Showing 129001 words to 132000 words out of 429394 words

Chapter 44 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

984

lemon tsami idan safiya tayi ta sake gigita masa kwakwalwa da zafafan shigar da takeyi sedai ya fita ya bar mata gidan wannan kuma tasan na dan lokaci ne dolensa ya bada kai bori ya hau a haka ya cinye hutun sati daya da aka bashi kafin yaci gaba da zuwa aiki office dinsa na nan Kano.

Tunda Sukayi maganar Hadiza da Hajiya ya fara jada baya da ita yawan wayar da sukeyi duk ya rage dan yana tsoron ta zargeshi da laifin yaudararta a gaba idan ya kasa shawo kan Hajiyarsa akan lamarin.
Tun tana yarda da uzururrukan aiki da yake bata ko kuma wani lokacin yace yana gidan idan ta kira harta fara gane kawai yana qoqarin yakiceta ne daman tun wancan zuwanda yayi gidansu ranar daya dawo be sake komawa ba ya dai je office dinsu sau biyu har suka je cin abinci a zuwansa na biyun tareda ita da Khausar a ranar ne yake nuna musu hoton Umaimah da Mu'ayyad Khausar din take tambayarsa ina Madam Hadiza tace har yanzu be hada su sun gaisa ba shine ya nuna musu hotonsu da suka dauka tare.
A hannun Khausar ya bar wayar tanaci gaba da kallon Hotunansu se zuzuta kyan da sukayi takeyi shi kuma suna yar hirar su da Hadiza seda lokacin break ya qare sannanya mayar dasu gurin aiki shi kuma ya wuce Site dan ranar be zauna a office ba.

A ranar chan gida kuma Umaimah ta karbi baquncin yayyenta Maman Asad, Yaya Naziyya data shigo Kano se Yaya Nuratu. A daki suka sakata suka fara dayi mata wankin babban bargo dan duk cikinsu babu wadda tasan zaman da Umaiman tayi a gida se daga baya. Yaya Naziyya na Minna, Maman Asad taje Umarah daman ta Somotto suka tafi garinsu Mijinta da suka dawo ma can suka yada zango Nuratu kuwa aiki ya hanata Sakat Mijinta ya tafi wani aiki ita take riqe masa Call tayi nata tayi nasa shi yasa bata samun lokacin kanta balle taje ko ina shiyasa basu sani ba seda Yaya Naziyya tazo Maman take gaya mata babu shiri ta kirawosu mitin din gaggawa.

"Amma Mama idan da laifin Umaimah kema da naki, na rasa wai fin qarfinku yarinyar nan tayi ko tsoronta kukeji da kuke zuba mata ido tana duk iskancin data ga dama. Me yasa sanda tazo baki saka ta a gaba ta kira Mijin kiji da kunnenki dagaske shi yace ta taho gida ba idan taqi kuma se ki kirashi ko ki gayawa Yaya Aminu? Gaskiya Mama sekun sake lale akan lamarin Umaimah idan ba haka ba kuma wallahi gaba se tayi abinda kowa zezo yana ya za'ayi tunda bata da tunani, ganin kuma idan tayi tana cin banza ya saka kullum iskancinta gaba yakeyi ba baya ba" Yaya Naziyya ta fada sanda Maman ta gama gaya mata yanda akayi washe gari da safe shine suka rankaya suka tafi gidan.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS>???>???*

*=؞?Barkan mu da warhaka en uwa mata, bugu da qari ba kadai a bangaren kayan gyaran aure ingantattu ta tsaya ba, ta na bada magunguna na musulunci akan cututtuka na yau da kullum wanda suke damun al'umma.*
*Cututtuka irin su matsanaicin ciwon mara a lukuta mabanbanta ko kuma lokacin al'ada, daukewan al'adan lokacin daukewan bai zo ba, al'ada ya rinqa wasa, rashin sha'awa ko ciwon kai, ciwon qirji wanda aka rasa gane kanshi ana tunanin ulcer ne, kuma anyi maganin amma har yanzu ba a dace ba, matsalar Ashiq wato aljanin soyayya(wannan sai bayan tambayoyi sannna za a tabbatar). Ciwon ciki, hawan jini, ciwon sugar, ciwon hanta, typoid/malaria, basir, ciwon baya da qafa, ciwon qashi da kuma matsalar infertility, duk da haihuwa Allah ne ke badawa amma kuma a wasu lokutan akwai cututtuka da kan kama mahaifa ko kuma reproductive system din mace wanda su kan iya hanata daukan ciki. Cututtuka irin su Endeomatriosis, cervicitis, fibroids, etc.*

