Showing 162001 words to 165000 words out of 429394 words

Chapter 55 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1012

ya sani musamman Hajiya kin san bata son damuwa musamman kuma akan abinda ya shafi Khalil" Jalilan bayan data amsa sallamar Umaimah.

Wayar ta harara a ranta tace 'aikin banza' a fili kuwa kukan qarya ta fashe dashi tana cewa
"Toh ya kike so nayi Anty Jalila so kike na zauna ina ji ina gani ya dakko mun masifa ya kawo gida? Na san baze taba fada muku gaskiya ba dan nima besan na sani ba shiyasa ban bi takansa ba kai tsaye na sanar daku dan nasan idan na fara masa magana qaryatawa zeyi sannan ya toshe duk wata hanya da gaskiya zata fito. Nidai wallahi tun wuri kuyi masa magana idan ba haka ba ni bazan zauna ba ya aurota haka kawai wani Gingimemen baka'i ya sauka a gidan mu ba iya kanta ze tsaya ba harda mu ze shafa" ta cigaba da rusa kuka kamar gaske ita dai Jalila ta kasa magana dakyar ta iya cewa
"Shikenan kiyi shiru hakan ma bazata faru ba da iznin Allah kuma na tabbaatr da shi kansa Khalil din be san haka take ba da babu abinda ze kaishi gurinta. Kuma ma ana ta neman layinsa kusan kwana biyu kenan daman bana samunsa ko a Whatsapp bana ganin sa Online in sha Allahu komai ze daidaita kinji ki dena kuka" daga haka sukayi sallama akan zata sake kiranta.

Tana kashe wayar ta sheqe da dariyar shaqiyanci dan ko a jikinta wai an mintsini kakkausa. Whatsapp ta shiga, Messages ta tarar rututu a duka? groups din nata kaitsaye kawai ta bude Group din daya fi mata dadi, kusan kaf maganar ita akayi tagging abinda ta tura jiyan, qarshe ta tafi inda taga wata tace

"Kai wannan ai Hadiza Musa ce, Lawyer ce kuma tana aiki a hukumar kare haqqin mata da qananan yara ta garin nan ko amma kuwa dai ta bata wayonta wallahi, kunsan yanda ake yabon kirkinta da kamun kanta kuwa ko kwatance za'ayi a gurin na mata masu kamun kai da ita akeyi amma ashe ashe tab abinda take aikatawa a boye kenan amma anji butur wallahi"

"Daman ai laifi bashi da kama yanzu da Allah ya tashi tona mata Asiri ai gashinan, kuma ta jira taga sakamakonta" Umaimah ta rubuta nan sukayo mata caaa kowa da tambayar a ina ta jiyo wannan magana dan daman tun cikin daren wadansa suka fara gani suke tambayarta, har PC gwanayen gulma suka bita tuni kuma da yawa suma sunyi forwarding saqon zuwa sauran group sedai Allah ya taqaita tsayuwarsa kawai.

Rufaida ce ta kirata a waya ta daga tana cewa
"Ke tun Asuba nake kiranki baki dauka ba"
"Bangani ba se yanzu na dauki wayar kuma banma lura da kiran ki a ciki ba" ta bata amsa, se Rufaidan tayi saurin cewa

"Umaimah ina kika samo waccen jaridar, naji fa ana ta fadar Lawyer ce matar kuma da Human right take aiki bakya tsoron labari ya koma mata ki shiga uku? Koma ba wannan ba kinsanfa irinsu wallahi daurin gindi ne dasu a qasa ance duk matan manyan nan harkar suce yanzu idan tana da Connection da wata babba kar ki jawa kanki fa kina zaman zamanki azo a kamaki".

