Showing 150001 words to 153000 words out of 429394 words

Chapter 51 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

969

ya miqa masa wayar yana cewa
"Gata, amma Ya akayi kayi wannan tunanin?"
Hafiz ya karbi wayar yana murmushi yace
"Na gaya maka wannan ai qaramin aiki ne, da nayi niyar na tura ne a karba a hannunta se kuma kawai naga ma ga hanya me sauqi kuma gashi an dace, kaga qarin Sa'a wayar tata ma babu Security akai amma dai wannan wawiyar yarinya ce ma ita haka ake Blackmailing din babu wani shiru babu matakan tsaro"

Bincike ya shigayi a wayar bayan ya saka Sim din a flight mood yanda kira baze shigo ba. Messages ya shiga, chat din dake sama ya bude ganin message din da aka turo mata
'Bani dasu kuma karki kuskura ki sake nemana idan ba so kike ranki ya baci ba' lokacin da aka turo ya duba yaga suna tareda Khalil ma se ya bude Saqon ya fara bin sauran saqonnin da sukayi musaya da me Number shine wanda yayi mata aikin hada hoton kuma a nan ciki ya samu tabbacin ita kadai ya turawa kamar yanda ya fada shima ya goge saboda haka ne qa'idar aikinsa baya ajiye hoto ko video bayanya hada maka saboda tsaro.

Seda suka bincike wayar tas daga suka samu tabbacin mutum biyu ta turawa da Hoton daga Khalil se Hadiza se kuma mutum daya da tayi saving da 'Best' ita kuma da ita suka shirya komai dan ita ta bata shawarar aikata hakan ma ita a son ta Akan Nude Video za'a dora fuskokinsu Khausar din tace Aa.

Bayan sun gama binciken nan take Hafiz yayi formating memoryn wayar gaba daya ya kuma bi duk inda yasan za'a iyayin back up ya goge shima. Miqawa Khalil wayar yayi yana cewa
"Case close hankalinka ya kwanta ka maida qibarka kaga yanda fuskarka ta zabge kuwa kamar wanda ya shekara yana jinya ni gaba daya ma ka bani kunya se kace na Namiji ba haba mana"

"Kai bazaka gane ba, yanzu dai tunda Allahya taqaita shikenan amma idanda ace Umaimah ta kai ga ganin hotunan nan, inaga sedai na dawo nan office din ku bani mafaka" dariya sukayi gabadaya Hafiz yace
"Mata mata wato na ko ina dai haka suke da kishinnan, ni fa ina ganin babu Wanda yakai tawa yar darun" Khalil yayi saurin tare shi da cewa
"Na tabbata ko yatsanta gidanabata kama ba kawai Allah yaci gaba da rufa mana Asiri"

"Amin, yanzu ya za'ayi da wannan wayar" Hafiz ya fada, Khalil ya daga kafada yace
"May be idanna samu wandaze kai mata a mayar mata da abarta ko"
"Haba dai taci banza ma kenan ai an musanya maya wayarta, wannan 12 pro ce ma aka bata pro max ai kaje da ita kawai ka rage kudinka" Hafiz ya fada, Khalil ya girgiza kai yace

"Ko nawa na kashe bazanji komai ba tunda na samu biyan buqata" cewar Khalil se Hafiz ya maida wayar kan Table dinsa yana cewa
"Kaga Allah yaci dani daga sama na samu waya"
"Shikenan kuwa ka samu ka riqe kawai" Khalil ya fada yana miqewa, kiran La'asar da akayi ya saka dole ya jira yayi sallah a gurin kafin ya tafi. Seda ya hau hanya ya tuna da Umaimah daya kai gida tun? safiya kuma ko shiga ciki beyi ba yace seya dawo lallai wani tashin hankalin ya girmi wani yanzu kuma se yazo yaji da nata tunda ya gama da wannan.

Hadiza ya kira ya shaida mata halin da ake ciki, Hamdala ta ringayi tana qarawa tace
"Nagodewa Allah nagode maka Khalil shiyasa bazan taba dena kukan rasa jajirtaccen Namiji irinka ba, ina kuma Addu'a idan da rabo a tsakanin mu Allah ya gaggauto dashi kusa"
Da 'Amin' ya amsa mata kafin sukayi sallama ya kashe wayar tausayinta yana tsarga masa. Gidan hajiya ya tafi ta sa shi gaba da tambayar meya same shi taga ya rame haka yace mata babu komai aiki ne, a can yaci Abincin rana dabe iya ci a waje ba. Seda yayi sallar Isha sannanya tafi dauko su Umaimah yana tunanin yanda zasu qare da ita kuma.

