba Salisu ya tafi bayan data gaya masa inda kudin Adashin data dauka suke. Be dade ba ya dawo da kudaden harda Receipt din Sarqar Umaimah yana nan a inda kudin suke gaba daya abinda aka samu dubu dari shida da sha biyar.

Mama ce ta kalli Khalil tace
"Kirawo mun Abokin naka kaji nawa gram din gwal yake yanzu" zeyi magana ta harareshi dole ya kira Bashir ya gaya masa ta bude wayarta ta buga lissafi ta nunawa DPO tana cewa
"Kaga kudin da zata biya nan, ga receipt nan a hannunka ka kuma ji farashin sa a kasuwa ka lissafa ka gani".
DPO ya karbi kudin ya saka akayi rubutu a takadda aka rubuta kudin sarqa da kuma abinda aka samu a hannunta da ragowar cikon da zatayi, Salisu ya nemi Alfarmar dasu barta ta koma gida, shi ze tsaya duk sanda ta samu kudin da kansa ze ringa kaiwa Police station din har a warware amma yana neman alfarmar su bata lokaci dan ta samu ta hada kudin, haka aka rabu DPO ya damqa kudi a hannun Mama nan take ta irge dubu sha biyar din sama ta miqawa Khalil tace

"Na cire kudina dan ni bazan dauki asara na yanda naga kana wani fuskar tausayinta tsaf zaka iya cewa ka yafe to kuje ku qarata in ta biya ku kukuka sani idan ma ta cinye matarka taja maka asara" tana gamawa tayi gaba abinta ta barsu suka qarasa.

Har sukaje gida tana mita da zagin Umaimah da tayi muqus, ita mamaki Maman Nihal ne ya cikata lallai mutum se a barshi.
Har aka kusa cinye sati Mama na mita kafin ta haqura tayi shiru da zancen, Mijin Abu kuwa ya cika alqawari dan da ya ganta da kudi seya san yanda yayi da kanta ba bayar aka kai Police station din, shi kadai yasan ta yanda yake tsoratar da ita kuka kuwa da tsinuwa da Allah ya isa tayi su babu Adadi.

A haka Umaimah taci gaba da jego cikin kulawa ita da yaronta sunyi kyau sunyi bulbul dasu abin sha'awa har suka cinye kwana Arba'in dinsu, ana gobe suyi Arba'in aka aiko da rasuwar Babban Yayansu Abba da suke kira Baban Qaraye dan shi acan yake zaune wannan dalilin yasa ta roqi Khalil akan ya barta suje gaisuwar idan sun dawo seta koma dukda beso ba haka ya haqura dan harga Allah a matse yake, shikadai yasan irin halin da yake ciki na rashinta a kusa dashi kullum cikin Azumi yake. Shi be taba sanin mabuqaci bane bama shi se bayan da yayi aure dukda tun kafin auransa daman yana da buqatar amma saboda ya tsare kansa yana yawan Azumi sannan baya kai idonsa ga kallon abinda ze tayar masa da hankali.

Sunje Qaraye seda akayi sadakar uku suka dawo ta tararda Khalil shi kuma ya tafi Sokoto wani aiki zeyi sati daya dan haka yace tayi amfani da wannan damar taje duk wani gaishe gaishen Arba'in da akeyi kafin ya dawo. Da bangarenta ta fara a kwanaki biyu ta gama zagaya duk inda zataje suka huta kwana biyu kafin Khalifa da kuma Habiba Hajiya ta saka suka ringa yawo da ita nasu dangin suna gaisawa, sun yawata sosai dan har Gaya sda sukaje suka kwana daya suka dawo kuma ranar ne zagayen su na qarshe a sannan saura kwana biyu Khalil ya dawo dan har su Maman Asad sunje sunyi mata shara da gyaran gida ita kuma washe gari zatayi lalle da kitso gyaran jiki ciki da waje kuwa daman sun dade suna yi.