Tsaki Umaimah ta buga kafin tace
"Wanda be kamani ba baya qaunar uwarsa da ubansa, ke an gaya miki ni ina tsoron ta mutu ne balle tayi rai? To bari kiji ba Lawyer ba ko ita ce An tourney matsalarta ce ita ya shafa bani ba. Bana kwaina seda zakara dan haka daga nan gar majalisar dinkin duniya muje inada shaidar da zan tabbatar da abinda na fada akanta, saboda bakisan wacece ita ba shiyasa har kike magana"

"Au wai kinsanta a gaske ne, ni na zata fa a social media kema kika samo kike yadawa?" Rufaida ta fada cikin salon son jin labari, nan Umaimah ta karkace ta fara zayyano mata hadinta da Hadizan, Rufaida ta qunduma Ashar kamar diyar Maguzawa tace

"Amma Allah ya isa tsakanina dake Umaimah yanzu haka ta faru baki gaya mun ba, me yasa tunda zakije gidan su matsiyaciya baki gaya mun mun hadu a hanya ba? Ai wallahi da se munci Abu ta kaza kazan uwarta kai lallaima. Banga laifinki bari ma ki gani yanzu zan dora a Facebook qarshen terere shegiya La'ananniya ta qara shan tsinuwa ta tagayyare yansa ko tuba tayi bazata samu me kallonta ba" Rufaida ta fada kamar zata fito ta cikin wayar sbaoda hayagaga.
Magana suka ci gaba dayi, ita a sonta ma su sake komawa gidansu Hadizan tunda Umaimah tace bata sameta na dukda ta boye mata dukan data sha ba seta ce mata su bari kawai iya wannan ma ya isheta sukayi sallama ta koma WhatsApp aka ci gaba da fafatawa masu tsinewa Hadiza da aibatata sunayi masu tausaya mata da nema mata shiriyar Allah sunayi ita dai Umaimah ta shiga wannan group ta fita wannan tana kallon yanda abubuwa suke gudana zuciyarta qal kamar an mata Albishir da wani muqami ko a yanzu Kasuwa ta tashi ita ce da riba.

Chat ta yiwa Khausar take gaya mata ta fallasa sirrin Hadizan a duniya yanzu kowa yasan wacece ita, ganin bata online yasa ta koma ta kirata amma layin a kashz ta tabe baki irin ko oho daman dan ta gaya matane kawai tunda itama tana da fushin Hadizan tunda bata dauka ba shikenan se kawai ta shiga sabgoginta.

HADIZA
Seda ta kwana biyu bata fita aiki ba saboda yanayin rashin jin dadi da take ciki, gaba daya Mama ta fita a sabgarta ballantana Yaya Isma'il da tasan Mama ce ta hana shi tabata amma in har suka hadu kallon dayake aika mata dashi bata iya ko gaishe shi take wucewa.

Ranar ta tashi da dan qarfin jiki saboda amsa gaisuwarta da Maman tayi har take tambayar ta dalilin rashin fita aikinta kwana biyu dan haka ta hau shiri a ranta tana Addu'ar Allah yasa Maman ta fahimceta ne kamar yanda kullum bata gajiya da addu'ar Allah ya wanketa a idon Maman daga mugun qazafin da Khausar take mata.

A qofar gida ta hadu da Isma'il daya zo gaida Maman kamar kowacce safiya, ya banka mata harara kamar koda yaushe tayi saurin kauce masa, ta tabbatar da Mamace ta hana shi taba lafiyarta da babu shakka se ya huce fushinsa akanta. Titi ta fita dan ta nemi abin hawa, ta tuna in lafiya lafiya ne zece ta jirashi shi ze sauketa a gun aiki suna tafe suna hirar su gwanin sha'awa amma banda yanzu da sam Khausar ta shiga ta fita ta hana faruwar hakan. Kallon qofar gidansu tayi, idan suka taho da Yayan se sun tsaya sun dauketa zasu wuce idan ma badashi bane seta biya mata tun yarinta har zuwa yanzu amma ashe ita tana da wani mugun nufi a ranta da take ajiye dashi tsahon lokaci
"Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu" ta fada a fili tana share kwallar data ziraro mata.

Sanda ta isa gurin aikin nasu kamar yanda ta saba tun daga gate ta fara gaisarda Ma'aikatansu manya sa qanana sedai yanayin da suke amsa mata ya bata mamaki ga wani kallo da suke rakata dashi da sam ta kasa fahimtar na menene ne haka ta wuce ciki jiki a sanyaye can dinma dai kamar na wajen dan ko sallamarta babu wanda ya amsa illah idanu da suka zubo mata kamar sunga Mujiya.

