Showing 144001 words to 147000 words out of 429394 words

Chapter 49 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1023

ze kirata ya gaya mata daga nan sukayi sallama.

Message ne ya shigo wayar ya dauka ya duba.
"Ba DSS ba Allah yasa FBI zaka kaini ka tabbata in har ka kai maganar nan gurin hukuma wallahi sena saki abinda ze sakaka nadama har Qarshen rayuwarka kuma ka turamun da Kudin ina jiranka" abinda ta turo masa kenan ya share zufar data keto masa yana salati a zuciyarsa. Wato tayi Hijacking wayar sa kota Hadiza ne da har take iya sauraron abinda suke fada tabbas Khausar Hatsabibiya ce kamar yanda Hadiza ta fada.

Rasa mafita yayi a lokacin ya kuma rasa shawarar wa ze nema. Gaba daya haka ya qarasa wunin ranar cikin tashin hankali da neman mafita, sanda ya koma gida kasa shiga yayi ya ajiye motar a qofar gidan. Gani yakeyi kamar Umaimah ta rigada taga hotunan nan be san kuma wane kalar tashin hankalin ze fuskanta a gurinta ba. Yana nan zaune a motar har aka kira sallar Magrib seya kulleta ya wuce masallaci a can din ma ya bata fin minti talatin kafin yayi qarfin halin miqewa ya tafi gidan.

A waje ya bar motar dan ya yankr shawarar zuwa gurin Mansur ne bashida Aminin daya fishi ya tabbatar kuma ze bashi shawarar abinda ya kamata yayi.
Da sallama ciki ciki ya shiga palour, Umaimah na kwance a qasa Mu'ayyad na gefe can ta zube masa kayan wasansa yana ta surutai irin na yara. Yunqurawa tayi dakyar ta tashi zaune tana kallonsa. Idan ba idonsa bane se yaga ta zabge idanunta duk sun shige ciki kamar wadda ta wuni tana kuka nan da nan gabansa ya yanke ya fadi kodai Khausar ta tura mata da hotunan amma kuman idan haka ne yasan abinda zatayi baze iya hasasoshi ba.

Dakyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da tayi masa yana qara kallon fuskarta yace
"Lafiya meya sameki naga fuskarki ta fada?"
"Banajin dadi wuni nayi da ciwon kai da zazzabi" ta bashi amsa tana yatsina fuska dan dagaske bata da lafiyar, yana fita kamar an aiko zazzabi da ciwon kan suka rufeta ba dan Hauwa ba da bata san ya zatayi ba.

"Sannu, bari na chanza kaya se muje Asibiti tunda likitan yace idan bakiji sauqi ba mu koma" ya fada kafin ya daga Mu'ayyad da se sannan ya lura dashi ya taho da gudu suka shige dakinsa. Wayarsa ya kunna masa ya shiga wanka, yana shiga yaji an kira sallah se yayi danasanin ya tsaya yayi isha gaba daya kafin ya shigo. A dakin yayi sallar sa yana jin yanda cikinsa ke qara alamar neman abinci amma bashida nutsuwar da ze iya saka wani abu a cikinsa. Sanda ya fito har sannan tana kwance a inda ya barta, shi ya taimaka mata ta saka hijabi yanajin yanda jikinta yayi zafi alamar zazzabin ya kulle gidan suka tafi Asibiti.

Har sukaje babu Wanda yayi magana a cikinsu, Khalil tunanin mafita yakeyi a zuciyarsa dan ko kafin su fito yaga Text din Khausar akan tana jiransa, idan ya kai gobe be tura mata ba ya kuka da kansa, ita kuwa Umaimah abinda takeji a jikinta shiya isheta. Sun isa Asibitin bayan yan tambayoyi likita ya rubuta mata teat yace suje Lab. Jininta suka dauka bayan yan mintina Aka basu Result, tundaga qofar Lab din ta fasa masa kuka dan ita aka bawa ta bude ganin abinda yake ciki yasakata Kukan Khalil kuwa yi yayi tamkar baya gurin dan damuwar da yake ciki tafi wannan shirmen banzan da take nema tazo masa dashi.

