Showing 294001 words to 297000 words out of 429394 words

Chapter 99 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

958

ta qofar godanta kike wucewa sedai Yayanta su ganki suce mata kin wuce se kace ba Yarki uwa daya uba daya ba anya Umaimah akwai hankali a lamuranki?"

"Toh sannu uwata Malika, yanzu a taqaice kiyi saving duk wadannan surutan ki fadi abinda ya kawoki kawai. Da zakice bana neman ku ku me yasa da ban kiraku ba ko banje inda kuke ba ku nemeni ko dole se nice zan nemeku? Kuma su duk basu da bakin qorafi se ke uwar iya zaki kwaso qafafu na zata ma wani abun arziqin ne ya kawoki ashe can kin gama hado Bomb dinki shine zaki wani taho kega yar uwata kinzo kiyi mun fada to sannu kinyi abin kirki, amma in gaskiya za'a bi ai Babba shi ya kamata ya ringa duba qarami yaga ya yake kuma da zakice bana zuwa gida wannan kuma sedai a qi Allah ayiwa mutum sharri tunda daman ba sonsa akeyi ba naga har cewa suke na ishe su na rage zuwa kuma naja baya an zagaye ana wasu maganganu wlh ku canza Halo kowa da abinda ya dameshi amma se Umaimah zaku saka a baki kuyita caccaka" Umaiman ta hayayyaqowa Nuratu kamar zata daketa.

Kallonta kawai ta ringayi hartayi shiru saboda tsabar yanda ranta ya sosu bata iya cewa Umaiman komai ba ta miqe ta dauki jakarta ta juya zata fita, se kuma Umaimah tayi saurin binta tana cewa
"Toh kuma muna magana kin wani suri jaka ina zakije? Ba fada kika zo ki mun ba se ki zauna kiyi ai in ma kina buqatar bulala in dakko miki ai kin Isa" ta qarasa tana kamo hannun Nuratun seta fizge a fusace ta juya ta kalleta tace
"Baki gama ci mana mutunchin bane ko ya akayi? Koda yake ba laifinki bane, laifina ne nida na tako nazo inda kike amma kiyi haquri bazan sake ba" tana gama fadar haka ta fice daga dakin Umaimah ta bita tana kiran sunanta taqi tsayawa.

A bakin qofar falon ta tsaya saboda Towel ne kadai a Jikinta ta kwalawa Ruqayya kira akan ta dakko mata Hijabi lokacin har Nuratu ta fice ta kusa kaiwa ina ta ajiye mota Umaiman tabi bayanta. Magiya ta shigayi mata tana bata haquri da rantsuwar ita ba abinda ta fada har zuciyarta bane kawai rantane a bace shiyasa ta fadi hakan amma tayi haquri.
"Saboda ranki yana bace se ki kasa lankwasa harshenki, idan kuwa haka ne wata rana se kin furta abinda ze kaiki ya baroki, kuma ni bazan koma cikin gidanki ba garama ki adana ban haqurinki baki mun komai ba, iya abinda zance miki shine kiyiwa kanki Hisabi, in har kinga cewar layin da kike akai daidai ne kici gaba, idan kuma keda kanko kin hango kuskuren abinda kike aikatawa tun wuri ki gyara kafin lokaci ya qure miki, ni na tafi yan uwana suna can suna jirana" Daga haka ta shige mota ta kunna, Umaimah ta riqr murfin tana cewa

"Toh ki jirani na shirya mu tafi tare ai dai kema kinsan ba'a fadamun za'ayi wani taro ba kuma taron menene ma akeyi?"
"Kiyi zamanki mun gama abinda zamuyi tun kafin na fito, daman magana ce akan Yayan Yah Aminu Anty Mami ta samu Miji zatayi aure shine ta ce zata dauki yaran Mijin yace ze riqe Mata"
"Agolanci? Allah ya rufa asiri yayan mu suyi Agolanci suje wani gida cin Arziqi a ringayi musu gani gani ana musu gori, taje can tayi auranta tsabar jaraba ko shekara biyu beyi da mutuwa ba zatace zata wani yi aure kamar daman jira takeyi ya mutun" Umaimah ta shiga kumfar baki, tsaki Nuratu taja ta taka mota tana ce mata
"Idan kinga dama ki kirasu ki basu haquri ki kuma gyara alaqarki da kowa dan ranar Naka dole se Naka, duk tarin qawayen da kike ganin sun fiye miki mu akwai gabat da za'azo da dole mudin dai mu zamu miki rana" daga haka ta daga Sammani ya bude mata Get ta fice daga gidan a fuska zaka dauka babu abinda ua faru amma cikin ranta kalaman Umaimah na nan suna nuqurqusarta.

