Showing 420001 words to 423000 words out of 429394 words

Chapter 141 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1004

bata kuma ai daman duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwan mugun halinta da abinda ta aikata a baya sune suka koma kunnensu har yasa suka hana dansu auranta ba wani abu ba daman kuma ai za'a rina, a zamanin nan ka shuka Alkhairi ma yaka qare ballantana kayiwa kanka mugun tabo? Ai keda aure dai yanzu sedai ki samu Dattijo irinmu wanda bashida me sakashi ko ya hanshi amma badai Matashi me jini a jika ba dan babu dan da uwarsa take raye da zataji abinda kikayiwa Halilu da uwarsa ta bari a auro ki cikin Ahalinsu" Baba Abdullahi ya amshe, kanta na qasa wani qululu daya taso mata tunda Baba Liman ya fara magana ya tokare mata wuya, sam ita maganganun Baba Abdullahi basu bata mata rai ba dan tuni ta haddacesu sedai idan basu haduba cinmutunchi se wanda ya manta ne baya mata.

Abba ne ya dakatar dashi jin ze cigaba da tijarar tasa yace mata
"Kije, karki saka damuwa a zuciyarki kinji kullum muna yi muku Addu'a da fatan Alkhairi a rayuwa komai ya faru da sanin Allah kinji"
"Toh Abba" ta fada muryarta na rawa kafin ta miqe ta fita daga falon. Bata tsammaci zataji ciwon fasa auranta da Abdulwahab yayi har haka ba, ita bata ma san tana sonsa ba se yanzu da wannan abun ya faru ranar kwana tayi tana sallah tana Addu'a tana kuka gwanin tausayi. Meyasa Abdulwahab zeyi mata haka? Dayasan ba auranta zeyi ba meyasa ze bata mata lokaci har ya bari ta sakashi a ranta meye ribarsa yanzu akan abinda yayi mata kenan ya bata lokacin sa da dukiyarsa a banza alhalin ba auranta zeyi ba duk a na me?

Hankalinta be qara tashi ba seda magana ta shiga yawo a unguwa, batayi mamakin yanda akayi zancen auranta da fasuwarsa ya bazu ba tunda da Alhaji Zakari akayi komai tasan kuma ko a bakin matansa maganar zata fita amma abinda aka ringa yawo dashi ana jifanta dashi yayi mugun tabata da har seda ta kwanta jinyar data qarawa magauta hujjar yamadidi da ita a gari cewa akeyi tayi cikin shege abinda yasa Abdulwahab ya fasa auranta kenan, yanke jiki tayi ta fadi lokacin da Yasir ya shigo yana maida musu da abinda yaji a Unguwa ana fada, da yammane, Masu zaman banzan unguwa sun kafa majalissu aka fita da ita Asibiti ranga ranga tuni labari ya chanza salo cewar gata can tasha maganin zubar da cikin an tafi Asibiti da ita harda masu cewar Jini har qofar gida sun ma gani da idonsu kai maganganu dai kala kala masu fadar dama sun sani kullum da motar da take zuwa gurinta aikin da akace tana zuwa ma duk qaryace kawai fakewa take da yawon ta zubar ba wani abu ba.

Bata taba zaton haka sharri yake da ciwo ba se daya fado kanta, tayi kuka babu iyaka har idanunta suka soye zuciyarta ta qeqashe, ta ringa tuna Hadiza ita da ba iya unguwa ba Nigeria gaba daya babu inda hoton batancinta be zaga ba har yau bata fitar da ran hotonta na kan yanar gizo da batancin da tayi mata ashe haka taji? Tabbas irin Hadiza basu da yawa a duniya, ta yafe mata abinda tayi mata gashi Allah ya saka mata cikin ruwan sanyi ya jarabceta da abinda ta jefeta dashi, idanta kalli irin quncin da Abba da Mama suka shiga akan wannan sabon Al'amari hankalinta na matuqar tashi batayi musu Adalci ba. A kullum burinsu su faranta mata sannan tayi musu sakayya da bacin rai. Ita ta fita zakka a yayan da suka haifa Maza da mata babu wanda za'a daga a kawo wani aibunsa se take kullm cikin janyo musu magana take.

