Showing 105001 words to 108000 words out of 429394 words

Chapter 36 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1017

tunda tana da account number ta data karba ta tura mata da 20k a matsayin gudummawar bikin Hamida wanda dakyar ta turo matan.

Ansha taron suna an raqashe kkwa ya koma gida cikin farin ciki, daga gurin suna Anty Hafsa kaitsaye gida ta wuce gurin Mama dan ita bataje gidan sunan ba wai me zataje tayi duk ga sunan Hajiyar Khalil dai taje abinta da sauran yan uwanta. A taqaice Anty Hafsa tayiwa Maman Bayanin ita fa bata yarda da zancen Umaimah ba dan idan dagaske ne da tun safe zata saka ya bude mata ta dauki duk abinda zatayi amfani dashi ai Mama tace mata ta rabu da ita kar kuma tayiwa kowa magana ai gobe zata zo gidan ta sameta.

Haka kuwa akayi washe gari da wuri sukayi suyar nama suka raba kowanne bangare suka dauki nasu, daman sun gama shirin su tsaf Anty ta kira Khalil daya fita tun safe akan zasu tafi yace besan zance ba, kashe wayar tayi ta kira Hajiyarsa dan tuni sun gama magana da ita tace ba matsala su jira kusan minti Ashirin se gashi yana cika yana batsewa haka yaje ya kaisu gida. A tsohon dakinsu da yake a gyare dan anan Nuratu ta zauna, ana gobe Umaimah zata haihu tayi arba'in ta koma gidanta dan haka qara shareshi kawai akayi aka zuba musu nasu kayan.

Se dare Mama ta sameta a daki tana zaune tana shayar da Mu'ayyad suna magana da Khalil dake ta faman zuba qorafi a waya, jiranta tayi harta gama sannan ta kalleta tace
"Ranki ya dade banga kinsaka sarqarki a hotunan suna ba, bata tayi ko kinyi kyauta da ita"

"Mama nafa gayawa Anty Hafsa tana cikin safe box din Abban Mu'ayyad kuma lokacin akwai mutane yace baze iya shigowa ba amma tana nan babu inda taje hauka nake zan bada aro? Mantawa nayi ma dazu da mun taho da ita amma zance ya kawo mun" Umaiman ta fada tana zumbura baki, Mama tayi qwafa tace

"Zaki ci ubanki keda Safe box din, Allah ya kaimu goben ki kira Khalil din kice ya kawo mun da safe kafin ya wuce aiki"

"Haba Mama kamar wani abin tashin hankali, a bari dai da daddare idan ze zo ganin mu seya kawo" ta fada tan dan murmushi, Mama tayi qwafa ba tareda tace mata komai ba ta fita.
Seda aka kwashe sati biyu tsakani Mama bata sake yi mata magana ba itama kuma da ba gaskiya ce da ita ba daman bata tada zancen ba, kullum cikin gwada layin Maman Nihal takeyi amma amsar daya ce a kashe yake a group ma tayi cigiyarta aka ce tace ta tafi America har Rufaida na mata tsiyar ita da Aminiyarta ai ita za'ayi cigiyar Maman Nihal a gurinta.

Da safe ranar Mama ta sake tirketa da zancen, Umaimah tayi fiqi fiqi da ido dan qaryarta ta qare Mama waya ta dakko tace zata kira Khalil din, cikim muryar damuwa tace
"Mama dan Allah karki kirashi, abinda yasa kika ga ina tayi miki kwana kwana wallahi sarqar Khalil din ne ya karba. Wata kwangila yakeyi kudi suka yanke masa, shine ya karba yace idan an biyashi se ya mayar mun da wata".

Kallonta kawai Mama takeyi har ta kai qarshen maganar, kwata kwata zancen be shiga kanta ba amma kuma bazata ce bata yarda ba saboda yana iya zama gaskiya Khalil din ya karba se kawai ta miqe tana cewa
"Toh Allah ya rufa asiri tuntuni me yasa baki fada ba kika tsaya kina nuqu nuqu"

"Shi yace mun baya so kowa ya sani kawai idan ya samu kudi ze siyamun wani" Umaimah ta fada tana dauke kanta gefe, Mama ta kalleta, bata yarda da zancen nan ba amma koma yayanw zata bincika taji dan lamarin Umaimah babu Allah a ciki.

Hafsa ta kira take shaidawa yanda sukayi da Umaiman,
"Zata iya yuwuwa Mama tunda kinga yayi hidima sosai da sunan nan ze mayar matan kamar yanda yace" Anty Hafsa ta fada. Mama bata haqura ba ta kira Naziyya, tana shaida mata ta bushe da dariya tace

"Kuma kin yarda Mama, Khalil din ne ze karbar mata sarqa ya siyar idan zeyi haka me yasa tun farko ya siya mata, ai seya bar kudinsa ya gama kwangilar sannan duk abinda zeyi yayi ko? Qarya takeyi ki matsata zata fadi duk inda ta kaita sedai idan kuma itan ce ta siyar wannan se muji inda takai kudin. Nidai akwai ranar da naje gidanta ta rako wata baquwa idan dai ba idona bane to sak sarqar na gani a wuyan baquwar".