Jikinta ta kalla ita dai bataga wani abu da ze saka a kalleta ba dan doguwar rigar Lace ce a jikinta ta dora dogon Hijabi ya wuce guiwarta, haka fuskarta tasan farar powder da kwalli kadai ta saka ballantana ace ko wani abun ne yayi yawa ta zama abar kallo, wucewa tayi Table dinta dake can loko ta ajiye jakarta ta fara karkade qurar da gurin yayi da alama babu wanda ya taba a kwanakin da tayi bata zuwan idonta ya sauka a mazaunin Khausar da babu kowa a ranta ta ayyana qila bata qaraso bane ko sun fita yin wani aikin.

Tana zama ko cikakken minti biyu ba tayi ba Zuhra Secretary Shugabar su ta zo kanta, bata ji zuwanta ba se dogon tsakin da taja tana kallonta kamar kashi tace
"Kije Hajiya tana kiranki kuma kiyi sauri karki bata mata lokaci" ta sake jan wani tsakin harda tsartar da miyau abinda yayi bala'in qonawa Hadiza rai amma ta hadiye bata kulata ba. A iya saninta suna shiri da Zuhra kai ita kaf gurinma bata da Abokin fada kowa gaisuwar mutunchi da wasa da dariya ne yake hadata dashi to duk me ya kawo wannan sauyin kuma yau? Bata da me bata amsa dan haka ta miqe da wayarta a hannu Zuhran tayi saurin dakatar da ita da cewa
"Tsaya ki dauki jakarki dan nasan daga can gaba zaki qara kinga ba sekinyi tafiya biyu ba" se kuwa ta tsaya ta tattara abubuwan data fito dasu ta mayar harga Allah a ranta ta ayyana wani aikin zata fita shine dalilin kiran da Hajiyar tayi mata dan haka ta sa kai ta fita tana jin wata na cewa
"Uhm a haka dai kamar ta Allah ashe Akuya ce da fatar kura, kai Allah yayi mana tsari da masifa ya shiryesu idan suna da rabo".

"Toh fa wai me yake faruwa ne?" Ta tambayi kanta abinda bata da me bata amsa. Tunani takeyi kala kala a zuciyarta harta isa office din Hajiya. Dukda daman ba Mace ce me yawan fara'a ba amma yanayin data ganta a ciki yasa tasha jinin jikint.

Kujerar gaban Table din ta nuna mata ta zauna a darare tana gaisheta, bata amsa ba ta turo mata wata farar takadda da biro akai kafin ta dago fuskarta sam babu fara'a tace
"Ki saka hannu a nan, takaddar suspension ce saboda bazamu iya ci gaba da aiki dake ba a wannan yanayin da ake ciki, idan da ta tawa ne zamuyi Firing naki ne take amma na samu directives daga sama akan karnayi hakan saboda suna ganin kinada Influence sosai a wannan ma'aikatar, to koma menene ni bazan taba tolerating misconduct irin naki ba, ba zan ci gaba da aiki dake ki jawo mana bacin suna a wannan Qungiya ba dan haka kije ki kuma dauka cewar mun koreki kawai dan ko zaki dawo kamar yanda suke tunanin badai ina nan ba, ba kuma idan nasan wanda yake heading Ma'aikatar nan ba".

Gaba daya kanta ne ya qarasa qullewa, taja takaddar gabanta tana dubawa badan tana gane komai ba saboda ya da tunani suka cushe mata harta rasa wanne abu zata tuna a ciki.
'Meta aikata da har yayi zafi haka?' Shine tambayar da takeyiwa kanta, tsawar da Hajiyar ta daka mata ce ta sakata dagowa da sauri ta kalleta,
"Kiyi sauri ki saka hanni Malama ki fita ki bani guri, bana son ganin wannan disgusting face din taki" ta fada cikin tsawa jikin Hadiza ya dauki rawa, dakyar ta iya riqe biron ta saka hannu kamar yanda ta umarceta ta fincike takaddar tana harararta tareda nuna mata qofa.

