Showing 357001 words to 360000 words out of 429394 words

Chapter 120 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1679

na fada miki zan sake jaddadawa aikin gidan nan kaf ya rataya a wuyanki kuma Tilas kiyishi akan lokaci sannan a mutunce yanda kikaga iyayenki sunayi.

Karki kuskura qarfe bakwai tayi baki gama abin karyawa ba a ranakun makaranta sannan duk rintse karki wuce biyu ba tareda kin sauke na rana ba haka na dare kin sani kafin na dawo daga Sallar Isha'i an ajiye mun abinci. Sannan maganar wanke wanke da shara bana so na sake maimaita miki daga yanzu kinsan yanda akeyinsu Kwanukan da kika ajiye tun Yamma kuma suna nan suna jiranki ki gyara su yau kin samu yan uwanki sun rage miki aiki gobe basa nan ke zakiyi komai kuma ki yarda kiyi wani abu da ba haka ya kamata ba zamu gauraya a cikin gidan nan maganar wannan abincin kuma( ya nuna kular gabansa yace) daga yau har zuwa sanda ze qare shine abincinki a cikin gidan nan Umaimah koda ace zeyi tsutsa Wallahi se ya qare zan ci gaba da baki abinci a cikin gidan nan idan kuma kika ci wani abu nawa ba tareda umarnina ba Allah ya isa"

A firgice suka kalleshi gaba dayansu Anty tayi saurin cewa
"Haba Alhaji me yayi zafi zakayi mata Allah ya isa akan Abinci?"
"Sharadi na bata idan kuma idan har ta qi bi na maimaita Ban yafe ba" ya sake fada cikin tabbatarwa se aka rasa wadda zata sake magana a cikinsu se Umaimah data rushe da sabon kukan tashin hankali dan lamarin kam ya girmama ya zarce tunaninsu, Abba kuwa ko a jikinsa yaci gaba da cewa
"Sannan komai ruwa komai Iska da Itace zakiyi girki ban yarda ki sake kunna mun Gas a gida ba tunda bada kudinki na siya ba wanda kikayi amfani dashi yauma se kin biyani".

Anty da Mama dai sun rasa ta cewa Umaimah ko kallonsu takeyi a qoqarinta nason su roqa mata sassauci akan wannan lamari ina zata kai wannan shinkafa da ta ranar ma dakyar ta iyaci muguntarta ta qare akanta kenan ai wlh gara yace ta biyashi kudin shinkafar kawai da wannan tsatstsauran hukunci ita zancen karta kuma ci masa abinci ma be dameta ba tana da yan kudadenta zata iya ciyar da kanta na tsahon lokacin da yace amma zancen tayi ta cin shinkafa ai bema taso ba. Ganin Abban ya miqe Alamar zeje ya kwanta kuma har sannan Anty da Mama basu roqa mata sassauci ba yasa ta zabura cikin kuka me tsanani tace

"Dan girman Allah Abba kayi haquri wlh bazan iya ci ba na yarda ayi lissafi zan biyq duk kudin amma ka barni na fita dashi na bawa Almajirai" s Abban ya dakata ya juya ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
"Wato saboda su basu da uwa da uba a kusa shine zaki basu abinda kika kasa ci ko? To ban yarda ba kuma ban janye maganata ba" daga haka ya shige cikin dakinsa ya barsu. Anty tayi tsaki qasa qasa ta miqe ta fice daga falon Mama ta bita da kallo a ranta tana ayyana idan ba'ayi wasa ba Umaimah na shirin rusa zaman lafiyar da sukeyi a cikin gidan dab tun a daren jiya ta lura da Anty ta kai maqura da Al'amuran Umaiman dan a daren jiya da Abban ya yanke jiki ya fadi bayan ya fito daga wanka Allah ya rufa Asiri Antyn na tsaye ta kai masa ruwan shayi ita ta tareshi tana kuka take cewa Maman
"Gaskiya kija mata kunne ta dena dagawa Alhaji hankali haka dan idan ya mutu bata da Asara ke kanki kukanki kadan ne dan duka yayanki kin aurar kuma suna da Madafa nice me qananan yara" tun a daren Jiyan maganar take nuqurqusarta amma ta shanye ko su Nuratu bata gayawa ba ta kuma tabbatar dalilin da ya saka dazu har Sharifa take sake maimaitawa Umaiman cewar karta kashe musu uba kenan qila ita Antyn tayi zancen da yayanta.

