Showing 189001 words to 192000 words out of 429394 words

Chapter 64 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1013

kwabeta zata fasa masa kuka taji yace
"Abba yayi mata huduba da Aisha ya gaya miki ko?"
"Be gaya mun ba, amma ba kace idan mace na haifa ba sunan Mama za'a saka mata?" Ta mayar masa da amsa tana maimaita Aisha daya fada sunan Hajiya kenan ai ba haka sukayi dashi ba

"Munyi magana Abban yace baza'ayi taron suna ba, Khalifa ze kawo raguna da duk abinda za'a buqata sannan zan saka miki kudi yanzu ina fatan babu wata matsala" ya bata amsa a dake ba tareda ya mayar da hankali kan abinda ta fada ba. Kuka ta fasa masa tanacewa

"Yanzu Khalil kayi mun adalci kenan, ka tsallake kayi tafiyarka ka barni baka damu da halin danake ciki ba, sama da wata biyu baka kirani ba ina raye ko na mutu duk ba matsalarka bace sannan na haihu na kwanta a Asibiti tsayin kwana uku baka kira kaji ya nake ba se yanzu ne kawai zaka ce kira saboda ka gaya mun ka sakawa yata sunan da bashi mukayi dakai zaka saka mata ba wannan ai rashin Adalci ne".

"Zan koma bakin aiki, idan da wata damuwar kina iya kirana tunda kin kunna wayarki" ya sake fada kafin ta bashi amsa ya katse kiran. Sororo tabi wayar da kallo wasu hawaye masu dumi suna bin kuncinta, ta daga kai ta kalli Anty Hafsa da bata san ta shigo ba se ji tayi tana cewa
"Bakiga komai ba Umaimah idan har dai bazaki nutsu ki kuma gyara bakinki ki kuma san abinda kikeyi yanzu kika fara ganin haka" ta juya ta fice abinta bayanta kwantar mata da Babyn data shigo kawo mata.

KHALIL
Tun bayan komawarsa kacokan ya mayar da hankali kan abinda yakeyi ya cirw duk wata damuwa da zata iya distracting nasa. Daman be tsammaci zata kirashi ba shi yasa ma be saka ko a kai ba, randa ta kirashi da wayar Anty yana ganin kiran jikinsa ya bashi itace dan suna magana da Yaya Aminu a bakin sa ma yaji cewar an kwace wayarta dan haka yasa jefi jefi yakan kira Mama su gaisa ya kuma tambayeta lafiyarsu, yanda bata taba cewa zata bashi Umaiman suyi magana ba shima be tambaya ba se ranardata kirashi yana kwance a Hotel room dinda yake, farkawarsa daga bacci kenan wanda cike yake da mafarkin Umaiman suna gudanar da irin soyayyar da yayi tsammanin samu idan ya aureta ya farka kenan yaji qarar wayarsa ya janyota ya duba kamar baze dauka ba kuma wata zuciyar ta saka shiya daga ba tareda yayi magama ba yana jin muryarta kawai ya kashe shi kansa besan dalilinsa nayin hakan ba amma kawai yana so ko yaya ne ya koyawa Umaimah hankali dukda dai yasan Umaimah dai Umaimah ce.

Haka yaci gaba da lallaba rayuwa, a duk sanda tunaninta da kewarta suka bijiro masa har yaji zuciyarsa na neman karaya ta sakashi ya kirata se yayi saurin tuno abinda tayiwa Hadiza da irin tozarcin da ta saka Hadizan a ciki dan har kawo yanzu hotunanta basu dena yawo ba,wasu ma se yanzu suke sake yada shi a matsayin sabon abu, qarin baqin cikinsa na rasa Hadizan da besan yana sonta har haka ba se lokacin da yayi tozali da katin daurin auranta da Musa Kallah nan da sati biyu masu zuwa.

Baqin ciki kamar yayi me, yanzu ta qishi ta zabi wannan tsohon da duk boko ta gama tsotse shi ya tabbatar babu abinda ze iya mata, bazata wani samu wata kukawa a gurinsa ba kamar ace idan shi ta aura haka ya wuni ya kwana ranar da takaici, haushin Umaimah ya sake cikashi, duk ita ta janyo masa tasa Hadizan taqi amincewa da auransa wannan tasa ya qara tsahon zaman da zeyi a SA, ya kamata ace ya dawo Nigeria yanzu amma ya zabi yaci gaba da zama acan zuwa sanda yake ganin zuciyarsa tayi sanyi ze kuma iya sauraran Umaiman.

