Showing 9001 words to 12000 words out of 429394 words

Chapter 4 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

926

hadin shine daidai, idanna dakko mara hayaniya irina ai gidan mu will be boring, gara dai a samu wadda zata ringa mayar dashi lively"

"Hakane, toh Allah ya tabbatar mana da Alkhairi abokina, kace wannan ziyarar bazata da ka kawomun ashe rabone ya kiraka"

"Amin amma da saura, ni yanzu babu ma shirin aure a gabana kasan dai yanda ake lallaba rayuwar ga aiki yaqi samuwa yar buga buga kawai akeyi, qoqari nake na gama hada Masters din nan nayi settling. Akwai abubuwa da yawa danake da buqatar kammalawa kafin na dakkowa kaina maganar aure tunda bazaka dakko yarinyar mutane kazo kana bata wahala ba dole tana da buqatar abubuwan more rayuwa ko yayane a gidan ka" Khalil ya fada.

"Hakane, amma kuma ko a yanzu Bayero ai Alhamdulillah rayuwarka na tafiya daidai zaka iya ajiye iyali, mutum nawa kafin cikin abokan mu da suke aikin abin fa duk intihani ne kawai amma idan kace seka samu yanda kake so zakayi aure zaa dade gaskiya" Nasir ya fada.

Se Khalil ya gyara zaman sa yace
"Hakane nima ba wai ina nufin sena tara kudi zanyi aure ba komai rabo ne a rayuwa, ta yuwu ma naka arziqin seka yi auran zaka same shi amma yanzu Nasir kadai san nauyin gidan mu a kaina yake. Nine ci, sha da suturar mahaifiyata da qannena guda biyu da suke gabanta, kai har masu auran idan suna da wata buqata nifa suke kira ka sani.

Yanzu haka ni ina Masters, ga Jalila nk nake dauke da nauyin karatunta, Halifa bana ze gama secondary ya shiga Jami'a shima ga dai abubuwa nan kala kala babu yanda zaayi yanzu na tattago maganar aure da wadannan nauyin a kaina bayan ba wani kwakwkwaran aiki ne dani ba, bani da muhallin da zan ajiye mace a yanzu, samun nawa na lokacine, se mun samu yar kwangila anyi sannan muke samu, muna dai ta fatan Allah ya buda ya bamu yanda zamuyi tunda dai Allah yaga zuciyar mu".

Numfashi Nasir ya sauke yana kallon abokin nasa da tausayawa, rayuwa kenan. A shekarun baya idan akace akwai wata rana da Khalil Bayero zasu shiga halin da suke ciki a yanzu babu me yarda. Irin gatan da suka tashi a ciki, mahaifinsu tsayayyan mutum me wadata iyalansa su kansu sun shaida tarin Alkahiran sa a rayuwa dan da yawan abokan Khalil da sukayi primary tare ta gomnati lokacin da budi yazowa babansu ya chanza musu makaranta zuwa ta kudi haka ya hada dasu duka ya kaisu ya ringa biya musu kudin makaranta.

Banda Scholarship daya samar musu na fita qasashen waje sukayi karatun degree dinsu gashi yanzu ganiyar sa suke ci, duk kuma abinda suka zama a rayuwa sanadin sa ne.

Bayan rasuwarsa ne abubuwa suka damewa iyalansa, wani amininsa da suke harkar kasuwanci yazo da takaddun da duk me hankalin daya gani yasan na bogi ne akan yana binsa bashin wasu maqudan miliyoyin kudade, ya samu goyon bayan qaninsa da suke uwa daya uba daya wanda ya bada shedar zur a kotu kan Marigayin da bakinsa ya gaya masa cewar akwai bashi tsakaninsa da Alhajin amma kuma babu wanda yasan da hakan ciki harda matarsa da Kuma Khalil din kansa wanda a sannan kusan komai na Mahaifinsu shine akai.

