Showing 81001 words to 84000 words out of 429394 words

Chapter 28 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1031

nan su Aliyu zan tambaye su koda gidan kitso kusa se naje kan ya dameni da yawa" ta sake fada sanda ta rakoshi bakin mota

"Yanda kasan wata me gashi bayan qwaiqwaido ce zaki damu mutane da wani kitso ki bari idan na dawo sena yi miki da kaina" Khalil ya tsokaneta, seta zumbura baki ya zuro kansa ta glass yayi pecking bakin nata kafin yaja mota tana daga masa hannu ya fice daga gidan. Tana qoqarin maida Get din ta hango Aliyu daya daga cikin yaran dake wasa a qofar gidan ita bata ma san dan wane gida bane tana dai aikensu wani lokacin ko idan tayi ragowar abinci ko abinda ta kasaci na kayan dadi ta fita ta raba musu.

Kiransa tayi ya tawo da saurinsa yana murna dan yasan bata kiran banza ko aikene idan ka dawo seta baka na alawa.
"Anty ina kwana" ya fada yana dan rusunawa, seta amsa masa tace

"Lafiya lau Aliyu, baka je makaranta ba ne yau na ganka da safe?"
"Ai babu makaranta yau public holiday akeyi" ya bata amsa seta daga kai tace

"Oh, yawwa ni a unguwar nan a ina ake kitso ne Ali?"
"Anayi a gidan mu Mamanmuce takeyi" ya bata amsa yana nuno mata qofar gidansu da yake kallon nata ta dayan bangaren.

"Yawwa jeka ka tambayomin naji yaushe zanje ayimun kaji" ta fada se ya juya da saurinsa ita kuma ta koma cikin gida, kayan wanke wanke ta fito dasu tsakar gidan bakin famfo ta shiga wanke wa, bata dade da farawa ba ta jiyo bugun qofa da surutunsu seta dauraye hannunta taje ta bude shida Hibban ne yaron Gidan dake jikin nata shi ta gane fuskarsa dan kamar sa daya da Mamansa da suka shigo mata tareda Rufaida.

"Wai tace ko yanzu ma kizo idan bakya komai" Aliyun ya fada mata saqon Mamansa.

"Toh shikenan, bari na qarasa wanke wanke sena zo"
"Kawo nayi miki Anty" Hibban din ya fada yana murmushi dan irin masu yawan Fara"ar nan ne, Murmushin ta mayar masa tace

"Aa nagode, gadai tsintsiya nan ku share mun tsakar gidan kafin na gama" suka Amsa da toh taci gaba da wanke wanken suna mata sharar suna yar hira har suka gama.

Ciki ta shiga ta kira Khalil a waya ta shaida masa zata shiga gidan su Aliyun ayi mata kitson yace ta duba rigar daya cire jiya da akwai kudi ta dauki dubu biyu tayi masa godiya kafin ta gyara fuskarta ta zura dogon Hijabinta ta hada kayan kitson a qaramar jaka ta fita. Seda ta daukar musu Apple daddaya da chocolate ta basu sunata godiya kafin suka rakata gidansu Aliyu.

Da sallama ta shiga wata mata baga mara jiki na zaune a tsakar gidan tana hura gawayi a Dutsen gugar charcoal ta amsa mata fuskarta da fara'a tana mata sannu da zuwa. A mutunce suka gaisa Umaimah na satar kallon gidan da a kallo daya zaka fahimci cewa mazauna cikinsa na fuskantar matsin rayuwa dan dukda cewa ginin zamani ne amma ya tsufa alamar rashin gyara a haka ma da alama dan mutanen gidan nada tsafta saboda a sannan ma tsakar gidan dukda qasace amma qal yake babu ko tsinken datti an share ko ina.

"Kitso nazo, Aliyu ya gaya miki ko" Umaimah ta sakw fada ganin matar tayi shiru bayan da suka gama gaisawa, se matar ta nuna mata dakin dake fuskantar su tace
"Tana ciki Maman Aliyun ki qarasa" daidai nan matar dakin tayi fit ta fito tana gyara daurin zaninta dake neman faduwa.

