Showing 375001 words to 378000 words out of 429394 words

Chapter 126 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1021

bata gama daidaita ba daman kuma duk sanda ciwon ya motsa masa yana fuskantar haka Gabansa ya tashi amma bana jin dadi ba na zallar Azaba da ciwo.

Saurin janye hannun tayi cikin kunya ta kwanta a jikinsa tana cewa
"Nidai babu ruwana daman gari na wayewa zamu tafi Asibiti a dubaka dan hankalina ya tashi da yanayinka, ko sanda kana Asibiti banga kayi murqusus irin haka ba"
"Yes baby ai ko baki fada ba dole naje Asibiti dan na samu tabbacin abinda nake yaqini in sha Allahu na samu lafiya Baby" ya qarasa yana qanqameta da haka bacci ya daukeshi, irin baccin da rabonda yayi shi tun kafin a daura auransa da Humaira.

UMAIMAH
*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 80

UMAIMAH

Washe garin ranar ta tashi da sanyin jiki fiye dana ko yaushe, yau kam ko arziqin daga hannun bata samu a gurin Mama ba data gaisheta da alama fushi takeyi da ita dagaske, hannu ta saka ta share guntun Hawayen daya zubo mata a ranta tana ayyana me yasa Maman take mata haka? Batayi fushi da ita bama ya ta qare? haka ta ringa ayyukan gidan da suka zame mata jiki tun tana jin wahalarsu harta saddaqar ta haqura dan ruwa da iska babu abinda yake hana tayi gashi wata qudura ta ubangiji a tsahon kama aikin nata batayi wani shahararran ciwo da ze saka a daga mata a qafa harta samu damar fita akaita Asibiti taga waje ba, ita kam ta manta ma yanda unguwarsu take yanzu shekararta Uku da watanni a kulle cikin gida kamar wadda ta kashe mutum.

Tana cikin share tsakar gidan Bayan La'asar saboda ruwan sama da akayi yazo da qura ta gama sharar ta tattarata guri daya ta fita Gareji inda babban Dustbin dinsu yake ta juye akayi sallama cike da mamakin wadda take gani a gabanta ta saki abin sharar tana kallonta lokaci daya wata irin kunya ta lullubeta. Rumasa'u ce tsaye gabanta da qaton cikin da zata iya juye shi a ko yaushe tayi qiba tayi kyau badan sanin data mata bana wasa bane tsaf zata iya cewa kamace, tambayar da takeyiwa kanta yaushe Ruma tayi aure har gata da ciki amma bata da labari?

Kamar yanda Umaimah ke kallon Ruman itama haka ta zuba mata ido tana so ta tantance itan ce ko kuwa a hankali ta kira sunanta Umaiman ta dago ta kalleta kadan ta sake sunkuyar da kai lokaci daya kuka ya kwacewa Ruman ta matsa kusa da uta babu bata lokaci suka rungume juna suka shiga kuka kamar an aiko musu da mutuwa
"Wane irin abu ne haka zaku zo kan hanya kunawa mutane koke koke ke daga zuwanki bakiga halin da take ciki ba zaki daga mata hankali? To saketa juya ga megidan naki can a tsaye daman be wuce ba" Abba daya shigo ya fada cikin fada fada se Ruma tayi qarfin halin sakin Umaimah ta kama hannunta suka shige ciki Abban na tsaye yana sababin akan me daga zuwa zata sakata kuka da tsohon ciki salon wani abu ya sameta. Su Umaimah kuwa dakin da take suka shige suka sake rungume juna suna garsheqar kuka, seda sukayi me isarsu, irin wannan damar Umaimah ta dade tana nema ta samu abokin kuka daze fuskancin dacin da takeji,
dakyar Ruma ta daidaita nutsuwarta ta miqe tana cewa
"Bari naje mu gaisa da Mama na kuma sallami Barr dan ziyarar tawa ta canza akala" seta fice tana jan qafa da alama cikin nata yayi nauyi dab take da saukewa.

