Showing 231001 words to 234000 words out of 429394 words

Chapter 78 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1000

da iya abincin sadaka da ruwa da akayi akanta bazata iya qayyade nawa suka lashe ba ita ta kora a ruwa haka kuma tabi wanda ya samo musu ta qare masa tanadi akan me?
Ji tayi kamar an kwada mata guduma akai saboda wani tunani daya fado mata, jiyan nan Hajiya Saude maqociyarsu take mata zancen yanzu lalacewar da duniya tayi ba iya mata ake neman lalata dasu ba kafin ayi musu abu harda maza, wani dan Qawarta yaje neman aiki aka ce seya yarda anyi Homo dashi yace ya haqura shine abin basu mamaki suke ta jajantawa karfa ace abinda Khalil dinta yayi kenan shima ya samu kwangilar Umaiman ta gane shine ta lalata?

"Hajiya wanda ya samo mun munyi yarjejeniya dashi akan zan auri yarsa, ranar nan da wancan abin ya faru bina tayi a baya naje gidansu yarinyar shine ta dawo tayi wannan haukan ta fasa kayan dakinta tsaf har ta jiwa kanta ciwo. Shine yau saboda na fada mata gaskiyar abinda yake faruwa na kuma bata tabbacin ba auran yarinyar zanyi ba na karba ne kawai dan na samu kwangilar nan kuma da zarar komai ya kammala shikenan zan rabu da ita shine yarinyar nan tace nazo na karbo mata danwake bayan na fita ta dauki wayata ta kira Dr tayi masa cin mutunchi sannan ta lalata mun takaddun ta goge softcopy din, ko inda zanyi backup bata barmun ba ta goge komai, Hajiya kinsan wahalar dana sha akan aikin nan kuwa? Kinsan tsahon lokaci da kudin dana kashe akan kwangilar nan amma wannan yarinyar ta lalata komai saboda haukan baqin kishinta?" Khalil ya fada idanunsa suka sake rikidewa sukayi jaaa bakinsa da hannunsa suna rawa.

Kasa cewa komai Hajiya tayi dan ita da kanta tasan irin qoqarin da yake akan kwangilar, kullum ne seya nanata mata akan tayi musu Addu'a, haka abincin sadaka tunda aka fara maganar sau biyu akeyi a sati sabanin da da sukeyi Juma'a Juma'a sadakar ruwa da alawa kuwa basa yankewa akwai masallaci a layin gabansu hade da Islamiyya can ake kaiwa kullum asha ayi alwala yara kuma a raba musu alawa
(Sadakar ruwa nada matuqar tasiri yan uwa mu daure koda sau daya a sati ki siya akai masallacin mutane suyi alwala haka alawa a ringa rabawa yan yara Sadaka maganin Musiba ce).

Gwauron numfashi ta sauke kafin a sanyaye tace
"Dukda haka wannan be kai ace ka shaqeta ba Khalil idan wani abu ya sameta fa me zaka cewa iyayenta? Akan ka rasa kwangila ka illata musu yari ya kome, ina rabaka da wannan zuciyar idan rai ya baci ai hankali ne yake nemo shi kuma abinda be faru ba shi ake gudu wannandaya rigada ya faru sedai ayi adfu'a Allah ya taqaita na gaba bata kyauta ba kaima kuma beci kayi hakan ba tunda kasan idanta sani ranta ze baci"

"Ranta ze baci Hajiya? Yanzu bacin ran Umaimah kike gudu akan Asarar dani ta janyo mun?" Khalil ya fada cikin zallar mamakin Hajiyar tasa seta gyara zama tace
"Ba haka nake nufi ba, gani nayi kuna zaune lafiya da matarka wata matsala bata taba giftawase irin haka ta faru tunda kasan zafin kishin matarka se kayi haquri da duk wani kule kulen mata tunda babu abinda ta rageka dashi koba haka ba?"