*Ku karzayo domin lafiya uwar jiki=ت?=ت?, sannan ta bangaren gyaran aure, sumayyas herbal ta lashi takobin qara zage damtse wajen inganta kayayyakin ta domin samun maslahan ku a* *rayuwar ku da auratayyan ku. Aure dai ibada ne a don haka gyaran aure wajibi ne, musamman idan kin samu in da zaki gyara kan ki da kayayyaki na kwarai wanda basu da illa ga lafiya kuma ba irin kayan da zasu Kai ki ga halaka ba,su saki rasa imanin ki duk wai da sunan gyaran aure. Ah ah er uwa ayi hattara kar garin neman gira a rasa ido.>??? @&? Allah ya tsare mana imanin mu=?O?=?O?*
*Garzaya ki dannan link din kuma kiyi saving number ta domin kuwa akwai alfano mai yawa.*
*Wa.me/+2347031876677*
*Ko kuma akan Instagram*

*https://www.instagram.com/p/CqQJVrVIdjq/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==*
*Allah ya biya mana buqatun mu na alkhairi amin.*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 35


An ci babbar Sa'a sun tarar da ita tana zaune a palour tana danna waya Hauwa na goye da Mu'ayyad tana mopping da yake Get din a bude yake ta aiki Aliyu bata so ya dawo yayi ta bugawa shiyasa sun zuwa suka shige se ganinsu tayi tsulum akanta.

Ashariya me maiqo Naziyya ta fara aika mata da ita sanda taga Hauwa ta fito daga dakin Khalil da bokitin mopping kafin taci gaba da cewa
"Babu shakka Umaimah kin shahara, kina zaune babu aikin fari balle na baqi wata zangamemiyar budurwa ce zata shiga ta gyara miki inda Mijinki yake kwanciya taga sirrin sa ko? To zakici ubanki, notikan kanki da suka kwance yau munzo da spanun da zamu daure miki su tamau"

Seta juya kan Hauwa da tayi tsamo tsamo tace
"Ke kuma a gidan nan kike ko kuwa?"
Da sauri Hauwa tace
"Aa zuwa nakeyi"
"Kwanto shi ki fita ki bamu guri" Naziyyan ta sake fada fuska babu wasa jiki ba rawa ta kwance yaron Maman Asad data fi kusa da ita ta karbeshi daman da Hijabin ta a wuya ta fice da sauri Umaimah dai tunda ta sunkuyar da kai bata dago ba tasan yau kan kashinta ya bushe a gurin Naziyya cinyeta ne kadai ba zata yi ba.

Seda suka fara da zageta tatas wannan ta aiko mata ta nan waccen ta aiko tata, fadan qazanta da sakaci suke mata Nuratu tace
"Ashe kishin naki na banza ne da har zaki bar qatuwar budurwa kamar wannan ta shiga dakin Mijinki ta gyara saboda sakarci da rashin sanin ciwon kai" murya na rawa dan ta zagu a gunsu tace
"Bafa ta zuwa se baya nan kuma kafin ya dawo ta gama yimun komai ta tafi"

"Dalla rufewa mutane baki a nan gyaran wannan gidan ne har wani abinda se kin nemo matayi saboda lalaci ina aikin yake? Kuma idan ma zaki nemi me aikin kiyi abinda hankali mana idan seta miki gyaran ta gyara palour zuwa tsakar gida da kitchen ke aikin uwar me kikiye banda Chatting din banza da bazakiyi komai ba? Ai wallahi Umaimah kin bani kunya mudai ba'ayi mata tarbiyyar qazantaba amma gashi nan ke kinzo kinayi kuma duk in kika sa aka zagi Mama Allah seya saka mata dan tarbiyya daya tayi mana gaba daya zubar da taki kikai a hanya" Maman Asad ta fada a hasale.

Haka suka kasa suka tsare seda ta tashi ta qarasa aikin da Hauwa ta fara dan daman mopping din palour kadai ya rage se wankin Mu'ayyad data fita dasu tsakar gida zatayi.

Se bayan da suka nutsa Naziyya ta tada maganar zuwanta gida da tayi ta share sama da wata babu wanda yasan Dalili, hade rai tayi tana kallon gefe tace
"Tafiya yayi kuma lokacin Babansu Shahida ya rasu shiyasa bamu tafi tareba da aka gama zaman makoki yace na zauna a gida kawai har ya dawo".

Kallon junansu sukayi Nuratu ta numfasa tace
"Amma Mama tace ko waya bakuyi ba har kika gama zamanki se qaninsa ne yake kai miki kayan amfani kuma da zaki dawo basu sani ba kika gudo, bayan nan ma seda aka ci kusan sati kafin ya dawo Kano"

"Toh wai dan Allah ina ruwanki kuma lauya kika zama da zaki tasani da tambaya ko yaya? Gajiya nayi da zaman na dawo gidana waya kuma lalacewa wayata tayi seda ya dawo ya kai mun gyara ai Maman ta sani" Umaimah ta fada tana hararar Nuratu tunda itace marainiyar wayonta ta baya Naziyya ta taske mata qeya ta dafe gurin dan zafin hannu ne da ita tace

