Showing 54001 words to 57000 words out of 429394 words

Chapter 19 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

963

ba ai, wayar waye wannan? ina taki wayar ma da kika kirani data mutane?"

"Ba ka tafi da jakar a motar ka ba wayar Rumasa'u na ara nasan ma koda ace wayata na nan idan na kira bazaka dauka ba.

"Oh ashe akwai wadanda kika yarda dasu haka da har zaki iya kirana da wayar su?"

"Ruma ce fa Aminiyata, nasan ko kowa zeci Amana ta a duniya banda ita amma ai ba barin number zanyi muna gama magana zan goge, yaushe toh zaka kawo mun tawa wayar? Nasan mutane suna ta kirana" Umaimah ta fada, se Khalil yace

"Nayi seizing dinta se kinzo gidana sannan zan baki nima zan duba ciki na gani yanda kike mun bincike a waya"

"Babu abinda zaka samu a wayata, amma ka taimaka ko Sim din ne ka kawomun na saka a qarama saboda qawayena da zasuje Kamu gobe zasu kirani"

"Zan duba na gani" ya bata amsa daga nan sukayi sallama.

"Gaskiya zan Hada Umaiman nan da Nusyta ta rakata inda takai sunanka nima a shawo mata kaina, jifa yanda ka gama masifa kana fadar maganganu kai zaka fasa, ka shigo fuska kamar wanda ya fada cikin kashin shanu amma daga jin muryarta ta kalallame ka duk kububuwar daka hau ka sakko kana wani kashe murya dole da abinda yarinyar nan ta taka shi yasa take iskanci son ranta" Mansur da tunda suka fara wayar ya saki baki yana kallon ikon Allah ya fada.

Se Khalil ya saki murmushi yace
"Inason yarinyar da yawa Mansur ko nayi fushi da ita baya dorewa tana da shiga rai yanda baka tunani"

"Naga alama" Mansur ya fada kafin yaja kwanon funkasonsa yaci gaba daci.

Umaimah kuwa ajiyar zuciya ta saki a fili tace "An rufe wannan case din saura na cikin gida".
Dakin ta koma ta tarar da Halima na shirin wucewa itada Fannah.

"Aa ina kuma zakuje" Umaiman ta fada bayan data miqawa Ruma wayarta se Haliman ta amsa ta da cewa

"Gidana zamu wuce ta huta se gobe idan mun hadu a gurin Kamu"
"Kedai ki wuce amma ita ai biki tazo dan haka babu inda zata je, yi haquri Fannah bari na kawo miki ruwa da abinci wallahi wata wuta na kashe ne se yanzu na samu nutsuwa" Umaimah ta fada tana mayar da Fannan ta zauna.

Haka Halima ta tafi ita kadai bayan da suka daukowa Fannan akwatinta daga mota. Cikin gida Umaimah da Ruma suka shiga karbo abincin, Anty ta samu da wasu qannen Mama biyu a kitchen suna hidima suka dibi wanda ze ishe su ga ruwa da Zobo masu sanyi, sabulun wankanta ta tuna yana dakinsu dan haka ta cewa Ruma tayi gaba gata nan zuwa.

A dakin ta tarar da Mama tana zaune akan gado Nuratu na durqushe a gabanta tana kuka.
"Zonan, ina kika tsaya tunda kuka dawo baki shigo gida ba?" Maman ta fada tana kallonta idonta da alamar itama kukan tayi ko take so tayi se Umaimah ta qarasa kusada Nuratun ta zauna a ranta tana cewa

"Bata bada labarin abinda ya faru ba kenan".

"Kamar yanda na fara gayawa yar uwarki daga yau ba zamu sake samun lokaci irin haka nida ku mu zauna ba, duk abinda ya kamata ku sani kun rigada kun gani a aikace tsahon shekarun da mukayi tare daku.
Kuna shirin shiga wata sabuwar rayuwa ce me cike da qalubale kala kala wadda idan kukayi haquri kuka jure sakamakonta me girma ne wato Aljanna.