"Babu abinda kika sani akan zamana da Umaimah Hajiya ban kuma san dalilinki na bin bayan duk abinda take aikatawa ba amma inajin tsoron ranar da haukarta zata gifta ta kanki" Khalil ya fada ba tareda ya kalle ta ba, se ta miqe jiki a sanyaye tana cewa
"Asibiti zan koma na gano yanda take ka tashi muje tare dan iyayenta sunzo nasan dole zasu buqaci jin abinda yasa kayiwa yarsu haka"

"Kiyi haquri Hajiya amma bazan iya zuwa ba, kuma daga can ta wuce gidansu bana buqatar ta sake dawomun cikin gidan nan" Ya fada se Hajiya data fara tafiya taci burki baki na rawa ta kalleshi tace
"Karka ce mun sakinta zakayi Khalil akan abin duniya me faruwa ya qare zaka saki matarka da tun baka dashi take tareda kai?"

"Ni ban yanke hukunci ba amma idan kika matsamun naje inda take a yanzu zan iya furta abinda duk baze mana dadi ba, ta tafi gidansu kawai" ya sake fadawa Hajiyan daga haka ya miqe yana tafiya dakyar ya haye sama kansa ne yake masa ciwo kamar me, ga Dr Sabitu shima kamar m kwantaccen kai se kiran sa yake a waya yana iko masa da Text kala kala, Threatening nasa yake akan seya saka an kwace masa Licence din company, seya lalata masa career ta yanda sharar fili baze samu a bashi ba ballantana gini kai shirme dai kala kala gashi nan.

BAYAN SATI DAYA
Uncle din Anwar daya yi musu hanyar ganin Dr Sabiyu shiya shiga ya fita dakyar ya kashe wutar dake tsakanin su Khalil da Dr Sabitu bayan ya kai masa burbushin takaddun daya ajiye suka bushe, Khalil ya roqi daya maido masa da copy din proposal da paper work din da yayi submitting tunda bashi zeyi aiki ba se a maido masa da basirar sa da wahalarsa Dr Sabitu ya banka masa harara ba tareda yace komai ba haka suka baro gidan zuciyar Khalil na masa zafi, idan ya tuna wanine ze mori wahalar sa se yaji kamar yayita kurma ihu irin basirar daya zuba a gurin tsara yanda ginin ze kasance ba kadan bace amma yanzu a bagas wani ze mori abinda yayi wallahi Umaimah ta cuce shi.

Wayarsa ce ta shiga qara ya zarota a Aljihu ganin me kiran ya sakashi daidata muryarsa kafin ya daga.
"Barka da Rana Alhaji" ya gaida Aminin Mahaifin nasa daya kirashi Alhaji Garba daga daya bangaren yace
"Barka dai Ibrahima ya gida ya mahaifiyar taku?"
"Lafiya lau Alhaji" ya sake fada kafin yayi shiru se Alhajin yace
"Waliyyin matarka ne ya kirani a matsayina na waliyyinka, yace kusan sati daya kenan ashe matarka tana can gidansu shine suka kira suji ma'anar zaman nata saboda tunda ta koma kamar yanda sukace daga Asibiti aka sallameta ko basuji komai daga gareka ba".

Numfashi yaja kafin yace
"Eh hakane Alhaji, sabani muka samu na barta ta zauna ne a can zuwa wani lokaci kafin muga yanda hali zeyi"

"Wace irin magana ce haka Ibrahimu kamar yaya yanda hali zeyi jingine musu yarinya zakayi ba tareda tasan matsayinta ba kenan se sanda kayi ra'ayi tukunna?" Alhaji Garba ya fada se Khalil yayi shiru dan be san me zece masa ba, shidai wallahi baze dawo da Umaimah yanzu ba se ya gama jinyar asarar data janyo masa sannan