Gajiya da kukan da Umaiman takeyi ya saka Maman miqewa ita ma se ta zabura ta bita har suka je bakin qofar Maman bata dena gunjin kukan ba ganin tana shirin shigewa daki ta barta yasa cikin kuka tace
"Dan Allah Mama dan darajar Manzon Allah kisa baki Abba ya haqura na bawa Almajirai abincin wlh bazan iya ci ba ni na yarda kar a bani abinci har tsahon lokacin daya kamata na cinye wannan din".

Yanda take kukan da magiya abin Da da Mahaifi se zuciyar Maman ta kamu da tausayinta dan haka cikin sanyi tace mata
"Ki samu Robobi ki juye ki saka a Freezer idan ta kitchen din bata dauke ba ki kawo nan ki saka a Fridge dare yayi yanzu da Safe maga yanda za'ayi" daga haka ta shige daki ta barta babu yanda ta iya ta koma ta dakko Kular abincin tayi yanda Maman tace dan tasan idan ma ta barshi ya lalace qarin laifi ne a gurinta. Seda ta gama Adana abincin tas ta kwashe kwanukan wanke wanken data bari bakin famfo ta shigar dasu kitchen kafin ta koma daki tana ci gaba da kuka, daren bata iya runtsawa ba tunanin yanda zata cinye shinkafar nan safe rana dare harta qare takeyi idan Abban be haqura ba seda Asuba ta gabato bacci ya fara fizgarta, motsin shigowar Abba dasu Salman daga Masallaci ya farkar da ita kamar wadda aka koro fit ta fice daga dakin ta tsaya gaban Abban tana muzurai so takeyi ta sake kafa masa magiya amma yanda taga fuskarsa a daure ya hanata iya bude baki tace masa komai se hawaye suka fara mata tsere Abba kuwa yayi wucewarsa ciki ba tareda yabi ta kanta ba indai juninta rashin ji yana da hanyoyin dafata cikin ruwan sanyi har tayi laushi kuwa.

Ciki ta koma tana sharar kwalla tayi Alwala tayi sallah, harta kishingida tana ci gaba da share Hawayen ta tuna da zancen girke seta fashe da kuka me sauti harda sheshsheqa musamman data tuna itace zata hura kai wannan bala'i da me yayi kama? Sanda tana gidanta iyanzu tana kan Royal Bed cikin Turkish Duvet ga sanyin Ac da qamshin freshner suna ratsata, tana kwance Ruqayya zata shigo mata da abin kari har kan gado ta shiga Jacuzzi tayo wanka taci a yangance ta sake kwanciya amma yanzu Murhune yake jiranta da Itace kai Allah ka kawo mata dauki. Kuka tasha bana wasa ba kafin ta lallabi kanta ta fita dan zaman ba amfani ze mata ba bandama ta sake ja wa kanta wata shiga ukun.

A qofar falon Mama ta durqusa ta gaisheta ta daga mata kai kawai a hakan ma taji dadi dan tunda ta dawo Maman bata taba amsa gaisuwarta ba, murya na rawa tace
"Me za'a dafa Mama?"
"Kunun tsamiya da Alala, wake yana nan an jiqa seki wanki ki bawa Yasir ya kai markade shima qullin kunun yana nan a Kitchen idan kinga dama ki bata ke zakiyi taci harsu qare" Maman ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba harta miqe kuma ta koma murya na rawa tace
"Mama kinsan idan na dama kunu tsinkewa yakeyi, sedai na dafa Abba kuma baya so a dafa".