Umaimah kuwa Nuratu na fita ta juya har ta kai bakin qofa kuma ta fasa shiga ta dawo nan Compound din taja kujera ta zauna bayan ta cewa Ruqayya ta kawo mata wayarta. Tafi qarfin awa daya a gurin a zaune, jira takeyi taga jama'ar da suka taru a bangaren Hajiyar sun fara fitowa amma shiru gashi tana tsoron ta shiga dan bata san su nawa bane a gurin haka ta gaji da zaman jira ta koma ciki suka ci gaba da Chatting da Safina dakw sake tausarta akan ta danne zuciyarta ta jira taga aikin Malam. Seda tayi sallar Magriba kafin tayi wanka ta saka Ruqayya ta shirya yara suka tafi gidansu.

Yanda Mama ta karbeta ya sa ta sake shan jinin jikin damanga Yah Naziyya na gidan itama gaisawa kadai sukayi ta fita a sabgarta, bata wani jima sosai ba suka tafi bayan Abba ya dawo sun gaisa shidai faran faran ya tarbeta yana tambayarta Khalil yaja jikokinsa yana musu wasa da zasu tafi ya basu kudi ita kuma ya sake nanata mata karatun da kullum suka hadu se yayi mata na ta nutsu ta zauna da Mijinta lafiya ya rufe da saka mata Albarka. Duk setaji babu dadi yanda Maman tayi mata, ita bata ga fushin me takeyi ba kawai sunje sun taru an hado da abunda tayi da wanda ba tayi ba sun gayawa Maman ita kuma ta hau ta zauna suda Allah ita basu san abinda yake a gabanta ba za'a qara mata wata damuwar.

KHALIL
Tun yana office Jalilah ta kirashi akan ta qarasa duk siyayar kayayyaki shi kawai take jira yazo ya gani, be samu ya shigo da wuri ba dan bayan ya bar gurin Humairah seda ya sake biyawa wani gurin dan haka be tarar da Jalilan ba se ubannin akwatuna na garari daya tarar a bangaren Hajiya guda goma sha biyu da sunan kayan lefen Humaira.

Buda baki yayi kawai yana kallon kayan, Hajiya tace
"Ai Rigimar Jalilah babu me iya mata, nan fa kudaden jama'a babu a gun wanda bata karba ba ta harhada ta siyo kayan nan, ina jinsu dazu lissafin bashin Miliyan kusan uku suke maka wai harda Sarqa zasu siya a saka a ciki nace musu sun baka ajiyar kudin ne ko Yaya?
Ga Lafayu can guda biyar Hajiya yagana ta aiko dasu magana kamar wutar daji labari ya watsu dangi wai zakayi aure ai da da wuri ka dawo gidan nan babu masaka tsinke yanda kasan yau ake bikin, nidai addu'a na ringayi su tafi salin alin ba tareda matarka tayi wani abun ba kuma Allah ya amsa mun har suka watse babu abinda akayi kuma tana gidan, ni yanzu da safe ma zuwa zasuyi su kwashe kayan nan kafin wani tsautsayin ya afka musu tun baka biya kudin ba".