"Me ya hadaku?" Alhaji Garba ya jefo masa tambayar, ya sakeyin shiru kafin ya nisa yace
"Laifi tayi mun kuma daman ta dade tana mun abu ina tarata shiyasa yanzu na bata hutu ko zatayi hankali ta dena abubuwan da takeyi" Khalil din ya fada kamar baya so se Alhaji Garba yayi murmushi yace
"Zuwa yau da Magriba idan kana da lokaci kazo nayi magana da Kawunku Alhaji Abubakar se muje can gurin iyayen nata tareda kai a sasanta, zaman aure ko ina haquri akeyi Ibrahimu su mata duk daya suke wani lokacin in sukayi maka abu seka rasa hukuncin da zaka dauka akansu amma haka ake shanyewa aci gaba da zama. Kayi haquri ta dawo dakinta kodan halin da take ciki an rigada an fara tara zuri'a be kamata ace shekarun da aka kwashe ana zaune qalau ba se yanzu ne da girma ya fara hawanku matsaloli zasu fara bullowa, mutane da magana yanzu se kaji wani abu na daban ace ka fara wulaqanta matarka saboda ka samu budin rayuwa baza'a binciki kai me takeyi maka ba".

Kamar ze rusa kuka haka ya amsawa Alhaji Garban badan yana so ba sedanbaze iya musu dashi ba. Haka sukayi sallama yana ayyana ko sunje Umaimah ba zata dawo masa gida a yanzu ba, a gaban iyayennata ze fadi abinda tayi masa ai sun san ya dade yana shanye takaicinta idan kuma za'a masa Adalci yanzu daya ce ta tafi baza'a takura masa ya dawo da ita ba.

Gida ya wuce ya tarar da Hajiya na fama da Rigimar Bibi data dawo daga gidan Jamila jiya tana ta kukan ina Mummynta, Mu'ayyad dai daman tunda ya tambayi tana ina akace tana gidan Mama yaci gaba da sabgarsa Bibin ce me rigima Hajiya nata lallabata taqi Khalil na shigowa tace
"Yawwa, gatan tunda taje ta buga qofarku ba'a bude ba ta tasa kukan Mummy bayanda ba'ayi da ita tayi shiru ba taqi haqura ko za'akai mata ita can gidan ne?"

"Babu inda zataje" ya fada yana kamo hannun Bibin ta fada jikinsa tana Dady zanje Mummy akaini gurin Mummy"
"Zakisha Ice cream?" Ya fada yana goge mata hawaye, dake sarkin son zaqi ce nan ta daga kai da sauri tana cewa
"Harda Chocolate da Pizza, Mummy J is not letting me eat some chocolate"
"Oh Mummy J bata kyauta ba, maza kije Raziqa tayi miki wanka muje mu siyo yanzu" Khalil ya fada yana jan kumatunta ta kusa yi murmushinta me kyau kafin ta falla da gudu Hajiya na cewa tayi a hankali.

Kallonta ta mayar kan Khalil da gaba daya ya rame a yan kwanakin nan tace
"Khalil baka cin abinci ne ko kaga yanda ka zabge kuwa"
Murmushi kawai yayi yaqi ce mata komai, seta sake cewa
"Yanzu dai ai ranka yayi sanyi ya kamata kaje ka dawo da matarka haka babu dadi ka barta a gida ga ciwo nasan iyayen sun zuba ido ne suga gudun ruwanmu kafin su biyo ba'asin abinda ya samu yarsu dan kwana biyu idan na kira mahaifiyarta ma naji jikin yanda take amsa mun nasan suna cike damu".