Wata harara ta makawa Abokiyar zaman nata se kuma ta saki murmushi ganin idon Umaimah akanta ta fara cewa

"Au Amarya ashe kece bismillah qaraso ai dangidan naki yace zakizo da fita zanyi ma na fasa"

Murmushin yaqe Umaiman ta sakar mata itama dan sam matar bata mata ba, ta tuna fuskarta itace Maman Hauwa wadda suka shiga tareda budurwar yarta da tana Amarya.
Cikin palour suka shiga Maman Hauwa nata faman jera mata sannu da zuwa Umaimah ta tsaya tana kallon kujerun palour tunanin inda zata zauna takeyi dan sunci uwarsu da datti ga wani zarni zarni na tashi kamar anyi fitsari a palour a haka har turaren tsinke taga an kunna.

"Zauna mana Amarya, kin tsaya" Maman Hauwa ta sake fada baki a washe, Umaimah ta dosana mazaunanta akan kujerar data ga nada dan dama dama a ranta tunanin yanda zasuyi kitso a wannan dakin takeyi dan tuni cikinta ma ya fara hautsina mata.

"Ina kwana?" Maman Hauwa ta fada, seta dawo daga kalle kallen da take ta amsa mata suka gaisa.
"Ai muna ta ganin abin arziqi komai Aliyu ya shigo dashi yace Anty ce ta bashi ko mijin Anty, nace ita Antyn taka ce bame son mutane ba aida mun shiga munyi godiya" Maman Hauwan ta sake sako magana, se Umaimah ta saki murmushi bata ce komai ba Maman Hauwa taci gaba da cewa

"Eh mana, tunda muka shigo muna ta zuba ido ko zaki shishshigar mana shiru. Lokacin haihuwar Rufaida ma matan layi duk an hadu ana ta tambayar ina Amarya a sannan yara sukace kamar bakya nan kai har ma aka gaji da tambaya kowa yace baki shigar masa ba dake mun saba nan idan aka kawo sabon zuwa zakiga duk za'a ringa haduwa ana gaggaisawa"

"Allah sarki" kadai Umaimah tace seta dakko wayarta ta shiga dannanwa dolen Maman Hauwa tayi shiru. Kusan minti uku a tsakani tana qarewa Umaimah data hade fuska tana danna waya kallo se tace

"Bismillah toh kinzo da kibiya ko na dakko?"
"Aa nazo da ita" Umaimah ta fada ta bude jakar ta dakko Comb, kibiya da Mai. Tana shirin zame Hijabinta aka dauke wuta, Maman Hauwa tace
"Oh sunyi halin nasu sedai mu koma tsakar gida dan yanzu zakiji dakin ya gume da zafi ga shi daman yara sunyi fitsari a gun"

Hamdala Umaimah tayi a zuciyarta ta tattara kayan tayi waje, ita badaban bama gudu zatayi amma yata iya tubda tazo zata daure amma dan ba qara.

A tsakar gidan suka zauna kitson sunayi dayar matar nata gugar kaya ta gama ta shiga hidimar girki Maman Hauwa nayiwa Umaimah hira ita dai sedai ta amsa da Eh ko Aa dan sam ba dadin hirar takeji ba gashi ta debar mata kitson qanana dan ma tana da sauri nan da nan zuwa sha biyu se gashi sun gama zuwa sannan gidan ya fara cika da Mata wasu yan kitso wasu kuma kawai hirarsu ce ta shigar dasu harda masu kai zubin Adashi dan taga duk wadda ta shiga zata bawa Maman Hauwa dubu daya ko dari biyar ita kuma tasa yara su rubuta a littafi duk wadda ta shigo kuna se an mata bayanin Amaryar can gidan ce.