"Ai kuwa dole ma ta fadamun yanda tayi da ita dan sam hankalina be dauki cewar Khalil ne ya karba ba, amma zanyi maganinta, Khalil din zan tambaya da kaina duk ma yanda akayi zanji" Mama ta fada daga nan sukayi sallama. Barinta tayi seda aka kwana uku tsakani ranar Khalil yazo da daddare, yana zaune a dakin da Umaiman take yana cin tuwo, Mu'ayyad na hannunsa yaron yayi bulbul dashi tabarakallah bazakace dan kwana Talatin da wani abu bane.

Mama tayi sallama a bakin qofa suka amsa ta daga labule ta shiga, seda suka sakw gaisawa a zuciyar Umainah tana ayyana maganar qarin kwanaki akan Arba'in din sune dan yan gidansu duka zasuyi tafiya zuwa Qaraye bikin diyar wani Abokin wasan Abbansu kwana biyu bayan Arba'in dinta, shine tace Anty ta sa baki Mama ta yarda A tambayi Khalil ta qara sati daya suje tare.

Rigigib qirjinta ya buga sanda taji Mama na tambayar Khalil zancen sarqa, ko kusa bata taba zaton Maman zatayi haka ba shi yasa data tashi ta jona qaryar dashi, Khalil ya saki baki tsabar mamaki yana kallonta Mama dake kallonsu gaba daya tayi murmushin takaici dan yanayin fuskarsa ya fahimtar da ita besan zancen ba.

"Wallahi Mama ko naira hamsin ban taba ranta a hannun Umaimah ba ballantana na karbar mata sarqa na siyar, nifa kyauta na bata bayan haka ba kudi na ne kadai a ciki ba harda naki idan ma zan karba ai se nace tayi shawara dake sannan" Khalil ya fada yana kallon Umaimah data duqe kai qasa kamar ta fasa kuka.

Mama ta kalleta tace
"Zaki fadi inda kika kaita ko kuwa har yanzu kina da sauran qaryar da zaki fada?"

"Wallahi Mama qawata ce ta ara kuma sun tafi America da Mijinta se qarshen watan nan zasu dawo nasan idan na gaya miki fada zakiyi amma akwai tata a gurina kuma tafi tawa tsada na sani" Umaimah ta fada tana janyo qaramin Kit din kayansu ta bude, Sarqar Maman Nihal ta dakko ta miqawa Mama ta karba tana cewa
"Wace qawar taki, Rumasa'u ko Halima?"

Seda ta kalli Khalil da mamakinta ya hanashi magana kafin cikin rashin gaskiya tace
"Maman Nihal, baki santa ba"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wace shegiyar barauniyar kika bawa sarqarki ta baki ajiyar wannan?" Mama ta fada cikin jimami tana daga barawon gwal din da Maman Nihal ta bawa Umaimah a matsayin zinaren gaske.

"Barauniya kuma Mama, baki ga girmansa ba yafi nawa ko? Tace nawan yana nan gidanta a Janbulo ta barwa Driversu ya kawo mun, idan ma baki yarda ba kawai ko siyar dashi ma za'a iyayi in dauki kudin nawa in tura mata sauran idan yaso ta riqe wancan dan inata nemanta a waya bana samunta har a WhatsApp kamar ma ta canza lamba ne ban sani ba" Umaimah ta fada, se Mama ta wullo mata qwandalelen kwadon sarqar ya same ta kuwa a goshi ta dafe tana cewa

"Kai Mama daya sameni a ido fa?"
"Ai gara ya sameki a idon yar banza mara hankali, banda kwakwalwar kifi ce dake wannan yayi miki kama da zinare? In banda hauka da rashin sanin ciwon kai a ina kika hadu da matar dan ni ban taba jin sunanta ma a gidan nan ba shine zaki dauki sarqar kusan miliyan biyu ki bata tunda bada guminki aka siyo ba, to zaku ci ubanku daga ke har ita ba America ba ko bangon duniya ta tafi seta fito dashi, ina kinsan gidanta tashi maza maza yanzu zamuje duk wadda za'ayi ayita a daren nan tashi muje" Mama ta fada tana miqewa se a sannan Khalil ya iya bude baki yace

"Mama ayi haquri yanzu dare yayi zuwa da safe idan Allah ya kaimu se aje tunda tace ta san gidan matar, ni daman tun asali mu'amalar su batayi mun ba saboda yanda matar sam bata da sirri komai ya seta fada"
Umaimah ta harareshi Mama tace