Sanda suka koma gurin likita kwanciya yace tayi a gado ya janyo computer scanning ya shiga dubata sega ciki ya tabbata kamar yanda Test ya nuna har na sati 13 ai nan Umaimah ta sake fasa wani kukan ciki wata uku ita tana me har haka ta faru bata sani ba. Ta gama sakan kancewa tunda bata Period bazata dauki ciki ba, shiyasa tace ma bazata Yaye Mu'ayyad ba seya shekara biyu, yanzu shekara daya da wata biyu ace tana da ciki har na wata uku ina zata saka kanta.

Kuka takeyi dagaske gaba daya ma ta hanashi fahimtar abinda likita yake gaya masa qarshe yace suje kawai idan sun nutsu sa dawo suji koma menene dan ya fahimci shima Khalil din hankalinsa a rabe yake.
A hanya kuwa seda yayi mata ihu kafin ya samu tayi shiru, suna isa gida a waje ya tsayar da motar yace ta shiga zeje ya dawo tana fita ya juya da Mu'ayyad dan karya bar matashi yasan ba kulawa dashi zatayi ba.

Gidan Mansur ya wuce kai tsaye, seda yaje qofar gidan sannan ya kira shi akan gashi a waje ya fito yana cewa
"Kai haka ake zuwa gidan mutane da ina Asibiti kuma fa" sedai ganin fuskar Khalil din ya saka yayi shiru suka shiga gidan yana riqe da Mu'ayyad, matarsa Umma tazo suka gaisa ta karbe shi tana tambayar Ina mamansa ta bari ya fito dashi da darennan yace mata bata jin dadi seta wuce dashi ciki ganin kamar yana jin yunwa ga bacci kuma.

"Bayero ya ake ciki ne, ka ganka kuwa kamar wanda Ya samu saqon Kidnappers duk ka hargitse fuskarka tayi zuru zuru ko Madam din ce abin nata ya motsa?" Mansur ya fada yana kallonsa. Hannu biyu ya saka ya dafe kansa da yake ji kamar ze tsage saboda ciwo kafin ya dago idonsa da sukayi Jaa ya kalli Mansur yace

"Mansur wannan matsalar tafi qarfinta Umaimah, wata yarinya ce take nema ta sakani a damuwa na rasa abinda take nema a gurina"

"Yarinya kuma, yaushe ka fara neman Mata bansani ba" Mansur ya fada yana gyara zama se Khalil ya jefa masa wata harara kafin ya dauki wayarsa ya bude hotunan ya miqa masa. Karba yayi yana dubawa ya gama ya dago fuskarsa da alamar tambaya se ya karbi wayar ya sake bude Messages din da ta tura masa ya bashi. Dariya Mansur yayi yace

"She must be Mad,1M akan wadannan yan hotunan me akayi a ciki da har zata nemi 1M akan su" yayi tsaki ya miqa masa wayar yana cewa
"Muje daga waje kasan ita kuma wannan labe take yiwa mutane yanzu karkayi mamaki ta kasa kunne taje me za'a fada" suka miqe suka koma harabar gidan.

"Yanzu wannan abin ne ya saka hankalinka ya tashi har haka ko kuma akwai wani abu tsakaninku da ita bayan wannan da baka so ta bayyana" Mansur ya fada yana kallonsa, se yaja qaramin tsaki yace

"Ta hoton daban, wadda ta turomun da Threat din daban"
"Ban gane ba?" Mansur ya fada yana gyara zama
A taqaice Khalil yayi masa bayanin Hadiza da kuma Khausar din, ya qarasa yana cewa
"Aswear Man none of this is true, hadawa tayi kuma ita Hadizan ta gaya mun Khausar nada connection da all those computer literates daman sun saba yin irin wadannan abubuwan shiyasa take jin tsoro kar tayi wani abin".

