Showing 282001 words to 285000 words out of 429394 words

Chapter 95 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1028

ace ya makara be samu yinta a cikin Jam'i ba tofa kafin gari ya gama haske yayi amma yau shine har takwas saura yana baccin da besan lokacin daya kwashe shi ba. Saboda yanda jikinsa yake a mace seda ya watsa ruwan sanyi kafin yayi alwalar ya fito. Ya dade yana istigfari bayan ya idar kafin yayi Azkar dinsa ya gama komai ya sake komawa bandakin. Wanka yayi sosai ya fito dan takwas ta wuce idan beyi da gaske ba ze makara fita aiki. Yana shiryawa ta fado masa a rai, seya ajiye body spray din da yake fesawa ya zura kayansa da sauri ya fita daga dakin.

A bakin qofarta suka hadu da Ruqayya ta fito da Tray a hannunta da alama abinci ta kai mata tana ganinsa ta rusuna har qasa ta gaidashi ya amsa yana shiga ciki da sallama. A tsaye ya tarar da ita tana saka hula akanta, kallo daya Umaiman tayi masa ta dauke kanta tareda qarasawa kan carpet ta zauna inda Ruqayya ta ajiye mata kayan abincin. Jikinsa har rawa yakeyi ya qara sa inda take ya durqusa a gabanta hannu biyu ya saka ya kamo hannayenta da yatsun suka kumbure yana kallon fuskarta yace
"Har yanzu kumburin be sace ba?"

Banza tayi masa ta kwace hannunta ta shiga zuba Kununta a Cup.
"Jiya nazo nayita bugawa kuma nasan idonki biyu dan baki dade da shigowa ba sannan amma kikaqi ki bude mun me yasa?" Ya sake jefa mata wata tambayar, yanda yayi maganar a sanyaye cikin kulawa yasa ta kalleshita mayar da kanta taci gaba da abinda takeyi, se kuma me ta tuna ta kalleshi tace
"Banji ba, nayi bacci lokaci, ina kwana?" Ta fada cikin sanyin murya,seya zauna dakyau yana amsa gaisuwar tata kafin yaci gaba da cewa
"Ki shirya idan kin gama se mu koma Asibitin"
"Ni bazanje ba, ba jiya kagama cewa rayuwata bata gabanka ba kona mutu ko na rayu duk matsalata ce kai baka da Asara wata zaka auro" ta fada cikin qunquni tana kallon cikin idonsa. Kansa yaji ya sara masa har seda ya dafe kan kafin ya kalleta shima yace
"Kiyi haquri bana nufin duk abinda na fada miki jiya ba har zuciyata bane kawai raina ne ya baci kinji kiyi haquri".

Baki ta sako galala tana kallonsa mamaki da Al'ajabi ya cikata da jin abinda yake fada, dagaske yakeyi jiyan ba har zuci yayi maganar ba ko kuwa aikin Malamin ne yaci a dare daya har Khalil din ya dawo qarqashin ikonta? Ta tambayi kanta, bata sake tsinkewa da Mamaki ba seda ya miqe yana ce mata
"Kici abincin ina jiranki muje Asibitin yanzu dan bana son wani abu da ze taba lafiyarki kin sani" ya sumbaci hannunta tareda furta mata kalmar
"I love you" da rabon da tajita a bakinsa tun randa ta rusa mata Kwangila.

Haka ta takashi da ido kamar somuwa har ya fice daga dakin kafin ta miqe da dauri ta dauki wayarta ta shiga kiran layin Safina.
"Umaimah jarabarki bata qarewa yanzu meya faru da safiyar nan zaki fara doko mun kira?" Safinan ta fada cikin muryar bacci da alama kiran Umaiman ne ya tasheta.
"Ke dallah sauraramun malama kira nayi ki in baki feedback, ni ban gane ba daman aikin Malam din nan take yake ci ne ko kuwa naga daga farawa jiya har yanzu yazo yana bani haquri akan abinda ya faru"