Mama kanta tayi mamakin ganin Ruman dukda tasan tayi aure kuma bata ga laifinta na qin sanar dasu na saboda ta dade da sanin Umaiman ta watsar da ita kamar yanda ta watsar da duk sauran qawayenta na kirki ta cicciba ta fita, Mijinta Barr na tsaye jikin motarsa yana jiranta dan ta sanar masa ba zama zatayi ba tun kafin suzo Kano dan a Sokoto take aure take nanata masa idan sunje zataje gidansu Umaiman da ya haddace sunanta saboda yanda take yawanyin hirarta, ta rasa number ta kuma tambayo duk qawayensu bata samu ba dan haka jiya suka zo yau tayiwa gidan tsinke danta gaida Mamanta kuma karbi number Umaimah se gashi taci karo da sabon Al'amari.

"Har kin fito?" Barr ya fada yana qoqarin bude mata mota seta yi qasa da kai saboda kar yaga idonta da sauran hawayen dake ciki tace
"Kaje kawai Barr zuwa bayan Magriba se ka dawo la daukeni na ma tarar da Umaiman tana ciki".
"Are you ok? Yanaga kamar ma kuka kikayi?" Ya fada yana matsawa kusa da ita tareda nazarin fuskarta setayi saurin juyawa dan tasan yanzu inya fara jera mata tambayoyi ba sauqi tace
"Kaje kawai idan mun koma gidan zan gaya maka koma menene" ta shige gidanta barshi yana binta da kallo tareda hasashen meya samu qawar tata tunda tace tana ciki ko duk kewar ta ce ta sakata kuka haka yaja motarsa ya tafi kafin Magribar tayi ya dawo ya dauketa.

Ruma kuwa dakin Umaimah ta sake komawa, tana nan inda ta barta ta zubawa bango ido alamar tayi nisa cikin tunanin da takeyi hawaye suka sake kawowa a idon Ruman data qarewa Umaimah kallo, ko a hasashe bata taba tunanin akwai taskun da ze sameta ta dawo haka ba, ta tabbata akwai wani babban Al'amari daya faru wanda bata da masaniya seta zauna a hankali ta dafa kafadar Umaiman tayi firgigit ta kalleta a tare kowacce ta sake fashewa da kukan da take riqewa suka rungume junansu kuka Umaimah takeyi me nuna raunin ta da irin halin da zuciyarta take ciki wanda tafe yake da tarin nadama da dana sani tareda neman mafita. Tun Ruma na kukan itama har tayi shiru ta shiga rarrashin Umaiman da dakyar ta iya hadiye kukanta badan ta gama gaba daya ba sedai kawai ta samu sauqin nauyin abinda ya danne mata qirji.

"Umaimah ki fada mun meya sameki, ki fitar dani daga rudanin da ganin yanayinki ya jefani meya faru?" Ruman ta fada cikin qoqarin son hana kanta sake fashewa da kuka dan yanayin Umaimah ya raunata mata zuciya da yawa. Seda Umaiman taja numfashi tana riqe da hannayen Ruma biyu kafin ta bude baki cikin muryar kuka tace
"Komai ma ya faru Ruma ni yanzu abinda kadai ya ragemun ganin ranar da zan koma ga Allah dan a duniya na rigada na rasa kowa da komai nawa"

"Kiyi mun magana a bude Umaimah kiyi mun bayani yanda zan fahimta, kamar yaya kin rasa kowa? Ga Mama da Abba na gani da Ransu basu mutu ba Yanayin dana ganki na san cewa akwai wani al'amari mara dadi a tareda ke Umaimah kin ganki kuwa kinga yanda kika koma?" Ruma ta fada tana kallon Umaiman tareda dauke kwallar dake qoqarin sake dawo mata. Umaimah ta dauke kanta gefe tana goge nata hawayen nauyi da kunyar Ruman ya rufeta idan ta tuna wukaqancin data mata a baya se taji bata cancanci ta sake hada ido da ita ba, Ta banzatar da ita a matsayinta na Aminiyarta tunta yarinta da take saita ta a hanyar kwarai take kuma gaya mata gaskiya.
Rabonta da Ruman tun Haihuwar Bibi, qarfi da yaji ta yakiceta daga rayuwarta saboda tana gaya mata gaskiya itama kuma tayi zuciya ta fita daga sabgoginta kamar yanda ta fada Umaiman bata da Aljanna ballantana taci gaba da binta tana wulaqantata tun daga nan suka yanke alaqa bata sake ganinta ba se yau da kwatsam ta fado gidansu kamar jifa a yanayin da tayi mamaki kwarai.