Numfashi Mansur yaja kafin yace
"Ni ina ganin abin nan me sauqi ne, kamar yanda ka fada ita ce ta fara showing interest akan ka kai kuma you went to her friend baka tunanin haushin wannan abin nr yasa tayi muku haka?"
"Toh ai yanzu itama qawar tata bama tare, kuma ko a lokacin da muke tare muna haduwa harda ita bata taba nuna wani abu akan haka ba" Khalil yayi saurin Katse shi se Mansur yace

"Hakan bashi yake nufi babu komai a ranta ba lokaci ta jira gashi yanzu kun gani,kana ji ko ka kwantar da hankalinka kayi tunani zaka iya warware komai. Tayi ne saboda haushin bata same ka ba kaje kana Neman qawarta you can turn the table ka koma mata ka nuna yanzu ita kake so ko daman can itan kake so ka damu ku daidai ta shikenan fa".

Kallon baka san me kakeyi ba Khalil yayi masa kafin yace
"Saboda a shirin film muke ko yaya, kasan yanzu duk abinda zan gaya mata bazata yarda ba dan tasan kawai saboda na yaudareta ne. Ni yanzu shawarar dana yanke zan yi magana da Hafiz Sale zuwa da safe, su zasu iya nemota su saka ta goge kuma suyi mana iyaka da ita"

"Wane Hafiz Sale?"
"Hafiz speaking"
"Oh, wai da securities kake so ka hada ta, think about it Khalil it will just worsen the situation ko ka manta abinda qawarta ta gaya maka ne kasan bazata yi abin nan ita kadai ba dole tana da backup, nidai a shawara kabi a hankali ka shawo kanta kuyi magana sannan idan taqi cooperating se ka dauki mataki akai" Mansur ya sake fada. Iska Khalil yaja kafin yace

"Zan gwada amma idan kuma na tsaya lallabata tayi mun shirme fa, think about what will happen idan Umaimah taga hotunan nan"
"Oh kai Umaimah ce kadai matsalar ka ma toh Allah ya rufa asiri, nidai shawarar da zan baka kenan kabi komai a hankali ka kirata kuyi magana ko ka nemeta ku hadu, and about the ransom she requested ka tura mata da wani abu ka gaya mata baka da kudi tayi haquri zuwa end of the month then you settle her" Mansur ya sake fada, akan haka suka rabu ya shiga ciki ya dakko masa Mu'ayyad da har yayi bacci abinsa se a sannan suka lura da lokaci sha daya da rabi ta wuce.

Kafin ya isa gida Sha biyu tayi ya samu ya shiga da mota ya kasheta sannan ya dauki yaron suka shiga. Da kukanta ya fara cin karo tana kwance kusada bakin qofar tana kuka qasa qasa alamar tayi ta gaji ne, kansa ya sara masa ya tsallaketa ya wuce seda yaje ya kwantar da Mu'ayyad kafin ya dawo dukda zuciyarsa na ayyana masa ya rabu da ita idan ta gajo dan kanta ta tashi amma ya kasa.

Dakinta ya shiga ya hada ruwa me zafi kafin ya dawo inda take ya dagata ba tareda yayi mata magana ba, zazzabin jikinta ya sauka ya wuceda ita bandakin tana kuka da komai yayi mata wanka tas ya nadota a towel ya kwantar da ita akan gado. Kitchen ya wuce ya hado shayi me kauri a kofuna biyu ya debo Cake dan shima yunwar yakeji sosai, a gaba ya sakata seda ta shanye ya hade fuska yana shan nasa ya kuma qi bata damar ta kawo masa wata maganar banza har suka gama ya dakko mata riga ta saka suka wuce dakinsa ta kwanta bayan tasha maganin ciwon kai cikin sa'a tana kwanciya bacci yayi gabada ita.