Kaitsaye Get ta nufa tana jin yanda duk inda ta wuce suke jifanta da maganganu marasa dadida har sannan ta kasa gane inda suka dosa a haka har ta fice daga gurinta tsaya bakin titi tana tarar abin hawa. Seda ta zauna a cikin Adaidaita tayi shiru tana saqa da warwara domin gano bakin zaren.e tayi da za'a dakatar da ita daga aiki, yanzu idanta je gida ma me zata gayawa Mama? Ji tayi kanta ya sara mata saboda tunanin da tayi, yanzu ace hotunan da Khausar tayi musu barazana dasu ne ta watsa kamar yanda tayi iqirari fa?

Babu shiru ja ciro wayarta dake cikin jaka saboda sauri har tana subucewa ta fadi qasa ta duqata daukota cikinrawar jiki ta kunna Dat ta shiga WhatsApp dana kwanakin bata samu nutsuwar yin chatting bama. Saqonni ne babu adadi suka ringa shigowa amma bata su takeyi ba, Searching sunan Khausar tayi ko zata ga ta aiko mata da wani saqo amma babu komai, qarshen maganarsu tunda ta tura mata da receipt na dubu dari biyun data sa ta aika mata basu sake magana ba.
Fita tayi daga chat din, saqonnin wasu mutane da ta manta rabon ma da su
magana ya dauki hankalinta, abin Mamaki da yawansu Tsofaffin samarinta ne se qawayen da sukayi karatu tare irin wadanda inbada babban dalili ba ko a chatting dinba l akeyi ba.

Yanda taga saqunan nasu a jejjere wani na bin wani ga kuma tarin numbobi da babu suna ya qara sakata a rudu seta bude chat din farko na Umar Tsohon saurayinta ne wanda daga shi ne ta hadu da Khalil, taso shi amma halayyarsu bata zo daya ba dan tantirin manemin matane tunda ya fito mata da muradinsa ta nuna masa ba haka take ba ya dauke qafa ya dena nemanta.
"Hadiza kenan, nayi matuqar mamaki na kuma tabbatar da baki da kunya, ke a yanda kike har kike iya mun wa'azi da gaya mun Allah yace Annabi yace ko? Koda yake daman na zargin hakan..." Kiran waya ne ya shigo ya katse mata karatun da takeyi seta daga ganin Anty Bilkisu ce matar Yaya Isma'il.

"Duk inda kike Hadiza ki maza kizo gidan nan yanzu karki koma gidan Mama" Abinda ta fada mata kenanta kashe waya daga muryarta ta karanci zallar tashin hankalin da take ciki seta kalli me Adaidaita dake ta yan waqe waqensa tace
"Malam bi nan Darmanawa zamu koma"
"Toh Hajiya" ya bata amsa yana shiga kwanar yan Katako suka ci gabada tafiya. A qofar gidan ya ajiyeta ta bashi kudinsa ta shiga, Anty Bilkisu na tsaye bakin qofar palour ta cikin shirin fita tana hangota tace
"Allah sa baki sallami me Adaidaitan ba fita zamuyi" seta juya da sauri har ya fara tafiya ta tsaidashi ta fito suka shiga yaja. Aisami tace ya kaisu unguwar su Anty Bilkin seta raya a ranta ko ba lafiya ba.

"Bani wayarki Hadiza" ta fada seta zarota a jaka ta miqa mata daidai sannan kiran Yaya Isma'il ya shigo zata daga Bilkisunta fizge ta kashe wayar gaba daya ta saka a jakarta. Tata wayarce ta shiga ruri, ta ciro ta duba shidin ne seta riqeta a hannu har kiran ya katse wani ya dake shigowa sanann ta daga. Seda ta daidaita muryarta kafin tayi sallama muryarsa ta katseta yana cewa
"Duk inda kuka tafi ku dawo yanzu Bilkisu keda Hadiza, wallahi in har kuka dara Minti talatin baki kawota gidan Mama ba a bakin auranki kuma saki uku" yana fadar haka ya kashe Bilkisu ta kalli Hadiza data tabbatar da taji abinda Yayan nata ya fada saboda kidima bata iya magana ba se Hadizan ce ta tsaida Me Adaidaita tace su Koma Na'ibawa ya karkata Mashin yana cewa
"Ba matsala hajiya aikin kudi nakeyi ai".

