Showing 258001 words to 261000 words out of 429394 words

Chapter 87 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1026

hira dasu ta qara gogewa ta san Halayyar Maza da yawa. Wannan maganar ce ta sakata ce masa
"Eh to zan gaya maka gaskiya dai Saurayina ne kuma shi nake so na aura, amma daman ina so na qarayin wasu Samarin nima dan qawayena duk ba saurayi daya ne dasu ba"
Yanda take ke maganar zaka gane zallar yarinta a tattare da ita, kafin yayi magana taci gaba da cewa
"Kuma dan uwan naka indai dan gayune irinka toh ina sonsa amma fa a Aboki ba saurayi ba dan ni inada wanda zan aura".

"Ikon Allah" ya fada a ransa a fili kuwa ya kalleta yace
"Toh ai shi gaskiya da aure yake sonki kinga babu dama kuma kice sedai kuyi abota, sannan wa ya ce miki ma Mace da Namiji suna Abota ne?"
"Sunayi mana a school ina da Abokanai yan class dinmu sannan Friends dina ma bayan yan class dinmu suna da wasu Abokanan a waje kuma manya ne ma ba kamar mu ba" ta sake bashi amsa Innocently se yayi murmushi yace
"Yan class dinku wadannan class mates ne karatu ne ya hadaku bayan haka babu wata alaqa ta Abota da za'ace tsakanin Mace da Namiji se ta soyayya, idan kinyarda zaki bashi dama ya gwada miki tashi soyayyar toh sena hada ku".

Shiru tayi tana tunanin maganarsa se taji yace
"Zan bashi number wayarki, sati daya kacal ze gwada Sa'a idan har kika fara sonsa shikenan idan kuma sati ya cika baki fada sonsa ba ze haqura kin yarda?"

Haka kawai ta kasa musa masa, na farko cewar da yayi Abokinsa ne tasan Dan gayune irinsa ita kuma tana son Namiji me gayu shiyasa take qara son Noor dinta abu na biyu kuma itama tana so ta gwada Double dating kamar yanda qawayenta suke ta kwadaita mata dan haka ta amince ba tareda bata lokaci ba.
"Bari na baki number sa kiyi saving dan karya kira baki san waye ba kiqi dagawa" ya sake fada yana ciro wayarsa. Number ya karanta mata tayo saving kamar yanda yace, Abokin Yah Khalil ta saka saboda tafi ganewa. Yanzun ma daya maida ta be shiga ba yace ta gaida Maman ya bata ledojin Abincin daya siyo kafin ya kama hanyar gida.

Yana zuwa ya tarar da Umaimah na murqususun ciwon Mara, ko zama beyi ba suka sake juyawa Asibiti. A can ya barta ya dawo gida dan yayi wanka saboda sunce zata dan kwanta ta huta zuwa yamma kafin a sallameta.
Already ya sanarwa da Anwar baze je office ba ranar shiyasa yanayin wankan ya samu abinci yaci ya haye gado dan yayi baccin da be samu yayi da Safe ba kafin ya koma Asibiti.

Qaramar wayarsa ya dakko ya kunna, ba kasafai ya fiya amfani da ita ba number Layin da yake kanta ya bawa Humairan a matsayin number Abokinsa, seya dakko dayar wayarsa ya kwafi number ta ya saka akai kafin ya dannan mata kira.

HUMAIRAH
Tana shiga bayan ta gama bawa Mama labarin Jarabawa ta dora mata dana Abokin Khalil daya bata number sa. Mama tace
"Ikon Allah, nifa nace zaryar nan ta Khalil da walakin, harna fara tunanin ko Dan uwansa Khalifa yakeyiwa kamu kinji ashe wani Abokinsa ne. Nayiwa Mansur zancen nasan baze gaza sanin waye ba, me yace miki sunan Abokin?"
"Tab ya manta be fadamun ba nima kuma ban tambayeshi ba kawai da Abokinsa nayi saving number" Humairan ta bata amsa se Maman ta sake cewa
"Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi, se ki nutsu idan ya kiraki kar kiyi masa maganar yarintar da kuka saba da Nura, kinga dai shi da hankalinsa dukda ban ganshi ba nasan Khalil baze hada ki da mutumin banza ba".

