Showing 171001 words to 174000 words out of 429394 words

Chapter 58 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

997

masa motar ya wuce yana sake jaddada mata akan karta bari kowa yasan da zuwansa ko halinda ake ciki.


*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 44

Gidansu Umaimah ya nufa kai tsaye, yana so ya fara tattara hujjojin da suke hannuntaa kafin ya hada Khausar da Umaimah da hukuma su girbi abinda suka shuka. A qofar gida ya tarar da Ummu-Salma da Yasir kowanne fuska face face da hawaye, ya kashe motar ya fito yana tambayarsu lafiya Yasir ya tafi da gudu ya fada jikinsa yana cewa
"Yan sanda ne suka zo suka tafi da Antyn Boy boy" ya sake rushewa da Kuka.

Kallon Ummu-Salma yayi cikin rashin fahimtar maganar Yasir yace
"Meya faru Ummu? Ina mutanen gidan kuke kuka haka?"
Ita tayi masa bayanin yan sanda ne sukazo suka tafi da Anty Umaimah, se sannan ya tuna Mu'ayyad suke cewa Boy boy, da sauri ya tambayeta me tayi ta watsa hannu alamar bata sani ba kafin taci gaba da gaya masa su Mama da Anty sun bisu, Yaya Aminu ne ya tafi kaisu dan Abba bayanan ya tafi daurin aure Qiru.

Dafe kansa yayi da hannu daya dayan yana riqe da Yasit dake rusa kuka kamar wanda aka ce Umaimah bazata dawo ba. Seya zaro wayarsa cikin rashin Sa'a ta mutu daman babu wadataccen chaji a ciki ya taho.
"Kina da waya ki kirasu muji inda suka tafi?" Ya tambayi Salma tace
"Aa, amma wayar Anty Umaimah na daki bata tafi da ita ba ko na dakko maka?" Kafin ma ta kai qarshe yace eh.
Ta ruga gida da gudu ta dakko wayar ta kawo masa ya karba ya bude dan yasan password dinta. Number Yaya Aminu ya kira cikin Sa'a ya daga suka gaisa yake sanar masa gashi a gida su Yasir sun gaya masa abinda ya faru suna ina ne?

"Daga dawowarka se kaji tashin hankali kuma, muna state CID wallahi yarinyar nan ce ta jangwalowa mutane bala'i ana zaune lafiya" Yaya Aminu ya fada kana jin muryarsa kasan yana cikin matuqar bacin rai, cikin Jimami Khalil yace masa gashi nan zuwa. Ya kalli Ummu-Salma da Yasir da suke jiran su bishi yace

"Ku shiga gida yanzu zanje na same su acan"
"Dan Allah zamu bika Yaya" Yasir din ya fada se ya kama hannunsa yace
"Aa ba'a zuwa da yara shiyasa ma kaga ba'a tafi daku ba. Kuma idan mun tafi gidan a bude babu kowa kaga za'a shiga ayi barna. Ku koma ciki ku zauna yanzu zamu dawo ba dadewa zamuyi ba kinji?"
Suka amsa da "Toh". Seda suka shiga gidan kafin ya tada motar ya bar gurin.
Tunani yakeyi a ransa me kuma ta sakeyi da aka kaita CID? Shikan Bala'in Umaimah ya fara shallake tunaninsa ace mace kamar Shaidan, daga wannan fitina se wannan gaskiya da sake, baze iya ba.

Ya isa CID ya tarar dasu Mama a waje duk wanda ka kalli fuskarsa kasan cikin tashin hankali yake. Abinda ya qara daure masa kai ganin Dr Ma'aruf Mijin Rufaida a gurin kenan tare suka jangwalo Koma menene shi daman ya tsani wannan qawancen nasu, ya rasa abinda yasa Umaimah bata sa'ar qawaye a rayuwarta duk kuma na kirkin daya santa dasu irin Su Rumasa'u ta dena hulda ta kusa dasu se abinda ya zama dole ko idan su suka kawo kansu sannan zeji tayi zancen su ko makamancin haka. Se taron marasa tunani irinta da babu meyiwa wani fada idan yayi ba daidai ba a cikinsu.

Yaya Aminu ne yayi masa bayanin suna ciki yanzu qoqari sukeyi a basu damar su gansu a kuma yi musu bayanin laifin da suka aikata amma dai kamar yanda sukaji wai Qungiyar masu kare haqqin Mata da yara ne suka shigar dasu qara dalilin me dai basu kai ga sani ba.