Dubu daya ta bata kudin kitson dan yayi kyau sosai ta kuwa ringa godiya kamar zata durqusa mata. Tana shirin fita daya matar ta fito daga kitchen tana murmushi tace

"Har kun gama kenan sannunku" Umaimah ta amsa mata da murmushi itama dan jininta yafi haduwa da ita sama dana me kitson, bata damu da hararar da Maman Hauwa da sauran dake zaune ba ta sake cewa Umaiman

"Ga Abinci ya kusa sauka bazaki tsaya kici ba Alalen gwangwani ne abin marmari"

"Toh uwar kinibibi gurinki tazo ko yaya da zaki tsareta da surutun banza ko tace miki mayunwaciyace ita duj inda taje se taci Abinci" Maman Hauwa ta hayayyaqowa matar sauran matan dake zaune suka hau qunqunin wai ta fiya cusa kai daga ganin mace zata fara mata shishshigi, baze wuce wanki da guga zata ce ta ringa kawo mata ba kuma ba samu zatayi ba dan duk dan dakin Maman Hauwa bazeyi hulda da Ramatu ba.

"Idan kin gama a bawa Aliyu ya kawo mun toh" Umaimah ta fada kafin tayi musu sallama tayi ficewarta a ranta tana mamakin wadannan mata da suka taru, a haka dai gasu kamar wayayyu ashe duk taron marasa sanin ciwon kai ne. To in banda rashin sanin ciwon kai qarfe sha biyun rana ki kullo gidan ki lokacin da kowacce Mace take qoqarin dora abincin rana ki tafi yawon daukar magana wani gidan toh Allah ya kyauta.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 24

Umaimah na zuwa qofar gida wayarta dake cikin jaka ta hau qara, seda ta zarota sannan ta bude qofar ta shiga, Khalil ne ya ke kira ta daga da sallama tana narke masa muryar shagwaba.

"Me kuma ya faru?" Ya tambayeta cikin rarrashi, seta narke fuska kamar tana gabansa tace
"Na gaji da zama kitson me yawa tayi mun duk yanzu bayana ciwo yakeyi".

"Ayya sorry Babe idan na dawo zan miki Massaging bayan kinji, na kiraki da zu Hajiya ma tace ta kira baki amsa ba"

"Lah wayar tana jaka se yanzu na dawo banma duba taba kiranka ya sake shigowa bari toh na kira Hajiyan sena sake kiranka" ta fada tana shirin kashe kiran ya dakatar da ita da cewa

"Base kin kirata ba daman su Habiba ne zasu zo da yaran Kawu Najib shine zata sanar miki"

"Ohk to shikenan se sunzo"? ta bashi Amsa daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Azahar tayi dan haka ta daura Alwala tayi sallah a ranta tana tunanin me zata dafawa?baqin nata dukda bata san manya ne ko yara ba dab Kawu Najib din kansa sunansa kadai ta sani, tunanin ta dora musu dafa dukan shinkafa da pepper chicken tayi, seta miqe ta shiga kitchen ta dakko kaza a Freezer ta gyarata tsaf ta hada kayan qamshi dasu maggi tayi marinating nata ta mayar cikin fridge dan ta tsumu dan ba tafasata zatayi ba.
Bazata dora abincin ba se sunzo dan kwanaki kusan sau biyu ta shiryi yin baqi se ta gama girki tsaf suqi zuwa sedai ta bayar kota aika dashi gidansu kona Hajiya shiyasa ta yanke shawarar dena yin girki idan zatayi baqi se sunzo, sedai ta tanadar musu qananan abubuwa da zasu dan taba kafin ta gama.

Daki ta koma ta miqe akan doguwar kujera kafin kace me bacci yayi awan gaba da ita can cikin baccin qarar wayarta data ajiye saman kanta ta fara qara, a firgice ta farka tana zare ido, ta daga wayar daga dayan bangaren Khalil yace

"Babe ina kika shiga ko wanka kikeyi? Gasu can a waje sunata bugu baki jiba". Cikin muryarta da tayi qasa saboda baccin da yazo mata me nauyi tace

"Waifa dan kwanciya nayi na huta shine bacci ya kwasheni"
"Ai ke dai yanzu kin zama kasa is a sace ki ma kina bacci baki sani ba" Khalil ya tsokaneta seta mayar masa sa cewa
"Naji din, idan zaka dawo ka taho mun da rake"
"An gama, jeki bude musu kinga ana rana suna tsaye a ciki" sukayi sallama ta miqe.