Shiru Maman tayi kamar ba zata ce mata komai ba se kuma ta numfasa tace
"Idan ruwan ya tafasa kizo ki gaya ki debi kwai ki dafa a saka a cikin Alalan" daga haka taci gaba da jan carbinta Umaimah ta ja qafafunta ta wuce Kitchen din. Waken ta fara dubawa ta sauke ajiyar zuciya ganin gyararrene har ya juqu ma dan haka ta wanke shi ta dubo Attaruhu da Albasa ta zuba cikin takatsan tsan, sedata hada markadan tsaf kafin ta wuce qofar dakin Anty ta kwankwasa dan babu wanda ya fito a yaran Lahadi ce kuma an musu hutun Tahfiz ga garin yanayin sanyi ya fara shigowa tasan suna nade a bargo se ita da uwarta bata sonta ce take gararanba a tsakar gida da farar safiya. Tafi Minti biyar tana bugu kafin Antyn ta bude fuska babu yabo babu fallasa tana kallonta, kamar karta gaisheta saboda qin roqar mata da Abba da batayi ba jiya amma ta dake tace mata ina kwana.

"Mama ce tace Yasir yazo ya kai markaden Alala" ta fada a cukule itama Antyn murya babu walwala tace
"Yasir ya tashi da Zazzabi sedai ko Sharifa dan Firdausi ma tabi Fatima jiya". Jin cewar se Sharifa yasa ta juya ba tareda ta cewa Antyn komai ba dan indai yar iskar yarinyar nan ce qarshe seta jawo mata wani laifin ace bata gama da wuri ba sawunta a likafa ta wuce ta kunna wuta danma itacen busashshene tana yi tana hawaye wai ita Umaimah ce ta sake dawowa girkin itace? Seda ta hada wutar ta dora ruwan kunu kafin ta leqa waje ta samo Almajiri ya kai mata markaden a ranta tana Mamakin duk Almajiran da suke musu hidima a gidan suna ina tunda satin ya kama ta dena ganinsu ko saboda an shirya maida ita boyi boyi yasa aka sallamesu.

Ta kalli tsakar gidan ta tabbatar kuma ita din ce dai me sharewa duk dan saboda a jance zancen cin shinkafa ta tattara kwanukan da aka fito dasu na wanke wanke a gefe ta hau shara, kafin ta gama bayanta ya riqe dakyar ta iya miqewa saboda Azabar ciwon daya dauka ta wuce dakin Mama tana kuka kamar yarinya dan ruwan ya tafasa Mama ta kalleta kawai bata ce komai ba, ganin Almajirin ya kawo markaden ta kama hada Alalan tana yi tana diga musu Hawayen daya kasa tsayar mata a ciki Mama dai ta dama kununta tafi ki mutu bata ce mata ba se sanann Anty ta fito suka gaisa ta kawo Flask din da ake saka musu Kunun Maman ta zubawa kowa nasa ta koma dakinta. Umaimah na zaune tana jiran Alalal ta dafu tana aikin kuka kamar matar Mamaci har yayi ta kwashe ta hada kwanukan ta hau wanke wanke. Tana kallo kowa ya debi abin karinsa yaci kamar kwayar idonta zata fita saboda kuka yanzu duk ta gama wahalar nan ba zataci ba kenan ake nufi haka ta wuce daki ta kwanta dakyar saboda ciwon jiki tana kuka data ci shinkafar nan ta gwammace yunwa ta kasheta kawai kowa ma ya huta tunda an tsaneta. Sha biyun rana Mama ta kwala mata kira, ta yunqura dakyar ta fita jikinta kamar wadda ta fado daga kan bishiya saboda ciwo ta tsaya tana kallon Zogalen dake jibge a qasa ba'a tsinke shi ba ta kalli Mama dake cewa
"Gashi nan Dambu zakiyi tsakin kwano biyu zaki auna dan za'a kai nan baya gidan Malam Bala anyi Rasuwa dazu ga Madambaci nan nasa a aro na gidan su Harira shi babbane sosai in kika hada da wannan zaki fi sauri".

