Showing 336001 words to 339000 words out of 429394 words

Chapter 113 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1008

tunda tasha marin Abba ta durqushe bata sake dagowa ba saboda wani Azababben ciwon mara da kai da suka dirar mata lokaci daya.

"Shikenan, taje na saketa saki daya" Khalil ya fada kamar wanda ze fashe da kuka.

"Uku zaka mata ka yanke duk wata alaqa da take tsakanin ku yanzun nan" Mama ta sake fada,

"Hajiya dayan ma yayi ba se ya qara ba" Hajiyar su Khalil da tunda ta fadi bata sake magana ba ta fada

"Wallahi se ya qara Hajiya ko beyi uku ba se ya mata biyu" Mama ta sake kafewa dole Khalil ya sake qarawa Umaimah da tayi mutuwar zaune jin wannan Drama da ake tsarawa.

"Durun uwar nan, ka sake ni Khalil a maimakon ka saki wannan Yar iskar daka auro? To wallahi dani da kai da ita sedai duk ayi biyu babu" Umaimah ta fada tana miqewa, dukda azabar da take ji a jikinta da a kwayar idonta ma kana iya karantar halin da take ciki haka ta yunqura, kafin kowa ya ankara ta finciki wani flower vase da yake kusa da ita babu bata lokaci ta saukewa Khalil a daidai Mazantakarsa, ihu daya ya kwalla ya fadi wanwar a gurin.

"Shikenan ta kashe shi, Ta kashe Khalil dama ta fada gashi kuwa ta cika ku riqeta Salman Na rantse da Allah yanda kika salwantar da ransa Umaimah da hannuna zan miqawa Hukuma ke" Abba ya fada cikin tashin hankali yana Kallon yanda Salman da Khalifa suka rufu kan Khalil daya ke nan babu alamar rai a tattare dashi.
"Baya numfashi Abba" Salman daya kama tsinyiyar hannun Khalil ya duba a matsayinsa na Dalibin litanci ya fada, Mama ta fashe da kuka tana cewa
"Allah ya wadaran haihuwa irin taki Umaimah Allah ya wadaran zuciya gafalalliya irin taki ki shirya karbar hukunci daidai da abinda kika aikata dan wlh idan har kinyi sanadin ransa sekin biya diyyar sa da naki Alhaji ku kamashi muje Asibiti in Allah ya yardada sauran shan ruwansa a gaba.

Qoqarin Kamashi suka shigayi, Hajiya da Numfashinta ya tsaya na wasu daqiqu ta gagara yin komai kamar ma bata cikin duniyar gaba daya, kukan Humaira dake cikin tsananin tashin hankali kadai ake ji a falon, babu wanda ya lura da Umaimah da tun da Khalil ya fadi ta qame tamkar ruhinta ya bar gangar jikinta. Kunnuwanta sunyi mata Dummm, kwata kwata bata jin abinda suke cewa ma a gurin abu daya data ji shine Khalil ya mutu da suka fada, a hankali ta motsa bakinta da niyyar magana kamar jikinta na jira lokaci daya wani Azababben ciwo da zata iya alaqantashi da ciwon mutuwa ya dirar mata kafin kace me Jini ya balle mata ta tafi zata kifa Humaira datafi kusa da ita ta tareta suka sake tafiya gaba daya Kujera tayi musu birki, cikin kuka Umaiman ta kalli Mama tuni su Abba sunyi waje da Khalil Hajiya kuwa na nan inda take zaune ba uhm ba uhm
"Mama jini take zubarwa kinga kamar itama ta suma" Humairan ta fada tana kallon Umaimah da idanunta suke lumshewa suke budewa, tsananin azabar da takeji bazata misaltu ba ta gama saddaqarwa wannan shine radadin zarar rai da ake fadin baze misaltu ba, ta kalli Mama kamar yanda itama take kallonta da wani irin expression da baze fadu ba, hawaye masu tsananin quna suka ziraro mata, Humaira ta sake kai hannu zata riqeta ganin nauyinta ya tura kujerar tana nemanta fadi amma dukda halin da take ciki seda ta yunqura ta bige hannun Hunairan