ABINDA YA FARU

Tun bayan da aka fita da Hadiza zuwa Asibiti dakyar Isma'il ya iya tausar Mama wadda itama jininta ya haye saboda damuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ranar a gidan ya kwana bayan ya kaita Asibiti sun dawo seda akayi mata Allurar bacci saboda ta kasa dena kuka. Adaren kwana yayi yana sallah da Addu'oi akan Allah ya bayyanar da gaskiyar wannan al'amari, washe gari ne iya zuwa aiki ba a nan gidan ya sake wuni saboda mutane magulmata da suke shigowa gidan da sunan Jaje suna qarawa Maman damuwa dan haka ya kasa ya tsare ya hana kowacce Mace shiga har sannan kuma basu bi ba'asin jin inda aka akai Hadizan ba.

Wurin qarfe biyar na Yamma ya kunna wayarsa da tun bulluwar labarin ya kasheta ya ajiye saboda yanda mutane suke kiransa suna sake tura masa da hotunan abin har mamaki yake bashi tamkar masu turo masa abin Alkhairi. Kirane ya shigo da baquwar number, a True caller yaga sunan me Kiran Musa Sale (SAN) aka rubuta, har beyi niyyar dagawa ba haka nan wata zuciyar tace ya amsa se ya daga wayar ya saka a kunne da sallama daga dayab bangaren me kiran ya amsa masa suka gaisa yana qoqarin tuna inda yasan muryar amma ya kasa.

"Sunana Barr Musa Kallah, kuma nine shugaban Lauyoyi masu aiki qarqashin hukumar kare haqqin Mata da Yara ma'ana hukumar da yar uwarka Hadiza take aiki" Mutumin ya fada cikin kamilalliyar muryarsa data ke bayyana ba yaro bane shi. Isma'il ya gyara zamansa a ransa yana ayyana dalilin kiran nada nasaba da abinda ta aikata kuma yasan korar ta sukayi daga aiki se yaji yana cewa

"Idan ba zaka damu ba inaso mu hadu da kai muyi magana akan abinda yake faruwa da Yar uwarka ne"
Ajiyar numfashi Isma'il yayi yace
"Toh ranka ya dade nasan baze wuce takaddar sallamarta daga aiki bace zaku bada indai babu damuwa a dan bani lokaci na samu nutsuwa se nazo na karba saboda a halin yanzu Mahaifiyar mu bata da wadatacciyar lafiya kuma ni nake kula da ita"

Se Barr Musa yayi yar dariya yace
"Har ka yanke hukuncin dalilin kiran kenan to ba wannan bane ba, wannan na kiraka ne a qashin kaina dan akwai abubuwan da nake so na tattauna da kai domin samun damar warware matsalar da ake ciki, maganar mu bazata dauki lokaci ba, zama mu iya yinta a waya amma na zabi mu hadu fuska da fuska dan mufi fahimtar juna dan haka idanbabu damuwa ka samu wani ya zauna da Maman na dan wani lokaci kuma in sha Allahu abinda zamu tattauna ze saka ta samu rangwame cikin gaggawa. Zantura maka da Address din gidana kazo ka same ni idan kuma ni zanzo inda kake babu damuwa ka sanr dani inda zan same ka" daganan sukayi sallama akan Isma'il din zeje dan dukda be sanshi a fuska ba yasan ba Qaramin mutum bane ko iya matsayin SAN daya gani a sunansa ya wuce yace shi yazo ya same shi.

Seda yayi Magriba ya cewa Maman zeje wani guri ya dawo ya barta da Bilkisu tareda Hajiya Zuwaira, a bakinta yaji zuwan Goggonninsu guda biyu Hajiya Barira qanwar Maman ce se Mama Innani ita kuma yayarta ce data ke bi, tuni suma labarin tashin hankalin ya riske su yasan rashin kyan hanya ne ya hanasu zuwa tun a jiyan dan ita Hajiya Barira a Zamfara take aure Mama Innani kuma tana Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Can Sharada NNDC yaje inda gidan Bart Musa yake, gida ne na alfarma dukda bashi da wani girman gaske amma ya tsaru iya tsaruwa kana gani palour gidan kasan me shi ya juqu a boko saboda yanda aka qawata gidan ya fito tamkar gidan turawa kuma babu wasu tarkace se tulin uban littattafi a kowacce kusurwa kan Shelfs masu kyau da aka kakkafa a bangwayen.