"Dambu" ta maimaita tamkar bata san kalmar ba, ta waiwaya jin Yaro yayi sallama da wani uban rafkeken madambaci ya ajiye take ta tuno da zuwansu gidan Qawarta Abu Maman Nihal a irinsa suka tarar da ita tana dambu shikenan ta shiga ukun ta ta lalace. Cikin kuka tace
"Wlh yunwa nakeji Mama bazan iya aikin dambu yanzu ba"
"Ga shinkafarki can ai ki diba ki dumama kici kuma ki hanzarta ki dora da wuri dan Abbanku yana gida kin san kuma Azahar nayi ze nemi Abinci" Maman ta bata amsa cikin ko in kula kafin ta zura Hijabin dake hannunta tana cewa
"Idan kin gama bamu dawowa ba ga Kwano nan(ta nuna mata wata fanteka) indai kinyi awon daidai ragowar ze cika wannan bayan ki debar mana na gida se bawa Ko Salman ne ya miqa gidan rasuwar se Mundawo" tana gama fada tayi gaba sega Anty ta fito da fitsararriyar yarta inji Umaimah a bayanta da alama tare zasu tafi suka rankaya suka barta a tsaye ta rasa abinyi se hawaye takeyi.*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 77


UMAIMAH

Daren Ranar bata iya bacci ba seda Anty ta kira wani me Chemist ya dubata yayi mata allurar rage zugi tasha magani sannan, washe gari da safe ta tashi da wani sabon tashin hankalin. Qarfe goma gaba daya yan gidan manya da yara suka hallara bisa umarnin kiran da Abban yayi musu tun daren jiya. Bata san kiran me ya musu ba tadai ga sun shige can bangarensa kuma sun dade suna magana dan har se gurin sha biyu sannan Salman yazo yayi kiranta.

Dakyar take tafiya saboda yanda jikinta yayi tsami, badan kar ta sake yin wani laifin ba daman da bazataje kiran ba. Irin yanda gaba daya suka dauke kai tamkar babu wanda yasan da tsiron halittarta a gurin ya mata ciwo daman tunda ta dawo gidan in ka cire Anty babu me shiga sabgarta Mama kuwa in zasu hadu sau dubu ta gaidata bazata amsa ba daman tun randa tadawo tayi mata iyaka da shiga dakinta tace bata buqatar ganinta a ciki. Tana zama kamar wata Mujiya a cikinsu suka fara darewa daya da daya duk su???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ka fice daga dakin kowanne yazo giftata seya bugamata tsaki sannan su harareta, seda suka fice gaba daya kafin Mama ta kalleta rai babu dadi tace
"Matso ciki".
Gaba kadan ta muskuta amma bata yarda tayi kusa dasu da yawa ba cikin rawar Murya ta shiga gaishe su ta kalli Abba dake Kishingide da gani bashida lafiya, babu wanda ya amsa gaisuwar Tata har Antyn yau tana daga gefe idonta yayi jajir alamar Kuka tayi se Umaimah ta sunkuyar da kanta qasa, muryar Abban taji cikin dakiya yana cewa

"Ina so ku zama shaida tsakanina da Umaimah zan kafa mata sharudda da har idan tana neman zaman lafiya a cikin gidan nan dole ta bisu. Ban yarda Umaimah ta taka ko nan da qofar gida ba tareda izinina ba haka zalika banyarda wani yazo gidannan gurinta ba, sannan zata bani wayarta" Abban ya fada yana kallon Umaimah data sunkuyar da kanta qasa tana hawaye, takaicin yanda gaba daya kowa ya tsaneta ya kamata, babu wanda ya dubi halin da ta tsinci kanta a ciki ita ta rasa Khalil a maimakon su tausaya mata suyi qoqarin kwato mata haqqinta se suka bige da tsanarta kamar ta aikata musu wani mugun laifi.