A wannan karon seda akayi dagaske kafin nutsuwarta ta daidaita, ciwon damuwa ya nemi kamata ta dena fita dan duk inda tayi nunata akeyi ana cewa tayi cikin shege ba ita ba Mama kanta seda ta dena zuwa taro a unguwar saboda yanda ake zundenta duk inda ta shiga saboda Umaiman, ance tana zaune shekara bakwai Ashe karuwancinta kawai takeyi se yanzu da ta samu Miji Asirinta ya tonu, Addu'a da tawakkali yasa suka cinye wannan jarabawar har masu surutu sukayi suka gaji rayuwa taci gaba da tafiya a yanda take. Yanda Abdulwahab be nemeta ba itama bata sake nemansa dan taji dalilinsa na fasa auranta ba, tasan dai koma menene yana da alaqa da rayuwarta ta baya haka ta sake fawwalawa Allah komai taci gaba da aikinta zancen aure ya sake fice mata daga rai saboda duk wanda zezo badan Allah bane se kuma Dattijai irin su Baba Abdullahin masu mata uku da yaya bila Adadin. Maman da take matsa mata da zancen auran ma ta haqura tana mata addu'a dan haka ta aje komai ta rungumi aikinta da sana'ar siyar da turaran wuta data fara dalilin na auran Abdulwahab da tayi, suna da yawan gaske sunfi qarfin tace zata ajiye ta ringa amfani dasu ita ba Gida ba ba Miji ba Maman Asad ce ta bata shawarar siyo container ta zuba su gwada tallatawa dan Turaruka ne masu kyau da Inganci tayi ai kuwa Allah ya saka mata albarka a sana'ar sosai take samun Alkhairi a ciki.

Rabuwarsu da Abdulwahab da kusan wata shida kamar daga sama Allah ya sake hadata da Alhaji Kabir taje kasuwar Sabon gari siyo Mai da sabulun wanka suka hadu a shagonsa tayi siyayyar babban dan kasuwane dan shagunan sa sun kai biyar a cikin kasuwar yana ganin Umaiman ya rikice nan duniya yace shi yaga mata, daya daga cikin yaransa yace ai ya santa unguwarsu daya, shi ya bashi labarin abinda ya sani game da Umaiman Alhaji Kabir yace yaji ya gani dan irinta yaie ta nemi tuntuni abinda ya hanshi qara aure kenan. Shiya kaishi gurin Umaiman, Matarsa daya da yara biyu babban dansa Sa'an Iman ne. Shekarun sa talatin da takwas ya bata shekara uku kenan Nasibin rayuwa daya samu da kuma kamala ta yan kasuwa yasa ake ganinsa kamar wani babba ita kuwa tunda ya sanar mata da shekarunsa ta rainashi, gurinta shekaru uku sunyi kadan tsakananinta da Mijin da zata aura musamman a matsayin da take yanzu. BTa bashi fuska ba dan tun a zuwan farko ta nuna masa cewar yayi haquri ita ba aurene a gabanta ba amma ya nace.