Yara biyu Maza da sukayi masa iso ciki su suka kawo masa ruwa da lemo suka sanar dashi babansu yace yana zuwa, qaramin ciki ne ya qara da cewa
"Waaya sukeyi da Momy amma sun kusa gamawa" babban ya harare shi yana cewa
"Aku, waya tambayeka" daidai nan Barr Musa ya sakko daga matakalar benen dake can gefe a cikin palour sanye yake da Jallabiyya ruwan madara a qiyasin shekaru ze kai Hamsin da biyar zuwa sama ya qaraso ciki yana miqawa Isma'il hannu daya tashi tsaye shima yana kallonsa. Tabbas yasan fuskarsa yana yawan ganinsa a TV ko shafin jaridu shiyasa ashe yaji kamar yasan sunansa amma ya kasa tuna a ina.

"Yi haquri fa na barka kana jira muna waya da Madam ne bata gari sunyi tafiya toh kasan su ba'a raba su da qorafi wai tunda ta tafi bamuyi wata doguwar magana ba shine fa yau na wanke laifina" Barr ya fada bayan daya zauna, Isma'il yayi dan murmushi ba tareda yace komai ba, shi ba wannan labarin yake so yaji ba dalilin kiransa kawai yake son ji.
Kallon yaran Barr yayi yana cewa
"Aa kai Baba ya zaku kawo masa ruwa da Lemo kadai baku da wani dan abin tabawa a gidan ne? Ina Amal bata gama abincin ba har yanzu kenan?"

"Wannan din ma yayi ranka ya dade a qoshe nake ma banjima da cin abinci ba" Isma'il yayi saurin tare shi se Barr ya miqe yana cewa
"Haba ai ko a qoshe kake dai ka dan taba wani abin" ya shiga kitchen se gashi sun fito tareda wata yar budurwa da gani ita ce yar tsakiyar Samarin sun jero ya dago kanta tana cewa
"Dady soyawa fa na tsaya yi, seda nace su bari a hado duka suka qi kuma Baba ne" ta ajiye a gaban Isma'il kafin ta durqusa har?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? qasa ta gaishe shi ya amsa yana kallonta dukka yaran da Baban suke kama sedai su Farare ne sabanin shi da yake baqi.

Zama Barr yayi yana cewa
"Bismillah Malam Isma'il ka sha ruwa se mu fara abinda ya ajiye mu ko?" Isma'il ya cika kofi da Ruwa ya kwankwade dan shi kadai ne abinda yake iya shiga cikinsa tunda suka shiga wannan tashin hankalin gaba daya ya fita hayyacinsa, yayi wata rama ta farat daya kana ganinsa kasan bashida nutsuwa.

Gyaran murya Barr yayi kafin ya dora da cewa
"Gaba dayan mu munsan abinda ya faru so maimaitawa bashida wani amfani. Bayan na shiga Office a jiya na samu saqon cewar an dakatar da Hadiza daga aiki dukda na rigada na samu saqon abinda yake faruwa amma abinya bani mamaki saboda idan kayi la'akari da zamaninda muke ciki a yanzu wannan abin ba wani sabon abu bane da har ze janyo cecekuce irin wanda naga anatayi kuma har ace an dakatar da ita daga aiki, kar kayi mun mummunar fahimta" Barr ya fada ganin yanda Isma'il yake binsa da wani kallo se ya ci gana da cewa

A nan cikin Ma'aikatar tamu da akwai Mata harda Maza masu irin wannan dabi'ar, wasu mun sansu wasu bamu sani ba kuma ana ci gaba da aiki tareda su ba tareda nuna musu wani abu ba shine tambaya ta farko dana farayi me yasa aka dauki matakin Korar Hadiza bayan ba ita kadai bace me irin wannan dabi'ar idan ma har da gaske ne abinda ake fada akanta? Amsar da suka bani duk wanda yakeyin nasa yana yi a boye ne, kuma ba'a taba kamasu da wani abu daya shafi aiki ba amma ita nata ya fallasu a gari kuma abin har ya fara shafar Qungiyarmu da yawa har suna cewa dalilin daya saka suke kashewa Mata aure kenan suna bude musu ido su koya musu karuwanci, ada ana rade radi ne amma yanzu gashi an sami tabbaci akan daya daga cikin ma'aikatan mu.