Ansha badaqala musamman da Iyalansa suka kafe akan basu yarda ba, da ace akwai irin wannan magana me muhimmanci da Alhajin ya fada tun yana jinya tunda ba mutuwar fuji'a yayi ba yasha jinya sosai da har seda ya fitar da rai da rayuwa kuma a sannan seda ya fadi duk wani da yake bi bashi ko shi ake binsa amma da yake duniya babu gaskiya, aka je kotun ma suka siye Alqali suna ji suna gani haka suka tattara kudaden daya ce suka bashi wanda seda suka hada da siyar da kadarorinsu kafin suka tada kudin, qarshe gidan da suke ciki kadai suka tsira dashi se wani qarami da suka saka yan haya a ciki. Duniya kenan wata shari'ar se a lahira.

Hira suka taba sosai kafin Khalil yayi masa sallama suka fito ganin dalibai nata zuwa karban exam card zaman shi kuma kamar yana raba masa hankali.

"Ka gaida Hajiya dan Allah, insha Allahu qarshen satin nan zamu shigo da madam tunda sunyi arba'in" Nasir ya fada daidai sanda suka isa inda Khalil ya ajiye Lifan dinsa.

"Aa abokina ina motar ne naganka da Mashin kuma?" Nasir din ya sakw fada.

"Kai rabu da motar nan, kasan 306 da matsalar belt, haka kawai ina tafiya se ya cire kai na gaji dai kawai na siyar da ita na siyi wannan yafi mun na shiga ko ina hankalina a kwance".

"Tab, gaye iya gaye ashe gurgune" Nabila Sani ta fada tana kallon Khalil dake buga machine, tunda suka fito ta saka su zama a kujerun da suke kusa da Office din saboda harga Allah Khalil din ya tafi da imaninta, jira take ya fito tasan ta yanda zata yi masa magana se ga wannan big turn off din, ashe ma wankan ne kawai aljihu babu ko sisi.

"Arziqi nufin Allah ne, kuma dan kin ganshi da lifan shine aka ce miki matsiyaci ne wallahi Nabila ki dena abinda kike shiyasa har yau kika rasa ko wanda ze kiraki a waya ki rage dare" Umaimah data kalli Khalil din itama ta juya tana gayawa Nabila.

"Allahu akbar, Allah ka nuna mana Annabi, yau Umaimah ce takewa wani fadan yayi ba daidai ba lallai inda ranka kasha kallo" Halima ta fada cikin sigar tsokana dan daman ita gwanace.
"Se ku tashi mu tafi ai" Nabilan ta fada a fusace fuu tayi gaba suka rufa mata baya suna sake caccakarta.

Murmushi Khalil da duk abinda suka fada yaji yayi dan da dan qarfi suke maganar bayan haka yana da kunne sosai, Kallon Nasir yayi dake danna waya yace
"Nas kodai na shiga gurin nan ne, dagaske fa yarinyar nan tamun over taking"

"Abokina ka shiga kawai mana tsoron me kake ji, babu komai in sha Allahu tsamu tsaya maka kawai dai ka shirya ina qara gaya maka akwai daru" Nasir ya fada yana bashi hannu,

"Shikenan zanyi tunani akai" daga nan sukayi sallama ya buga mashin dinsa yayi gaba. A bakin get ya sake haduwa dasu suna jiran abin hawa, sukayi ido hudu da Umaimah ta kuwa murguda masa baki da harara yayi mata murmushi ya wuce abinsa.

Cikin taimakon Allah suka qare jarabawarsu tsaf saura jiran sakamako, ranar ansha hotuna anyi celebration, akwai Dinner da suka shirya yi an dade ana hada kudi daman dan harda anko suka fita Umaimah ta biya kudin komai amma bata jin zataje, tasan ma baza'a barta ba yanzu kuwa da take gudun laifi bazata fita babu izini ba. tunda suka fara jarabawa daman a faduwar gaban abinda yake gaba take, furucin Abba na idan bata fitar da Miji ba ze bada ita sadaka na bala'in damunta ta kuma rasa yanda zatayi.

Ta nemi shawarar Rumasa'u akan maganar tace mata tayita Addu'a kawao Allah ya yi mata zabi na gari, ta kuma ce mata ta gwada neman wanda taga hankalinta yafi kwantawa dashi cikin samarinta na baya ko Allah zesa a dace amma babu nasara.
Duk wanda tayi qoqarin bugun cikinsa akan batun aure zillewa suke, qiriqiri suke nuna mata suna sonta da gaske amma bazasu iya da halinta ba wannan abin na bala'in qona mata rai, ita wane hali ne da ita?
Shin laifi ne dan kayi kishin abinda kake so su ba abin alfaharin su bane ma ace ana kishin su?