Matsa hannunta Ruman tayi cikinsigar lallashi tace
"Ki tuna a baya babu abinda muke boyewa juna, Rumanki ce fa idan baki sanar dani damuwarki ba wa zaki gayawa?" A hankali Umaiman ta bude baki muryarta na rawa tace
"Ruma rayuwata ta gamu da qalubale kala kala a halin yanzu ina cike da Nadamar abubuwan dana aikata a rayuwata na godewa Allah daya kawo mun ke a daidai lokacin danake buqatar taimako wlh Ruma a yanda nake ji na tabbata wata rana za'a iya wayar gari a tarar da gawata zuciyata ta buga na mutu saboda irin baqin cikin da nake kwana dashi nake tashi"

Ki dena fadar haka Umaimah duk abinda kikaga ya samu bawa a rayuwarsa da sanin Ubangiji"
"Haka Ruma kuma duk abinda ya sameni ni na hawa kaiba, halina ya jefani a yanayin danake ciki kuma nasan da cewar haqqin Khalil ne ya fara bibiyata tun yanzu, Ruma banida nutsuwa bana iya bacci har na rasa me nake tunani kaina da qirjina tamkar zasu fashe haka nake jinsu gashi a cikin gidan nan babu me saurarata kowa haushina yakeji basa kulani sun gazayi mun uzuri su karbi cewar tawa kalar qaddarar ce a haka" Umaimah ta sake fada tana fashewa da kukan daya fi nada rauni ita dai Rumana riqe da hannu ta tana matsawa alamar rarrashi tana kuma qoqarin gano inda bakin zaren maganar Umaiman yake a hankali ta Sake ce mata

"Qawata me yayi zafi har haka, me kika aikata da har su Mama sukayi fushi dake? Yanzu yan uwanki da har kwatance akeyi daku saboda yanda kowa ya shaida qaunar dake a tsakaninku suka banzatar dake me kika aikata Umaimah?"
Shiru Umaiman tayi kafin ta nisa a nutse ta shiga warware mata iya abinda take ganin ya kamata ta sani. Ruma ta ringa kiran sunayen Allah saboda rudanin da labarin Umaimah ya jefata, a sanyaye tace
"Umaimah kinyi kuskure kin kuma shafawa kanki baqin fentin da gogeshi zeyi wuya domin kin taba martabar da ba kowa zaka keta masa ya dauke kai ba, na tabbata yau da ace rigimarki ta tsaya iya kan Khalil da tuni kowa dade da mantawa saboda tsakanin Mata da Miji daman ana sabawa kuma a koma a zauna kamar ba'ayi ba amma Uwa fa Umaimah kin keta alfarmar Mahaifiyar sa koda ace Allah ya qaddara da sauran zama a tsakaninku a duk sanda ya kalleki se wannan abun ya dawo masa sannan mafi muni shi a karan kansa kin bar masa tabon da har abada baze manta dake ba a kullum ina gaya miki ki dena biyewa zuciyarki ki ringa amfani da kwakwalwarki yanzu kin gane abinda nake nufi? Ita zuciya a koda yaushe tana qawata mana son ranmu duk kyau ko munin abu yayinda kwakwalwa takanyi lissafi ta tantance abinda ya kamata da wanda be kamata ba. Na tabbata a lokacin da kin yi amfani da Tunaninki ba son zuciya ba da yanzu haka bata faru ba amma duk da haka lokaci ne qure miki ba kina da damar ko tubarwa Allah ki kuma nemi gafarar duk wadanda kika batawa amma a farko se ke a karan kanki kin yarda da cewar kinyi ba daidai ba"