Seda ta wanke fuskarta ta gyara daurin dankwalinta dan bata san su waye ba karsu rainata kafin ta yafa mayafinta ta fita, tana budewa Habiba qanwar Khalil na tsaye da dutse a hannunta se wasu guda biyu da bata san fuskarsu ba Habiban ta saki murmushu tace

"Yawwa Anty Umaimahtundazu muke bugu seda muka kira Yaya yace qila bakya nan ba bari ya kiraki" Habiban ta fada da murmushi se Umaimah ta mayar mata da martanin murmushin ta qarasa ta bude musu qofar tana cewa

"Kitso na shiga can gidan ai ba nisa nayi bama dana dawo kuma bacci ya daukeni shiyasa banji bugun naku ba bismillah ku shigo" tayi ciki suka rufa mata baya. A mutunce suka gaisa tana binsu sauran biyun da kallo qasa qasa musamman farar ciki da se wani yatsina take tana qarewa Palour kallo seta tashi ta kawo musu ruwa da lemo, tana da sauran Samosa danya a Freezer ta soya ta hado musu da ita ta zauna tana cewa

Solar taje ta kunno saboda an dauke wuta ta kunna Musu Tv ta miqawa Habiba remote tana cewa
"Bari na dora abinci Habiba ku fara da wannan, sedai baki gaya mun su waye baqin nawa ba"

"Lah na manta ban miki bayanin su ba, wannan Yaya Shafa'atu ce yar gidan Yayan Hajiya da akayi bikinta kwanaki kin tunata? Wannan kuma Yaya Lubna qanwarta ce" Habiba ta fada bayan data Ajiye kofin da tasha ruwa.

"Ayya Amarya sannu ai munso zuwa Allah beyi ba" Umaimah ta fada tana fadada fara'arta, Shafa'atu tayi mata murmushi tace

"Babu komai ai gashi yanzu mu munzo" se Umaiman ta miqe tana cewa

"Kusha ruwa bari na dora abincin rana tana qarayi"? se Habiba tabi bayanta tana cewa

"Muje na tayaki Anty". Tare suka shiga kitchen din ta bawa Habiba gyaran Attaruhu da Albasa ita kuma ta fito da Kazar data saka fridge ta shiga ta dora mai.

"Ita dayar bata da aure ne?" Umaimah ta jefawa Habiba dake yanka Albasa tambayar se tayi shiru dan bata tsammaci da ita take ba, seda Umaiman ta sake maimaita mata kafin tace

"Wa? Wai Yaya Lubna? Bata da aure ta tsaya ruwan ido dan da tare zaayi bikinsu da Yaya Shafa'atu aka fasa. Itafa nan a dole da Yaya take so, idan kinga kukan data sha lokacin bikinku se kinci dariya bafa ta zo ba ko yanzu dakyar Hajiya ta sakata ta biyo mu" Habiba ta jerowa mata bayani.

Sakare tayi tana jnta, zafin da taji ya ratsa mata hannu har zuwa cikin kwakwalwarta ya sakata watsar da robar data zuba naman kazar da zata soya. Sam ta manta da ta dora mai tana shirin zubawa ne take tambayar Habiban ta tsoma hannunta bata sani ba.

Da sauri Habiba ta taso ta shiga yi mata sannu da qoqarin riqe hannun da Umaimah keta faman yarfewa saboda Azabar radadi.
"Sannu Anty, kawo a zuba ruwan sanyi Allah yasa karta tashi" Habiba datayi saurin dakko ruwan qanqara ta sakr fada. Se Umaimah ta miqa mata hannun tana sakin kuka kamar wata yar yarinya? kukan baqin ciki biyu.

