Showing 12001 words to 15000 words out of 429394 words

Chapter 5 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

921

goyata ai, tun dazu da kin bani ita da yanzu ta dade da yin baccin ai" ta saba yar a baya ta daure da zani.

"Gani nayi kin sha aiki da yawa ai Anty ita kuwa babu abi da tayi, ina jinta dan iskanci cewa tayi inta taba danyan nama kanta ciwo yake amma kin iyaci idan an soya ko?" Hajiyayye ta fada tana Hararar Umaimah, ko a jikinta ta zauna kusa da ita tana latsa waya, ba jimawa suka jiyo sallamar su Fauziyya Umaimah ta fita da dan gudunta ta taro su.

Seda suka gaisa da Maman Asad kafin suka qule a dakin da Umaiman take, se yaba haduwar gidan suke dan sabon gini ne suka yi ko shekara basuyi a cikinsa ba.

Basu tashi tafiya ba se dab da magriba suka fito bayan da suka sake kwalliya kowa ta baza turare aka kashe daurin dankwali.

"Bazaku bari ayi sallah ba zaku tari goshin magriba ku fita" Maman Asad ta fada tana qare musu kallo,
"Bari kawai muje Anty, Allah ya raya a gaida su Asad da Mimi" suka hada baki gurin fada

"Zasuji suna gidan qanwar Babansu hutu, ki duba kitchen ki daukar musu kullin nama" ta fada kafin ta shige daki ta barsu tsaye suna jiran Umaimah data tafi kitchen.

"Ke ai irin unguwar nan dab da magriba ne kake ganin mutanen ciki ta, kinsan yan gayun nan basa yawo a rana yanzu ne daidai masu fita sallah sun fito masu dawowa daga aiki suna shigowa da qafa zamu taka har titi ko Allah ze sa mu dace da rabo" Nabila ta fada tana rarraba ido tana qarewa qerarrun gidajen unguwar kallo, unguwa ce ta yan gayu me kyau da tsari,

"Kedai Allah ya shiga lamarin ki Nabila naga alama kina neman zaucewa akan neman Miji, koda yake tsarin da kika dakko ne bame bullewa ba kin tsaya ke se hamshaqin me kudi bayan su kuma ba irin ki suke so ba" Fauziyya ta fada tana qunshe dariyar dake son kufce mata saboda yanda Nabilan ke faman rangwada da karairaya se jefa dogayen qafafunta take ala dole tana yanga.

"Wallahi Fauza zan miki rashin mutunchi, idan Allah ya kawo munme kudin dan Allah ki hana shi aure na banza yar baqin ciki" ta fada a fusace tana kallonta, har Fauziyyan ta bude baki zata bata amsa Umaimah ta dakatar dasu tana cewa

"Malamai ya ishe ku zaku fara halin naku kamar kaji, ke kuma sauka daga titi kafin ya rage miki farashi" ta qarasa tana kamo Nabila gefe saboda hango Khalil daya fafaro mashin dinsa kamar ze tashi sama.

"Wannan kamar guy din nan na office din Sir Nasir" Nabila ta fada tana binsa da kallo se Umaimah ta gyada kai tace
"Tabbas shine, daman ina ta tunanin ina na san fuskar sa ashe saurayin Nabila ne" ta fada da sigar wasa.
Baki Nabilan ta tabe tace

"Wallahi ya hadu kawai dai matsakar sa rashin chanji, kome yazoyi nan oho qila gidan su wani abokin nasa yazo" tayi tambaya ta bawa kanta amsa duk ita kadai se Umaimah ta nuna mata gidan su tana cewa

"Kinga gidan su can, ko zaki shiga ki gaida surukarki"

"Aa kakan surukata banason wulaqanci" daga haka suka ci gaba da tafiya har ta raka su bakin get din layin kuwa babu wanda yace musu tafi ku mutu dukda ga Maza nan samari da magidanta suna ta qoqarin Shiga masallaci dan an kira sallah kota kansu basu bi ba. A bakin Get din tayi musu sallama ta juya.