"Khalil gara muje tun yanzu dan jikina ma baya bani za'a samu sarqar nan amma dukda haka muje mu kama barauniyar zaune dan kwandala bazatayi ciwo ba idan babu sarqa seta bada kudinta"

"Wai dan Allah waya ce guduwa tayi matar da tafi qarfin dan wannan abin shine duk za'a ringa wani tashin hankali kuma wannan Mama idan baki yadda me kyau bane a kaiwa Bashir mana ya auna a gani" Umaimah ta fada tana zumbura baki Mama ta kai mata mari tana gocewa tace

"Wallahi sena bata miki rai idan baki rufemun baki ba sakarya da bata da tunani, idan rashin mutunci ne da tsiya kala kala babu wadda baki iya ba amma kwakwalwarki sam bata aiki balle tayi tsinkaye, yanzu zamuje idan kuma qarya kikeyi mata dan ubanki duk idan munje maji yanda akayi".

Mama ta dage akan adaren nan qarfe kusan goma za'a tafi idan Maman Nihal dakyar Anty da ta shiga itama suka hadu da Khalil suka lallabata ta bari seda safe, washe gari kuwa qarfe takwas bata cika ba Mama ta tasa Umaimah a gaba suka tafi gidan Maman Nihal Salman ya kaisu dan Mu'ayyad ma a gurin Anty suka barshi yana bacci.

A bakin babban Get din gidan salman ya faka mota, Megadin dake sanye da Uniform ya fito suka gaisa yana tambayarsa gurin wa suka zo haka Umaimah tace gurin Maman Nihal,
"Amma bakusan dokar gidan nan se Hajiya ta bada umarni daga ciki baqo yake shiga musamma ma ku da kuka dako wannan sammakon, ku kirata a waya, zata bamu unarni idan tace a barku ku shiga toh" Me gadi ya fada musu kafin ya koma can bakin qofa inda sauran yan uwansa masu gadi suke.

"Se ki kirata, gadai gida nan har gida amma matar ciki yar damfara" Mama ta fada tana hararar Get din kamar shine Maman Nihal, Umaimah ta kira layin kamar kullum dai a kashe ta kalli Mama kamar zatayi kuka tace
"A kashe take Mama, dan Allah kiyi haquri mu koma gida nasan ba guduwa tayi ba gadai gidanta kin gani idan lokacin da tace zasu dawo yayi bata dawo mun dashi ba sannan se a dauki kowanne mataki"

"Karki fita kisan yanda zakiyi su bude miki get din" Mama ta fada ba tareda ta kalleta ba, haka Umaimah ta fita daga motar kamar zata rusa kuka daidai sanda aka bude Get din mota ta fito, ta gane driver wanda Walid shine ya dakkota wancan karon da tazo ga su Nihal a baya da uniform ze kaisu makarantaya tsaya dan ya gane ta shima, Niihal ta leqo tana dagawa Umaimah hannu itama ta daga mata ta qarasa jikin motar Nihal din ta gaisheta

"Mamanku tana ciki?" Umaimah ta tambayeta ta daga mata kai, seta maida kallonta kan Driver tace
"Inata kiran wayar Mamansu bata shiga Me gadi kuma yace se na kira ta bada umarni ze barmu mu shiga". Shi yayiwa masu gadin magana suka bude musu shi kuma ya wuce kai yaran makaranta.

A palour na farko akayi iso, Mama tabi palour da kallo tana tabe baki kusan minti goma sha biyar sannan Maman Nihal ta shigo palour da sallama ciki ciki kamar wadda akayiwa dole jikinta sanye da kayan bacci alamar tashinta kenan.

Kallon Umaimah tayi da mamaki kamar yanda itama take kallo ta, cikin muryar isa tace
"Baiwar Allah lafiya, ko kinyi mantuwa ne a gidan nan?" Maman Nihal ta fada tana kallon Umaimh,
"Saqon na da Maman Nihal ta bari nazo karba" Umaimah ta bata amsa kai tsaye, seta kalleta irin kallon bangane abinda kike nufi ba Mama da gaba daya haushin matar ya cikata bama itace Maman Nihal din ba kenan ta harareta tace

"Sarqa da Maman Nihal ta ara a gurinta tace ta barta a nan ita muka zo karba"

"Ban gane me kuke magana ba akai Hajiya nice Maman Nihal ko wata daban kuke magana a kai, kedai na ganeki kece qawar Abu da kika zo kwanaki lokacin kamar kinada tsohon ciki koh" Matar ta fada tana kallon Umaimah, se Mama da Umaimah suka kalli juna jin wata sabuwa kuma,

Itace Maman Nihal, wace ce kuma Abu da take fada???