Kansa na qasa yake sauraron Hajiyar dan ya kasa hada ido da ita. Kunyarta yake ji ace matarsa ta zageta amma ya gagara daukar mataki akai, a hankali ya daga kansa ya kalli gefe yace
"Daman itama tace zata dawo ta kwashe goben, munyi magana da Baba Abu Dazu yace ranar Juma'a zamu tafi can Jalingon, to ban sani ba ko ze yuwu ace an tafi da kayan ko kuma se daga baya dai wannan se kunyi magana dashi kun yanke yanda za'ayi"

"Eh nima ya kirani da yamma, da na gaya masa ga Lefe ma har an hada yace babu damuwa ze tuntubesu yaji, idan cam za'a kai gara a hada ayi tafiya daya idan kuma nan gidan Hauwa za'a kai kaga za'a iya bari se lokaci ya matso tukunna. Nadai yi musu zancen kayan ita Umaiman Jalilah tayi tsalle tace ba za'ayi ba to ni babu ruwana ba kuma zan goyi bayan rashin Adalci ba, idan kudi zaka bata ta siyi abinda take so to idan kuma kayan zaka mata toh gasu nan ka duba abubuwan da suke ciki ka siya mata itama" Hajiyan ta sake fada se ya daga kai ya kalleta ganin itama shi take kallo yasa ya mayar da kansa qasa cikin taushin murya yace

"Hajiya, kiyi haquri da abinda ya faru jiya dan Allah"
"Haqurin me kake bani Babana ni baka yimun komai ba, idan ma dan abinda Matarka tayi ne ni ya wuce a gurina na kuma yafe mata kaima kuma ina so kaci gaba da haquri dan daman ai kasan abinda ka dakko dole ka shirya karbar duk wani sakamako daya biyo ba. Kawai kaci gaba da Addu'a ka kuma ci gaba da lallabata". Shiru yayi yana sauraron Hajiyar, idan ya tuna zagin da Umaiman tayi mata zuciyarsa bugawa takeyi amma ya gagara daukar mataki me yasa?

Abinci ya buqaci Habiba ta kawo masa yaga Taliya ce yace ta mayar se ya miqe yayiwa Hajiya sallama ya fita. Kai tsaye ya wuce bangarensu, tunda ya shigo bega motarta ba daman yasan bata nan, seda yayi wanka ya canza kaya kafin ya sakko qasan lokacin har Ruqayya ta jera Abinci, Sakwara tayi musu da Miyar Agushi, se farfesun naman rago yana bude kwanon maganar Jalilah ta fado masa da tace jiya Umaimah ta dafa nama da magani ta bawa Hajiya taci se ya maida kwanon gefe ya zuba Sakwarar yayi bismillah tafi qafa dari kafin yayi shahada ya faraci.

A falon Umaimah ta tarar dashi yana cin abinci, shaf ta manta da saqon da ta taho dasu dazu da bazata fita ba har se an gama abincin ta zuba masa amma akwai gobe. Da ido ya bita ganin ta dauke kai ta kalli wani guri daban yaran kuma gurin sa suka tafi da gudu. Khalil ya sauke ajiyar zuciya yaci gaba da cin Abincinsa tareda yaran. Seda suka qare Mu'ayyad ya zaro kudin da Abba ya basu ya bawa Khalil din yace ya ajiye musu, se sannan ya san daga inda suke, yana nan zauneda yaran suna kallo har qarfe tara kafin yace suje su kwanta. Dakin da Umaimah take ya shiga da sallama bayan da yayi knocking ta bada Umarnin a shiga. Tana zaune gaban mudubi tana shafa mai da alama wanka tayi gashinta data wanke ya manne a fatar wuyanta zuwa bayanta, kallo daya yayi mata tsigar jikinsa ta tashi wani abu daya dade beji akan mace ba ya taso masa seya qarasa bayanta a hankali ya dora hannayensa kan kafadarta yana matsawa.

Umaimah, yanda yayi matan seda yasa tsikar jikinta itama suka zuba amma a fili bata nuna ta karbi saqon nasa ba sema qara tamke fuska da tayi ta ture hannun nasa daga jikinta ba tareda tayi magana ba ta miqe, rigar baccinta data ajiye ta dauka ta saka fuskar nan kamar Kunu ta haye gado ba tareda ta kalli inda yake tsaye yana binta da kallo ba. Seda ta kwanta taja bargo ta rufe qafarta zuwa cikinta kafin yabita shima ya shiga qoqarin kwanciya a bayanta.