A qofar masallacin taga Khalil yana alwala ya bita da kallo ta galla masa harara se ya sakar mata murmushi ba shiri ta dafe qirji jin zuciyarta ta buga da qarfi kamar wadda ta tsorata. A haka ta shiga gidan faran faran kamar wadda aka biyo saboda yanda taji gaba daya zuciyarta na tsere kanta har wani sarawa yakeyi.

"Ke lafiyar kuwa kika fadowa mutane babu ko sallama" Maman Asad ta fada tana qare mata kallo, se Umaimah ta kalleta tace

"Inaga Gamo nayi, wani mutum na gani, kai ba mutum bane Aljanine" ta fada kamar me tantamar abin

"Idan ma rauhanine zaki gani ai, saboda baku da hankali da magribar nan haka kuka kwashi qafa kuka fita, ni sam bana son wadannan qawayen naki gaba daya basu da nutsuwa har gara gara Halima a cikin su daman amma wadannan biyun bansan wadda tafi wata rashin hankali a cikin su ba"

"daga abin arziqi kuma shine zaki zagesu yan gidan mu nawa suka haihu basuje musu barka ba seke, daman mantawa nayi baa miki abun kirki dama basu zo ba" Umaimah ta fada tana zumbura baki,

"Da suka zo din uwar me na qaru da zuwan nasu fitsararriya? Ki shiga hankalinki idan ba haka ba kuma sena hadaki da Abba ina daman an raba ki dasu kinqi ji ko? Shikenan" Hajiyayye ta fada tana wuceta, Umaimah ta rakata da harara, wallahi badan tafi samun yanci anan ba da gidan su zata tafi haka kawai mata ta sakata a gaba ta ringa mata masifa daga an mata abin kirki anzo mata barka? Ai shikenan maganin ta itama gobe ta qara.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa da dadi babu dadi Umaimah na zaune gidan Hajiyayye har Sukayi arba'in ranar kuwa bata qara kwana a gidan ba ta tattara ta wuce dan daman tuni taso tafiya Mama ce ta hana saboda Anty Larai ta tafi qauyensu yarinyarta bata da lafiya gashi su Asad sun dawo daga hutu dan haka hidimomin sunwa Hajiyayyen yawa.

A dan zaman da sukayi ko fada anyi shi yafi sau cikin kwando, Umaimah rashin jiz Hajiyayye rashin haquri, haka zata biye mata suyita hayaniya musamman da Mijinta ba mazauni bane shiyasa Umaiman ke samun yanda take so.

Sam ta manta da wani Khalil da shirginsa dan tun waccen ranar bata sake haduqmwa dashi ba daman ba fita ta fiya yi ba, idan ma ta fita ko kallon gidan su batayi, abu daya ta kasa gane kansa Khalil din na yawan fado mata a rai, duk kuma sanda ta tuna shi se taji irin faduwar gaban ranar na har ta ringa ayyana a ranta kodai maye ne? Idan ma mayene to sedai yaci kansa amma ita kam kurwarta daci ne da ita.

ko ranar da Hajiyarsu ta shiga gidan yiwa Maman Asad barka qin fitowa tayi su gaisa tana ji tana ta tambayar ta ina take ta bige da baccin qarya, tana jinta tana wasu soki burutsun data kasa gane kansu.

Ita kanta Yaya Hajiyayyen bata fuskanci abinda Hajiyar take magana akai ba kawai dai ta ringa binta da toh, koda ta sake tambayar Umaiman itama babu wata magana daga gareta da haka zancen ya shiririce.

Komawarta gida da kwana biyu result dinsu ya fito masha Allah ta fita da sakamako mekyau, nan da nan aka shiga hidimar registration na NYSC bayan dan lokaci kadan suka shiga Camp, badan taso ba aka barta a Kano saboda gaba daya qawayen nata basa Kano, Fannah sun koma Miduguri da Mijinta dan shima dan can ne, Rumasa'u ma Jigawa ta tafi zata zauna a gidan Yayarta, Fauziyya, Nabila da Nadiya daman Kudu suka ce zasuje wanda itama tayi niyyar bin ayarin dukda bata da tabbacin a gida za'a barta amma dai da ko iya camping taje tayi in yaso daga baya a nema mata Relocation se gashi ana fara Registration din Yaya Aminu ya shiga ya fita ta hanyar abokinsa aka barta a Kanon tayi Camp dinta a Qaraye bayan sun fito akayi posting nata nan cikin Sakatariyar Audu Baqo.