Aure ya wuce duk yanda kuke zato, duk abinda kuke hange a cikin rayuwar gidajen wasu zahiri ne amma badinin aure bazaka sanshi ba se randa ka tsinci kanka a cikin sa. Abinda nake so ku saka a ranku shine Aure ibadar Allah ce, kamar yanda zakuyi sallah dan lada to ku tabbata duk wani abu da zaku aikata a cikin gidan aure kuyi shi domin samun lada.

Banida matsala da Nuratu amma dukda haka zanja kunnenku gaba daya shi Miji shugabane ubangiji ne ya bashi wannan girma da darajar dan haka a matsayin mace da take qarqashinsa dole ta girmama shi in har tana so ta gama lafiya.

Umaimah duk wata rashin kunya da fitsara da kikeji dasu ki tattara su ki ajiye a cikin gidan nan domin idan har kika tsallaka da daya zuwa gidan aurenki ki tabbata da cewar kin qulla guzurin kai kanki wuta da qafarki Allah ya kiyaye. Girmamawa tsakanin ku da Mazajen ku dolece haka iyayensa da duk wani da yake gaba daau dole ku girmamashi tamkar yanda kuke girmama na gaba daku sannan kuso qannensu kamar yanda kuke son naku.

Karku zama masu yawan qorafi da kai qara, Banda fitar da sirrin gidan auranku, matsala idan ta faru ku zauna ku warwareta a tsakanin ku indai ba tafi qarfin ku ba shine zaku sako na gaba daku a ciki.
Ku zama masu tattali da kula akan duk abinda Mijinku ya kawo kuma ku zama masu godiya da nuna jindadi idan sunyi muku abu komai qanqantar kyauta ku gode koda kuwa abun beyi muku ba ko bakqmwa so hakan yana qara musu qarfin guiwar suyi muku.

Umaimah banda jajibe jajiben qawaye, Kullum addu'ata Allah ya rabaki da qawayen banza Allah ya karbi Addu'ata ina fatan zaki dore kici gaba da rayuwarki a haka tunda babu abinda ya ragu a jikinki saboda kin dena tara qawaye sema qarin samun nutsuwa da kika samu a rayuwarki to kiyi qoqari ki dore a haka.

A qarshe ina so ku dauki rayuwar gidannan data sauran yayyenku dan ta zame muku madubin dubawa. shekarata Talatin da Tara a cikin gidan nan tareda Mahaifinku amma daidai da rana daya ban taba fita da sunan yaji ba, da dadi babu dadi nayi haquri mun zauna gashi har na haife ku kun girma ina shirin aurar daku da kuka rage a gabana kunga bani da abin cewa sedai na godewa Allah na kuma qara gode masa kuma ba komai bane jigon zamana se haquri da Addu'a sune manyan makaman da in har bawa ya riqe su baze taba tabewa ba a rayuwarsa.

Allah yayi muku albarka, Allah ya albarkaci gidajen auren ku yasa mutuwa ce zata fito daku, Allah yasa ku zama sanyin idaniyar abokanan zamanku ku ya basu ikon riqe ku da Amana".

Kuka Nuratu takeyi Hajiya Umaimah kuwa jiki dai yayi sanyi se qifta idanu takeyi. Muryar Mama taji tana cewa Nuratun taje taci gaba da sabgoginta se itama ta miqe Maman ta dakatar da ita tace

"Zauna ban gama dake ba" seta nemi guri ta zauna a ranta tana cewa
"Ashe da saura na zata bata fada ba wallahi kuwa in har aka mun fada itama se ranta ya baci sedai muci bikin kowa da bacin rai".

"Umaimah" Maman ta kira sunanta sam babu wasa a muryarta kafin taci gaba da cewa

"Bana buqatar jan wani dogon bayani, Allah ya gani a cikin yaya bakwai daya bani ban banbanta wani da wani gurin bayar da tarbiyya ba, na raine ku akan turba daya na koyar daku abu daya amma kin fita daman da sauran ta kowacce siga.