Kiran waya kamar maye haka idan bezo yau ba gobe zezo tun tana shareshi harta haqura ta fara kulashi musamman da kowa yake ce mata tunda tana addu'a ta saurareshi ta yuwu Alkhairin da kowa yake roqar mata ne yazo. Abba da kansa yayi mata magana saboda nacin Alhaji kabir din yayi yawa kuma a yanayinsa mutumin kirki ne ga ladabi idan ya bazo babbar rigar nan tasa har Yasir girma yake bashi autan gidan gaba daya wadannan abubuwan suka saka dole ta fara sakar masa fuska tana qoqarin ganin sun fahimci juna a sannu har maganar aure tayi qarfi a tsakaninsu a wannan karon bata maimaita kuskuren da tayi lokacin Abdulwahab ba. Da kanta ta bashi labarin duk abinda ya faru a baya cikin tsantsar nadama da dana sanin da fuskarta ta gaza boyewa, Mamaki ta kusa kasheta sanda yake ce mata yaji komai hatta da sharrin ciki da aka mata ya sani kuma shi wadannan dalilai ma suka qara masa sonta har yake son auran nata a maimakon taji dadi se abin ya shiga bata tsoro. Ya za'ayi yace shi komai da tayi burgeshi yayi hakan nema yasa ze aureta anya qalau yake kuwa? Ko ita a karan kanta tasan halintavna baya bame kyau bane kuma idan da ace wata ce take da wannan Halin wanda ta sani ze aureta zata hana. Addu'a ta sake tsanantawa a kan lamarin, babu wani shiri da tayi wannan karon dan gani ta ringayi kamar shima auran bame yuwuwa bane yan uwansa zasu hana kamar yanda daga baya ta samu labari a bakin Hadiza cewar Hajiyarsu Abdulwahab dince ta hanashi auranta bayan uwargidan Alhaji Zakari taje qafa da qafa ta bata labarin gaskiya da qarya daya faru itace kuma ta kafa masa sharadin ko sake waiwayar Umaiman yayi bata yafe masa ba, wata biyu kenan daya auri diyar Alhaji Zakarin yanzu ita bata ma san shi ta aura ba seda Hadizan take gaya mata shiyasa take taka tsan tsan da Kabir kar shima iyayensa suji wani abu daga baya suce zasu hanashi auranta sedai kamar yanda akace Al'amarin aure da Mutuwa daya suke idan lokaci yayi babu fashi se gashi cikin hukuncin ubangiji ranar wata Juma'a aka daura auran Umaiman da Kabir auran da yazowa mutane da yawa a bazata irinsu Khalil dan ba'asan da labarinsa yinsa ba.

Al'amarin ya dakeshi matuqa da har ya kasa jurewa seda kwanta Asibiti magashiyyan kowa ya gane halin da yake ciki. Beji neman auran ba kamar na wancan karon da daga baya yaji ance an fasa se kawai ji yayi wai ta daura aure badan a bakin Hajiya yaji ba da tabbas qaryatawa zeyi. Ya dinga rama a tsaye abinci se an masa dole zeci ya dena fita aiki na kusan sati biyu tun Humaira na fushi tana ganin abun kamar cin fuska harta ajiye komai ta fahimci yana da buqatar tallafi, ita shaidace akan son da yakewa Umaimah amma tambayar da takewa kanta me ya hanashi dawo da ita duk tsahon lokacin nan se yanzu da tayi aure ze nemi kashe kansa a tsaye da tunani? Hajiya kanta ta shiga damuwa, ta ringa ce masa
"Me yasa Babana, kasan kana son dawo da matarka duk tsahon lokacin nan meyasa baka maido ta ba?"
"Hajiya ni bani da ra'ayin dawo da ita" ya bata amsa cike da dacin zuciya, Jalilah datazo dubashi tayi caraf tace
"Qarya kakeyi kuma sedai so ya kashe ka wlh badai ka sake zama da Umaimahba mara zuciya kawai wato kai nan da lambu lambu kayi kana jira lokaci ya qara turawa ka maidota ko to ko bayan ran Hajiya baka isa ba balle yanzu da take a raye"

"Kiyi mun shiru Jalilah ni na gaya miki haka?" Hajiyar ta daka mata tsawa kafinta juya kan Khalil daya rintse ido saboda yanda kansa yake sarawa idan ana magana da qarfi tace
"Kayi qwauran baki Babana da kuma ni bana adawa da dawowar Matarka, idanhar dan abinda tayi mun ne wlh na dade da yafe mata tuntuni idan da ka nuna mun kana ra'ayin dawo da ita tuni dana shige maka gaba kuma ko yanzu zanci gaba dayi maka addu'a idan har da Alkhairi a zamanku Allah ya kawo dalilin da zata dawo gareka"
A ransa ya amsa da "Amin" Jalila kuwa a fili ta furta
"In sha Allahu babu, ba zata sake dawowa zuri'armu ba data samu ta auru dakyar taje can ta qarata muda ita sedai dan zuri'ar dake tsakani amma da babu abinda ze sake hadamu".