Khausar
Tana isa gidan su Shema a tsaitsaye ta gaida Mamansu ta shige dakin Sheman tana cewa
"Qawata Na shiga uku, yanzu ya za'ayi?"
"Kiyi dagaske har Mama tajiyo ta san me kika qulla zaki wani shigo tun daga waje kina wa mutane terere" Shema dake kan gado ta fada, se Khausar ta rufe baki da hannunta tace

"Au wlh kaina ne ya dauki zafi na manta" ta zauna kusada ita tana sake cewa
"Ki bani mafita me ya kamata nayi yanzu kafin abubuwa su cakude mun?"

"Mafita daya ce da zata saka ya shiga taitayinsa kawai ki turawa Matarsa" Shema tta fada ba tareda ta kalleta ba Khausar tace
"Matarsa? Kina ganin hakan dabara ce nafa gaya miki yanda yake son matar nan tasa da kuma irin haukan kishinta da na samu labari idan na tura mata baza'a samu matsala ba?"

A hasale Shema ta kalleta tace
"Toh ke ina ruwanki kece a cikin hoton ko kuma ke zatayiwa haukan da kike jin tsoro? Kinga ni idan ba zaki ringayin abinda na gaya miki ba kije can ki qarata da yawarki karki kuma nemana"

"Haba Qawata abin be kai haka ba ai kawai dai ina jin tsoron kar wani abu ya faru nice sila yaqi aurena a qarshe kuma dai kinga abinda nake yiwa fafutuka kenan" Khausar din ta fada jiki a sanyaye se Shema ta sake galla mata harara tace
"Toh ai seki zauna kinga kinyi asarar kudinki da lokacinki a banza da wofi, kuma ki tashi ki fita karki sake kirana wallahi duk abinda ya faru"

"Aa baza'ayi haka ba yanzu nan zan tura mata bari kiga" ta fada tana zaro wayarta daga jaka. Budewa tayi sabanin hotonta dake kan wallpaper se taga babu daman tun sanda Waiter dazu ya miqo mata ta lura amma saurin da takeyi ya saka bata mayar da hankali ba.

WhatsApp ta shiga nema bata gani ba, se a sannan hankalinta ya dawo jikinta ta lura da wannan wayar kamar babu komai ma a cikinta. Miqawa Shema wayar tayi tana cewa
"Ke tayani dubawa, daidai nake gani ko duk rudewar ce"

Shema ta karba ta duba seta kalleta tana cewa
"Ya haka wayar babu komai akai? Allah yada ba a garin rawar jiki kika yi Restoring nata ba, ke kamar ma fa babu Sim akai" ta sake fada ganinbabu alamar Network. Wurin kira ta shiga ta loda number ta ta danna yaqi tafiya seta miqa mata tana dariya tace

"Tab lallai mutumin nan a shirye yake, ni daman nayi mamakin da ace wai zaku hadu keda bakya aiki da kwakwalwarki kika kwashi jiki kikaje, gashi nan ya nuna miki ya fiki iya wasa chanza miki wayar yayi".

Hannu biyu Khausar ta dora akai tana zare ido, se kuma ta tuna da Khalil ya rigata tafiya,
"Anya, bashi bane saboda ya rigani tafiya kuma se bayan ya tafin na kiraki"
"Toh a ina aka canza miki? Daga gurin se ina kika tsaya?" Shema ta sake tambayarta. Khausar da hankalinta idan yayi miliyan ya tashi tace

"Ban tsaya ko ina ba se office kuma ko a can ban fito da wayar ba sannan idan Khalil ne dole zan sani dan tunda muka zauna har ya tafi wayar tana gabana ko tabata beyi ba sedai idan..."

"Sesai idan me?" Shema ta fada tana kallonta,
"Shine ma wallahi, wani Waiter yazo daukar kwano wayar ta fadi ya miqomun sedai idan shiya musanya mun da tasa" Khausar ta fada kamar zatayi kuka. Dariya Shema tayi tace
"Na yarda dai Khausar baki da wayo, haka nan ze chanza miki wayane sedai idan saka shi aka yi gaba daya abin Set up ne kinga ke baki samu biyan buqata ba ya kwace wayar gaba daya, da ace kin ajiye a wani gurin nema da sauqi se ki godewa Allah da ya baki wata kuma kamar ma babbar taki ce kinga Asarar tazo miki da sauqi sorry babe" Ta qarasa tana fashewa da dariya se ganin hawaye tayi sha suna bin fuskar Khausar ta kuwa samu ta ringa tuntsira mata dariya kamar mahaukaciya.