Juyi ya ringayi a gadon kawai ya rasa me yake masa dadi, gurin qarfe uku Mu'ayyad ya farka yana kukan neman nono dole ya tashi ya hada masa madara a feeder ya bashi dan lokacin sosai jikinta ya sake daukan zafi har rawar dari takeyi ya samu ya lallabashi ya koma bacci kafin ya drbo ruwa ya goge mata jikinta itama zafin yadan ragu. Ganin baze iya bacci ha ya saka shi tashi yayiwo alwala ya shiga jera salloli yana roqon Allah daya bashi mafita akan abinda ya tunkaro shi, bayi aune ba seji yayi ana kiran Sallar Asuba. Wanka ya sakeyi ya canza jallabiyar jikinsa ya fita masallaci se a sannan ya fara jin baccin na neman daukarsa dakyar ya dawo gida ya tarar Umaimahta farka har tayi sallah kuma da alama jikin nata da sauqi dan har ta hadawa Mu'ayyad da shima ya farka Shayi a feeder yana sha, a taqaice suka gaisa ya tambayeta jikinta tace da sauqi, kafin ta kawo wata maganar ya shige daki ya kullo qofar harda saka muqulli dan jin kansa yakeyi tamkar ze fashr tsabar damuwa da rashin bacci. Yana kwanciya ko minti biyar beyi ba baccin ya kwashe shi gaba daya ma ya manta da cewar ranar aiki ce be tashi farkawa ba se qarfe Sha daya harda rabi shima qarar wayarsa da ya manta ya ajiyeta a saman kansa ce ta tashe shi.

"Wato ka dauka da wasa nakeyi ko shiyasa kayi banza da maganar da mumayi, daman na gaya maka idan ka tsallake jiya ka kuka da kanka da duk abinda ze biyo baya dan haka ka saurara ka gani" Khausar ta fada bayaj ya daga wayar babu shiri ya miqe tsaune yana goge ido dan baccin da yayi ya taimaka masa ya manta da duk wata damuwar da yake ciki"

Cikin taraddadin abinda ka iya faruwa yace
"I'm sorry Khausar tun jiyan bana jin dadi ne ko office ban fita ba yanzu ma haka bacci nakeyi kiranki ne ya tayar dani, kiyi haquri ki bani dama muyi magana a waya ko ki fada mun inda kike so mu hadu nayi miki alqawari zanyi duk abinda kike so kinji".
Cikin wani irin lallashi yayi mata maganar dashi kansa seda ya gama yake mamaki, shiru tayi kamar ba zatayi magana ba har ya cire rai se ji yayi tace

"Shikenan babu damuwa ka samu kasha magani idan kaji sauqi a yau ka kirani se na gaya maka inda zamu hadu idan babu dama ka bari se gobe Allah ya qara afuwa"

Qara narkewa yayi yace mata
"Amin nagode kwarai, se na kirakin" daga nan ya kashe wayar yana tuna maganar Mansur da yace ya lallabata zero iya shawo kanta gashi kuwa ya gani ashe duk iskancin nata ma na qarya ne.

Wanka ya farayi yana jin cikinsa kamar anyi yasa babu komai a ciki, qananan kaya marasa nauyi ya saka ya zauna a gefen gado ya shiga kiran layin Sakatariyarsa Hajjo ta daga suka gaisa tana tambayarsa lafiya be shigo ba kp Site ya tafi yace mata baya jin dadi ta rubuta report duk abinda aka turo office din wanda zata iya tayi attending wanda bazata iya ba idan softcopy ne ta tura masa ta Email sukayi sallama.