"Meye haka Malam zaka shigowa mutane daki harda hawar musu gado?" Ta fada a fusace tana tashi zaune, da yasan yanda take ji a zuciyarta da be kuskura yaje kusa da ita ba dan tsaf idan da makamo kusa zata iya qaddamar masa yanzu.
Khalil kuwa dan murmushi yayi jin abinda ta fada seya sauke qafafunsa qasa, taja wani dogon tsaki kafin ta sake kwanciya ta juya masa baya tana qunquni.
"Umaimah" ya kira sunanta, bata amsa ba shima be saka ran zata amsa din ba dan haka yaci gaba da cewa
"Ina so duk abinda zakiyi ya tsaya iya kaina nida ke karki sake sako Mahaifiyata a ciki ballantana har ki iya bude baki ki zageta, ban taba zaton ko kallon banza kika ga wani yayiwa Hajiya zaki yi shiru ba se gashu keda kanki baki ji nauyin komai ba kika zageta"

"Khalil, nace Hajiya munafuka ce qarya nayi ko batayi munafuncin ba? Ta nunamun tana sona ta jani a jiki har ta fifitani akanka sata haifa she duk na yaudara ne rana daya ta nemo maka auran yar Qawarta idan ban kirata da Munafuka ba Annamimiya kake so nace mata kome?" Umaimah data tashi zaune ta fada tana kallonsa ido cikin ido babu tsoro ko shakkar komai a fuskarta.

Wani yawu me daci ya hadiye ya rufe idonsa da lokaci daya ya rikida yayi ja saboda bacin ran da kalamanta suka dira masa, yana jinta taci gaba da cewa
"Ai na gaya maka kaida zaman lafiya har abada a gidan nan Khalil ba dai aure kace zakayi ba toh mu zuba mu gani" taja wani tsaki kamar zata katse harshenta kafin ta yunqura ta shige bandaki ta barshi a gurin.

Bibbiyu yake gani da haka ya ringa dafa bango har ya haye sama a nan kan carpet ya kwanta yana dafe da kansa daya sara masa yana hawa saman. Ya rasa abinda yasa a kwanakin yake jin haka kwana yakeyi da ciwon kai ga wano baccin Asara daya sameshi daya rasa kona magani da menene baya sanin sanda yake daukarsa duk kuma yanda yayi ya yakice shi kasawa yake yi balle har ya samu damar tashi yayi Nafila cikin dare Sallar Asuba kanta kwana ukun nan a makare yakeyi amma ya ta'allaqa hakan da rashin kwnanciyar hankali da yake ciki a kwanakin.
Da hannu biyu ya dafe kansa, wancan fada masa akayi yanzu kuma ta maimaita masa harda qarin wasu kalaman da suka fi na farko muni duk akan Hajiyarsa anya idan yaci gaba da zama da Umaimah kuwa ya cika dan Halas? Macenda zata kalli cikin idonsa ta zagi uwar data haifeshi zagi mafi muni ta cancanci yaci gaba da zama qarqashin inuwar aure da ita kuwa?

Be ga ta inda ya kamata ace yayiwa Umaimah uzuri ba bayan wannan abun da tayi masa, idan zata zageshi ya shanye baya tsammanin ze jure cin mutunchin mahaifiyarsa kuma dole ya nuna mata cewar yana martaba Hajiyarsa kuma be hadata da kowa da komai a duniyar nan ba. Dakyar ya iya miqewa ya bude jakar Office dinsa dake ajiye a falon ya dauki biro da takadda ya zauna amma ya kasa rubuta abinda zuviyarsa take ayyana masa. Ya gwada rubutun yafi sau goma amma ya kasa yanda kasan an daure masa yatsu haka yakeji ga wata faduwar gaba tamkar zuciyarsa zata tsaga qirjinsa ta fito haka yake ji se yayi jifa da takaddar da bironya miqe tana layi ya isa gurin Dispenser ya tsiyayi ruwa me sanyi ya ringa sha har seda yaji kamar zeyi amai kafin ya haqura, a nan gurin ya tsugunna ya dafe kansa da hannu biyu, wani irin abu yake ji a cikin jikinsa, ikon Allah ne ya bashi qarfin bude baki ya shiga karanto duk addu'ar da tazo bakinsa be san tsahon lokacin daya dauka a halin da yake ciki ba sejin qarar wayarsa yayi ya bude ido dakyar yana kallon inda yake, anan gana Dispenser yayi bacci, ya yunqura dakyar ya tashi zaune nauyin da kansa yayi masa ya ragu wayarsa ta sake daukar qara ya shiga lalubenta ya dakko, qarfe biyar da minti Ashirin ya gani Alarm din daya saita ne tun qarfe biyar ze yanzu Allah ya bashi ikon ji.