Ina so ki sani daga yanzu zaki koma cin gashin kanki ne kuma zuwa nan da wani lokaci kema zaki zama uwa me bada tarbiyya dan haka kisan abinda kikeyi. Ki nemi guri ki zube duk wani shirme da rashin hankali da kika mayar dabi'a ki gane ainihin rayuwa da inda ta saka gaba.

Aiki da ake sakaki kiqi yi ko kiyi abinda kika ga dama, girkin da kike cika mana gishiri ko yaji a ciki da duk wasu sauran Iyashege da kikeyi a cikin gidan nan tamkar karatune yanzu ne zaki fara zana jarabawar abinda kika koya, idan kinyi da kyau ki wuce lafiya idan kin fadi kece a ruwa dan ni babu ruwana Allah shine shaidata duk abinda ya kamata Uwa ta koyawa yarta na koya miki.

Ina sake jaddada miki batun qawaye babu ke babu su, ki tattara kowa da komai a gefe ki fuskanci gobenki Umaimah, wannan Azabar kishin da kika sakawa ranki ki cire idan kinqi ke zaki sha wahala dan karki taba zaton yanda yake biye miki a waje kici mutuncinsa ki bashi haquri daga baya ya haqura ki zata haka zata ci gaba a cikin gidan, bana miki fatan ya zama daga cikin mazan da suke shanye wulaqancin Mace a waje idan ta shiga hannunsu su rama amma koma me ya biyo baya ke kika siya da kudinki dan abinda kika shuka ne zaki girbe".

Da sauri Umaimah ta daga kai ta kalli Maman tace
"Mama karkiyi mun baki dan Allah ki yafe mun duk abinda na tabayi miki na ba daidai ba wallahi sharrin shaidan ne kuma in sha Allahu Mama se kinyi Alfahari da aurena se na bawa kowa mamaki duk wanda yake jiran yaji wani abu mara kyau a kaina sedai ya gaji amma babu abinda ze faru" ta qarasa maganar tana sakin kuka saboda wasu tunani da suka yi mata dirar mikiya a zuciya.

Irin labarin izayar da mata suke sha a hannun maza datake ji kota karanta a Novels yanzu idan ta fada cikin irin wannan rayuwar ina zata saka kanta.

"Ba baki na miki ba Umaimah a kullum ina roqon Allah da karya kamaki da laifin bata mana da kikeyi cikin sani ko rashin sani kullum Addu'ata itace Allah ya shirye ki yasa ki gane gaskiya ki dena abinda kikeyi kuma in Allah ya yarda Addu'ata bazata tabe ba, zaku samu kyakykyawar rayuwa a gidan auranku tamkar sauran yan uwan ku amma dukda haka se kin dage kin chanza halinki, na yafe miki duniya da lahira Umaimah, Allah yayi miki Albarka Allah ya zama gatanki" Maman ta qarasa tana miqewa saboda kukan daya taho mata.

Babu shakka dagaske Da mara ji yafi shiga zuciyar iyaye dan a cikin yaranta son da takewa Umaiman na daban ne haka ma Abbansu ta sani amma Halinta ne yasa suke dannewa suke nuna tamkar basu damu da ita ba.

Kuka Umaimah tasha sadidan ga tunanuka kala kala na gifta mata a kwakwalwa, yaya gidan auranta ze kasance? Zata samu farinciki da soyayyar da take hasashe a gurin Khalil? Shin Khalil din ma ze dore da halayensa na yanzu har cikin gidan auransu ko kuwa shima yana cikin irin mazan da suke kwantar da kai a waje dan su samu abinda suke so?.
Tsoro da fargaba ne suka rufeta har tana jin kamar zazzabi ze kamata dan ita bata taba zama tayi tunani akan yaya makomarta a gidan aure zata kasan ce ba, shin idan Khalil ya canza mata ina zata tsoma ranta?..