Washe gari da safe Hajiya ta kirata akan idan babu damuwa ta shirya yanzu Khalifa zezo ya kaita gidan Goggo Zahra'u qanwar Mahaifinsu Khalil da shaf ta manta basuje can ba se jiya ta kirata tana qorafin an kaita ko ina a dangi ta gaishe su bada gidanta saboda ita bare ce.
Wadda zatayi mata kitso da lalle ta rigada tazo amma haka ta saka doguwar riga ta dauki Mu'ayyad suka tafi tana ta Mita Mama ta kwabeta.

Goggo Zahra'u ta karbe ta faran faran ta rasa ina zata sakata haka yaranta suka ringa zuwa suna gaisheta ita dai hankalinta yayi ta tafi gida tayi uzurin gabanta, sun kwashe sama da awa daya a gidan sam Umaimah ta kasa taba komai na abinda aka kawo musu ita kuwa Goggon ta qanqame Mu'ayyad tana ta janta da surutu, suna haka tayi baquwa suka gaisa ta zauna take tambayar Goggon wacece Umaimahn tace mata matar Khalil din Yaya Bayero ce seta riqe baki tace

"Oh kinga rabo wani baya haifar dan wani, da yanzu yaron Bariyyah ne"
"Kin rigani a fili ne Hajara ni kaina tun shigowarsu Nake juya yaron nan a raina ina cewa da yanzu na Bariyyah ne, idanda rabo ai seta haifi qannensa" Goggo Zahara'u ta fada tana yar dariya.

Kallonsu Umaimah ta ringayi har suka dire zancensu ji tayi kanta yana juya mata kamar wadda tayi hajijiya, bata manta sunan nan ba Bariyyah, tsohuwar budurwar Khalil cousin dinsa daman nan ne gidan su shine saboda rashin mutunchi za'a ce tazo ta gaishe su lallai ai kuwa yau zasuga qarshen rashin mutunchi kuwa se sun gane ita din ba kanwar lasa bace. Maganar da baquwar ta sakeyi tace

"Ai dai wallahi duk munso hadin Allah ne beyi ba da kuma rabo amma yanzu kinga se azo a sasanta kuma zamanku zakuyi lafiya lau dan naganki kema shiru babu ruwanki kamar Bariyyan" Baquwar ta fada tana kallon Umaimah

"Sedai mu zauna da kutumar uban Bariyyah, ni za'ayi wa rashin mutunchi ace nazo na gaishe ku sannan ku sakani a gaba kuna kawo mun zancen wata kucaka karuwa da taqi auruwa wai na hada miji da ita to wanda be fasa ba, ba ita ba harke uwarta se kin saka kanki a masifa da bala'in da baki zata ba wallahi aikin banza kawai" Umaimah ta fada kafin ta miqe ta fizge Mu'ayyad dake hannunta tayi waje, a bakin qofar suka ci karo da wadda take da tabbacin ita ce Badariyyan dan ance tana Islamiyya ganin mace ta shigo da Uniform ba tayi wata wata ba ta kwasheta da mari tace
"Wallahi ko inuwar mijina kika kalla se nayi Ajalinki ballantana ki saka tunanin hada miji dani a ranki banza garwa kawai" taja tsaki ta fice.

Khalifa na qofar gidan dan tuni ya gaji da soki burutsun Goggon tasu ya fita ya barsu se ganinta yayi kamar an jefota ta bude motar ta shiga tana huci dan haka yabi bayanta shima ya shiga ya tayar da motar, sau daya ya tambayeta meya faru tayi shiru bata amsa masa ba daga nan shima ya kama kansa be kuma ce mata komai ba har suka isa gida ya ajiyeta ta fice daga motar ba tareda ta rufe ba jakar goyon Mu'ayyad ma se shi ya bita ciki dasu.