"Na nawa kuma Ruma na rigada na yarda da cewar na aikata kuskure nayi dana sanin komai daya faru rashin mafitar yanda zanyi na gyara shine abinda ya dameni yake cin zuciyata duk dare da wannan baqin cikin nake kwana nake tashi. Iyayena muna zaune gida daya dasu Ruma na rasa alfarmar da zasu amsa koda gaisuwata yan uwana kaf babu meyi mun magana na zama kamar wata mujiya a cikinsu yau tsayin shekara uku da watanni kenan Ruma ban sake saka qafata a qofar gidan nan ba tunda aka sallamoni daga Asibiti Abba ya kafa mun dokar babu fita kullum ina zaune nike aikin komai a cikin gidan nan amma dukda haka be sa sun rangwanta mun ba a kullum qara kyarata da hantarata akeyi a cikin gidannan a ganina ko Mutum na kashe ai iyakar abinda zasuyi mun kenan" Umaimah ta fada muryarta na rawa se Ruma tayi qaramin murmushi tace

"Umaimah kenan iyayenki da yan uwanki suna yi miki haka ne saboda ki gane kuskurenki kuma koda ace kinyi nadama ke a karan kanki bana zaton kin nuna musu hakan kinga kuwa dole zasu ci gaba da nuna miki halin ko in kula tunda baki nuna musu kema kin gane kuskurenki kuma kin shirya gyarawa ba".
"Toh ya zanyi, ta yaya zan nuna musu na karbi kuskurena Ruma?" Umaiman ta katseta se Ruma tace
"Tun da al'amarin nan ya faru wa kika taba samu a cikin su ke dashi kika bashi haquri kika nuna musu cewar kinyi nadama kuma kin karbi kuskurenki?" Ruma ta fada tana tsareta da ido a sanyaye tace
"Babu"
"Dama na tabbatar da amsar Babu ce danna sanki farin sani tun ba yanzu ba baki san kiyi laifi ki bada haquri ba nayi tsammanin aure yasa kin canza ashe har yanzu kina nan da baqar kafiyarki da da babu abinda take ja miki kullum se wahala. Har ki iya zama tsayin shekara uku Mahaifanki suna fushi dake ku kwana gida daya ku tashi bama kya tsoron ki mutu a wannan halin me zaki gayawa Allah meye hujjarki ta kasa neman yardarsu?"

"Wlh Ruma nayi, Abba cewa yayi karna qara gaisheshi Mama ta hanani shiga dakinta itama idan na gaidata ba amsawa takeyi ba ya zanyi?"

"Ya zakiyi kike tambayata, saboda sunce karki sake gaidasu se kiji ki dena gaishe shin saboda tsabar rashin tunani irin naki ai a lokacin nema ya kamata ki daura dambar gaidasun da duk wata kyautatawa da kika san zata saka zuciyoyinsu yin sanyi su sauka da fushin da sukeyi da ke amma se kika zauna kina jira su gaji da fushin su sakko su su nemi kushirya kome ashe ma ke kika haife su basu suka haifeki ba" Ruma ta fada fusace se Umaimah tayo saurin cewa
"Ba haka bane wlh..."
"Na sanki Umaimah babu abinda zaki gayamun wanda ba gaskiya ba na yarda idan na rantse bazanyi kaffara ba muguwar zuciyarki har a yanzu tana ayyana miki cewar abinda kikayi daidaine shiyasa kika qi Sasantawa da Mahaifanki ki nemi gafarar su to tun wuri idan kin shirya gamawa da duniya lafiya Umaimah ki san abinda kikeyi ki kuma maida Al'amuranki ga Allah shine kadai Mafita a gareki yanzu".

Maganganu masu shiga jiki Ruman ta ringayi mata ta fito mata da laifukanta ta kuma bata hanyoyin da zata gyara har wata nutsuwa Umaiman taji tana sakko mata saboda ta samu ta amayar da abinda yake cinta kuma an bata mafita in sha Allahu kuma zatayi amfano da duk a?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? binda Ruman ta fada mata. Nisawa Ruma tayi ta gyara zamanta tace
"Toh yanzu ina yaranki, suna tare dake ko ya riqesu?"