Washe gari akayi Kamun Amare tareda Mother's Eve a hade, Amare sunsha kyau cikin shigar Lace da sukayi iri daya kai tsaye bazaka iya cewa ga wadda tafi wata kyau ba saboda yanda kayan sukayi matuqar karbarsu, Dangin Khalil sun nuna mata qauna kowa fadi yakeyi tayi sa'ar dangin Miji se fatan Allah yasa su dore a haka, seda aka kusa tashi Angwaye suka je gurin wanda Anty Laure ce qanwar Mama ta takura se sunje ko yaya ne saboda mutane su gansu musammab Khalil tunda ita Nuratu washe gari idan an kaita zasuyi dinner.

Umaimah nacan tsakiyar Qawayen ta suna kwasar shoki akayi sanarwar shigowar angwayen, a zaton ta Dr Sagir ne kadai tunda daman shi dan bidi'a ne tasan ze aikata Khalil kuwa ko kafin su taho bayan an gama mata kwalliya sunyi video call yana kwance a dakin Mansur dan can ya kwana tasan baze zo ba.

Wani qum taji kamar an buga mata guduma akai lokacin da angwayen suka shigo, Dr Sagit da Architect Khalil suka jero a tare sun sha Milk din shadda dinkin babbar riga iri daya kamar yanda amaren nasu suka saka Lace kalar cream saboda dukkan su fatarsu bame haske bace dan haka kalar ta haskaka su sosai.

Kallon daga sama har qasa tayi masa a qasa da second talatin, yanda ya kafa hula yana sakin wannan murmushin nasa saboda Jalila dake binsa ta gefe tana rada masa abinda Umaiman bata san ko menene ba, kallon mutanen da suka ciro wayoyinsu suna daukar angwayen hoto tayi, idan ba qarya idonta ya mata ba fiye da rabinsu Khalil suke dauka. Daga gefenta ta ji daya daga cikin qawayen ta tana cewa

"Lah Amina ina wayarki ki daukar mana Angon Umaimah Sabo mu samu na dorawa a status ai a sittin ta juya sedai cikin rashin sa'a tsinin takalminta ya karkace ta tafi luuu ta gama saddaqarwa Amarya zata sha qasa taji ta ta fada jikin mutun ya saka hannu biyu ya riqeta da kyau yana ce mata

"Yi a hankali Babe karki ji ciwo". Fuskarsa ta shiga qarewa kallo, ashe kyan data hango yayi mata daga nesa wasa ne se da yazo kusa sannan taga asalin kyau, askin da yayi da gyaran fuska an gyara masa gemun daya fara tarawa ga kuma Kyan Angonci suka qara bawa fuskarsa wani kwarjini na daban, yanzu haka duk matan da suke gurin zasu kalle shi harma sun dauki hotunansa a wayarsu amma wallahi an cuceta kawai se gani Khalil yayi ta fashe da kuka yanda kasan wadda ya fallawa Mari.



PROMO
PROMO
PROMO


BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA =?G?
08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO


SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
PAGE 17


"Menene?" Khalil ya fada yana qoqarin miqar da ita tsaye daidai lokacin da Yaya Hafsa ta qaraso gurin tana tambayarsa lafiya ko taji ciwo ne.

"Me yasa kazo bayan kasan bana so kowacce mace ta ganka? Yanzu gashi nan har hutunanka suke dauka da wadda ta isa da wanda bata isa ba suna yaba kyan da kayi, wallahi ka fita idan ba haka ba sena watsa taron nan kowa tashi" ta fada tana ci gaba da ziraro da hawaye.

Tsabar takaici sakinta kawai yayi ya miqe tsaye daidai sanda Anty Hafsa ta qaraso tana tambayarsa lafiya ko ciwo taji, a taqaice yace mata
"Wai saboda nazo ne take kuka yammata zasu kalleni su dauke hotona"

"Amma Umaimah ban taba sanin yar kutumar uba bace ke se yau, a gurin taron bikin ma sekin siyar da hali? Toh karki fasa na rantse da girman Allah yanda bakiyi hankalin ajiye haukarki a gida kafin ki fito ba haka nima bazan ji shayin nada miki dan iskan duka a gurin nan ba,karki miqe ki koma mazaunin ku wallahi se kinci ubanki" Anty Hafsan ta fada a fusace dole Umaimah ta miqe bayan data share hawaye dan tasan idan iya shege take ji dashi Hafsan ta fita, kamar yanda ta fada ta daketa a gurin ita ba wani babban abu bane a gurinta.