Sati biyu aka saka tariyar Umaiman, ana saura kwana hudu ta tare yaje gidansu cikin matuqar qarfin hali. Ba Umaimah ba hatta su Mama sunyi matuqar mamakin ganin Khalil din da kuma yanayinsa daya nuna baya jin dadi har seda Mama ta tambayeshi yayi murmushi kawai yace mata rashin lafiya yayi ya kasa dauke idonsa daga kan Umaimah data sha gyaran Amarare tayi bulbul tana sheqi daya tuna matar wani ce a yanzu seya sadda kansa qasa wani abu me daci da maiqo yana taso masa. Shirun da Khalil din yayi ya saka Mama tashi ta basu guri, da alama zuwannata ne bayan tsayin shekaru yau ya waiwayi Umaiman kenan qila daman irin wannan lokacin yake jira.

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

*DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH SWT DAYA BANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFI, INA FATAN ALLAH YASA MU'AMFANA DA DARUSSAN DA SUKE CIKI, INDA MUKA KUSKURE UBANGIJI KA YAFE MU DARAJAR ANNABI DA ALQU'ANI* >?2??2? *AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKU MASOYAN RUBUTUN UMMU-MAHEER, UBANGIJI YA SOKU, YA JIBANCI LAMURANKU, NAGODE DA TARIN QAUNAR DA KUKA NUNAMUN KUNE QARFIN GUIWATA KUNA DOMINKU NAKEYI. WANDA NA BATAWA A TSAYIN LOKACIN DA NAKE RUBUTUN NAN INA NEMAN AFUWARSU, A BANGARENA NA YAFE DUK WADDA TA ZAGENI NA YAFE MATA >?r?>?r? ALLAH YA YAFE MANA BAKI DAYA SE MUN SAKE HADUWA A SABON LITTAFI NA DA ZEZO IDAN ALLAH YA YARDA*
*MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER*

*Last page*

Bayan Mama ta fita sun kwashi kusan minti biyar kafin ya nisa a hankali ya kira sunanta, tsigar jikinta suka zuba dalilin saukar muryarsa da lafazin da yayi amfani dashi gurin kiran sunanta se ta shiga a'uziyya a zuciyarta tana kiran sunayen Allah. Cikin sanyi ya shiga ce mata
"Umaimah, da farko zan fara da tayaki murna bisa auran da kika daura, Allah ya sanya Alkhairi ya kuma kade duk wata fitina da abin qi a gidan aurenki ya sanya Albarka da farin ciki a rayuwarku sannan se abu na biyu ina roqon a tsayin zaman mu idan nayi miki wani abu na kuskure ki yafe mun" kuka ta fashe dashi jin abinda ya fada, idan ba dai son ya qara mata laifi ba wace magana ce kuma wai ta yafe masa ita me yayi mata sedai idan so yake yace baze yafe mata ba kawai yafi ya fito kai tsaye akan wannan alayenda yakeyi.

"Ki dena kuka dan Allah, ko ba zaki iya yafe mun ba?" Ya fada muryarsa a karye seta dago da sauri ta kalleshi, idanunta sun gaza boye tarin qaunarsa da kewarsa dake cinta ya kauda nasa idon daga kallonta yana tunatar da kansa matar wani ce cikin kukan tace
"Bakayi mun komai ba Khalil, Allah ne shaida ka kasance Mijin kwarai kuma uba na gari gurin Yayansa, ni na zalunceka kuma naga sakayyar hakan akaina haqqinka yana ta dawainiya dani, ka tausayamun ka yafe mun ko zan samu nutsuwa a sabuwar rayuwar da zan shiga" ta fada cikin tsananin kuka. Yaqe yayi yadan kalleta yace

"Na dade da yafe miki Umaimah, abinda kikayi mun tsakanina dake ban riqeki ba, daga randa Hajiya ta furta ta yafe duk abinda kikayi mata nima na yafe fushin tabata da kikayi"
"Hajiya ta yafe mun?" Ta tambayeshi cikin tsananin mamaki seya daga mata kai cike da tabbatarwa yace
"Ta yafe miki tuni, Hajiya bata kwanciya bacci da fushin kowa a ranta kuma muma akan haka ta horemu mu ringa yafiya akan duk abinda aka mana. Babu abinda riqon wani a zuciyarka ze qareka dashi a rayuwa sabanin haka idan ka yafe se kaima Allah ya dubeka ya yafe maka naka kurakuren da suke tsakaninka dashi". Qirjinta ya ringa bugawa, wani sabon nauyi da kunyarsu ya sake lullubeta a ranta ta ringa godewa Allah da bebi ta halinta ba ya zabarwa Yayanta tsatso na kwarai, sukam sunada karamci gashi su rabauta da zuciyar da ba kowa Allah yayiwa Arziqin irinta ba ta yafiya. A hankali cikin rarrabewar harshe tace
"Toh toh me yasa duk tsahon lokacin nan tunda ka yafe mun amma ka kasa waiwayata?" se yayi murmushi kawai ba tareda yace mata komai ba har ta fitar da ran samun amsarsa taji yace
"Kina so kisan meya hanani waiwayarki tsahon lokacin nan?" Ya fada yana kallon idonta seta girgiza masa kai alamar Eh ta sauke kanta qasa