"Ki rabu da ita ta mutu idan Allahya sota tayi shahada se ya zame mata kankarar zunuban data diba a rayuwarta Mama ta fada tana wani irin kuka kafin ta matsa inda Hajiya take tana cewa
"Tashi muje Hajiya Allah yana kallo baze dauke miki shi yanzu ba Alfarmar Annabi da alqur'ani"

"Subhanallahi Jini kuma" Abba daya dawo kiran su dan su tafi Asibitin ya fada tuni Salman da Khalifa sunyi gaba da Khalil, ya tabbatar daga Hajiyar Har Mama da shi kansa suna buqatar ganin likita shiyasa ya tsaya. Dukda zafinta da yakeji a sannan rashin imaninsa be kai yaga Mace a yanayin da take ciki ya kauda kai ba balle yarda ya haifa a cikinsa koda baya son halinta yana qaunarta a matsayin jininsa
"Na kashe Khalil Abba nima mutuwa zanyi" Umaimah ta fada kamar wadda take a gangara daidai Abban ya kamata, be kulata ba ya kalli Mama dake riqe da Hajiya yace

"Zo ki kamata mu tafi"
"Bazan iya tabaya ba Alhaji kar kuma ka sakani dole" Maman ta fada kafin ta juya ta fice daga falon tana kuka. A yanda takeji da da abinda ze kankare zamowar Umaimah yarta a yau da tayi.
Humairan dai da bata so ita ta kamawa Abba ita dakyar suka sakata a mota jikinsu yayi face face da jini baki dayansu. Ikon Allah ne kawai ya kaisu Asibitin dan Abban tuqi kawai yakeyiba danyasan abinda yake ba, suna isa aka karbeta kai tsaye suka shiga da ita Theatre Dr Al'amin kuwa kamar ze ari baki saboda Masifa babu Wanda ya tankashi to wama yake da lokacinsa a cikinsu kowa ta ishe shi, Hajiya ma gado suka bata, Mama dai Kukanta yaqi tsayawa Abban kansa kujera ya samu ya zauna saboda yanda yakeji ya tabbata idan yaci gaba da tsayuwa faduwa zeyi faduwar da baya zaton ze tashi da sassan jikinsa gaba daya.

Istigfari kawai yake a zuciyarsa, suna zaune kusan awa daya kafin Dr Tahir likitan daya karbi Khalil ya fito daga dakin da suka kwantar dashi Salman da Khalifa suka nufeshi da sauri cikin nutsuwa data bayyana har a muryarsa yace
"Alhamdulillahi yana raye kuma numfashinsa da bugun zuciyarsa sun daidaita, for now zamu kula dashi zuwa safiya whenhe is fully awake sannan zamuyi masa gwaje gwajendaya kamata, ku kwantar da hankalinku in Allahya yarda babu wata matsala".

A tare gaba dayansu suka saki ajiyar zuciya, Humaira dake can labe kamar mara galihu tana ta kuka ta kalli Khalifa daya dawo ya zauna tace
"Yaya Khalifa ka tambayeshi za'a iya ganinsa"
"Zaki iya Yata tashi kije ki ganshi Allah ya tashi kafadunsa" Abba ya fada dakyar yana kallonta seta miqe tabi bayan Khalifa da shima ya miqe suka shiga dakin tana ganinsa ta sake fashewa da wani kukan Nurse din dake tsaye kansa tana nazarin na'urar da suka jona masa tace
"Aa ya haka kuma baiwar Allah ki fita idan kin shigo ne ki qara masa hayani"

"Kiyi shiru ze samu lafiya in sha Allah" Khalifa ya sake nanata mata. Ta hadiye kukan tana share hawaye ta Kalli Khalil dake kwance marabarsa da Matacce numfashi, tunanin abubuwan da suka wakana a tsakaninsu dazu ta shigayi yanzu idan mutuwarce ma haka zata daukeshi da ace bata yarda dashi ba da harta mutu ba zata dena dana sani ba
"Allah karka sa ya mutu dan Allah" ta fada cike da yarinta tana fashewa da wani kukan Nurse din ta kalleta ba tareda ta shirya na ta fashe da dariya jin wannan addu'a ta humaira seta kalleta tace
"Da alama kina ji da Yayan nan naki, ki kwantar da hankali babu abinda ze same shi in Allah ya yarda"

"Ba qanwarsa bace Matar sa ce yau ta tare a gidansa" Khalifa ya bata amsa seta riqe baki cike da mamaki lokaci daya ta hada kan lissafi bata san sanda tace
"Kai kar dai kuce mun daya matarsa ce ta masa wannan aika aikar?"