Lafia lau take fita aikinta da take jin dadi a yanzu ko ba komai yana debe mata kewa, zancen manena dai abu shiru kamar anyi ruwa an dauke, ita a yanzu bazata iya tuna yaushe rabon da ace ana sallama da ita ba. Duk samarin sun zama sedai a kira waya ko ayi chatting, data fuskanci gaba daya ma bata mata lokaci sukeyi tunda babu wanda ya yarda da maganar a fito ayi aure wasu ma sedai su sako wata maganar banzar nan take kuwa zata qarewa mutum tanadi kafin ta dannawa lambarsa block, gaba daya ma ita ta fita sabgar samari yanzu, inda take dan samun nutsuwa ganin Abba be tada maganar ba, amma a tsorace take dan tasan yana iya mata dirar mikiya a koda yaushe gashi har yanzu bata samu tsayayye ba, a cikin haka Me neman auran Nuratu ya turo da saka rana shekara daya yayi daidai da kammala karatun Likitancinta haka itama Umaimah lokacin ta kammala Bautar qasa.

A daren ranar da Abba ya tara su ya shaida musu tare ze hada ya aurar dasu ita da Nuratu ba qaramin dadi taji ba, ta tabbatar da yardar Allah shekarar nan bazat cika ba seta samu wanda zasu daidaita su kuma daddale da maganar aure.

Akace wai ana zatom kura tayi lafiya ashe da sauran zawo, ranar wata Asabar babu aiki, tana kwance a dakinsu suna Voice call dasu Nabila mutanen Lagos acan suke bautar qasar su. Sun samu guri suna tsula tsiyarsu babu me ce musu su gyara sedai fatan shiriyar Allah kawai.

"Ke qawata ina ta so na miki magana se na manta ina guy din nan kuna haduwa kuwa idan kinje gidan Anty Hajiyayye" Nabila ta fada daga can bangaren, Kwanciya Umaimah ta gyara bayan data zura Earpiece a wayar tace mata

"Wane mutumi kuma, kefa a rayuwarki baki da zance sena samari kodan baki dasu ne se Allah"

"Karki nemi ki gaya mun magana malama daman kinsan ance wani jinkiri Alkhairi ne toh da alama nima nawa jinkirin ze zama Alkhairin" Nabila ta fada tana fari da ido, se Umaimah tace

"Toh ina jinki meya faru yanzu?"
"Last week bana fada miki munje Birthday partyn wani corper da muke service guri daya ba a wani Restaurant akayi, kawai in gaya miki se gashi mun hadu da Guy din nan na office din Sir Nasir. Oh my God Umaimah kinganshi kuwa yanda ya hade cikin wasu J and T wallahi da farko ban ma gane shine ba kawai naji ya qara tafiya da imanina seda muka matsa kusa na ga fuskarsa na gane shine ashe.

Akayi Sa'a cikin wadanda muke tare kawai naji wani Ya kira Sunansa *Architect Khalil Umar Bayero* bansan sanda na saki ihun murna ba, Maims daga yanayin kayan jikinsa da abincin da sukayi order kadai kinsan akwai chanji a hannuna, se daya bude baki yayi magana gaba daya ya qarasa kwance mun kai kinji Husky Voice dinsa Umaimah? Kinga wata arniyar mota daya tuqa suka bar gurin? Na rantse i can die for that guy yayi mun to the core shine daidai mijin da nake ta jira na samu, ga kyau ga aji a yayan banki ashe basaja kawai yake yi a Kano yana yawo akan Lifan".