"Aa to ke da me kika dauka? Sha yanzu magani yanzu ake gaya miki aikin Malam tamkar yankan wuqa ne ga kuma lasting da ba kin tsaya kina ta wani kokonton banza ba yanzu ai gashi a qasa da awa ashirin da hudu kin tabbatar da abinda nake gaya miki, seki turo mun da kudadena Malama kuma harda qari akai tunda aiki yaci" Safina ta fada. Umaimah na niyyar sake magana aka kwankwaso qofar dakin dan haka tace mata
"Bari zan kiraki anjima dai" tana fadar haka ta kashe.
Ruqayya ce ta shigo da dumamen tuwon da tace ta kawo mata ta ajiye har zata juya ta tsaida ita. Jakarta tace ta miqo mata, dubu goma ta qirga ta bata bayan ta sake jaddada mata ta siyo mata kan Tinkiya ba Rago ba kuma kar a fasashi kamar dai yanda Malam ya gaya mata ta karbi kudin ta fita a ranta tana mamakin me Umaiman zatayi da Kan Tinkiya ita da ba cin naman kai takeyi ba ko dafawa sukayi qarqari tasha romon amma abun me ciki ta yuwu kwadayinsa ne ya taso mata kuma bata son wanda suke dashi a gidan se Sabo ita dai ta wuce ta qarasa soya Dankali da kwai ta shiryawa Khalil akan Dining kafin ta tafi aiken Umaiman da zummar idan ta dawo ta karya.

Khalil kuwa yana komawa sama a falo ya zauna saboda wani ciwon kai dayaji ya taso masa wanda ya kasa gane na menene. Gaba daya jikinsa ya mutu haka yayi masa nauyi, yana zaunen ji yake kamar bacci ze daukeshi seda yayi da gaske yana karanto Addu'oi kafin ya iya miqewa ya shiga dakinsa ya qarasa shiryawa. Wayarsa dake kan mudubi ya dauka ya bude,Missed call daya ya gani na Humaira se saqon barka da safiya da take tura masa kullum tareda qorafin beje ba jiya kuma be kirata ba.

Danna kiran layin nata yayi gabansa ya yanke ya fadi yanda kasan wanda yayi karo da wani mugun abu haka zuciyarsa ta shiga bugawa harta daga ya yanke kiran ya zauna yana jera ajiyar zuciya se kace wanda yayi tsere, yana kallo ta biyo kiran amma ya kasa dagawa, gaba daya ya gaza fuskantar abinda yake ji a jikinsa da ruhinsa gaba daya, ya kasa ma yin wani tunani me amfani Umaimah kadai ke fado masa a rai duk sanda yayi niyyar raya wani abu a zuciyar tasa. Yana nan zaune Humairan tayi masa kira uku amma ya gaza dagawa, dakyar ya iya daukar wayar ya tura mata saqo akan ze kirata yana wani abu, yana tafiya kuwa ya goge saqon ya saka wayar a Silent ya jefata a aljihu sannan ya fita daga dakin kamar wani mara gaskiya ya sauka qasan.

Kadan ya ci Dankalin ya shanye shayin daya hada ya miqe ya tafi dakinta. Tana kwance akan gado tana danna waya ya shiga, a gefen kanta ya tsaya yana cewa
"Ya naga kin kwanta kuma?"
"Ni kayi tafiyarka kawai lafiyata qalau na gaya maka yanayi ne kawai kuma ma naje Asibitin da kaina jiya sunce babu komai" ta fada tana yamutsa fuska, kallonta yayi kamar meson tabbatar da abinda take fada kafin ya matsa yana cewa
"Shikenan, ni bari naje amma idan kinji wani abu fa ki kirani".
Da "Toh" ta amsashi taci gaba da danna wayarta, a gefen qafarta ya ajiye mata kudi da batasan ko nawa bane amma suna da yawa yace
"Gashi nan ko da abinda zaku siya, kiyi list zuwa gobe na abinda kike da buqata na haihuwa inaga ai watan ya shiga ko?"

