Showing 318001 words to 321000 words out of 429394 words

Chapter 107 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1009

ko to inaga shi Mama takeyi" Safina ta fada cike da shaqiyanci se Umaimah tace
"Kema kya fada, ni gudun kar abun ya bata mun rai ma daki na shige na barsu"
"Ke kuma ya haka gaskiya baki kyauta ba Maman zaki tashi ki bari a zaune tana miki magana matsala ta dake Qawata kanki akwai ruwa wani lokaci ai duk iskanci a dagawa Mama qafa dai" Safina ta fada se Umaimah ta yanutsa fuska tace
"Ai tashin nawa yafi zaman Alkhairi saboda kalar zancen data zo dashi badan ita bace bama da sena zagi uwar wanda ya fada wlh kafin in gurje masa baki"
"Toh Allah yayi mana tsari da mugun ji da mugun gani, yanzu dai ki turamun da ragowar kudadena dana ranta akayi miki aiki tunda dai aiki yaci ina da buqatar kudi gobe ma Qaraye zanje Sailuba ta hadani da wani sabon Teacher kinsan fa shi aikin Suleiman idan ba rubdugu akayi masa ba baci yake ba dan Uwarsa a tsaye take akansa imata in gaya miki sau da yawa ma da nata aikin nake basaja na cusa nawa idan ta kawo Masa Rubutu dasu hayaqi sena canza na ajiye masa nawa yayi tayi to yanzu ta dena bashi sedai kullum yaje gidanta yayi koma menene shiyasa nake so ayi mun kwaf daya kawai, farraqu nake so ayi masa da uwar ta yanda ko inda take baze ringa zuwa ba balle ta ringa lalata mun aiki"

"Toh Allah ya tsare ni kam bazan iya aikin shuka dusa ba" Umaimah ta fada mata cikin izgili se Safina tace
"Na nawa kuma ai kin shuka sedai kiyita aikin ban ruwa kuma qaryar banza da wofi kawai" Safina ta fada a hasale Umaimah na shirin bata amsa Khalil ya turo qofar da sallama qasa qasa kamar wanda akayi qara a Kotun qoli ganinsa yasa Umaimah ta fasa fadar abinda tayi niyya tace mata
"Zan kiraki anjima" daga nan ta kashe wayar tana kallon Khalil daya qwamo wani baqin Glass cikin dare kamar sabon Makaho ya kuna kasa daga kai ya kalli inda take.

"Khalil ciwon ido kakeyi?" Ta fada tana miqewa tsaye seya daga mata kai still be kalleta ba yace
"I think Apolo ne ya kamani daman Anwar yana yi may be gurinsa na dauka"
"Kai Allah ya sauwaqe gara ma daka saka Glass kar mu dauka muma musammani da idona yake kwalamamme kar na tashi dashi gobe" ta fada tana ja baya kamar wanda yace mata ya gamu da cutar kuturta shidai Sama ya nufa yana riqe da numfashinsa dan ba qaramar qundumbala yayi kafin ya shigo gidan ba. Babban abinda ya bashi qarfin guiwar dawowa tabbacin da Jamila ta bashi akan Lafiya lau gidan yake babu abinda ya faru har suka tafi kai Lefe, kuma ta tabbatar masa da cewar Mama tazo, to meya faru dayaga Umaiman cikin nutsuwa tamkar babu abinda yake wakana wane irin abu Mama tayi amfani dashi da har tayi nasarar shawo kanta haka ta karbi Al'amarin da Salama? Koma dai menene baze tona ba, tunda Allah ya dube shi ya amsa addu'arsa ya tausasa Zuciyar Umaiman shikam ba abinda zeyi sedai ya qara Godewa Allah.

Seda yayi wanka ya gasa jikinsa dan wunin ranar bega ruwa ba tunda ya fita daga gidansu Umaimah office ya wuce babu kowa yau se Masu gadi saboda ba ranar aiki bace ya bude office dinsa kawai ya shiga yana jiran tsammanin jin gidansa ya kama da wuta amma har yamma beji wani labari ba, tunanin ko dai kowa na gidan ya mutu ne yasakashi kiran Jamila ta tabbatar masa da yanzu suka baro gidan Mama Hauwa sun kai Lefe ita ta wuce gida ta tabbatar masa da lafiya lau suka fito kuma gama wayarsu kenan da Hajiya ma da wani abu ya faru bayan fitar su zata gaya musu.