"Baban Qoqi ya kirani, yace sunyi magana da Baba Habu wai yau zamuje can gidan amma ni gaskiya Hajiya ki kirashi kice yayi haquri ya qaramun lokaci" Khalil ya fada se Hajiya ta kama baki tace
"Au magana na fika iyawa kome dakai ka kasa gaya masa hakan seni kake so na fada? Ok so kake ka janyo mun bakin duniya ace ni na saka ka kori matarka ko? To ahir dinka ka kuma fita a ido na. Har wani abin duniya daka rasa yafi ta a gurinka da zaka dauki fushi ka hana ranka sakat saboda shi, rabo ne bana ka ba kuma koda ba'ayi hakan ba bazaka samu na se Allah ya kawo wani sanadin da ze saka ka rasa ballantana ka zauna kanayiwa mutane baqin rai in ka haqura ka dangana se kaga Allahn ya maida maka da wanda yafi haka"

"Da se ta bari wani silar ya gifta ai base ta zubar mun da mutunchi taja mun bala'i ba, Hajiya na fuskanci baki san girman Asarar da Umaimah ta jawo mun ba ko? Kinsan qarfin Dr Sabitu a cikin gwamnati kuwa? Kinsan abinda ze iya yi?
Hajiya yau idan yaga dama yace a rufe company na take za'ayi haka babu me tambayarsa dalili ko yanzu dukda Uncle Mus'ab da wasu abokanansu sun shiga ciki an sasanta kin??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a zaton har zuciyarsa ya haqura ne musamman da ita yar tasa da yake komai saboda ita yanzu haka fa tana Asibiti bata da lafiya saboda ance na fasa auranta.
Ni kadai nasan damuwar da nake ciki Hajiya amma idan na rasa komai dani da itan daku duk tare zamu zauna musha wahalar" ya fada yana miqewa cikin sabon bacin ran daya taso masa. A rutsin nan banda wannan babbar kwangilar seda ya rasa wasu guda biyu daya har sun fara ginin ma mutumin ya kirashi yace ya dakata ashe wai Surukin Dr Sabitun ne yana auren yar yayanshi, to idan aka ci gaba da haka ai yana cikin cakwakiya banda qungurmar Asarar record din Ayyukansa na baya wasu tun kafin ya shiga Jami'a yake zanensu yana ajiyewa seda ya nutsu yaga ashe ba iya waccen folder ta taba ba wannan Ifrituwar matar ta goge komai ai wallahi idan ya maidota nan da shekara daya ma ya mata Adalci adai abinda tayi masa.

"In sha Allahu bazamu shiga wahala ba babu kuma abinda ze iyayi maka ai Allah ne yakeyi bashi ba kuma dashi muka dogara. Kayi haquri kawai ita jarabawar ubangiji babu ta inda bata fa bawa idan kuma kayi haquri se kaga ka tsallake ta, yanzu dai kuje din kuma duk yabda iyayenka sukace kayi karka musa musu kaji ko" Hajiya ta fada Khalil kuwa tafiya yaci gaba dayi yana jinta kawai, Indai Umaimah ce ai gata gatanan, sedai Allah ya kiyaye randa zata hado su kawai.

UMAIMAH
Seda ta kwana biyu a gidan kafin ta iya fara hadiyar abinci da kyau saboda yanda wuyanta ya daure dan ba qaramar shaqa Khalil din yayi mata ba. Sau daya Mama tayi mata tambayar meya hadasu ta saka mata kuka dan bata san me zatace ba. Idan tayi qarya kuma gaskiya ta fito daga baya ita ce a ciki haka in ta fadi gaskiyar ma ba fita zatayi ba dan qila qarasa shaqeta Maman zatayi kawai dan bata manta kashedin datayi mata lokacin case din Hadiza ba, taja mata kunne ta gargadeta tace mata yau ko cikin gidanta Khalil ya dakko mace ya kawo koda wasa karta kuskura ta ce zata dauki wani hukunci a hannunta, ta gaya mata kota kira yan uwanta karta yarda tayi amfani da tunanin da kwakwalwarta take bata to yanzu idan taji akan Macen ta sake wannan aika aikar ai qarasata zatayi kowa ya huta.
Anty Laure ce take kareta duk sanda aka tada maganar jin meya hadasu ita zata shiga zayyano qarya da gaskiyar abinda take hasashe, tace Kule kulen mata yakeyi dan kullum seta ganshi yana waya yana dariya ko yayi wanka ya fice da daddare tsabar sharri cewa tayi sau biyu tana tsintar dan kunnen Mace akan Dan Table din da yake ajiye muqullin mota da yake a bakin qofar palour qasan wai yana ajiyesu tare be sani ba, ita ta gama concluding neman mata yakeyi shine ta gane sukayi rigima ya shaqeta Umaimah dai in tana bada labarinta sedai ta sunkuyar dakai, jira take ta sake jin dama dama ta neme shi ta bashi haquri salin Alin ba se wani yaji abinda ta aikata ba.