Bayan yayi wanka ya shirya ya fita masallaci, a sahun baya yayi sallah sabanin da da kullum yana sahun farko. Bayan an idar da sallah be tashi ba yana zaune a gurin yana jan carbi, Malam Hashim Dattijo ne baban daya daga cikin Maqotansu ne ya dakko shi daga garinsu bashida lafiya, kullum a sahu daya suke SallarAsuba da Khalil din, haka Magriba da Isha indai a gida yayi su kwanakinya lura da Khalil din baya zuwa sallah masallacin se yau ya ganshi yana shigowa a yanayin da be saba ganinsa ba. Kusada Khalil ya zauna yana kallonsa yanda yayi zuru yana jan carbi ya saka wa guri daya ido bashi da tabbacin yasan abinda yake karantawa m seya kai hannu ya dafashi Khalil yayi firgigit ya kalli Dattijon kafin ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga gaishe shi.

"Ibrahimu kwana biyu baka zuwa Masallaci har na tambayi wannan yaron ko kayi tafiya ne yace Aa yana ganin gilmawarka, lafiya dai naga dukka rame ka fita a hayyacinka haka?" Dattijon ya fada har sannan hannunsa na kan kafadar Khalil din se ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Tsohon yace
"Ina nan Baba, kwana biyun banajin dadi shi yasa bana iya fitowa amma yanzu Alhamdulillah na samu sauqi"
"Toh Allahya qara rufa Asiri, amma kaganka kuwa wane ciwo ne yake damunka haka daya saka duk ka firgice?" Tsohon ya sake fada yana qare masa kallo se Khalil ya sunkuyar da kansa qasa dan be san me zece masa yana damunsa ba. Shi kansa in banda ciwon kai babu abinda zece gashi yana damunsa dan haka ya bude baki a hankali yace
"Ciwon kai nakeyi Baba, aiki ne yake mun yawa kwana biyu yake saukar mun da ciwon kai"

"Ko naji kasan shi ciwon kai yafi saurin gigita mutum gaba daya kaga ya fitar da mutum daga hayyacinsa, amma bayan ciwon kan babu abinda yake damunka kuma" Baba ya sake fada se Khalil ya daga masa kai alamar Eh Tsohon yaci gaba da cewa
"Bari idan na shiga gida zan duba maka wani magani da na taho dashi daga gida, kwanaki da wannan yaron shima yayi fama da ciwon kan harda jiri yayi ta yawon Asibiti suna cewa jininsa ne ya hau ana bashi magani, tunda ya shaqa maganin nan sau daya kan ya sauka, da yake shi hade hade ne duka da maganin miyagu da makaru na sihiri kuda kuke harka ta mutane daman dole se kun nemi tsari dan baku san zuciyar wadanda kuke tare dasu ba. Sannu bari na shiga gidan yanzu zan dakko maka na bawa takwarana ya kawo maka Allah ya qara afuwa ya ci gaba da doraku akan maqiya".

Da Amin ya amsa danya gaji da surutun tsohon, sun saba sosai kullum se sunyi hira amma yanzu da kansa yake masa kamar ana daka baya buqatar wani dogon surutu, tare suka fita Baban ya wuce gidan dansa shi kuma ya shiga gida. Badan akwai ayyukan da yake so ya qarasa ba saboda tafiyar da zasuyi da yau baze fita aiki ba. Be ko saurari abin karin da Ruqayya ke hadawa na ya wuce bangaren Hajiya a can

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login