Sanda ya samu saqon an kaita Asibiti sosai hankalinsa ya tashi, ya tuno naqudar Mu'ayyad wadda tayita akan idonsa ya tuna irin wahalar data sha se yaji zuciyarsa ta fara tsinkewa. Ya tabbatar da tana buqatarsa a kusa da ita ya riqe hannunta yana mata sannu kamar yanda sukayi wancan tare ta yanda bazataji cewar ita kadai bace yana tare da ita a kowanne yanayi. Yana nan yana kaiwa da komowa yana mata addu'ar sauka lafiya be samu nutsuwa ba seda yaji kiran cewar ta sauka ya ringa Hamdala a fili da zuciya, ransa qal dayaga kyakykyawar yarinyar data haifa masa kuma a kallo daya ya hango kamar da takeyi da Hajiyarsa babu bata lokaci ya ayyana sunanta kenan takwarar Hajiya ce.

Tun a ranar yaso magana da ita se daga bayane ma aka sanar dashi Ballewar jinin data samu lokacin har komai ya daidaita babu wata matsala dukda haka hankalinsa be kwanta na seda ya ganta a Video call tana bacci hankali kwance aka kuma hadashi da likitan da ta dubata ta tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya samu nutsuwa. Babu dadewa matar wani abokinsa Mannir ta haihu lafiya har suna shirin tafiya gida jini ya balle mata kafin kace me Ajali ya risketa shiyasa ya godewa Allah da basu gaya masan bama har seda komai ya daidaita dan qila da fargaba ce zata kashe shi kafin ita.

Kullum seya kira yaji jikin nata, yanda bece su bata wayar ba haka babu wanda yace masa gata se yau da safe bayan an sallamo su daya kira shine Nuratu tace zata kai mata wayarta seya kira tacan.
Sam beyi mamakin maganganunta ba indai Umaiman daya sani ce zata aikata sama da haka ma amma a halin da suke ciki beyi tsammanin har zata iya ce masa wani abu ba dan ya saka wa yarsa sunan da bashi yayi mata akqawari ba kuma fa sunan uwarsa ya saka ba wata ba ballantana tace kai Umaimah dai bazata canza hali ba.
Da har yayi niyyar komawa amma wannan abun da tayi masa yasa ya fasa, ze ci gaba da zama har se randa tayi hankali tasan abinda takeyi idan ta nemi su shirya sannan zasu shirya.

A bangaren Umaimah kuwa sabon fushi ta dauka da baqin rai, sam tunani ta be kawo mata cewar bata yi daidai ba, a yanzu ma gani takeyi ai ita yayiwa laifi, ya tsallaketa ya tafi uwa duniya sannan yanzu ya sake zuwa ya saka wa yarta sunan uwarsa bayan tata uwar yayiwa alqawarin takwara ai kuwa bazata sabu ba, badai Abba yace yayi mata huduba ba? To dakanta zata gayawa Abban yanda sukayi ai dai shima se yafi so a saka sunan matarsa akan wata. Kukan da Babyn ta fara ya saka ta dauketa ta shiga shayar da ita. Fuskar Khalil take gani sak dan kamar ma tafi Mu'ayyad kama dashi, ta sake qanqame yarinyar wata irin qaunarta da kewar Mahaifinta na shigar ta kome ta tuna kuma ta zumburi baki tareda kwantar da ita a gefe dukda da alama bata qoshi ba dan tana cire ta ta fara kuka a fili tace
"Bazaki sha din ba ubanki yazo ya baki nasa" ta dungure mata kai kamar wata meyi da sa'arta yarinta kuwa ta canyara kuka.

Anty Laure data debo garwashi ta shigo da sauri dan a zatonta ita kadai ce seta tarar da Umaiman na dannan waya
"Wallahi idan baki aje wayar nan kin dauketa ba se kin ci ubanki Umaimah" ta fada tana aje garwashin hannunta. Umaimah ta zumburi bakinta da be gama sacewa ba kafin ta harari yarinyar tace
"Nafa bata shegen cine da ita kamar gara, kumani zafi yake mun sedai a hada mata madara".