Tura baki tayi gaba tace
"Nifa cewa yayi sati daya kawai idan ban fara son Mutumin ba shikenan kuma kema kinsan inada wanda nake so kawai dan kar Yah Khalil din yaga na masa rashin kunya ne shi yasa na yarda". Se Maman ta kama baki tace

"Eh ai ni gashi kina mun rashin kunyar, ke ni na dawo daga rakiyar wannan alaqar taku da bata da Alqibla, Addu'ata kawai Allah ya zaba miki Miji na gari da ze rungumeki ya kula da ke ko bayan raina na samu nutsuwa nasan bazakiyi kukan maraici ba. Dan haka kema kiyi ta addu'a kawai lokaci da yawa abinda kake nacin So bashine Alkhairi a gareka ba".

Ita dai jin Maman kawai take amma ta tabbata babu wani Alkhairi a rayuwarta daya wuce Noor, shiyasanta yake kuma Sonta tun bata san kanta ba ta tabbatar kuma ze tarairayeta ya riqeta Amana kamar yanda Maman take mata fata. Bacci ta kwanta, a cikin baccin taji qarar wayarta tana farkawa taga Abokin Khalil ne yake kira. Kafin ta daga wayar ta katse se ga wani kiran ya sake shigowa dan haka ta miqe zaune tana goge ido kafin ta amsa wayar da Sallama tana tattaro dukkan Nutsuwarta kamar yanda Mama tace ta nutsu.

KHALIL
Yanajin ta amsa wayar tayi sallama gaba daya seya duburburce ya rasa abinda zece mata, meyasa kai tsaye be gaya mata shine ba yanzu idan ta gane muryarsa ai girmansa ya fadi zataga yayi mata qarya ne daya sani kai tsaye kawai ya fada mata shine ba wani Abokinsa ba. Sallamarta data sake ratsa kunnensa ya sakashi tattaro nutsuwarsa gaba daya ya amsa mata da dakakkiyar murya se sukayi shiru gana dayansu kafin ta shiga gaishe shi.

Maganar Minti goma sukayi, ya sanar mata da sunansa Ibrahim kuma shi dan Kano ne yana da Mata daya da yara biyu, Jim tayi kafin ta amsa masa dukda daman tasan da wuya ace Abokin nasa ya zama saurayi amma daya fada mata cewar yana da matar taji wani iri to wai ma meya shafeta ko mata dari ne dashi?
Itama a taqaice ta gaya masa Sunanta Aisha shikenan tayi shiru, ya tambayeta mutanen gida da kuma yaushe ya kamat yazo suga juna kafin magana tayi nisa a tsakaninsu se tayi shiru bata ce masa komai ba.
"Naji kinyi shiru Aish, koda akwai matsala ne?" Ya fada jin bata amsashi ba. Gabanta ya fadi, tunda suka fara magana daman muryarsa take mata wani iri, kodan ta sakawa ranta ne taji kamar Muryar Khalil din oho amma maganar da yayi yanzu ta sake jin muryar tankar ta Khalil din seta bude baki a hankali tace

"Ai munyi magana da Yah Khalil be gaya maka ba?"
"Be gaya mun komai ba, kawai ya turomun da number yace nakiraki shikenan" ya bata amsa.
"Toh ka tambayeshi kaji ze gaya mata yanda mukayi" ta sake fada masa se yayi murmushi yace
"Aa, ai Khalil ya fita daga cikin Maganar mu yanzu ni dakene, ki fada mun komai kanki tsaye karkiji nauyin komai kinji".

Dan Jim tayi kafin tace
"Daman na gayawa Yah Khalil ina da saurayi, sedai kawai in kana so mu zama Abokai se yace Aa, wai na baka 1 week ka gwada Sa'arka, idan kafin satin daya ban fara sonka ba shikenan" tayi shiru

"Idan kuma kika fara so nafa?" Ya tambayeta cikin sigar wasa se ta yi murmushi ba tareda tace komai ba ya sake ce mata
"Hakan ma nagode ni kuma na tabbatar miki kafin cikar wannan wa'adin sena kafa gwamnati na a zuciyarki tunda ina sonki zan kuma yi duk yanda zanyi kema ki soni. Ki saka a ranki kawai kin zama tawa dan satin nan yana cika tofa babu wata sauran magana se kawai na turo iyayena ayi maganar auranmu ba kuma nason ya wuce wata daya kin zama matata".