"Suna gurinsa, tunda muka rabu ma se jiya aka taba kawo su kuma basu dade ba matarsa tazo ta daukesu" Umaimah data rafka tagumi ta bata amsa se Ruma tayi wani murmushi me ciwo tace
"Kayya kin gani ko? Duk haukanki da tashin hankalinki babu abinda ya hana gashi nan tana zaune dashi ke kuma kina gida cikin qunci da takura meye ribar abinda kikayi? Ai wlh Umaimah da ace kinsan me kikeyi tundaga sanda aka ce miki an rigada an daura aure ya kamatavki zubda makamanki saboda kinsan cewar yaqin ya wuce kan Khalil Ubangiji yayi ikonsa idan kika matsa abinda bazaki so ba ze faru gashi kuwa"

"Harta haihufa Ruma" Umaiman ta sake fada kamar zatayi kuka wani mugun kishin Khalil din yana taso mata amma tayi qoqari ta hadiye is Ruma ta tafa hannu tace
"Kinji ba, to qila da baki bar gidan bama ki mutu tunda baki yarda da qaddara ba Rabon sa na jikinta da a titi kike so ya haifi dan" se kuma ta kama baki tace
"Ikon Allah bashi da haqqinki nakasar da kika so ja masa Allah beyi ba".

Yanda kasan ta cakawa Umaiman Mashi a qirji haka taji, Khalil ya samu lafiya kenan yanawa yarinyar nan kalar abinda yake mata shiyasa harta kasa ganeta tayi qiba tayi fresh jiki duk madara kawai ta fashe da kuka ba tareda ta shirya ba tunanin Khalil na Mu'amala da Humaira kamar ze zautata
"Tab toh Allah ya kawo miki dauki Umaimah gashi can ana kiran sallah bari mu tashi nasan da an idar Barr ze dawo" Ruma ta fada tana yunqurawa Umaimah ta rage qarfin kukanta tana cewa
"Baki fada mun yanda naki al'amuran suka kasance ba se kawai ganinki nayi da ciki bayan tsahon lokaci"
"Wannan labarin wata rana ne Umaimah se hankali ya kwanta kedai kiyi hanzarin gyara alaqarki kafin lokaci ya qure miki" daga haka ta shige bandaki ta barta tana jan Majina.

A dakin sukayi sallah har bayan sun idar seda Ruma ta sake yi mata tunatarwa akan yawan ibadah,
"Ki daure Umaimah cikin dare idan kin juya ko raka'a biyu ce kiyi ki kaiwa Allah kukanki yafi kwanciyar da kikeyi alhalin ba bacci kike ba bakinki karya zauna shiru daga ambaton Allah kiyawaita yin tasbihi da istigfari sannanki rage damuwa dan babu abinda zata miki sedai ta haifar miki da ciwo ta lalata miki jiki ko a yanzu baki ga yanda kika koma ba kamar me ciwo duk ina gayunki Umaimah kalli fatarki yanda ta yamushe kamar ta tsohuwa"

"Uhm Ruma kenan har wani maganar gayu kikeyi keda kike cikin nutsuwar zuciyata data jiki ke kike buqatar kwalliya wa zanwa" Umaimah ta fada tana janye tagumi kafin Ruman ta bata amsa wayarta ta shiga qara ta daga ganin Mijinta ne yake kira ya sanar mata yana waje seta miqe bayan ta kashe wayar tana gyara gyalenta Umaiman ta kalleta tace
"Badai tafiya zakiyi ba?"
"Tafiya zanyi mana zamuyi waya idan kuma na samu dama gobe ko jibi zan dawo" ta bata amsa se Umaiman ta miqe tsaye itama tana cewa
"Na fada miki banida waya yanzu, dan Allah ki dawo Ruma wlh bakiji yanda naji dadin zuwan ki ba da zan samu ace kullum kizo dana rage kewa"

Dariya Ruma tayi tana cewa
"Lallai ko kiyi qoqari ki gyara kura kurenki zakiji dadin rayuwarki Umaimah dan rabuwarki da Khalil bashine yake nufin rayuwarki tazo qarshe ba kici gaba da Addu'a in sha Allahu zaki samu madadinsa a gaba" daga haka tayi waje Umaiman ta bita a baya kamar kazar da kwai ya fashewa gaba daya bata ji dadin kalaman Ruman na qarshe ba yanda ta nuna bata da sha'awar ta koma gidan Khalil kenan. A tsakar gidan suka tarar da Mama tana qarasa girki dare Anty na zaune daga bakin qofarta suna hira se sannan Ruma ta gaida Anty ta amsa da fara'a Mama tace
"Kin fito Ruma?"
"Na fito Mama ya dawo zamu wuce ne" ta bata amsa tana sunkuyarda kai, taso a daki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login