Banza Anty laure tayi mata ta shiga tattare kayan wanki kafin ta watsa mata harara ganin har sannan bata dauke ta ba tace
"Ki bari na dawo wallahi sena zaune ki a gurin nan shashasha kawai" ta fice abinta. Umaimah tabita da kallo kafin ta dauki yar tana ayyana yanda tsaf zata zaunetan kuwa da wadannan qattan mazaunan nata. Anty Laure irin masu qaton Duwawun nan ce har idan tana tafiya seka tsaya ka kalleta saboda girman su kuma da alama sam basa damunta ita dan abinda siriri zeyi tsaf zakaga tayi itama.

Nonon ta cigaba da bata tana dannan wayarta. Layin Rufaida ta kira wayar tayita qara harta katse bata dauka ba ta sake kira nan ma dai seta haqura qila tana wani abun idan ta gani daga baya ta kirata. Tunda suka rabu a CID basu sake haduwa ba daman ba waya balle ta kirata se yanzun, daga nan Data ta kunna ta shiga whatsapp, messages suka ringa shigowa amma duk sunqi budewa saboda dadewar da tayi bata hau ba. Status ta wuce ta dora cewar ta Haihu, ta samu baby girl kafin ta aje wayar lokacin babyn tayi bacci ta kwantar da ita a gefe itama ta kwanta tana jiran kiran Rufaida har bacci ya kwasheta bata kira ba.

Surutan Mu'ayyad suka farkar da ita yana tsaye akanta tana bude ido ya daneta cikin murna yana mata gwaranci. Rungumeshi tayi itama cikin farin ciki, rabon data ganshi tun kafin case dinsu da Hadiza se yau din. Ta daga shi ta dora akan gado tana tambayarsa shidawa sukazo, ya gane me tace amma babu bakin mayarwa dan haka kawai yace mata "Papa, Bibi". Bata gane abinda yake nufi ba tayi dariya kawai ta miqe ta shiga bandaki, fitsari tayi ta canza pad kafin ta fito bata tarar dashi a dakin ba dan haka ta saka safa a qafarta ta zura Hijabi ta fita jin muryar Khalifa a tsakar gidan da Alama tare suka zo.

Gaisawa sukayi tana cewa
"Aa badai tafiya ba ka shiga ciki mana"
"Ai daga cikin nake mun dade da zuwa akace bacci kikeyi zanje seda yamma zan dawo na tafi dasu daman saqo na kawo shine Hajiya tace a taho da Mu'ayyad yaga Baby suna ciki shida Habiba" daga nan yayi mata sallama ya tafi. Parlour Maman ta shiga inda take jiyo Hayaniya, gurin cike da yan barka, ta samu guri kusada Habiba ta zauna ta gaidasu kafin Habiban dake riqe da baby ta shiga gaisheta fuska washe da fara'a.

"Mama, Bibi" Mu'ayyad ya sake fada yana leqa Babyn, se sannan ta gane wato Babyn ce Bibi tayi murmushi kawai ba tareda tace komai ba, Habiba ta katseta da cewa
"Anty me za'a ringa ce mata, Yaya yace sunan Hajiya taci"
"Ku zabar mata duk sunan da kukaga ya dace nidai Aisha zance" ta fada tana dan murmushi, Habiba ta kalleta ta kalli yarinyar fuskarta ta nuna alamun rashin jin dadin abinda ta fada din amma seta qirqiri murmushi tace
"Itama Hajiyan haka tace kar a boye amma Yaya yace Aa baza'a fada ba"
Umaimah kuwa qin yarda tayi ta kalli Mama wadda ta tabbatar da taji abinda ta fada dan tunda ta shigo ta saka mata ido, daga qarshe ma tashi tayi tana cewa Habiban tazo suje can dakin.