Haka aka qarasa taron biki Amarya Umaimah da Angonta dai babu armashi daga bangarensu, Daga ita har Khalil din fuskarsu babu fara'a, shi tsabar takaicinta ne ya hadu ya qume shi. Da murnar sa ya shigo, irin kyan da ta masa baze misaltu ba yana jira yazo ya rada mata a kunne irin yanda ta burgeshi yayi mata liqi da sabbin dollars din da aka bashi kyautarsu dazun da safe saboda ya sake nuna wa mutane ita din yar gatansa ce se gashi kalar tarbar daya samu a gurinta kenan ita kuwa takaici da baqin ciki qiris ya rage su qarasata, yanda ake ta daukar su a hoto sam mutane basu damu da hade fuskar ma da sukayi ba kai kace su kadai ne Amaren a gurin ita kuwa Nuratu da Dr ta shagalinsu sukeyi sun more ranar tarihinsu dan ba sake dawowa zatayi ba.

Da aka tashi a mota daya suka tafi, tana zama tun bata kai ga rufe qofa ba dan ya rigata shiga ya tare ta da cewa

"Na rantse da Allah Umaimah wallahi kika kuskura kika qure haqurina bazata mana da kyau ba, ke bakya gudun abin kunya a rayuwarki? A gurin taron biki ma se kin nuna musu rashin nutsuwarki?
Akan me? Kanki aka fara aure ko yaya ko a kaina ango ya fara zuwa gurin biki da zaki nemi ki jawowa mutane magana?

Ai wallahi da kinci gaba da abinda kika fara da kinga qarshen hauka yau ai na gaya miki bake kadaice saitin kanki yake gocewa ba" Khalil ya fada cikin masifa kamar ze rufeta da duka Mansur dake gaba kuwa yace me zeyi idan ba dariyacenDariya yake harda dungurawa dantun farkon Dramarda akayi a Hall din har video yayi a ransa yana sake jajantawa abokinsa dan dagaske yanzu ya yarda ya dakko cin kai.

Allah sarki Umaimah ko sakato tayi tana kallon Khalil dake zabga bala'i, seda yayi shiru dan kans kafin ta sunkuyar da kai qasa se sababbin hawaye shar suka fara zubo mata.

"Kinsan Allah akan ina miki fada kina mun kuka se kin gane kurenki, kawai saboda kin mayar dani wani sauna se kinmun laifi ina miki fada ki fara kuka ki mayar da abun kamar ma nine nake cin zalinki ko kici gaba" Khalil ya sake hayayyaqo mata ita dai kanta na qasa tana hawaye, idan ta tuna yanzu fa hotunan Khalil nacan suna yawo se taji kamar ta kurma ihu haka suka dauki hanyar gida tana hawaye Khalil na buga tsaki.

A Murtala Suya Mansur ya tsaya ya juya ya kalle su da murmushi yace
"Afuwan Amarya bari na karbo miki kaza nasan hidima bata barin ku kuci abinci" be gama rufe baki ba ta dago a fusace tace
"Naqoshi"
"Kinwa kanki, Malam karbo mana mu zamu ci" Khalil ya fada yana galla mata harara se? Mansur ya juya yana ci gaba da dariya yace

"Easy Ango kasan Amarya fa s ana lallabata", be wani jima ba ya dawo da ledoji ya bude sit din gaba da babu kowa ya zuba suka qara gaba, seda ya sake tsayawa a Rufaida ya siyo Yoghurt da Lemo kafin suka qarasa gidan su Umaimah yana tsaida motar tun be ida parking ba ta balle murfin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login