Amma dai yanzu duk wannan ta rigada ta wuce, kuma mun shirya committee domin binciko mana gaskiyar wannan al'amari kuma Alhamdulillah a yanzu har munyi babban kamu da ze kaimu ga samun duk wasu bayanai da muke da buqata, ina nufin mun samu cikakkun bayanai akan wadda ta fara wallafa labarin a shafin Facebook, dukda ance daga WhatsApp aka fara samo shi kaga zeyi wahala mu iya binciko number data fara watsa labarin amma shi Facebook cikin sauqi mun gano wanda keda alhakin yadawar".

Cikin qaguwa da surutan da Barr yakeyi Isma'il yace
"Ina ganin idan har akan wannan ne ranka ya dade bakuda buqatar bata lokaci gurin binciken komai. Ni kaina da farko bayan da saqon ya riskeni seda na nemi kwararru da suke iya tantance hoton gaskiya da kuma wanda aka hada kuma na samu tabbaci daga gurinsu cewar hotunan gaskiya ne kaga duk wani bincike ma be taso ba tunda ga babbar hujja an samu. Baya ga haka daman tuntuni munsan Hadiza tanataba rashin jinta, kawai dai abinya riskemu ne a wani yanayi da bamuyi tsammani ba sannan kuma yanda labarinya watsu a duniya kaga ba ita kadai ya shafa ba illar abinda ta aikata kuma ze ci gaba da bibiyar mu ne da Ahalinmu gaba daya".

"A haka dai gaka nan a haka kamar wayayye amma kalamanka sun nuna akasin haka" Barr ya fada kafin Isma'il yace wani abu yaci gaba da cewa
"Yanzu kai ka yarda da qazafin da akayiwa yar uwarka kenan har kana kafa hujja da daman tana rashin ji, kana da shaida akan hakan? Yanzu zaka iya tsayawa a gaban Alqali ka bada shaidar cewa gaskiya ne abinda aka fada akanta ta aikata?
Gaskiya ka bani kunya da har ka kasa shaidar yar uwarka da kuka fito ciki daya, uwa daya ta raineku tayi muku tarbiyya sedai idan kuma irin tarbiyyar da kuka tashi da ita kenan shi yasa baka zaka musanta duk abinda aka ce ta aikata ba".

Da sauri Isma'il dake kallon qasa ya dago kai ya dube shi, Barr ya daga masa kai cikin tabbatarwa yace
"Kwarai hakan ne kadai zesaka farat daya ka yarda da duk abinda aka ce ta aikata idan daman kasan akan haka ta ginu amma babu yanda za'ayi rana daya azo ace mutum yayi abu dukda ba'a shaidar mutum amma Akwai abinda idan an gaya maka akan wani seka tirza ka ciza ko kuma kaga kwakwkwarar shedar da babu wanda ze qaryata sannan kuwa amma kai ka kafa hujja da hotunan da nida kai munsan basu isa su tabbatar da zargin da akeyi ba.

Kasan girman laifin da ake zargin qanwar ka dashi kuwa? Dani dakai duk musulmaine mun kuma san menene Madigo da hukunci da makomar me aimatashi a duniya da lahira.
Yanzu idan kotun musulinci akaje se an samu Shaidun gani da iso guda uku wanda suka ganta tana aikatawa sannan ne katu zata karbi shaidarsu ta yanke mata hukunci ko kana zaton akwai alqalin da ze saurari wadannan shirman hotunan da ake yawo dasu ana mata qazafi akan su.

Na tabbatar a cikin wayarka yanzu idanan duba se an samu wadanda suka fisu muni idan ba'ayi wasa ba. Nidakai mun sani ba wani abu bane a gurin yammatan yanzu daukar hotuna su bayyanar da sassan jikinsu su turawa samari kaima na tabbatar ba zaka rasa wadda take tura maka ba Nida kai munsan komai babu abinda zaka boye mun idan kuma qarya nakeyi ka kawo wayarka na kawo tawa a gani idan baza'a samu ba".

Yanda kasan qasa ta bude Isma'il ya shiga haka yaji, se yake ganin kamar Barr yasan abinda yake cikin wayar tasa ne dan gaskiya ya fada Yammatan da suke tura masa da hotunan da videos dinsu na tsiraici bazasu irgu ba wasu ma bashi yake tambayarsu ba. Wata ma daga sama baka san wacece ba zata kawo maka tallan kanta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login