Tunda Nabila ta fara magana ta fuskanci akan wa takeyi taji wani irin duhu ya fara mamaye mata idanu, gaba daya ma dena fuskantar ta tayi tana jinta ne amma sam bata gane me take cewa idanunta kawai hasko mata Khalil suke yanayiwa Nabilan wannan tsadaddan murmushin nasa daya saka ta fara tunanin mutum ne ko Aljani?

"Umaimah kina jina kuwa kin barni se magana nake kinyi shiru" Nabilan ta fada jin shirun yayi yawa.

Bata san ya akayi ba se jin bakinta kawai tayi yana furta "Daga yau Nabila babu ni babu ke, idan kuma kika sake kika qara yi mun magana na rantse da Allah se naci kutumar ubanki, yar iska kwartuwa mebin mazan mutane" tana gama fadar haka qit ta kashe wayar tayi wurgi da ita ta hadu da bango nan take ta tarwatse.

Hannu biyu ta dora akai ta fasa ihun daya saka nuratu wuntsulowa daga kan gado dan tuni tayi suman zaune tun sanda Umaiman ta fara korawa Nabila warning.

"Meya faru? Akan waye? Sune tambayoyin da Nuratu takewa kanta da bata da me bata amsarsu se Umaimah dake birgima tana zunduma ihu a qasa kamar wadda ta hau iskokai.

*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR>?p?=?y? (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 5

Da gudu Nuratu ta fita kiran Mama ganin yanda Umaiman take ihu tana birgima kawai wadda ta hau iska.
"Nuratu leqa ki kira Malam Sadi ko Auwalu suyi mata ruqiyya, mun shiga uku a ina kuma Umaimah ta kwaso iskoki" Mama data shiga dakin zani a hannu Anty na take mata baya ta fada suka shiga qoqarin riqeta amma ina se zillewa take tana ihu da kururuwa haka Malam Sadi ya same su ya shigo da dogon carbin sa ya samu guri ya zauna daga gefe ya su riqeta, qarfi suka hada su ukun suka mata muguwar dannan shi ko ya shiga karanto Ayoyin ruqiyya yana tofeta daga i da yake zaune.

Banda Kukan baqin ciki babu abinda Umaimah takeyi, wannan shine duka biyu, ga abinda yake damunta sannan anzo an wani danne ta ana mata ruqiyya se kace tace musu iskokai takeyi.
Ganin da Malam Sadi yayi ta dena bige bigen se kuka ya saka shi cewa su saketa kowa taja gefe tana numfashi kamar wanda sukayi gudun famfalaqi, se ya cewa Nuratu ta samo garwashin wuta, fita ta debo masa ya ciro wani qullin magani daga Aljihunsa yana kallonsu yace

"A samo abu a rufa mata se ku fita daga waje, idan kuma zaku iya shaqar hayaqin maganin ku tsaya tunda sunqi magana gara a sakasu ta dole" ya qarasa yana barbada magani a kaskon nan take suka fara jera Atishaqa saboda wani yajida maqaqi da suka taso lokaci daya suka nemi su shaqe su, shi kansa tarin yake ba shiri aka fara rige rigen fita daga dakin harda Umaimah da damanita ba shiri take da hayaqi ba.

"Ku riqota karku bari ta fita" Malam Sadi ya fada ganin ta nufi qofa Nuratu ta matsa da niyyar riqeta ta hankadevta tana cewa

"Dallah kyaleni ni lafiyata qalau babu wasu Aljanu da nakeyi, abu ne ya same ni ku barni nayi kukana ko zanji sanyi kun wani dakko shi bayan ma ko Ruqiyyar be iya ba" tana gama fada ta zaka kai tayi waje ta barsu da baki bude.

"Hajiya baku san sharrin Jinnu ba qarya ce irin tasu kawai sunji magani ne shine zasu fake suce itace da kun kamota ta shaqi hayaqin nan da kansu zasu bar jikinta yanzun nan" Malam Sadi ya sake fada. Se Mama ta daga masa hannu tana cewa

"Kaje kawai mungode, Nuratu fita da hayaqin ki kashe a bude winduna iska ta shigo" tayi waje itama.