"Saboda ina sonki, bana iya riqe kaina idan ina tare dake. Zuciyata bata taba fushi dake idan har nazo inda kike tabbas nasan zan karaya na kasa cika alqawarin dana daukarwa kaina na haqura dake har Abada Umaimah".
Zabura tayi ta dago ta kalleshi saboda abinda ya fada, hawayen da ta samu suka tsaya suka sake balle mata cikin tsananin kuka tace masa
"Saboda baka yafemun bako?"
"Na yafe miki amma bazan miki qarya ba duk sanda na kalleki nasan zan ringa tuna sanda kika tsaya gabana kika zagi Hajiyata" ya fada idanunsa suna sake canza kala da alamar abinda ya fada din ya sosa masa rai. Umaimah ta duqar da kanta qasa, da tana da damar maido da baya data canza abubuwa da dama cikin rayuwarta, Khalil yaci gaba da cewa "bana so mu sake komawa rayuwar aure tare son da nake miki yakai girman da zan iya jure komai da zakiyi mun naji tsoron kar soyayyata ta halakar damu gaba daya kar kawaicina ya kaimu wuta saboda Allah babu ruwansa shiyasa na zabi haqura da son zuciyata na barki badan bana sonki ba ko na dena sonki ba kuma dan bana son ci gaba da zaman aure dake ba sedan kawai hakan shine maslaha a rayuwarmu gaba daya kullum nayi sallah sena roqi ubangiji ya zaba mun mafi Alkhairi a cikin komai na rayuwata duk abinda na rasa kuma ina fatan yasa nayi tawakkali ya bani dangana kuma Alhamdulillah, ina cikin farin ciki tattare da musanyar da yayi mun kullum cikin gode masa nake kema ina miki fatan ki samu farin ciki sama da wanda nake ciki a yanzu zanci gaba da Addu'a yanda na rasaki a duniya, Allah ubangiji ya hadamu qarqashin inuwa daya a Aljanna ya dawo mun dake a matsayin MATATA a inda babu DAMUWA babu BAQIN CIKI babu KISHI babu SAKI babu MUTUWA balle SAKIN AURE".

Kuka take tamkar ranta ze fita shikansa dauriya ce kawai irin tasa amma da zeyi kukan yasan ze samu sauqin radadin da yake ciki. Ya ajiye mata wata Leda fara mara girma sosai sannan ya ciro wata Envelope daga Aljihunsa ya dora akai yana cewa
"Kiyi haquri da wannan akwai ayyukan da nakeyi duk na zuba kudade kuma abin yazo babu shiri, Naji Hajiya tace zatazo gobe may be su taho tareda yara dukda yanzun ma nacewa Mu'ayyad yazo ya rakoni yaqi da alama kishi yake sosai fa" ya fada yana dan murmushi da bekai zuciya ba, bata dago ba kuma bata bar kukan ba, ya sake cewa
"Ki dena kukan nan haka kar Angonki yaci tarata yace na saka masa kuka Amarya, yawwa sannan dan Allah banda tsaki banda muguda baki mazan yanzu saurin hannune dasu be zama lallai yana da haquri iri na ba kar azo ana daddoke mana ke" dukda kukan da take seda tayi dariya dan yanda yayi maganar tasa yace mata
"Ko kefa, bari na tashi naje dan ban gayawa Babyna inda zanje ba kar ta jini shiru" ya miqe itama ta miqe tabi bayansa maganar Babynsa na sukar zuciyarta.

Sauri Mama tayi ta bar bakin qofar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login