Shiru kawai tayi tana jin ikon Allah ji wani azarbabi to taji ta gani ai ita dai tasan ba zata taba son wani bayan Noor ba kawai dai zata bata masa lokaci nr sati yacika ya kama gabansa da haka sukayi sallama akan ze sake kiranta.

Wasa wasa a hankali cikin kwana biyu wata irin shaquwa ta shiga tsakaninsu. Rashin lafiyar da Umaimah takeyi ta sake bashi damar samun lokaci da Humairan dan ta koma dakinta na qasa gaba daya bata hawa saman sedai shi ya sauka ya sameta shiyasa ya samu guri yake baje kolin soyayyarsa da yar yarinyar da a hankali ya fuskanci bata san komai ba. Soyayyar da take iqirarin tana yiwa Noor din soyayya ce ta yarinta kawai dan haka yayi amfani da wannan damar ya cusa mata sonsa a ranta ba tareda ta sani ba. Kullum sukanyi waya sau uku sau hudu ko be kirata na zata kirashi ita, Chat kuwa duk sanda ya bude ze tarar da saqonta dukda maganar tasu rabi duk shirmen yarintarta ne wanda yake masa dadi sosai.

Ranar da suka cika kwana shida da yarjejeniya da daddare yana kwance a Falonsa suna waya yake ce mata
"Kinga Gobe wa'adin da kika dibar mun ze cika, dan haka ya kamata ki fada mun sakamakona idan har naci nasara a goben zan bayyana miki kaina, idan kuma banyi nasara ba se in ce miki Allah ya hadamu da Alkhairi, idan mun hadu a Aljanna na gaya miki nine Ibrahim".

Humaira da shaf ta shagala ta manta da wani zancen Yarjejeniya a tsakaninsu, tana zaune a kusada Mama suke wayar seta tashi dan bata so taji abinda zata fada masa. Daman tunda ta fahimci yawan maganar da sukeyi da Ibrahim din take mata tsiya. Noor kansa yanzu ba wani bashi lokaci take kamar da ba da yawanci ita take nacin kiransa ko tace yazo yanzu da ta samu wani yasa idan ya kirata mara ba idan be kira ba shikenan ita da kanta ta gane banbancin soyayyar yarintar da ake ta fahimtar dacita data babban mutum.

Ita da Noor ko yaya tayi masa abu ya ringa fada da Masifa kenan se tayi ta bashi haquri amma Ibrahim ko lallabata yake kamar kwai baya son bacin ranta ko kadan. Ko waya suke yaji muryarta wani iri ya ringa tambayar meya sameta ko me take so kenan ita kuma daman tana son ayita lelenta seta shagwabe tayi ta masa sangarta yana biye mata abinda bata samu a gurin Noor.

Seda ta kwanta akan Gadonta kafin ta bashi amsa da cewa
"Toh ai da sauran lokaci har zuwa gobe, sannan nima bazan fadi maka sakamakon ba se na ganka ido da ido wannan ne qarashen cin jarabawar dan bazanyi cinikin biri a sama ba. Kai ka sanni kasan komai a kaina amma ni sunanka kawai na sani ko Yaya Khalil dana tambaya hotonka cewa yayi kace karya nuna mun. Toh gobe kazo na ganka sannan se na yanke hukunci".

Murmushi yayi a ransa yana cewa " Ashe tana da wayo" a fili kuwa yace mata
"Shikenan, amma ina so kiyi mun wani alqawari, koda ace kin ganni in har a zuciyarki da farko kin yarda da soyayyata karki canza"

"Ban gane ba?"
"Ina nufin idan kika ganni karkice saboda matsayina a gurinki zaki qini, in har dagaske kin kamu da sona karki bari wani abu ya canza miki ra'ayi..." Maganar ce ta maqale saboda ganin Umaimah da yayi tsaye akansa. Yayi nisa cikin shauqin soyayya da sam beji zuwanta ba. Kashe wayar yayi ya miqe zaune yana kallonta. Duk wata dakiya da Mazantaka dayasan yana dasu seda ya tattaro ya yafa dukda yanda zuciyarsa take bugawa da irin kallon da take jifansa dashi amma haka ya dake, dakyar ya iya bude baki yace mata

"Wani abun kike buqata, me yasa baki kirani a waya nazo dakaina ba kika hawo bene bayan likita ya hanaki?"