Yunwar da yake ji ta sakashi sake sauka qasan dole, har ya kusa kaiwa qasa ya koma ya dakko Glass dinsa ya saka tubda ya laqawa kansa qaryar ciwon Ido ya ya iya?
Umaimah na zaune tana kallo ya samu kujera daga can gefe ya zauna cikin dar dar kar yaje gadar zare ta shirya masa, Ruqayya ya kwalawa kiraz ta fito ta durqusa daga nesa cikin ladabi ya tambayeta abinci ta wuce Kitchen, a kan Center table ta ajiye masa dan yace baze iya hawa Dining ba. Ua zuba abincin ya fara ci kenan Umaimah ta kalleshi tace
"Dazu Mama tazo ita da Anty Laure"
Shinkafar da yake taunawa ta sarqesgi ya shiga tari babu ji babu gani Umaimah ta matsa ta zuba masa ruwa ya karba yasha kadan ya ajiye idonsa sukayi ja sosai yana maida numfashi, seda taga ya dena tarin kafin taci gaba da maganarta dan ita bata ma lura wai abinda ta fada ne ya kwarar dashi ba.

"To dai tazo tana ta wasu maganganu kayi aure wanene wanene nace ni meye nawa a ciki kaina matar zata zauna ko ni zan ringa ciyar maka da ita ai kanka ka qarowa wahala ko ba haka ba?" Ta qarasa tana kallonsa. Yanda kasan gunko haka Khalil ya zama a gurin, Umaimah taci gaba da cewa
"Ni dana gaji daji ma na shige daki nayi bacci gaba daya bansan me aka daukeni ba wai zata akeyi tsoron kishiya nakeji ne ko Yaya ni yanzu ba mace daya ba ko uku zaka cike an gaya maka hankalina ze tashine nasan duk tsiya badai ka auro wadda ta fini ba kuma koma wacece zatazo a bayana take dan haka Allah ya kawota lafiya ta shigo gata ga gidan ai".

Da yana shaye shaye tabbas ze gasgata abinda ta fada amma ko a magagin mutuwa yake yasan wannan maganar ba gaskiya bace sedai idan ita Umaiman ce ta fara shaye shaye ba kuma ya raba daya biyu akwai wani abun data taka shiyasa tayi wannan ladab din.

"Toh yaushe Amaryar taka zata tare kuma?" Ta sake jefa masa wata maganar seya fara in ina dukda besan ma sanda ya budr baki yayi magana ba yace
"Uhm eh kin gane Umaimah nasan dai Mama tayi miki duk wani bayani ni yanzu bani da bakin da zan kare kaina Allah kuma shine shaidata baniyi komai da niyyar na musguna miki ba, al'amari ne yazo daga Allah babu kuma wanda ya isa ya hana faruwar hakan"

Tsam tayi tana kallonsa har ya kai qarshe seta dauke kanta gefe tana cewa
"Idan ka gama cin abincin Inada Panadol Night zan dakko maka kasha kayi bacci" daga haka ta maida kai kan Tv abinta ba tareda ta bawa maganganunsa muhimmanci ba. Babu shakka shima kan babu dadi ko kuma wani wasan kwaikwayo Mama ta shirya musu to can su gane, kai wannan abun ma babu qanshin gaskiya a ciki, babu yanda za'ayi Khalil yayi aure kamar yanda ake iqirari sannan ya iya zama a gabanta haka ai ba mahaukaci bane shi tsaf yasan abinda zata aikata masa.