Basu bata amsa ba amma kallon da suka mata ya tabbatar mata da hakane, tsabar saurinta fita ta watsa gulma nan ta bar Takaddar Checkup din da Likita yace ta kai ta fice daga dakin, kiran sallar da akayi yasaka Khalifa shima tashi yana cewa Humaira zeje ya duba Hajiya daga nan yaje Masallaci. Yana fitowa Dr Al'aminda suka shiga da Umaimah Theatre ya zo gurin shima. Ya kalle su ransa a hade yace
"Mun samu nasarar ciro baby girl but she is in the PICU saboda long term da tayi a ciki ga kuma abubuwan data fuskanta ya saka she is critically ill i just hope she survives, ita kuma zamu kaita dakin hutu dan Allah kar Wanda ya shiga inda take har seta farka munga state din lafiyarta" yana gama fada ya juya abinsa.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 74

Guraren qarfe tara na safe Khalil ya farka cikin wani matsanancin ciwo da duk wanda yake gurin seda ya tausaya masa yanda ya dafe mararsa yana juyi akan gadon tareda nishi meqarfi wanda yake tsananin azabar da yake ji amma dauriya irin tasa ta hanashi ya kurma ihu, Humaira dake zaune dashi a dakin tayi kuka har hawayenta sun qafe. Tun wayewar gari Mama da Abba suka tafi gida saboda gaba daya su biyun suna buqatar nutsuwa badan sunqi ba gado likitan yaso ya basu kamar yanda Hajiya take kwance tun Asubar itama tana bacci taimkon Allurar da akayi mata. Har kuma sannan Umaimah bata farka ba bayan tafiyar su Mama Anty Hafsa da Nuratu sukazo amma Nuratun bata jima ba saboda zata wuce gurin aikinta ta tafi cike da Alhinin abinda ya faru se Anty Hafsa ta zauna a gurin Umaiman.

Da taimkon Allah da taimakon wani Likitan da ya karanci bangaren matsalolin Al'aura ta maza wanda Asibitin suka gayyato Khalil ya samu sauqin Azabar da yake ciki. Allura yayi masa wadda ta kawo masa sassaucin azabar da yake ji dukda ciwon Marar be tafi gabadaya ba amma ya samu rangwame sosai, basu da Na'urar da zeyi amfani da ita gurin binciko ainihin inda matsalar Khalil din take dan haka sukayi referring nasa zuwa Asibitin Malam, babu bata lokaci suka dashi tareda Khalifa dakyar Jalilah ta lallabi Humaira suka koma gida bayan an wuce da Khalil din dan ta samu itama tayi wanka ta huta saboda yanda gaba daya ta fita a hayyacinta.
Tafiyar su da kadan Hajiya ta farka Qanwarta Hajiya Maimuna da Anty Amina dake zaune da ita sukayi kanta da sauri suna mata sannu.

"Ina Khalil, anyi jana'izar shi ko?" Shine abinda ta fara fada Hajiya Maimuna ta girgiza mata kai tana cewa
"Baba yana raye an dai tafi dashi Asibitin Malam yanzu akwai gwajin da zasuyi masa ki kwantar da hankalinki babu abinda ya same shi"
Ajiyar zuciya ta sauke me qarfi kafin ta koma ta kwanta Amina ta fita kiran Likita Hajiya Maimuna taci gaba da tausar yar uwarta tana bata tabbacin Khalil ze tashi, da Asuba suka wayi gari da mugun labari dole tafiyarsu ta tashi ta taho Asibitin babu shiri tsinuwa dai baza'a iyakance wadda Umaimah tasha ko ince take kan sha ba saboda tuni labari ya watsu kamar wutar Jeji a dangin Khalil babu wanda be samu labarin ta'asar data aikata ba tun sassafe suka fara tururuwar zuwa Asibitin suka dakatar dasu se iya makusantansu aka bari suka zauna dasu.