Kwananta biyar Baba Abdullahi yazo gidan da safe Abba ya kirawo shi, tana zaune gaban Murhun gawayi Anty na soya musu qosai dan ranar Kunun gyada da qosai tace tana sha'awa Baba Abdullahin ya shigo ta gaishe shi yace
"Ke me kike a gidan nan da sassafe haka, badai nan kika kwana ba?"
Qasa kawai tayi dakai suka gaisa da Anty ya wuce bayan tace masa Abban yana ciki shi yake jira.

Anty ta hada abin kari ta tafi kai musu tana cewa Umaimah
"Kince se me zafi gashi nan a gabanki kuma kin bari yana hucewa".
Umaimah ko gaba daya Kosan ne ya fita a ranta, bata so Abba ya kira Baba Abdullahi ba tasan yanzu Asirinta ze tonu bayan yau take shirin ta kira Khalil ta lallaba abunta yazo su tafi salin Alin babu wanda yaji amma yanzu Abba ya rusa komai, Baba Abdullahi da taratsinsa zuwa zeyi yace zeyi masifa in jayi an dake tan daga nan kuma liqi ya balle.

A cikin palour Abba kuwa fada Baba Abdullahi yakeyi kamar ze hadiye harshensa yake cewa
"Wallahi Yaya bana jin dadin abinda kake mun musamman akan Umaimah, yanzu haka kwanaki yasa aka kulle yarinya a Cell kamar mara galihu ba'a gayamun ba, aka gama wannan ya jingineta a gida sama da wata biyar harta haihu yarinya tayi wayo sannan ta koma kawai dan kun nuna masa bata da gata in ba haka ba a ina ka taba ganin ana wannan abun da yakeyi?
Shikenan daga ta masa abu seya korota gida se sanda ya mula yace ta koma who does that?

Dan ubansa haka ake aure? Ko kuwa saboda an tsani yarinya ba'a bin ba'asi duk sanda suka samu matsala sedai a dora mata laifi ai qarfe daya baya Amo shi kadai amma kun rigada kun nuna masa bata da wani gata yayi yanda yaga dama da ita ai dole yanzu gashi nan anzo gabar da ya fara dukanta yana shaqeta, tunda yasan ko kasheta yayi qarshe ita za'a dorawa laifi ace ita ta nemi halakashi in the process of self defence ya kasheta ko to wallahi bazata sabu ba, ni ina son abata in ku duk bakwaso zan kuma kwato mata haqqinta daga nan police station zanje in aka bi mata kadin Shaqeta da yayi sannan yazo muji matsayar auran na gaji ya sallameta kawai ai ba rasa masu auranta zatayi ba yarinya da kyanta da komai bazata zauna baqin cikin Miji ya kasheta ba bayan ta gama shan naku.





[8/18, 9:52 PM] KYAUTA: *TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*.
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY* .

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 55

Kallonsa Baba Absullahi kawai Abba yakeyi baki bude saboda mamaki koda yake be kamata ma yayi mamakin ba sanin waye Baba Abdullahin ai daman shi Umaimah ta gado kuma da ace Mace ne shi daman Hassana da Hussaina zasu zama gurinjaye jayen bala'i kpda yake yanzun ma ya aka qare rigima ai se wadda ya manta ce baya janyowa kuma saboda halinsa sedai a haqura a barshi dan ko bashida gaskiya se ya san yanda ya ci galaba akanka.

Miqewar daya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login