"Kira nawa zanyi maka Munafuki? Gara da baka daga ba ai saboda Allah naso na yana so nazo na tarar da cin Amanar da kakeyi mun yasa shiyasa baka dauki wayar ba. To wallahi ka dauka yanda kake iqirarin ta fada soyayyarka ka dauka cewa ta fada a ramin masifa da bala'i ne dan koma wacece kake magana da ita senaga bayanta wallahi" Umaimah ta fada tana huce kamar wadda ta hadiyi Maciji.

Wani kallo ya watsa mata kafin ya miqe tsaye yana kallonta shima yace.....
"Kin san yanda kika huda zuciyata ba tareda sallama ba kika shiga? Toh haka tayi mun. Ki saka a ranki keda ita matsayinku daya a zuciyata kuma ki saka ran shigowarta cikin gidan nan bada dadewa ba" yana gama fadar haka ya wuce ya bar Umaimah da mamaki ya sa ta kasa rufe bakinta. Seda ya shige daki kafin ta dawo hayyacinta babu bata lokaci tabi bayansa tana cewa
"Wallahi baka isa ba Khalil qarya kakeyi babu wata mace da zaka iya so bayan ni ballantana har ka kawota cikin gidanka, duk kuwa wadda tayi kuskuren shiga rayuwarka ta fara qirga kwanakin da suka rage mata a duniya"
'Bam' ya bugo qofar dakinsa ya rufe daidai ta tura kai zata shiga har seda ya bugeta. Ihu ta fasa ta shiga buga qofar da qarfin gaske tana zage zage amma ko Gezau Khalil dake cire kayan jikinsa beyi ba. Wanka ya shige dan fita ma yake so yayi daga gidan, gara yaje gurin Humairanshi ya ganta ko zeji sanyi a ransa Umaimah ko idan taga dama ta qona gidan saboda Masifa amma a wannan karon babu gudu babu ja da baya yaga matar aure.


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 60

"Wallahi baka isa ka fita daga gidan nan ba yau" Umaimah da tayi caraf ta riqe rigar Khalil ta fada. Kallonta yayi yanda ta birkice gaba daya kamar wadda ta shiga hauka shida yaji shiru ta dena bugun qofar ma ya zata sauka tayi ashe tana tsaye. Qoqarin zame rigarsa ya shigayi a hankali dan baya son abinda ze saka ya jajjigata saboda jikinta amma ina ita bata duba hakan ba sake cukuikuye shi takeyi tana zabga Masifa wanda shi bama gane abinda take fada yake ba. Ganin tana neman bata masa lokaci yasa ya daka mata tsaawar da ta saka ta sakinsa babu shiri taja baya, da hannu ya nunata yace

"Ki kiyaye ni Umaimah" se ya ja tsaki ya barta a tsaye, wayarsa da muqullin mota ya dauka ya fice, kafin ta sakko qasan se jin tashin motarsa tayi alamar ya bar gidan gaba daya ma. Bata damu da yana yin da take ciki ba ta fice zuwa bangaren Hajiya tana rusa kuka kamar wadda aka aikowa da saqon mutuwar Mama. Hajiya dake kishingide kan kujera bata jima da dawowa daga Asibiti ba jikine ya motsa mata daren jiya kwana tayi da ciwon kai seda taje aka ce hawan jininta ne ya tashi gama shan maganinta kenan tana hutawa Umaiman ta fado seda qirjin Hajiya ya buga ganin yana yinta ta tabbatar da ba lafiya ba.

A qasa ta zube tana kuka kamar ranta ze fita, Hajiya ta rude tambayarta take meya faru amma ta kasa bude baki tayi magana sema qara qaimi take gurin Kukan tana dafe kai da ciki ita dai Hajiya ganin ba zatayi magana ba ya sa ta wawuro wayarta ta shiga kiran Khalil.