Tana shiga kai tsaye dakin da take ta shiga ta ajiye Mu'ayyad akan gado, safa da marwa ta shigayi a dakin ji takeyi tamkar zuciyarta zata fashe saboda zafin da takeyi mata idan ta tuna maganganunsu se taji kamar ta koma ta shaqe su duk su biyun har se sun dena numfashi wai me ma ya saka ta taho ba tareda ta lallasa su ba amma ba laifinsu bane, laifin Hajiyar da tace taje ta gaishe su ne daman sun san rashin mutunchin da suka shirya shine za'ace taje ita gaishe su?

Wayarta ta janyo ta shiga kiran Khalil, tana so taji dalilin turata a wulaqantata da sukayi sedai tayi Rashin sa'a wayar a kashe.
Mama data gaji da kiran Umaiman tun shigowarta ta bita dakin tana cewa
"Lafiyarki kin shigo ana magana kinyi banza da mutane kin wuce, sannan tun dazu ake kiranki a waya kun tafi kunyi zamanku ko kin manta da kin bar mata tana zaman jiranki"

"Ni Mama ta tafi na fasa bazanyi lallenba" ta fada ba tareda ta kalli Maman ba, se Mama ta qarasa shiga dakin tana kallonta tace
"Uhm, fadan kukayi ko? To ki wuce tun muna shaida juna kije ayi miki abinda za'ayi miki kafin ranki ya baci yanzun nan"

Kuka ta fasa mata tana cewa
"Ni wallahi bazanyi ba, gidan ma bazan koma ba se yaje ya auro yar uwar tasa ya sakata a gidan ai amma ni na gama zama dashi"
Baki Mama ta bude tana kallonta har ta gama kafin tace
"Allah ya rufa asiri" ta juya abinta.

A can gidan Goggo Zahara'u kuwa daga ita har baquwarta kasa motsi sukayi har Umaimah ta gama tijararta ta fice ta barsu, qarar mari da Kukan Bariyya ne ya dawo dasu daga gajeran suman da sukayi suka zabura gaba daya sedai kafin su kai qofa Umaimah ta fice daga gidan.

"Zara'u wannan wace irin tijararriyar yarinya ce kinga tashin hankali daga magana se cibi ya zama qari har ta bi yarinya da tukuicin Mari gaskiya karki bar maganar nan gara ki kira Yaya Aishan ki gaya mata abinda surukarta tayi" Baquwarta ta fada tana kama baki,

"Wa ai fada ma bata baki yanzu kuwa zan kirata da take zagin Bariyyah tana kiranta mara tarbiyya ai ga qarshen rashin tarbiyya nan matar danta tazo ta mana, kuma wallahi bata daki banza ba auren Khalil da Bariyyah kuwa idan taga ba'ayi ba toh kice bana numfashi" Goggo Zahara'u ta fada tana numfarfashi nan take ta kira Hajiyar su Khalil a waya ta shiga tsara mata qarya da gaskiya wai Umaiman tazo tayi musu cin mutunchi ta daki Badariyyah dakyar aka kwaceta,

tsaf Hajiya ta gama jinta bata kama zancenta ba saboda sanin matsayar da suke da ita dan har a sannan bata haqura ba tana mata nacin in da hali Khalil ya qara da Badariyyan shiyasa yanzu ma ta dauka duk cikin sharrin tane daman tunda ta damu da suje din tayi tunanib wani abu. Suna gama wayar Khalifa ta kira lokacin ya ajiye Umaimah kenan take tambayarsa meya faru a gidan Goggon tasu tax be sani ba danshi daya gaji waje ya koma ya zauna amma yaga ta fito ranta a bace ya tambayeta bata kulashi ba ya ajiyeta gashi nan a hanyar gida yanzu yana hanyar dawowa.

Maida akalar kiran tayi kan Umaimah, seda wayar ta qaraci qararta tana daf da katsewa sannan ta daga cikin muryar kuka.

UMAIMAH
Tana zaune tana saqa da warwara taga kiran Hajiyar, zuciyarta ta ayyana mata karta daga, wani bangaren kuma yace mata ta daga ta daddana mata Ashar ai duk bakinsu daya ai. Rasa wanne zatayi a ciki tayi har seda taji wayar na neman

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login