Tashi zaune tayi tana kallonsa da mamaki kafin cikin izgilanci tace
"Ai na zata baka san da cikin ba da har zuwa yanzu baka ce komai akan tanadin zuwansa ba"
"Se na dawo" ya fada tareda juyawa ya bar mata dakin ba tareda ya maida hankali akan abinda ta fada ba. Shidai haka nan yau ya tashi dason kyautata mata dan haka baze tsaya sa'insa da ita ba balle har ta kaisu ga bacin rai. Motarsa ya hau ya fice bayan Sammani ya bude masa Get ko bangaren Hajiya be tuna shiga ba abinda be taba tsallewa ba tunda suka dawo zama gida daya da ita. Duk Asubar duniya idan ya dawo daga Masallaci bangarenta yake fara shiga ya gaisheta sannan idan ze fita aiki se ya shiga ya mata sallama tayi masa Addu'a da fatan Alkhairi haka idan ya dawo seya fara shiga ya sanar mata daya dawo kafin ya shiga gidansa duk ranar da haka bata faruba kuwa dayan biyu sedai idan ba'a gidan ya kwana ba ko kuma ita Hajiyar ce bata nan to wannan ze kirata a waya su gaisa se gashi yau ya rasa tunanin daya dauke masa hankali har ya kasa shiga ya gaida mahaifiyarsa.

Daya isa office dinma kai tsaye ayyuka ya shiga dan jiya kwatakwata be samu ya shiga ba. Seda suka tafi sallar Azahar yaga Missed call din Hajiya ta kirashi sau biyu da na Humaira daya, ya dafe kai yana salati shi kam yau meya same shi haka ne kamar wanda ya gamu da cutar mantau. Kiran Hajiyar yayi suka gaisa tana cewa
"Babana lafiya yau banganka ba ina fatan dai ba damuwar jiya ka saka a ranka harta haifar maka da ciwo ba ko?"

"Aa Hajiya lafiya qalau wlh yau makara nayi ban fita sallar Asuba ba shiyasa kika ga ban shigo ba kuma na tashi na fita a gaggauce munyi baqi suna jirana se yanzu muka sallame su shine naga Kiranki ma" ya shatowa Hajiyar qarya dan be san me zece mata daya hanashi shiga ya gaidata ba.
"Toh ai shikenan dan har hankalina ya tashi danaga har goma babu motsinka kuma yara sun shiga sunyita bugu ba'a bude ba se yanzu Ruqayyan ta shigo take cewa Maman tasu bacci takeyi kai kuma ka fita tun safe sannan hankalina ya kwanta daman ita kwana biyu ta dena shigo mana ballantana yanzu da ka sake shafa mana baqin fenti a gurinta amma babu damuwa kayi aikinka Allah ya taimaka idan ka taso se muyi magana dan dazu Kawunku yazo kuma daga nan yace zeje can gidan Hajiya Hauwa ne saboda ta hadasu da Maza da zasuyi magana dasu ba'ayita magana da Mace ba" Hajiya ta fada, seya shafa kansa kamar yana gabanta yace

"Toh Hajiya duk yanda kukayi ai daidai ne, ita kuma batajin dadi ne. Bakiga yanda duk ta kumbura ba kuma nayi nayi da ita muje Asibiti taqi wai lafiyarta qalau"
"Toh subhanallahi Allah ya bata lafiya amma dai ya kamata ta daure kuje din dan kumburin idan yayi yawa bashi da dadi gara a gane koma menene sikarsa tunda wuri a magance. Shi yasa nace ka ringa binta a sannu da maganar auran nan saboda yanayin da take ciki Allah dai ya raba lafiya" Hajiya ta sake fada aga nan sukayi sallama ya kashe wayar.

Zancen Hajiya Hauwa da tayi yasa ya tuna da Humairan ma dan shaf kamar an shafe masa ita daga tunaninsa gaba daya. Office dinsa ya koma ya zauna, a maimakon ya kira Humairan seya danna number Umaimah. Seda wayar ta katse ya sake kira shima kiran na dab da katsewa kafin ta daga murya can qasa kamar me bacci.
"Bacci kikeyi na tasheki ko?" Ya tambayeta a sanyaye, cike da Izza kamar wata basarakiya tace masa
"Bacci nakeyi, kuma dakyar na samu ya daukeni gashi yanzu ka tadani".
"Allah ya baki haquri ki kwanta kiyi baccinki, idan kuma yaqi sake daukanki ki kirani se nazo na lallabaki kiyi kinji" ya fada jikinsa har yana rawar daya rasa dalilinta.