Umaimah na kwance akan Tiles ya fito, rigar baccin data kwana da ita ce jikinta fuskarta tayi qozai qozai alamar kuka ga kuma rashin jin dadin jikintada batayi, kallonta yayi yace
"Me yasa kika kwanta a qasa cikin sanyi ki tashi ki koma kan Carpet mana idan kwanciyar qasan kike so"
"Nafi jin dadin nan" ta bashi amsa tana goge hawaye se yayi kamar be gani ba ya wuce kitchen dan yasan bata girka komai ba.

Ruwan zafi ya dafa, ya soya musu kwai ya hado komai har sannan tana kwance a qasan ya ajiye.
"Ki tashi kici abinci" ya fada yana kallo ta ta toshe hancinta ta tashi zaune tana cewa
"Banason qarnin kwan" tana rufe bako ta fara yunqurin Amai yayi saurin qarasawa ya dagata suka wuce bandaki tayi Aman, kuka ta fasa masa tana cewa

"Bana son cikin Khalil dan Allah ka rabani dashi wallahi ban shirya sake haihuwa yanzu ba".

Be kulata ba ya saketa ta sake kwanciya a qasan ya wuce gurin abincinsa ya shiga karyawa, kukanta ya dameshi amma yaqi kallon sashin da take, kalmar bata son ciki na qonamasa rai amma yayi shiru dan abinda yake gabansa yanzu yafi qarfin maganar ciki shiyasa ya qyaketa tayi kukan harta gaji dan kanta ta kwanta se kuma tausayinta ya kamashi.

Kanta ya tsugunna yana tambayarta me zata ci tace babu komai daya matsa ta sake fasa kuka akan ita ya kaita gida yace toh ta tashi ta shirya se a sannan ya lura da Beji Motsin Mu'ayyad ba zuciyarsa ta bashi yana gidan da take kaishi kenan,

Shiya taimaka mata tayi wankan tana sake nanata masa bata son cikin har sannan be tanka mata ba. Seda ta shirya sannan yace ta kira a dawo da yaron babu dadewa Hauwa ta kawo shi da kwanon Alala da tace ta siyo mata a bakin titi, shi taci shi kuma yayi masa wanka ya shirya shi ya hada mata jakar kayansa da duk abinda yasan tana sakawa kafin suka fita ya kaita gidansu.

Bayan ya ajiyeta kai tsaye ya shiga kiran layin Khausar, sunyi da ita zasu hadu a Zazu nan da awa daya yana kashewa ya nemo number Hadiza har ze kira ya tuna da jiya be san ta yanda akayi Khausar tasan abinda suka tattauna ba seya fasa. Zuciyarsa ce ta ringa bashi qarfin guiwar Ya kira Hafiz dole shima baze rasa abinda ze iyayi akai ba koda ace ya yaudareta bashida tabbacin ze iya sakawa ta goge kuma idan ma yayi nasara shidai ba ci gaba da Mu'amala zeyi da ita ba kenan idan ya barta zata iya sake hada wasu kenan.

Wayar Hafiz din ya kira, seda sukayi wa juna tsiyar rashin zumunchi kafin yace masa yanaso su hadu dan Allah idan babu damuwa kai tsaye Hafiz ya amsa yace ya same shi a Office yanzu babu abinda yakeyi. Da awa dayar data bashi kafin su hadu ya je gurin Hafiz suka tattauna, be boye masa komai ba ya bashi hotunan harda number wayarta duk ya karba yace kwantar da hankalinsa zeyi bincike akanta ya tabbatar da abinda ta fada idan gaskiya ne sannan su san ta inda zasu bullo mata kuma yaje su hadun hakan ma ze saka su sake samun wasu Informations akanta. Ya rufe da cewa

"Yanzu sabuwar hanyar da mata suka samu kenan ta blackmailing, ranaku kadan ne zakaga baa kawo case gurin nan na kaga babban mutum da mutunchinsa amma yazo da qarar wata yarinta tana masa barazana da hotuna ko wani abu nasa da be kamata duniya ta sani ba, Allah dai ya rufa asiri amma karka damu wannan ba wata matsala bace.
*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login