Haka suka qarasa wuni yan barka nata shigowa Umaimah nata faman duba waya ko zata ga kiran Rufaida amma shiru, kuma taga ta bude status dinta amma batace mata komai ba. Se yamma lis su Habiba suka tafi dakyar da kuka shabe shabe aka dauki Mu'ayyad daya dage se su tafi da Bibi, Umaimah daya fito daga wankan yamma tana shiryawa Mama wayarta dake kan mudubi tayi qara ta dakkota ta duba, Naziyya ce ta kirata akan zancen dinkin suna dukda ba taro za'ayi ba dai ya kamata tayi kwalliya a cewarta. Ta tabe baki tana cewa
"Ni babu abinda na siya ma wallahi, idan kinada latest kaya ki turamun na zaba toh"
"Bani da kaya amma bari na baki lambar *Ummu-Maheer Collection* kiyi mata magana, duk abinda kike so daga kan Atamfa, Laces, Voile, Mayafai, takalma da Bags duk tana siyarwa kuma latest and unique design da se ki gama yayinsu ko a hoto baki ga me irunsu ba akan farashi me sauqi daidai da al???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?jihun kowa" Naziyyan ta fada se Umaimah tace

"Toh ki turo yanzu amma kinga lokaci ya qure saura kwana uku, wai har zan samu dinki ma kuwa?"
Dariya Naziyya tayi tace
"Bakida matsala da wannan dan tana da kwararrun Tailoli da zasuyi miki dinki daidai da zamani idan kin siya kaya sedai kawai ki aika da measurement ko kije da kanki a gwadaki"
"Turamun da number tata yanzu kuwa nayi mata magana tunda ga sauqi daga Allah" Umaimah ta fada kafin suka kashe wayar sega number Naziyyan ta tura mata
(Zaku iya tuntubar mu kai tsaye akan 08142548705
Ko kuma ku dannan wannan link din ku shiga group dinmu kai tsaye domin samun sababbin kayayyaki akan farashi me sauqi
https://chat.whatsapp.com/FKsWield4wPKepHDZwtPUP)


Bata bata lokaci ba ta dannan mata kira, suka gaisa ta gaya mata ita qnawar Naziyya ce nan suka sake gaisawa cikin fara'a dan Naziyya customer tace sosai. Magana sukayi akan tana son kaya Ummu-Maheer din tace tayi mata magana ta WhatsApp nan ta tura mata da Latest Laces da take dasu ga hadaddun Atamfofi na yan gayu Umaimah saboda yanda ta rude kasa zaba tayi gani takeyi idan aka ce ta kwashi gaba daya ma tana so. Dariya dariya Ummu-maheer ta ringayi mata qarshe ita ta tayata zabe bayan ta nemi ta tura mata da hotonta dan ta ga kalar da zata dace da fatarta ta kuwa yi mata zabe me kyau, Laces ta diba yan ubansu guda uku se Atamfa biyu ba Brocade shima biyu tace ahada mata da mayafin kowanne sukayi total take ta saka mata kudinta suka rabu akan da safe zata shiga gidan Maman Nana ta aunata seta aika da measurement a dinka mata wanda zatayi amfanin suna dasu.

Se gurin qarfe goma Abba ya dawo gida kuma har sannan tana zaune batayi bacci ba saboda tana son magana dashi duk haushin ragunan da Khalifa ya kawo dazu an daure su ta bayan dakin da take se kuka suke sun cika mata kunne. Kamar mara gaskiya ta zumbula Hijabi ta fita daga dakin, Mama data hado kayan abincinsa zata kai masa sukaci karo a hanyaz gabanta ya fadi dan bataji motsin tafiya ba se ganin Umaiman tayi da uban baqin Hijabi ko a ina ta samo shi oho taja tsaki bayan dataga fuskarta tace
"Ke kuma ina zakije a daren nan haka?"

Umaimah da sam ganin Maman be mata dadi ba taji kamar ta juya amma ta dake tace
"Gurin Abba zanje ina so muyi magana dashi"
"Wace magana ce da bazaki iya bare seda safe kuyita ba zaki fito yanzu da danyan jego ga gari da sanyi" Maman ta sake fada tana harararta, Ummaimah tayi qasa da kai, Abba daya jiyo su yace ta shigo mana, yana kallon Mama yace
"Ya zaki hanata shigowa kika san abinda take so ta gaya mun"

Mama ta wuce inda yake cin abinci ta dire kwanuka tana kallon Umaimah data nade a qasa kamar ta Allah tana gaida Abban, tun dazu taso su kebe tayi mata fadan abinda tayi a gaban Habiba amma baqin da suketa zuwa suka hana gara ma da suka hadu yanzu a nan din ta samu ta kwabeta.