Qaramin tsaji taja kafin tace
"Nidai ka katse mun baccina haka kawai me zanyi maka toh?"
"Babu komai kawai so nakeyi naji ya kike, sannan Yara sun shigo qofa a kulle idan kin tashi se ki kirawo su ko na zatama kin shiga kun gaisa da Hajiya ai" yanda yake maganar kamar wani me tsoronta ko tsoron fadar wani abu daze bata mata rai, baki ta tabe kamar yana ganinta tace
"Idan na tashi naji daidai zan shiga ai kasan bana jin dadi dai" se yayi saurin cewa
"Na sani, to kiyi kwanciyarki ki huta idan na dawo se mu shiga tare kawai ba se kinje ba".
Sallama sukayi ya ajiye wayar yana sauke numfashi, shi dakansa yasan abinda yakeji is unusual, wata muguwar shakkar Umaiman yakeji da ya rasa ta mecece. Humaira ce ta fado masa a rai seya dauki wayar ya kirata dukda yanda zuciyarsa ke qoqarin hanshi tana nuna masa ran Umaimah fa ze baci idan ta gano yayi waya da wata. Seda wayar ta kusa tsinkewa kafin ta daga wayar da sallama ya amsa se tayi shiru
"Fushi kikayi" ya fada a sanyaye, shiru tayi batace masa komai ba seya gyara zamansa yana sake yin qasa da murya yace
"Haba qanwata yanzu fushi kikeyi da yayan naki ba zakiyi mun uzuri ba bayan kinsan aiki nakeyi tuquru saboda in tara kudin auranki?"

Bata amsa shi ba dan haka ya sake cewa
"Haba mana Umaimah ta kiyimun magana naji muryarki ko zuciyata zatayi sanyi kinji Autar Mata" kamar tana jira se ji yayi ta fashe masa da kuka harda shashsheqa,a rikice ya miqe daga kujerar da yake zaune ya shiga zaga office din yana salati tareda tambayarta abinda ya faru me ya sakata kuka.
"Ni daman nasan ba sona kakeyi ba shiyasa ma tun jiya kake tayi mun wulaqanci na kiraka kaqi dauka duk message din dana tura maka babu reply sannan yanzu saboda ka nunamun ka fi son matarka bana gabanka harma manta sunana kayi kake kirana da nata" Humairan ta fada dakyar tana kuka.

Dafe bakinsa yayi jin abinda ta fada, yaushe akayi haka ya kirata da Umaimah shi wallahi be sani ba bema yarda ya fada ba amma yasan idan yace ze tsaya kare kansa rigimar ba qarewa zatayi ba dan Huamira yar daruce itama idan ta murde dan haka cikin rarrashi yace mata
"Kiyi haquri wallahi idan ma na fada banyi dan na bata miki rai ba, yanzu muka gama magana da ita a waya inaga shiyasa sunan yazo bakina ban sani ba kiyi haquri kinji Shatuna ki yafewa Yayanki kuma ni ba ina sane duk naqi daukar wayarki ba akasi aka samu amma kiyi haquri".

A maimakon tayi shiru sema qarawa kukanta amo tayi tana cewa
"Oh daman da ita kake waya nayita kiranka kanaji baka amsa ba ai dai ko second biyar ne seka dauka a gunta kace mun zaka kirani aidai zansan ka damu dani ba kayita share mun waya ba tunda dai naga nima din matarka zan zama"
"Humairah kishi, toh kiyi haquri bazan sake ba daga yau koda qa nake qaya indai ba Hajiya bace zan dauki excuse na amsa wayarki shikenan?" ya fada cikin lallashi da mamakin yanda take magana yau, rage kukan tayi nan ya shiga aikin rarrashi, besan adadin lokacin daya kwashe ba seda Anwar ya shigo office din yana gaya masa lokacin shigarsu Meeting yayi sannan ya ankare da a qalla sunfi awa daya suna waya. Sallama sukayi bayan da yayi mata Alqawarin daya tashi ze biya ya ganta saboda ya qara wanke laifinsa sannan ta haqura ya kashe wayar.

"Kai Subhanallahi" ya fada yana dafe kansa, shikenan idan wannan ta garo shi ta nan se waccen ta bugo shi ta nan kenan to Allah ya bashi wuyan dauka.