Kusan sati da gama makarantar su babu wanda yace mata qala akan batun aure, ba kamar baya ba yanzu komai ya dawo daidai a gidan itace ma take dararewa wani lokacin saboda gudun kar a diro mata da maganar fito da Miji katsahan. Fita ce dai aka hanata, dan ko Islamiyyar da take zuwa Asabar da Lahadi ma Abban ya soke yace yawo ne kawai, daidai gwargwado ta samu ilimi ta zauba agida tayita tilaqar abinda ta sani amma fita indai bada dalili me qarfi ba be yarda ba.

Ana haka Yayarsu Anty Hajiyayye ta haihu, dayake CS akayi mata da farko akace a dawo da ita gida ta zauna idan jikinta ya warware seta koma tunda a can babu mataimaki ga yara kuma amma Abban su yaqi, daga qarshe dai dakyar Mama ta lallabashi akan tunda Umaimah bata komai taje ta zauna mata tareda wata mata da aka samu har zuwa sanda zata warware.

Seda ya kafa mata warning sosai ya kuma jawa Hajiyayyae kunne akan duk in yaji ba daidai ba se ranta yafi na kowa baci haka ta tattara ta tafi gidan Yaya Hajiyayyen.

Washe garin suna da yake ba taro sukayi ba bayan an gama suyar nama an kasa Yaya Hajiyayye ta bata tace ta shiga gidan da yake kallon nasu takai.
Dogon Hijabi har qasa ta dora akan Doguwar rigar material din jikinta fuskar nan kamar ko yaushe babu ko digon kwalli akan ta amma da yake kyanta daga Allah ne se gata ta fito shar abin ta.

Tun daga wajen gidan ta tabbatar da gidan masu arziqi ne, idan ma a yanzu babu to tabbas da an samu ta tura qofar get din da take a bude ta shiga qaton compound din gidan da sallama. Babu kowa a tsakar gidan, taja ta tsaya ganin qofofi biyu ne manya bata san wanne ne ta shiga ba, gashi ma ta manta ta tambayeta wa zaa kaiwa dan qila mata biyu ne a gidan.

Daga bayanta taji ance
"Ya kika tsaya? Bismillah ki shiga suna ciki" seta juya a firgice dan bataji takun takalma ba se magana kawai, ido hudu sukayi da Khalil dake tsaye a bayanta yasha wanka da wata danyar Shadda Fara gurin gaba daya ya karade da Qamshin turarensa.
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 4

Ya ganeta, amma da alama it bata gane shi ba tace,qasa qasa ta harareshi tace
"Ka tsorata ni wallahi, kuma bansan qofar shigan ba. Daga gidan Maman Asad nake ta bada naman suna a kawowa Hajiya" ta qarasa tana miqa masa ledar Naman. Se yayi gaba yana cewa
"Muje na nuna miki"

Tsabar neman magana irin nata bibsa take a baya tana kwaikwayon tafiyar sa da yake yi cikin nutsuwa kamar me qirga takunsa. Gulmarsa take a zuciya tana cewa
"Ji yanda yake wani yanga dan Allah kamar mace ya ware qafa yayi sauri Aa se batamun lokaci yake" a haka ya tura babbar qofar dake part din farko ya shiga da sallama ta rufa masa baya.

"Zauna, bari nayi mata magana inaga tana sama" ya fada yana wucewa matakalar bene, seta nemi daya daga kujerun palour ta zauna tana bin ko ina da kallon.
Kayan cikin palour sun dan tsufa amma da yake masu kyau ne da asalin tsada ga kuma ingantacciyar tsafta da suke samu seya boye tsufan nasu. Ko ina qalqal se daukar ido yake ga qamshin turaren wuta daya hadu da sanyin Ac suka qarawa gurin nutsuwa ta musamman.