Duk yanda yaso yayi mata magana ta hade girar sama da qasa taqi bashi dama haka ya tashi ya koma sama abincin da beci ba kenan dan tunda ya kware ya haqura dashi daman, kwana yayi yana juyi da Jimami, ranar litinin za'a zo yiwa Humaira Jere kamar yanda Baba Abu ya yanke cewar ranar Laraba zata tare, da yamman nan se kashe wayarsa yayi saboda Rigimar data dira masa akan ita ba haka sukayi dashi ba se ya kira Iyayenta yace musu a qara masa lokaci danita ba zasu saurareta ba shiko a sannan yana jiran jin yanda ta qare da Gimbiyarsa bema tsaya wani sauraronta ba yace zasuyi waya daga haka ya kashe wayarsa gashi yanzu Alamu sun Nuna kwakwalwar Umaimah ta qi karbar saqon da ake aika mata, shi kuwa bega abinda ze saka Humaira ta tare a gidansa Alhalin besan makomarsa a hannun Umaimah ba.

Washe gari da safe bayan ya dawo daga Sallar Asuba ya taddota a daki ta idar da Sallah itama tana zaune a qasa, suka gaisa ta kalleshi fuska dauke da Murmushi tace
"Ango Ango"
Gabansa ya yanke ya fadi seya juya ya fasa zaman da yayi niyya Umaimah ta fashe da dariya ganin ya fita kafin ta miqe ta koma kan Gado ta kwanta abinta kafin gari ya qara wayewa tasan abinda zata saka Ruqayya ta shiryawa su Maman Asad da sukace zasu zo yau.

Khalil kuwa bangaren Hajiya ya tafi a daki ya sameta tana sallah dan ta makara tashi yau seda ta idar ta shafa addu'a kafin ya gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin yanda duk yayi zuru zuru tace
"Jiya na manta ince maka Hajiya Malika ta zo, wlh banji dadin ganinta ba gaba daya kunya ta dabaibayeni amma naji dadi data fahimci abun kuma Alhamdulillahi gashi ta fahimtar da Umaiman ta karbi qaddara kaga fa yarinyar nan Lubna ashe saboda son tada zaune tsaye da zasu tafi kai kaya har qofa ta kwankwasa mata wai tazo ta gani cikin ikon Allah ta tura mata aniyarta bata kula su ba kaga kuwa ai addu'a tayi tasiri sedai aci gaba da roqon Allah ya sake kore shaidan daga zuciyarta danshi yake ingizata take yin komai amma ba halinta bane".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Hajiya ni na kasa fahimtar ta ne gaba daya ma, yanda take magana kamar bata yarda da abinda aka fada bane Kwata kwata fa Hajiya babu alamar damuwa ko wani abu a tattare da ita yanzu fa har tsokanata tayi wai Ango ni wlh Hajiya tsoron ta nake ji saboda Umaimah bata shiru komai qanqantar abu idan akayi mata se tayi magana idan kuwa kikaga tayi shirun to abinda zata aikata se an gwammaci sau dubu ta fitar da abinda yake cikinta wai fa cewa takeyi ina ruwanta idan ma mata uku zan aura ai ba akanta zasu zauna ba Sannan ace lafiya kuwa Hajiya"

"To in banda abunka Babana Mahaifiyarta ce fa tazo da kanta gidan nan kuma dai ka sani a duniya ita kadai take sakata kota hanata abu tayi babu musu yanzun kasan irin abinda ta gaya mata da jan kunnen da tayi mata ka ringa kyautata mata zato mana kuma ma ai wani lokacin idan zuciyar mutum ta qeqashe haqura ma yakeyi da komai. Saboda Allah me kake so tayi kuma aure ne ka rigada kayi to kuma ta wahalar da kanta a wane dalili ai gara ta sallama ta miqa lamarinta ga Allah kawai. Nidai ina da kyakykyawan yaqinin har ranta kamar yanda ta fada babu komai babu din, ka rabu da ita karka ce zaka takurata dole akan seta fitar da fushinta idan ka tunzurota bamu san iya inda rigimar zata tsaya ba dan haka ka barta tunda Allah ya tsayar mana da kansa".