"Kinyi shiru Yar Umai ya akayi, ina kika bari Indon taki" Abban ya fada cikin tsokana ganin tayi shiru se sunkuyar da kai takeyi, Umaimah ta dago ta sace kallon Inda Mama take tsaye itama itan take kallo tayi saurin mayar da kai qasa, Abba yayi murmushi ya kalli Mama yace
"Dan bamu guri Malikah, kinsan fa ki din nan idan kika bata rai kamar Boss kike koni wani sa'ilin tsoron magana nake a gabanki" ya fada cikin sigar zolaya Mama ta murmusa itama tace
"Kunsan zaku fadi ba daidai ba shi yasa kuke shakkar fada a gabana dan an san bazanyi shiru ba nima, kiyi maza dai ki tashi ki koma kinbar jaririya ita kadai" tana gama fada ta fice daga dakin dan daman bata kawo masa butar shayinsa ba tasan kuma seya nema.

"Uhm ina jinki ya akayi" ya sake fada yana kalllonta. Umaimah ta shiga wasa da yatsun hannunta tana cewa
"Daman Abba dazu munyi magana da Khalil ne yace ya fada maka sunan da zakayi wa Babyn huduba ko?"
"Eh ai tun washe garin da kika haihu ma nayi mata ashe Mamanku bata fada miki ba"

"Bata fadamun ba Abba, kuma shima ba haka mukayi dashi ba tun kafin na haihu yace sunan Mama za'a saka idan macece ae kawai yau yace wai Hajiyarsa ya saka" Umaiman tayi saurin katse Abba se ya tsaya yana kallonta cikin rashin fahimta yace
"To yanzu yaya akayi dai a taqaice bangane inda maganarki ta dosa ba?"

"Ni Abba gaskiya sunan za'a chanza tunda dai shi yayi alqawari in yana son saka sunan Hajiyarsa ba seya bari idan na kuma haihuwa ba amma sabida rashin Adalci Mu'ayyad ya saka Babansa sannan yanzu ma yace Hajiya ze saka se kace ni banida Iyaye haba gaskiya ka kirashi kawai ka ce masa ka canza sunan Mama aka saka mata" Umaimahta fada cikin iyakar gaskiyarta.

Tsabar mamaki Abba baki kawai ya bude yana kallonta, kai shifa wautar Umaimah ta fara bashi tsoro ace yarinya ita abinda ranta ya raya mata kadai shine daidai babu ruwanta kuma ko a gaban waye zata fadi ra'ayinta ko yayi maka daidai ko kar yayi ita dai in ya mata shikenan.
"Dan Allah Abba ka kirashi kaji, kaga ni haushina yakeji har yanzu akan budurwarsa, tunfa lokacin se yau mukayi magana a waya nasan kona masa maganar ma baze kula ba amma idan kaine ka bashi umarni bazece komai ba ze yarda" Umaimah ta shiga magiya jin Abban bece komai ba seyaja numfashi ya ajiye kafin ya soma magana cikin lallami dan ya fuskanci fada baze tafi da Umaimah ba, nasihar dai ita ta dace da ita dan da alama kwakwalwarta tunanin yara takeyi.

"Naji be kyauta ba gaskiya daya karya miki alqawari amma kinga shi suna duk wanda kika ga an sakawa mutum toh Allah ne ya zaba masa, yanzu ya rigada ya saka sunan mahaifiyarsa har an fadawa kowa kinga baze yuwu ace an chanza da wani ba, daman dai ace sunan wata daban ne can ya saka to idanan mayar dana mahaifiyarki babu wani abu amma yanzu Umaimah ai baxe yuwu ba. Kamar fa kece ace ya fara saka na Maman naki se kuma ya canza ya mayar dana Hajiyarsa zaki yarda?"

"Tab baze yuwu bama wallahi" tayi saurin katse

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login