"Yanzu duk abinda nayi ya tashi a banza kenan babu biyan buqata se wahakar banza dana sha" Khausar ta fada cikin kuka se Shema ta tsagaita dariyarta tace
"Maganin mara jin shawara kenan, ba yanda banyi dake baki samu wani gurin ki ajiye copy kikace Aa, idanma ni baki yarda dani ba nace ki siyi Flash ki saka a ciki duk kikaqa gashi yanzu baki ga tsuntsu baki ga tarko"

"Wlh banzan yarda ba zuwa zanyi na gaya masa nasan me yayi ya bani wayata ko na kai qararsa" Khausar din ta fada tana miqewa tsaye se Shema ta dakatar da ita da cewa
"Ki tabbata kin shirya tafiya kurkuku dan yanzu na tabbata idan ma qararki zeyi yana da duk wasu hujjoji a hannunsa karki manta wayarki sukutum ce a hannunsa, duk wani sirri ba naki ba har shi wanda ya hada abin yanzu yasan ko waye, bari ma na kira Dini na gaya masa yayi ta kansa a garin wawancinki kin tona muku Asiri" ta fada tana janyo wayarta Khausar ta riqe tana cewa

"Karki kirashi dan girman Allah, baki san irin warning dindaya mun akan idan aka samu matsala karna kuskura na sako sunansa ba idan ba haka seya mun ninkin abinda nasa akayi musu. Ki bari zansan yanda zan shawo kan abin dan wlh bazan haqura ba be isa yaci bulus ba".

Ajiye wayar tayi tana kallon ta tace
"Me kuma zakiyi yanzu bayan duk abinda kike taqama dashi ya goge?"

Goge hawayen fuskarta tayi ta janyo jakarta ta zazzage komai a qasa sega Memory ya fado, a wayar Sheman ta sakashi ta bude duka hotunan data aikawa da Dini yayi Editing ne a ciki Shema ta kalleta tace
"Amma wace toshewar basira ce ta saka kika iya ajiye wadannan amma baki ajiye masu amfanin ba? Wlh Khausar Dusa ce akan ki yanzu me zakiyi da wadannan hotunan?"

"Zasuyi amfani saboda a yanda na samu labarin matarsa tana da bala'in kishi yanda baki tsammani. Tare sukayi Poly da Bilkisu Auwal a gurinta na samu cikakken bayani akanta kuma zan sakw karbo lambarta a gurinta dan nasan bazata rasa ba idan ma bata da ita zata nemo mun kinga kuwa hotunan zasuyi amfani, wlh Khalil seya san ni ya yaudara dan wannan karon bazan bi takansa ba kaitsaye ita zan tun kara" Khausar ta fada tana wani murmushin mugunta.

"Kinyi dabara, amma ki bari ba yanzu zaki tura mata ba. Ki bari a dauki lokaci seya gama sakankancewa a qalla nan da wata biyu ko uku a sannan ya manta da abinda ya faru kuma baki neme shi ba, lokaci daya ki kunna masa wuta ki koma gefe kisha kallo" Shema ta fada tanabata hannu suka tafa.
*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ?AR'UWA, WATA-?ILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
?ar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassa?e da garin magunguna na gargajiya, waWanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taSa haihuwa ba?* Ko kuma sun taSa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa Sari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? ?ar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata Waya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haWa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*?ar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haWa miki magunguna kala biyar, waWanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daWewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haWi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiWa?* ?ar'uwa ko ki faWa ko kar ki faWa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan Waya wanda zai dinga shan ?aramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ?ara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huWu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haWin sabaya=?
?* HaWin sabayarmu duniya ne ?ar'uwa. Baza muyi miki ?aryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga she?i, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haWin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk Wauri Waya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuWin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuSeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo=?
?=?
?=?
?*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 40

Umaimah
Tana shiga dakin Mama ta samu kan kujera ta zube kaman jiqaqqun kayan wanki daman Mu'ayyad tun daga qofar gida Salman ya karbe shi. Mama na daga gefe tana sallar walaha seji tayi Umaiman ta fashe da kuka, gabanta ya yanke ya fadi, surar da take karantawa ta kwace mata se kawai tayi kabbara ta tafi ruku'u. A sujjadarta ta dade tana roqon Allah da koma menene Umaiman tazo dashi ya zama me sauqi ya kuma bata ikon iya dauka dan zuciyarta ta gama ayyana mata an sako Umaiman ne.