A can gidansu Umaimah kuwa suna isa kowanne ya wuce dakinsa, cikin wani yanayi me ban tausayi Mama ta zube a tsakiyar falonta ta sake rushewa da Kukan daya tokare mata maqoshi, bata damu da kashedin da akayi mata yanzu a asibiti ba akan ta daure ta cire damuwa jininta ya hau sosai to ta ina ma hankalinta ze kwanta duk duniya babu wanda ze fahimci irin zafi da qunar zuciya da takeji se ko Abba wanda suka da matsayi daya dashi a gurin Umaiman. Yau a wayi gari a ce dan da ka haifa a cikinka ne ya zama taqadiri Umaimah bata kyauta wa kanta ba bata kyauta musu ba. Kuka takeyi tamkar ranta ze fita, tunani takeyi idanhar Khalil ya rasa ransa Umaimah ce sila daman ta dade tana fadar zata kashe shi basu taba yardar da gaske takeyi ba se yanzu domin irin dukan datayi masa a makasa ya nuna daman ta shirya yin hakan.

Maman Asad ce ta shiga falon da sallama tayi saurin wullar da jakarta ta isa gurin Maman cikin kukan itama ta dagota tana cewa
"Kiyi haquri Mama dan Allah ki dena kuka kodan saboda lafiyarki idan wani abu ya sameki mu ta shafa ita bata da Asara dan bata dauki kowa cikin Ahalinta da muhimmanciwani.ldan Allah Mama karki bari bacin ranta ya shafi lafiyarki ki barta kiy mata Addu'a Allah ya shiryeta idan tana da rabon shiriyar" suka hada kai suna kuka riris babu merarrashin wani Anty ta shigo fuskarta itama jiqe da Hawaye ta zauna tana cewa

"Hajiyayye keda zaki rarrasheta kuma se ki tayata kuyi dan Allah Kiyi haquri qaddara ce a rayuwa kowa da kalar tasa ina fatan kuma abun ya tsaya iya haka sannan hakan ya zame mata izina a rayuwa"

Seda sukayi me isarsu kafin kowa ya bawa zuciyarsa haquri yayi shiru. Dakyar Hajiyayye ta lallaba Maman tayi wanka tasha ruwan shayi da maganinta ta kwanta Anty Ma gurin Abba ta koma dan seda yayi wankan yasha shayi da magungunansa bacci ya dauke shi daman kafin ta fito gurin Maman. Mamaki ya kamasu ganin yanda yan uwa da maqofta suka ringa shigo musu Jaje, Maman Asad ta tambayi Anty Zee cousin dinsu da tazo tana ta kuka itama a bakinta taji wai a WhatsApp ta gani an tura da hoton Umaimah da Khalil din harda na Amaryar wai Uwargida ta kashe Ango saboda kishi a daren Angwancinsa.

A can Asibitin Malam kuwa bayan kammaluwar duk wasu gwaje gwaje daya kamata ayiwa Khalil din suka sake mayar dashi Asibitin Dr Al'amin zuwa sannan ya dan samu nutsuwarsa dukda dai baya magana kallon Likitocin kawai yakeyi da Khalifa da suketa kai kawo akansa har aka mayar dashi Asibitin bayan likitan ya fita ya kalli Khalifa dake zaune gefensa yace
"Ina Hajiya?"
"Tana nan an bata gado itama tun jiyan" Khalifa ya bashi amsa seya gyada kai kawai kafin a hankali ya sake cewa
"Humaira fa? Ina fatan babu abinda ya sameta"

"Lafiyanta qalau dan tana tareda kai se da zamu tafi AKTH ne bata bimu ba, bari naje gurinsu Hajiya na gaya musu mun dawo probably tana tare dasu" daga haka Khalifan ya miqe ya fita Khalil ya bishi da kallo a zuciyarsa yana hakaito abubuwan da suka faru a daren jiyan. Ajiyar zuciya yayi ya gyara kwanciyarsa gaba daya ji yakeyi daga qugunsa zuwa qafafunsa kamar ba a jikinsa suke ba, Umaimah ta cutar dashi ta nakasa masa rayuwa
A iya saninsa babu komai tsakaninsu se Alkhairi me yayi mata daya cancanci wannan danyan hukuncin daga gareta?
Ko ba'a fada masa ba yasan bashida sauran amfani a matsayin Da namiji ta kassarashi.