UMAIMAH
Suna gama waya da Khalil ta miqe daga kan gadon ganin daya ta gota, seda tayi sallah kafin ta fita zuwa kitchen. A Freezer taga saqon da aka siyo mata gashi nan kan guda ba'a fada ba ta ciro ta ajiye shi cikin sink tana toshe hanci saboda qarnin da ya fara hawar mata kai. Safina ta kira ta sake tambayarta yanda zata dafashi ta gaya mata seta wuce dakinda Ruqayya take ta sameta ta idar da Sallah tana lazumi.

"Idan kin gama ki sake wanke kan can ki dora ki hadashi duk yanda kikeyi idan ya kusa dafuwa se ki gaya mun amma fa kar a fasashi na gaya miki"
"Toh Hajiya sedai sun zazzage kwakwalwar a can ban sani ba ko anyi laifi?" Ruqayyan ta fada se tayi gaba tana cewa
"Babu damuwa ki hadashi yanda nace.
Haka kuwa akayi tsaf Ruqayyan ta hada Kan a qatuwar tukunya tana yi tana mitar meye dalilin da za'a dafa kai sukutum se kace na tsafi danma pressure pot din tasu nada girma ta dauke shi, seda ya dakko dafuwa kamar yanda ta buqata taje ta sanar mata.

"Ki wanke mun bandaki amma kar ki saka Hypo bana son warinsa" ta fada tana miqewa Ruqayya ta bita da kallo, ta rasa gane alqiblar uwar dakin nata. Dazu data gyara dakin ita tace ta bar bandakin karta wanke yanzu kuma tanaso a wanke kai wannan yarinya dai kamar me juju haka ta shiga aikin tana mita ita kuma ta wuce kitchen din. Tsaf ta barbade naman da garin maganin da Malam ya bata, ta debi romon ta dandana seda ta hadiye kuma ta zaro ido
"Kema zaki iya ci" kalaman malam suka dawo mata se sannan ta samu nutsuwa harta hadiye yawun data fara tattarowa dukda romon ya rigada ya shiga cikinta. Mayar da murfin tayi ta rufe ta koma palour ta zauna. Saboda ita ta saka kanta zama tayi har naman yayi laushi sosai lokacin Ruqayya ta gama tace ta farfasashi a raba a zubawa kowa nasa harda su Hajiya da Sammani. Ba sabon abu bane dan haka Ruqayyan bata kawo komai a ranta ba tayi yanda tace ta zubawa kowa. Umaiman da kanta ta dauki na Hajiya ta saka Hijabi ta fita dashi, Ruqayya kuwa Buredi ta dauka ta zauna taci abunta tana dangwalar romo, ta huta da tunanin me zataci da rana kafin a dora girkin dare dukda ba wani abu zatayi da daren bama doya kawai zata soyawa Oga yaci da Romon kan tunda an ajiye masa.

Da sallama ta shiga falon Hajiyar, seda tayi qoqari ta daidaita fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna akan kujera Khalifa dake aiki a Laptop dinsa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa Hajiya yace tana kitchen sega Hajiyar ta fito Umaiman ta zame qasa ta shiga gaidata ba tareda ta bari sun hada ido da Hajiyar ba.

"Sannu Umaimah" Hajiya ta fada tana zama kafin taci gaba da cewa
"Dazu yake gayamun bakya jin dadi ai ban dauka kumburin yakai haka ba kuma kike zaune ba zakuje Asibiti ba haka ai be kamata ba gaskiya idan ya dawo kuje kiga likita asan abinda yake damunki".

"Munafuka se kace ta damu dani" Umaiman ta fada a zuciyarta a fili kuwa ta qara rausayar da kai tace
"Ai jiya naje Hajiya sun dubani sunce babu komai kawai na ringa motsa jiki sosai" seta tura mata Flask din Naman tana cewa
"Gashi Hajiya sha'awar Naman kai nayi shine na dafa daku".

Hajiya taja flask ta bude qamshi ya cika falon tace
"Madallah mun gode Allah yayi Albarka, aida baki wahalar da kanki ba kinyo waya ko Khalifa se yazo ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login