Babban Enlargement photo dake kafe a bangon palor ta ringa kallo, Wanda take kyautata zaton shine megidan tareda matar gidan se yaransu guda bakwai maza biyu mata biyar.
Kallon su take tanaso ta tuna inda tasan fuskar dan kusan duk kamar su daya sedai wasu sunfi wasu haske a ciki amma ta kasa tunawa.

Bataji sakkowarsu ba se maganar babbar mace da take cewa "Sannu da zuwa yammata"
Zamowa tayi daga kujerar tayi ta shiga gaisheta ta amsa mata cikin sakin fuska.

Kanta a qasa saboda kwarjinin da matar tayi mata ta miqa mata ledar tana cewa "gashi inji Maman Asad tace a kawo"

"Toh naman suna ne aka biyo mu dashi dukda bamu shiga ba? An gode Allah ya raya Ummu-salma, kice mata tayi haquri wallahi qafata ce ta motsa abinda ya hanani fitowa kenan amma in sha Allahu zanzo naga baby" Hajiyan ta fada kafin ta cigaba da cewa

"Qanwarta ce ko qanwar Habibu?"
"Qanwar tace ni" Umaimah ta bata amsa cikin qaguwa, to tambayar kuma ta mecece haka.

Ita kuwa Hajiya cikin son janta da hira ta ci gaba da cewa "Allah sarki ban taba ganinki ba, na dan san qannen nata kuma musamman Nuratu indai tazo takan shigo mu gaisa"

"Gwana uwar an cusai kenan, wato taga qaton gida har wani shiga take su gaisa Allah ya sawwaqawa Yaya Nuratu dai" Umaimah ta fada a ranta a fili kuwa tace
"Allah sarki ai Nuratun nake bi, nice autar su a Mata" se ta miqe tsaye
"Aa badai tafiya ba kuma muna cikin yar hirar mu, gashi ma ko ruwa baa kawo miki ba 'Habiba kina ina ne? Ki kawo mata ruwa" Hajiyan ta fada.

Se ta fara tafiya tana cewa "Aa wallahi babu komai Hajiya bari naje aiki mukeyi ne se an jima"

"Toh shikenan ki gaida gida na gode, se kin sake shigo mana ko, yaya sunan yar tawa?"

"Umaimah" ta bata amsa tana dan murmushi

"Toh Umaimah ki gaishe da Hajiyayyen nagode kinji" daga nan sukayi sallama ta fice kamar wadda take akan qaya.

Tana fita Khalil ya fito daga wata qaramar qofa ya canza kayan jikinsa zuwa dogon wadon jeans da T-shirt yanata zuba qamshi.

"Sannu Babana mutanen zazzau kunsha hanya amma kunyi sauri kamar wanda kuka taho a iska"

Seda yasha ruwan da aka kawowa Umaimah bata sha ba kafin yace "aikinsan yanzu hanya ta gyaru sunci qarfin aikin titin sosai shiyasa tafiyar take sauri kuma bamu zauna ba ana daura auran muka taho harda Amaryar dan a shirye suke suma"

"Masha Allahu Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana na yan baya lafiya, kana kallo dai daga sa'anninka gashi nan layi ya fara zuwa kan qannenka sun fara aje iyali kai ko kunya baka ji sedai kasa shadda ka tafi daurin aure ka kasa yunquri kai azo naka" Hajiya ta fara qorafin nata na kullum indai aka yi zancen aure.

Murmushi yayi ba tareda ya bata amsar maganar tata ba ya waiwaya yana duban palour yace "ta tafi kenan"

"Wacece?" Hajiyan ta tambaye shi, seda ya sake kurbar ruwa kafin yace
"Umaimah" shikansa se da yaji wani iri, yama akayi ya riqe sunanta?/yanda ya kira sunan seka rantse shiya rada mata shi.

Kallonsa Hajiya tayi da mamaki jin ya kama sunanta, "ka santa ne daman?" Ta tambaye shi tana tsare shi da ido. Seya duburburce, ya manta shaf da halin Hajiyar tasa, yanzu abinda be faru bama tunda akayi haka seta qullo shi wai wa ma ya aike shi nuna ya santa ne? Koda yake yarinyarce, ta shige masa yanda beyi zato ba.