Tana jin Abban ya gama maganarsa, zancen ba zata fita ba ko ba za'a zo gunta ba be dameta ba kamar na karbe mata waya. Idan ya rabata da wayarta ta ina zata samu damar magana da Khalil harsu daidaita ta koma dakinta? Tsawar da Mama ta daka mata ceta sakata miqewa da sauri dan dakko wayar, tana hawaye kamar yarinya ta bashi wayar tata ya karba a gabanta ya zare layin ya ballashi biyu kafin ya sake kallonta yace
"Abu na gaba
daga yau duk wani aiki na cikin gidan nan ya dawo hannunki, ina nufin daga kan shara girki wanke wanke da duk wasu sauran ayyukan tsakar gida ke zaki cigaba da yinsu har wankin kayanku idan kuna da buqata ku bata tayi muku dan ba zan ringa ciyar da ke a banza ba tunda kinqi zaman aure kiyi na Farilla ki samu lada zakiyi Mustahabi anan. Idan har na kamaki da laifin saba daya daga cikin sharuddan nan ina me tabbatar miki da cewar sekin gane kuskurenki tabbas".

Da sauri ta daga kai ta kalli Abban bakinta na rawa alamar son yin magana amma mugun kallon da Mama ta aika mata dashi yasa ta kasa cewa komai ta maida kanta qasa hawaye suka sake balle mata kamar famfo.
"Rayuwar da kika zabarwa kanki kenan zaman gida ba gaki ga gidannan se kici uwar da kika ajiye a ciki. Kinsan dai ba zamu zauna muna goga kafada dake a cikin gidan nan ba mu dafa mu baki kici ki ajiye kwano mu share guri ki zauna na iya lokacin da aka miki ma Allah ya bamu lada dan haka dolenki kiyi aiki in har kina son zaman lafiya damu koda yake ma bata bakina nakeyi saboda na manta da kin rigada kin zama yar kanki kiyi duk yanda yayi miki Umaimah babu wanda zesake tilasta ki akan kiyi daidai amma kin sani matuqar kika qi ji ba zaki qi gani ba kuma kinji abinda Mahaifinki duk ya fada se ki zaba zama lafiya kibi abinda yace ko ki fara neman wani gidan uban da zakije kici gaba da yanda kika ga dama" Mama ta fada cikin fushi ita dai Umaimah kanta na qasa in banda hawaye babu abinda takeyi.

Shiru sukayi na kusan Minti goma babu wanda ya sake cewa komai se Abban ya yunqura ze tashi Mama da Antyn suka miqe a tare suma dan taimaka masa ganin Anty tafi kusa dashi yasa Maman ta tsaya ita kuma ta kamashi suka shige cikin dakin
"Idan baqin cikin ki ya kashe shi se ki zuba ruwa a qasa kisha" Mama ta sake cewa kafin ta juya ta fice daga falon ta barta tana kuka da tunanin ita me tayi kuma da za'ace baqin cikinta ze kashe Abba? Haka taja qafafunta da suka sake yin tsami saboda zama ta fita daga, a bakin qofa sukaci karo da Sharifa zata shiga da Flask qarami a hannunta ta kalli Umaiman tayi tsaki qasa qasa tace
"Wlh mutum ya kashe mana Uba ba yarda zamuyi ba se munyi shari'a dashi" tayi gaba a hasale Umaiman ta fincikota baya tareda watsa mata maridukda ba wai taji abinda ta fada bane saboda ta sauke fushin su da take cike dashi tace
"Dan uwarki ni sa'arkice da zaki mun qunquni?"

Kuka Sharifan ta fasa, Nuratu data taho da Kwanuka tayi saurin direwa a qasa ta fincike hannun Umaiman data shaqe Sharifan tana cewa
"Karki sake gigin taba lafiyar wani daga cikinsu"
"Ke kuma ina ruwanki ai ban saka ki a ciki ba balle ki shiga" ta sake zaburowa Nuratun seta daga mata hannu tace
"Karki kuskura kice zaki zageni dan nima kinsan ba sa'arki bace ba, kuma iskancin da kika sabayi a baya muna daga miki qafa yanzu kinyi kadan wlh duk wanda kika nemi ki taka se ya mayar miki da raddi dan haka ki kama tsumman rayuwarki kija sauran mutunchin daya rage miki, mtsww" taja tsaki ta dauki kwanon data ajiye tayi cikin falon Sharifa ta faki idon Umaimah tayi mata gwalo kafin tabi bayan Nuratu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login