Koda ta idar tafi minti biyar kafin ta iya tashi ta isa kanta ta tsaya har sannan kuma Umaiman Kuka takeyi tana juyi akan kujerar kamar qaramar yarinya, kallon tsaf tayi mata, a haka dai batayi kalar tashin hankalin da za'ace sako ta akayi ba, ramar da taga tayi a fuska yasa tayi tunanin ko bata da lafiya se ta saki ajiyar zuciya taji sanyi a ranta seta nemi guri ta zauna tana cewa

"Lafiyarki Umaimah zaki kwanta kina kuka kamar wata qaramar yarinya meya sameki?"

Tashi zaune Umaiman tayi jin muryar Maman ta fada jikinta tana sake fashewa da kukan dayafi na farko, cikin kukan take cewa
"Na shiga uku Mama dan Allah ki kirashi kiyi masa magana da kanki qila yaji wallahi bazan iya na bana so".

Gaba daya ta jefa Maman a rudani, data furta shiga ukun nan seda taji wani rugugi a kanta amma maganganun da suka biyo kuma suka daure mata kai, zarginta na saki ya wanku sedai idan kuma wata tsiyar ta qullo. Ganin bazata nutsu tayi mata bayani ba se uban kuka takeyi ya sakata rabata da jikinta tana cewa

"Ya isa ki dena kukan Naji zan kirashi amma se kin yi mun bayani sosai dan ni ban fahimci abinda kike nufi ba, menene bakya so meye kuma bazaki iya ba? Wani abun Khalil din ya sakaki da bazaki iyayi ba kome?"

Hadiyar zuciya ta ringayi tana qoqarin tsayar da kukan dakyar Mama ta bata ruwa me sanyi tasha ta ringa jera ajiyar zuciya ita dai Maman ta zuba mata ido kawai tana kallonta, seda ta gama daidaita kanta kafin dakyar ta bude baki tace

"Ciki ne dani fa Mama, kuma na gaya masa bana so ban shirya ba amma ko magana yaqi yayi mun, yi yakeyi kamar ma baya jin me nake fada nidai ki kirashi ki gaya masa da kanki bana son cikin nan bazan iya haifarsa ba" tana gama maganar ta sake fashewa da wani kukan.

Hannu biyu Mama ta daga tana kallon gabas tace
"Allah kai ka bani ita saboda kasan zan iya, Allah karka barni ni kadai ka kama mun a cikin lamuran Umaimah" tana gama fadar haka ta miqe dan bata san me zata ce mata ba, kai idan ta ci gaba da zama a gurin tsaf zata rufeta da dukan da ze iya sanin cikin jikin nata da take iqirarin bata so, Allah ya shiryi Umaimah kawai yasa ta gane gaskiya kafin lokaci ya qure mata.

Dakin ta ta shige ta barta nan palour tana ganshe qar kuka, kiran sunanta da Anty take kwalawa ya saka ta fito, Antyn na tsaye kan Umaimah dake Amai tsabar yanda ta galabaitar da kanta da kuka tana ganin Maman tace
"Bakijiyo kakarinta ba? Nifa tun daga tsakar gida na jiyota banma san da zuwanta ba dan na dauka ma Nuratu ce tazo itace me lalura".

"Uhm banji ba nika baccine ya fara kwasata, kuma tsabar iskanci duk gidan nan ki rasa a ina zakiyi wa mutane Amai se a cikin palour na, to ki tashi ki gyara gurin wallahi kafin raina ya baci nayi miki abinda ba zakiji dadi ba" Mama ta fada tana kallon Umaimah dake mayar da numfashi se Anty tayi saurin cewa

"Haba Mama bakiga halin da take ciki bane kiyi haquri kin fa san yanayin Amai idan ya taho ba'a iya tare shi"
"Nata ai na iskanci ne masifarta ce ta janyo shi, wallahi Umamaih kibi duniya a hankali idan ba haka tam" Maman ta sake fada tana juyawa ciki Anty ta bita da kallo gaba daya kanta ya daure da maganar Maman seta juya kan Umaimah dake sabon kuka qasa qasa, 'uhm' ta fada kafin ta kamata ta miqe daga cikin Aman tana cewa
"Ki shiga ki gyara jikinki bari na gyara nan" ta shigar da ita dayan spare dakin Mama ita kuma ta fita dakko paker da tsintsiya.

A cikin daki Mama kasa zama tayi ta juyo ta dawo palour ganin Anty na kwashe amai yasa ta tambayeta tana ina ta nuna mata dakin da take seta ta wuce ciki kaitsaye daidai sanda Umaiman ta fito bayan ta wanke fuskarta.
"Zonan Umaimah" ta fada

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login