Tausayin Humaira me girma ya lullubeshi, idan da yasan jarabawar da zata afka masa kenan dabe tabata ba, dabe rabata da burcinta ya dora mata iddarsa ba haka kawai domin yasan dole ze haqura da ita ko yana so ko baya so baze cutar da ita ba ta hanyar zama da ita alhalin bashida ikon sauke mata haqqin da shi ya banbanta Matar aure da Marar aure. Zuviyarsa ta tambayeshi
Waya ce masa ya nakasa da har yake tunanin baze qara amfanuwa ba? Take ya bawa kansa amsa da tabbacin hakanne ba kuma ya buqatar wani ya gaya masa shi kansa a Jikinsa ya sani ya rasa lafiyarsa. Wasu hawaye masu dumi suka ziraro masa yayi saurin daukesu saboda qofar da aka bude. Hakiya ta shigo sauran yaranta da Yar uwarta biye da ita a baya tana ganinsa ta fashe da kuka ta qarasa gaban gadon ta kama hannunsa ta kasa cewa komai se Kuka takeyi abinda ya karyar da zuciyar sauran gaba daya suka saka kukan suma Khalil ne yayi qarfin halin cewa

"To kuma kukan me kukeyi bayan ba mutuwa nayi ba ai murna ya kamata kuyi tunda dai gani a gabanku a raye"
"Allah ya isa tsakaninmu da wannan shaidaniyar yarinyar, ranka ta nema da Allah yasa da sauran shan ruwanka a gaba gashi ka tsallake kuma in sha Allahu se taga sakayyar abinda ta aikata maka tun a duniya ba se taje lahira ba. Duk wahalar da kasha ta sanadinka da baqin cikin data qunsa mana se taga ninkinsu a kanta da yardar ubangiji seta qare rayuwarta cikin nadama mara amfani" Hajjya Maimuna ta fada cikin matsanan ci kuka se Khalil yayi saurin dakatar da ita yace

"Haba Mama ki dena magana haka ko babu komai Umaimah uwar yayana ce duk wata muguwar Addu'a da kikayi akanta zata iya shafarsu, ki nema mata shiriya a gurin Allah shi kadai ne abinda take da buqata"
"Ai Allah ba Azzalumin sarki bane babu ta inda zaluncin Umaimah ze shafi Ahalinmu sedai ma haqqin ubansu data dauka dasu kansu ya bibiyi rayuwarta. Allah dai ya kwashewa Umaimah Albarka kaikuma Allah ya baka lafiya abinda take baqin cikin wata ta mora sedai ta mutu dan tana Kallo zaka samu lafiya kaci gaba da Sasakar matarka tana zazzago maka Yaya" Hajiya Maimuna ta sake fada tana kuka dukda halin da suka ciki seda maganarta ta qarshe ta basu kunya Khalil ya sunkuyar da kansa qasa, ransa ya rasame yake ji akan abinda Umaimah tayi masa, ko kadan beji ya tsaneta ba amma abu daya ya sani koda ace ita kadai ta rage mace a rayuwa ya haqura da ita kuma har abada ze dawwa ma yana nema mata shiriya a gurin Allah domin ya yarda tana da lalura da kowa ya gagara ganewa.

UMAIMAH

Bayan Azahar ta farka, surutai da ta ringa yi cikin fitar hayyaci ya saka dole suka sakeyi mata wata allurar data dauketa har zuwa bayan Isha'i kafin ta sake farkawa a lokacin Anty da sauran yayyanta duk suna Asibitin. Daga yanda suke mu'amalantarta zaka tabbatar sunayi mata ne kawai Albarkacin zumunchi idan sukace zasu bi ta halinta babu wanda ze taka qafarsa yaje Asibtin gurinta. Iyakar bacin sunan data ja musu ya isa, a iya yau mutanen da suka je gidansu qafa da qafa da wanda suka kira a waya bazasu irgu ba duk akan Abinda Umaiman ta aikata. Labari nata yawo a gari anqara masa gishiri da maggi babu ta sigar da ba'a chanza zancen ba, wasu sunce ma har ana kamata tana hannun Yan sanda, wasu kuma suka ce yan uwan Mijin ne suka mata dukan mutuwa tana Asibiti a kwance masu son tabbatar da yanda akayi ne suka ringa binsu gida su dai babu wanda suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login