*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 30

Wayarta ta danna alamar kira bayan an daga tace
"Walid idan ka dawo ga baqi nan a palour ka kaisu gidan Abu" tana gama magana ta miqe ta kalle su tace

"Za'a raka ku gidanta yanzu"
"Ban gane za'a raka mu gidanta na ita wa kuma ke din wacece?" Mama ta fada tana miqewa tsaye itama ganin Maman Nihal din ta juya, seta kalli Mama tace
"Ita wadda kuke nema din nan ba gidanta bane, kuma ba wannan ne karo na farko da tayi qarya da sunana ko gidana ba amma wannan ne na qarshe, kuje can ku warware matsalarku ni ban san komai a kai ba" tana gama fadan haka ta juya ta barsu a palour.

Mama ta tafa hannaye tana salati Umaimah dai tagumi ta buga to idan Maman Nihal qarya take yi wanne irin kusanci ne da ita da wannan matar to da har ta bata damar shiga gidanta tayi abinda take so kamar matar gidan. Zuwan Walid ya sakasu tashi suka fita, a motar da suka zo suka dunguma gaba daya Walid na gaba yanayiwa Salman kwatance tiryen tiryen har suka isa Unguwar Hausawa ya nu????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? na musu wani gida ginin bulo ne amma babu fulasta ta wajen yace musu nan ne daga nan yayi musu sallama ze juya Mama ta dakatar dashi tace

"Ina zakaje, ai se mun shiga mun tabbatar ita dince ka kawo mu gurinta kafin ka bar nan dan bangama yarda daku ba"
"Walid yayi murmushi ya qarasa soron gidan suna biye dashi daidai sannan wata yarinya da bazata haura shekaru goma ba ta fito daga gidan, cikin fara'a ta gaida Walid ya tambayeta Mamansu tana ciki tace eh ta juya tana cewa
"Bari na gaya mata kazo" ya dakatar da ita da cewa
"Aa wuce aikenki Amina baqi na rako zasu shiga ciki" seta wuce abinta. Umaimah ya kalla yace

"Yanzu kin yarda ko kuwa" ta daga masa kai alamar Eh saboda tun ganin yarinyar kamanninta da Maman Nihal din suka tabbatar mata dan haka yayi musu sallama ya tafi.

Mama ce kan gaba suka shiga gidan, Abu na zaune gaban murhu daya turnuqr da uban hayaqi tana fifitawa saboda jiqewar da itacen yayi sakamakon ruwan saman da akayi a safiyar ga wani rafkeken madambaci akai da alama dambu takeyi se yara biyu maza da Mace daya suna wasa da ruwan da aka tara a babban baho daga gefenta. Daya daga cikinsu ya jefa dan uwansa a ciki ruwan yayi fallatsi har inda Abun take

"Wane dan abu ta kazan uban ne ya watso mun ruwa, wai ku wadanne irin shaidanun yara mara sa jin magane ma dan ubanku ba tun dazu nace ku bar wasan ruwan nan ba shegu masu kunne qashi wallahi duk wanda sanyi ya kama sedai ya mutu amma kwandalata bazan kashe gurin siyan magani ba" Abu ta fada cikin masifa yaran duk sukayi tsuru suna kallonta.
Labulen daki aka daga wani dogo baqin mutum ya leqo yana cewa

"Wai Zainab sau nawa zan miki magana akan tsinewa yaran nan ke ace baki da aiki s zaginsu dayi musu mugun baki se kace bake kika haife su ba"
"To ina ruwanka kasan me sukayi mun ne kana cikin daki saboda mutuwar zuciya ni ina nan ina fafutukar yanda zanyi na rufawa kaina asiri s an zage su ne zaka fito kace zakayi magana aikin banza zaku wuce daga nan ku bani guri ko se na tarar daku" ta qarasa atsawace tana zare musu ido. Gaba dayan su suka zabura, cikin tsautsayi daya daga ciki ta ture robar da Abu ta zuba zogale ya zube cikin jar qasar data sha ruwa a tsakar gidan.

"Na shiga uku yanzu dan ubanki kika zubarmun shegiya me kama da yayan Allah bani toh wallahi kiyi maza kije duk inda zaki ki samo mun wani idan ba haka ba yau na riqeki se na miki dukan mutuwa" Abu ta fada tana miqewa ko kafin ta qarasa yarinyar ta arta da gudu tayi waje, bata haqura ba ta bita nan idonta ya sauka kan Mama da Umaimah da sukayi mutuwar tsaye tun shigowarsu ganin wannan balahira ta Abu.

Dafe qirji tayi se kuma me ta tuna cikin iya bariki ta shiga washe baki tana cewa
"Hajiya sannunku da zuwa, kuyi haquri banji shigowarku ba"
Wani kallon banza Mama tayi mata, Umaimah kuwa

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login