"Anty Bilki ki gaya mun abinda yake faruwa dan Allah dan na fara rasa tunanina. Daga zuwana gurin aiki aka bani takaddar sallama, kin kirani babu shiri kince nazo sannan ga maganganun da Yaya ya fada menene dalilin da z kafa sharadi a bakin auranki? Meyake faruwa dani dan girman Allah ki gaya mun saboda nasan abinda zan tunkara" Hadiza ta fada tana jijjiga Bilkisu da tayi shiru kamar wadda ruwa ya cinye, kallon tausayi tabi Hadizan dashi ba tateda tace komai ba ta maida kanta tana kallon waje ganin haka ya saka itama Hadizan taja Hijabinta ta rufe har fuskarta a zuciyarta tana maimaita duk addu'ar datazo bakinya. Bata san menene ya tunkaro rayuwarta ba amma tana fatan koma menene Ubangijin daya jarabceta dashi ya bata ikon dauka.

Tundaga qofar gidan tasan ba lafiya ba, Kukan Mama da kururuwarta dake jiyowa da wasu muryoyi da bata tabbatar da masu su ba suna bata haquri nan take jikinta ya dauki rawa ta coge a qofar soron saboda wani matsanancin tsoron abinda zata tarar daya dirar mata a zuciya. Anty Bilki ce ta kama hannunta tana cewa
"Muje Hadiza Allah yana tare da me gaskiya muma kuma muna tare dake karkiji tsoron komai in sha Allahu ubangiji ze wanke ki"
"Me akace na aikata?" Ta fada cikin wata irin karyayyar murya tana kallon Anty Bilki da kwalla ke zubo mata, seta jata suka shiga gidan ba tareda ta amsa mata ba, a tsaitsaye suka tarar da Mata uku, Malama Lawisa maqociyarsu ce kuma Aminiyar Mama se Hajiya Zuwaira itama qawarta ce ta kusa da sukayi aiki tare se kuma Alhaji Sunusi Mahaifin Khausar wanda suka riqe tamkar uba.

"Yawwa gatanan, na gaya miki daman babu inda Hadiza zataje, kiyi haquri ki sauqaqawa zuciyarki Karima idan baki shaidi yarki ba waye ze bata kariya a duniyar nan" Hajiya Zuwaira ta fada tana kamo hannun Hadizan zuwa gaban Mama data yi saurin ja da baya tana cewa
"Ta fita bana son ganinta, ta fita na barwa duniya ita. Yanda kika ci mutunchinmu hadiza kika tozarta mu kema Allah yayi miki haka. Kin cucemu kin cuci Ahalinmu kije kici gaba da abinda kika zabawa kanki amma daga yau ki saka a ranki baki da uwa, ki fauka tamkar daga sama kika fadi baki da kowa ki riqe rayuwar da kika zabawa kanki ta zamar miki uwa da uba da dangi kije gaki ga duniya Hadiza".

Sulalewa tayi daga hannun Hajiya Zuwaira ta zube ta shiga jan guiwoyinta har zuwa gaban Maman dake kuka kamar ranta ze fita, cikin rawar jiki ta kai hannu zata tabata kafin ta kai ga hakan Maman ta dauketa da wani gigitaccen Mari da seda jinta ya dauke na wani lokaci kafin ta kalleta tana cewa
"Idan kika kuskura kika tabani da qazamin hannunki ban yafe ba ki kuma tashi ki fice daga gidan in har ba qarasani kike so kiyi da baqin cikin ki ba, wallahi Hadiza nayi nadamar haihuwarki. Da nasan abinda zaki jawo mun kenan dana danneki tun dana haifeki kin mutu kowa ya huta"

"Subhanallahi wai Karimatu bazaki dena jifan yarinyar nan da mugayen kalamai ba. Koma menene hannunka baya taba rubewa kayar, addu'a da neman shiriyar ubangiji ita take da buqata a yanzu ba mugayen kalaman da zasu qara tagayyara rayuwarta ba. Ke Hadiza tashi kije, kuje can gidan ki zauna karkije ko ina daga nan ina zuwa" Alhaji Sunusi ya fada cikin bacin ran abinda Maman takeyi. Tunda mugun labarin ya riske shi yana kasuwa yaji yaran shagonsa suna surutu da la'antar yarinyar har yaji daya yana fadin yar unguwarsu ce ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login