Umaimah ko can kan Dandamalin qofar dakin Mama ta samu ta zauna taci gaba da rusa kukan da bata san ko na menene ba, idan ta tuna wai Nabila taga Khalil kuma tana sonsa ji take kamar tayita buga kanta a bango har se ya fashe ta dena tuna abin.

"Zo Umaimah" Mama ta fada a tausashe kafin ta shige uwar dakinta ta zauna bakin gado tana jiran Umaimah, ita fa wannan lamari ya fara bata tsori, a yanda take abubuwa tabbas duk wanda ya gani zece shafar Aljanu ne amma kamar yanda tace lafiyarta qalau itama ta yarda da hakan bari tazo taji menene dan gaskiya idan ba Aljanu ba qila toh yarinyar nan nada tabin kwakwalwa basu gane ba.

"Meya sameki kike ihu haka gaba daya kin rikitamu?" Maman ta sake fada a tausashe tana kallon Umaimah dake jera Ajiyar zuciya kamar zata shide, wannan tambaya da Mama tayi mata ta sake fama mata ciwon aiko ta fashe da gunjin kuka tana riqe kai Mama dai se ido dan abin ya fara tsoratata. Seda tayi me isarta ta tsagaita tace

"Nabila ce, wai..wai tana son Khalil"
"Waye Khalil?" Maman ta sake tambayarta, seda taja numfashi ta dan ja baya daga gaban maman kafin tace

"Wani ne, a makaranta ta taba ganinsa, shine yanzu suka hadu a Lagos kuma wai tana son sa auransa zatayi" ta qarasa tana fashewa da sabon kuka kalmar auran data fada tana mata ciwo.

Mama da taji bacin rai ya mata dirar mikiya saboda ko kusa kalaman ta babu na hankali a ciki bata ma fahimci me take nufi ba, daga Nabila taga wani tana so zata aure shi se ya zama dalilin da zata ri ga wa mutane irin wannan Haukan a gida, cikin kaushin murya tace mata

"Kinsan ni ba sa'ar wasan ki bace da zaki zauna kina gaya mun shirme, zaki fada mun dalilin kukan ko sena saba miki yanzun nan"

"Wallahi Mama gaskiya na fada miki, wai son sa take yi ni Kuma bana so, akan me duk mazan duniya zata ce shi take so? Wallahi baze aure ta ba sedai ta tafi can ta samu wani"

"Saboda uwarsa ce ke ko ubansa? Meye ma hadinki dashi da shiga sharafin rayuwarsa?" Mamanta sake fada cikin bacin rai kamar zata kai mata duka, se Umaimah ta miqe tana ci gaba da kukan tace

"Bani da hadi dashi amma wallahi baze aureta ba sedai ya tafi can ya nemi wata matar badai ita ba, haka kawai ya aure ta na ringa ganin shine mijinta ai bazey...." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta yasa tayi shiru, tsawa ta daka mata tana nuna mata hanya tace "fita daga nan fitinanniyar yarinya da bata qaunar a zauna lafiya. Tsabar neman masifa ina ruwanki da sabgar ta? Kiji da kanki mana ko kuwa baqin ciki kike mata ta samu miji ke kina zaune kin rasa?
To kici gaba karki fasa daga mana hankali a gidan nan dan ubanki idan kika kaini bango ni kaina bansan abinda zan miki ba Umaimah".

Fada sosai Mama ta ringayi dan abin ba qaramin qona mata rai yayi ba, tama kasa gane kan dalilin wannan rashin hankali amma shikenna zatayi maganinta ne.

Umaimah kuwa har dare tana ta ciwon rai, idan abin ya ciwo ta ta zura kanta cikin pillow ta fasa ihu dan Mama ta ce wallahi ta sake jin muryarta seta mata dukan mutuwa a gidan, tasan kuma zata aikata dan haka ta qule a daki tasha kukanta ita kadai, tambayar da takeyiwa kanta data rasa amsa shine wai duk wannan abin da takeyi a wanne dalili me?
Meye hadinta da Khalil din da har taje jin wannan zazzafan Kishin akansa? Ko kuwa kishin nata ya burunqasa ne ya zama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login