Shidai ko kusa be gamsu da zancen Hajiyar ba amma babu yanda ya iya baze zauna suyi ta ja inja da ita ba amma lashakka yasan babu wata magana da za'a ce wai Umaimah tayi tawakkali farat daya akan maganar auran nan abu biyu ne kuma ciki dole daya ya tabbata, kodai dagaske ta toshe tunaninta taqi fahimtar abinda ake gaya mata saboda tana ganin hakan baze taba yuwuba ko kuma tanada wani tanadi na daban akan al'amarin a cikin biyu babu wanda yake so ya zama gaskiya saboda dukka sakamakonsu baze kasance me kyau ba. Yinin ranar shima beyi shi a gidan ba, kafin ya fita seda ya faki idonta, tana Kitchen tareda Ruqayya ya Ya dakko spare keys din gidan da suke a dakinta ya ciri wadanda yake da buqata. Seda ya bude Part din daya ginawa kansa amma jarabarta tasa ya haqura da amfani dashi gashi yanzu tayiwa kanta baki kuma ya kamata.

Sammani ya kira da wani Yaro Ahmad dake gadin maqotansu, cikin taka tsantsan ya shigar dasu, seda suka share gurin tas suka goge dukda ba qurace kawai babu wani datti a gurin ya duba komai lafiyarsa qalau sannan ya sallame su ya koma dakinsa yayi wanka ya shirya ya fita, gidan Unaizatu ya fara zuwa ya kai musu Key kamar yanda suka buqata, Be samu Humaira ba daman sunyi waya ta sanar masa zataje can gidan Mama da akwai qannen Mahaifiyarta guda biyu da suka zo daga Gashaka jiyan Mama tace taje saboda sunce akwai abubuwan da suka zo mata dasu gashi babu isashshan lokaci dan haka kome zasuyi ya kamata ayi da wuri.

UMAIMAH
Lafiya lau taci gaba da sabgoginta, guraren sha daya suka gama shiryawa su Maman Asad kayan maqulashe wanda Ruqayya tayi ita kuma tana bata Umarni, ta fito daga wanka tana shiryawa suka iso Maman Asad, Nuratu se Anty Hafsa kowacce ta samu kujera ta zauna jugunjugun kamar gidan Mutuwa dan tun jiya da labarin ya riske su kowacce ta rasa kuzari. Hajiya Umaimah ta sako Bubunta ta fesa turare ta fito tana daga qafa dakyar, fuska a washe ta tari yan uwan nata kowacce ta amsa mata da murmushin yaqe, ita dai Ruqayya nata aikin kawo abinci a ranta tana mamakin wannan ziyara da yan gidan nasu Umaimah suke kawowa daga jiya zuwa yau kuma kowanne yazo jiki babu kuzari ta gama ajiye musu abinda zata aje ta wuce dakinta a ranta tana fatan koma menene Allah yasa ya zama Alkhairi.

Ruwa kadai suka iya sha shima bisa tursasawar Umaimah, Anty Hafsa ta dake ta sake nanata abinda Mama tazo dashi jiya ta akai Aya Maman Asad ta dora da nata lallashin tana sake nusar da Umaiman muhimmancin haquri da yarda da qaddara a duk yanda tazo maka. Seda tayi Shiru Umaimah ta kalli Nuratu da bata ce komai ba tace
"Ke kin rafka tagumi baki da abin cewa ne halan?"
"To me zance Umaimah ai sun rigada sun gama magana nidai fatana kiji ki kumayi amfani da abinda suka fada na tabbata zaki ga ribar hakan a gaba" Nuratu ta qara da nata se Umaimah ta gyara zama tana kallonsu su ukun tace
"Toh duk naji ku amma ina so ku sani cewar badan ina ganin mutunchin ku ba da wlh se na muku rashin mutunchi a cikin gidan nan. Ai na gayawa Maman tun jiya kawai dan ita ce shi yasa har nayi shiru bance mata komai ba amma yanzu ku da kuka kwaso qafafu kun yarda da abinda ta gaya muku ku gaku zakuyi mun nasiha ko to iya abinda zance muku Allah yasa kuga irin wannan kishiyar a gidajenku, Ke daman Maman Asad taki tana tafe banga laifinki ba tunda kin karbi rabonki kowa ma ya samu ba damuwar ki bace ke kuma Anty Hafsa me mata uku zaki aura in sha Allahu sannan ke Hajiya Likita kina Asibiti kin tafi Duty zaki dawo gida ki tarar da kishiya keda Naziyya dukda bata nan nasan bakinku daya kuma shawararku daya dan haka tun ina ganin sauran mutunchinku ku tashi kowa ta kama qafarta tayi gidanta kuje can kuci gaba da jaye jayen masifarku kuma ta qare muku akanku".