Na farko ga radadin zahiri na qonewar da tayi ga radadin zuciya najin budurwar Mijinta ce tazo mata gida, ai kuwa setaci ubanta seta gaya mata dalilin daya kawota da har ta jawo mata guzurin qonewa, sannan shima ze dawo ya sameta, wato saboda budurwarsa nae har yake cewa taje ta bude suna tsaye a rana ko

Habiba na gama zuba mata ruwan ta fice daga kitchen din dan bata ga ubanda zata girkawa abinci ba kuma, dakinta ta shige Habiba na biye da ita fuskarta dauke da damuwa tace
"Anty ko???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?na kira yaya na gaya masa?"

Kallon hannun Umaimah tayi, dukda tana jin radadi a saman yan yatsunta da sukayi jaa amma bata zaton qunar tayi munin da se anje Asibiti musamman da an zuba ruwan sanyi ta tabbatar ze taimaka gurin hana ta tashi seta girgizawa Habiban kai tace

"Aa karki kirashi, kije ki fara girkin ina zuwa" se Habiba ta juya tana qarayi mata sannu ta fita.
Shafa'atu ke tambayarta lafiya ta gaya mata Umaiman ce ta qone seta miqe tana cewa "subhanallahi muje na gani amma bada yawa bane ko?"

"Eh en yatsuntane suka shiga cikin Mai Allah yasa beyi dai zafi sosai ba" tayi gaba ta kwakwasa qofar dakin Umaimah data kwanta shiru zuciyarta na suya, a fusace ta miqe ta bude qofar, suka shiga Shafa'atun ta shigayi mata sannu tana tambayarta ko zasuje Chemist tunda taga wani a kan layin nasu.

"Babu komai fa ai Man beyi zafi sosai ba kuma an zuba ruwan sanyi na kuma tofa Addu'a daman yanzu zan fito na qarasa girkin" Umaimah ta fada tana qaqalo fara'ar dole se Shafa'atu ta tareta da cewa

"Wane irin girki kuma ga Habiba da Lubna nan s su qara sa idan da wani abinda za'a miki ma duk se muyi kafin mu tafi ki zauna ki huta".
Kamar tace wace shegiyar Lubnan ce zata shigar mata kitchen sedai ta danne ta qaqalo murmushi tace

"Aa wallahi zan iya ai ya dena radadi hannun ya za'ayi na saka baqina aiki"? ta shiga qoqarin fita daga dakin suka bita a baya Shafa'atun na cewa

"Haba Anty Umainah ai wallahi indai mu zaki dafawa bazakiyi ba gara mu zauna da yunwa idan bazaki barsu suyi ba in kuma na Yaya ne ki gaya masa kawai yayiwo take away ko ya karbo a gidan Hajiya tunda nasan bazeci girkin su ba"

"Kamar ya baze ci girkin mu ba, me kike nufi? Idan da Allah yayi naga girkin wa ze ringaci?" Lubna da bata saka musu baki ba tuntuni ta fada a tsiwace tana kallon Yayarta.
Se Umaimah ta zuba mata ido kawai, badan tana tsoron hukuncin da Khalil ze sake dauka akanta ba da babu abinda ze hanata nadawa wannan yar iskar duka a cikin gidan. Ita mamakin kanta ma take yau da har ta iya tsayawa inuwa daya da yarinyar da ake iqirarin budurwar Mijinta ce koda yake gashi ma ta tabbatar mata ta fada da bakinta.

Tanajin Shafa'atun ta rufeta da fadan bata da kunya ne waye sa'anta a cikinsu Lubna data dauke kai ta harde a kujerar Umaimah ko a jikinta tana danna waya har yayar ta gaji tayi shiru se Umaimah ta saki murmushin takaici tace

"Ki barta ba laifinta bane kinsan quruciya akace dangin hauka gaskiyarki kuma Habibi bazeci

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login