Yana tafe tuqi yake cike da nishadi saboda zejr yaga rabin ransa. Kiran Hajiya ya shigo wayarsa ko ba'a fada ba yasan Umaimah ce dan haka ya amsa wayar ya saka a Speaker yaci gaba da tuqinsa. Muryar Hajiya yaji tana cewa
"Khalil lafiya? Me ya faru? Meya samu Umaimah take irin wannan kukan ko mutuwa aka mata?"

A tausashe ya kira sunan Hajiyar jin yanda take magana yasan hankalinta a tashe yake dan haka yace
"Hajiya, kinga dazun nan muka dawo daga Asibiti kuma sunce ki samu hutu karki bari wani abu ya dameki. Dan Allah ki tafi sama ki kwanta ki qyale Umaimah, babu abinda akayi mata, damuwarta ce ta motsa take so se ta dagawa kowa hankali ki rabu da ita kawai gani nan dawowa gidan nima na fita abu zanyi yanzu zan dawo ba dadewa zanyi ba. Dan Allah Hajiya karki biye mata ki shiga daki ki kwanta saboda jikinki".





"Amma Babana meya faru har haka kaga kaga irin kukan da takeyi kuwa...?" Hajiya ta sake fada se yayi saurin katseta ga kuka me hade da ihun da Umaiman takeyi ya dame shi yace
"Na sani Hajiya nidai ina roqonki karki damu kanki ki barta yanzu zan dawo koma menene zanji dashi"

"Shikenan, seka dawo din amma kayi sauri" ta fada kafin ya kashe wayar. Tagumi ta rafka tana kallon Umaiman dake rusa kuka duk ta hada zufa saboda masifa, Ajiyar zuciya tayi ta miqe sakyar tana kallonta tace
"Kiyi haquri kiyi shiru Khalil din yana hanya bari na shiga ciki idan yazo se naji abinda ya hadaku" tana gama fada ta wuce sama dakyar take takawa saboda kanta dam sara mata ga jiri haka ta ringa kama qarfen Benen harta haye.

Umaimah data tsayar da kukanta kamar anyi ruwan sama an dauke tabi Hajiyar da kallo baki sake saboda tsabar mamamkin abinda tayi mata.
"Bantan uban nan" ta fada a fili kafin ta yunqura ta miqe. Fita tayi ta koma part dinsu, a falon ta ringa safa da marwa tana lissafin abinda zatayi, wato hade mata kao zasuyi shida uwarsa, ke nan ma tasan da zancen auren da yake iqirarin zeyi? to wallahi ko sama da qasa zasu hade ba'a isa ayi mata abinda ake shirin yi ba, daga shi har Hajiyan daidai take dasu. Zabura tayi ta shige daki, Ruqayya dake goge goge tana satar kallonta a fili tace
"Allah ya kyauta' dan tunda aka fara rigimar tana jinsu har sanda Khalil din ya fita Umaiman ta bishi, da ace uwar dakin nata me fahimtace da tayi mata magana akan abubuwa da yawa da takeyi da basu dace ba. Ta girmi Umaimah nesa ba kusa ba da ta fita ilimin zaman duniya shiyasa take ganin baiken Umaimah akan irin abubuwan da takeyi.

Khalil
Yana fita daga gidan ya kira Humairah a zuwan Ibrahim akan gashi nan a hanya. Ce mata yayi tafiya ta kamashi yau da daddare dan haka baze iya jira har gobe ba kafin yaji amsarta ta tanadeshi kawai yana tafe. Suna gama wayar sega kiranta a dayan Layinsa, seda yayi dariya son ransa har kiran ya katse kafin ya bita. Haka take, duk sanda Ibrahim ya rikita qaramar kwakwalwarta seta kirashi neman mafaka yanzun ma tana dagawa tace
"Yah Khalil abokinka ne, wai kaji yanzu ze zo bayan kuma se gobe ne kwana bakwai din zata cika"
"Eh munyi magana dashi wani aikine ya taso masa ze tafi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login