Yan uwan Humaira basu samu zuwa yin jere ba ranar litinin kamar yanda suka tsara saboda qaryar da Khalil yayi musu akan ana sake fentin gurin dan haka suka bari se ranar Laraba ranar da Amarya zata tare suyi gaba daya saboda talata Mama zatayi wunin biki. A bangaren Khalil kuwa babu wani fenti da ze sake ya dakatar dasu ne kawai saboda har sannan be samu gamsuwar da yake da buqata daga Umaimah ba ta tabbacin ta karbi auran, hankalinsa be qara tashi ba seda sukayi waya da Nuratu ta gaya masa abinda Umaiman tayi musu daya samu Hajiya da Maganar Jalilah Amara na zaune nan take ta fitittike ta hana hajiya cewa komai, fadi takeyi duk Umaiman ta gama haukan qarya da nuna bata san abinda akeyi ba aure dai an daura Amarya kuma zata tare babu kuma abinda ta isa tayi dan suma ba zuba mata ido zasu hakanan tayi yanda take so ba. Ita ya zame ta sake kiran Baba Abu ta gaya masa Khalil ya hana azo ayiwa Amarya jere ya kuwa kirashi yayi masa tatas yana sake jaddada masa muddin be bari an kawo Amarya ta lallami ba to kuwa za'a kawota ta tsiya dan haka washe gari Talata tun safe yacewa Umaimah ta shirya zasuje Asibiti, ya gama tsara ze kaita kawai su kwantar da ita. Idan ma da akwai Allurar da za'ayi mata a qalla tayi sati tana hutawa bayan anyi Mata CS din ayi kawai shidai su rufa masa Asiri ta rabu da cikin jikinta kafin duk wani tashin hankali ya biyo baya.

Qarfe tara suka bar gidan, suna fita motar masu kayan gado da Kujera ta kunno kai dan danan yasan da suna tafe, shirita Umaiman ta tsayayi har suka kai wannan lokacin basu fita daga gidab ba. Suna hanya Jalila ta kirashi akan ya tura mata da kudin kwalliyar Amarya dan gaba daya ita ta karbe bikin daidai da kayan da Amaryar zata saka yau din na yinin ita ta zabar mata ta kai dinki haka gurin da zasuyi Yinin da kudinta ta kama dan da A gida Mama tace zatayi dukda Khalil ya sallami Amaryarsa ya bata kudi kamar yanda akeyiwa kowa amma ya gaya mata baze samu damar halartar duk wani abu da zatayi ba dan haka Maman tace suyi a gida kawai a huta amma Jalila ta kafe akanba haka ba,shi kanshi Khalil seda suka haura kafi ta sarara masa danda cewa tayi se yaje koda yake ko yaje ko kar yaje duk abu daya ne hakan kuma baze chanza duk tsarinsu ba.

Bayan sun isa Asibitin, duk su biyu Dr Al'amin ya ringa surfawa bala'i damanita Umaimah ya cire ta a layi saboda a cewarsa ya dade bega mutumin ba besanciwon kansa ba kamarta to Khalil dinma yabi sahunta, ciwon qafar da yaje yana yi ma daga cewa ya dawo washe gari ayi X-ray se yau ya sake ganinsa haka yayi tayi musu fada kafin ya bashi form ya cike ya biya duk wasu kudi da ake buqata suka bata daki bayan akan washe gari qarfe goma na Safe za'ayi mata aikin. A office ya tarar da Dr bayan ya raka Umaimah dakinda aka bata wanda a VIP section ma ya biya mata saboda ta fi samun nutsuwa da kulawa sosai.

Dr Al'amin ya kalli Khalil bayan ya gama sauraron duk abinda yake fada na ya girgiza kai kawai yace
"Kasan me,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login