"Magana nake maka ka tsareni da ido kayi shiru, ko baka ji me nace bane?" Ta fada ganin gaba dayama hankalinsa baya gurin, se yayi firgigit yana shafa kai yace

"Aa fa Hajiya ni ban san ta ba, sau daya na taba ganinta dalibar Nasir ce ranar dana je makaranta gurinsa na ganta a office din shine fa naji ya fadi sunanta se kuma dazun na ganta a compound wai an aikota amma ba wani abu daban bane da kike tunani"

"Toh ni me kaji nace Babana, yarinyar ma ai ta gidace qanwar Hajiyayye ce kuma dai kai shaidane akan nagartar Hajiyayyen tunda Mijinta kusan abokinka ne kaima kana yabonta, babu komai Allah ya tabbatar mana da Alkairi" Hajiyan ta fada tana murmushi me kama da dariya saboda murnar wannan al'amari, ita daman tunda taga yarinyar tayi mata, harta fara saqa yuwur hadi ta da Khalil din nata se gashi ma ashe tuni Allah ya hada abinsa, to Allah yasa abokiyar arziqi ce.

Khalil da gaba daya ya rikice jin Hajiya na neman kwanto masa ruwa ya miqe yana cewa
"Nifa Hajiya ba wani abu tsakanina da ita idan baki yarda bama ki aika a kirawota kiji idan ko sunana ta sani karma ki kawo wannan maganar" ya fice da sauri kafin ta kwanto masa wata kurar.

"Ja'iri, ai har na fara tunanin kodai baka da lafiya ne ace mutum shekara Talatin da dori amma babu wanda zece ya taba ganinka a qofar wani gidan da sunan kaje zance, to yanzu hankalina ya kwanta, bari na kirawo yan uwanka na shaida musu abin arziqi sannan na kirawo kawunka ma na fada masa dan da zafi zafi ake duka qarfe" Hajiya ta fada, nan ta shiga kiran Habiba akan ta kawo mata wayarta, Habiban na cewa

"Oh Hajiya kina jin fa abinda yace shine zaki fara yayatawa se yazo ya baki kunya daga baya"

"Ke dallah tafi can kece baki gane borin kunya yake ba, amma daman ina kallonsa dazu nasan da wata a qasa itama baki ga duk a takure take ta kasa sakewa ba? Ga yarinyar kuwa tabarakallah kyakykyawa da ita ga nutsuwa Allah yasa ta dore da haka"

Ita dai Habiba dariya ta ringayi tana kallon ikon Allah dan dagaske Hajiya take, waya ta ringa kiran yayanta kaitsaye gaya musu take Khalil ya samu mata su fara shirin biki kowacce aka fadawa kuwa nan zata hau murna a fara lissafin abinda zaayi da auran nasa.

Tana komawa gidan wanka ta fada dan saurin da take tayi daman su Fauziyya ne zasu zo wa Yaya Hajiyayyen barka, ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? gama shirin ta tsaf ta shirya cikin wasu riga da skirt na Atamfa da suka matuqar yi mata kyau. Bata daura dankwali ba se hula ta zura akanta ta fesa turare ta fito palor inda Yaya Hajiyayye da Anty Larai dake taya ta da wasu aikace aikacen suke zaune suna hira.

"Dan Allah Umaimah goya yarinyar nan bacci zatayi take ta rigima" Hajiyayyen ta fada tana miqa mata Ummu-Salma seta ja da baya tana cewa
"Tabdi haka kawai daga fitowata kice wani in goyata in bacci zatayi a kwantar da ita mana tayi kawai tun jiya nake goyata da daddare kusan kwana tayi a bayana gashi yanzu tasa mun ciwon baya".

" yanzu Umaimah wannan abar da bata fi nauyin pure water ba ce ta saka miki ciwon baya kedai kiji tsoron Allah, koda yake kamar yaune kema kin kusa ki haifi naki se naga uban da ze goya miki ba ciwon baya ba wannan ko ciwon qunquru duk ya hada ya saka miki" Anty Larai ta fada tana miqewa ta karbi yarinyar tace

"Kema neman magana yasa kika ce ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login