"Haba Yaya Naziyya da zafi fa"
"Ai daman saboda kiji Zafin na dakeki dama ban daukeki da mari ba, duk cikin mu babu yaro kuma babu sakarai irinki ballan tana kiyi mana wasa da hankali. Uban me kikaje yi gida har kusan wata biyu bayan kowa yasan duk Tafiya kota kwanaki ce tare kukeyinta da Khalil wallahi ki fada tun a mutunce idan kinqi zan kirashi na tambayeshi yanzu" Naziyya ta fada se Umaimah ta hau zare ido, ganin babu sarki se Allah da Naziyya ta kirashi ya fadi gaskiyar yanda akayi gara tayiwa kanta qiyamullaili tayiwa zancen kwaskwarima yanda baza'a ga laifinta ba dan haka tace

"Nifa ba wani abu nayi masa ba tafiya ce ta taso masa ranar da zamu tafi Mijin Anty Hafsa ya rasu ya barni ya tafi shi kadai ni kuma daman bani da lafiya, da aka gama zaman makokin yace na bishi na gaya masa bani da lafiya shikenan fa yayi fushi yace na zauna ko naje babu amfanin da zanyi masa"

"Baki da lafiya wace irin cutace take damunki data hanaki binsa kuma duk bamu sani ba sannan akan me zeyi fushi in har dagaske rashin lafiya ce ta hanaki binsa" Maman Asad ta katseta, Umaimah ta matso hawayen qarya tace

"Toh ai kansa kawai ya sani daman shi dai biyan buqatarsa ne matsalarsa shiyasa da nace bani da lafiyar yayi fushi ai"
"Dan ubanki wace rashin lafiya kika samu abinda muke so muji kenan" Naziyya ta sake zaburo mata se Nuratu tayi murmushi tace

"Bata bakinku kuke babu kowacce rashin lafiya baze wuce tace bazata bishi bane yanda ta saba shine zeyi fushi kuma daman ai dole za'a zo nan, duk sanda zeyi tafiya bazata bishi ta dadin rai ba daman wata rana zeyi zuciya yace ta zauna a gida mana".

"Ai wallahi nidai na dade banga Macen da bata san kanta ba irin Umaimah. Duk ni'imar da mace zata roqa a gidan aure Allah yayi mata amma bata godewa to kici gaba idan baki godewa Ni'imar Ubangiji ba zaki godewa azabarsa. A zamanin nan Ki samu Miji ya ringa yawo dake ai abin ki gode Allah ne kina ma da matsayin da baya so yayi nesa dake Allah na tuba matan gasu nan birjik a titi idan ya fita ze samu dari da zasuyi masa rakiya duk inda zeje amma Allah ya tsare miki mijinki ya tsare mutunchinsa shine kike so ki turashi duniya ko kici gaba" Maman Asad ta fada se Naziyya taci gaba da cewa

"In banda daqiqiyace ma Umaimah Mijinki mabuqaci kin sani amma har a ringa tababa dake akan binsa wani guri idan be tafi dake ba gurin uwar wa kike so yaje ya sauke lalurar sa ko kuwa matan banza kike so yaje ya nema? Ai idan kinada hankali wallahi dama kika samu da zaki qara kafa kanki a zuciyarsa duk inda ya shiga kina gefensa kina bashi farinciki ta yanda babu wadda ta isa ta sako miki kai amma ki saki Miji a bariki Yanzu wata biyun da kika barshi shikadai a can kina nan kina ballan sorinki kinsan abinda yaje yayi ko kuwa se an zo maganar kin ganshi da Mace ne zaki fara yiwa mutane hauka kina rashin hankali
babu kintsi babu gyara se Tijara da rashin mutunchi kika kware dayi ko to ki kuka da kanki wallahi duk abinda yaje ya dawo da kudinki kika siya kuma ko Matan banza ya nema ki tabbata zunubinki yafi nasa ga tsinuwar mala'iku ta saba masa da kikayi ga kason zunubin duk tsiyar daya aikata naki ma seya fi nasa yawa".

Kamar Kazar da ruwan sama yayiwa duka haka jikinta yayi sanyi qirjinta ya shiga dukan dari dari yanzu fa tsahon kusan sati uku da dawoqar Khalil banda kwanakin da yayi a can ace be nemi wani abu a gurinta ba ga rashin gaskiyar da take gani idan an kirashi waya yanzu ko tashi daga aiki ya qara lokaci seya kai Bayan Magriba be shigo gida ba wata ran har Isha kao abubuwan da yawo se yanzu ma take tunano su haka ranar nan taji qamshin wani turare a kayansa abinda yasa batayi magana ba taga turaren a Jakar Office dinsa amma ai ba cikakke bane qila ma ragowar na budurwar tasa ne ya karbo, Su Naziyya nata magana se gani sukayi ta dora hannuwa biyu aka tana kiran

"Na shiga uku shikenan Khalil ya fara neman Mata"
"Uhm kunga kalar haukan nata ko duk cikin maganar da mukayi ita abinda zuciyarta ta ayyana mata kenan anya Umaimah kitse be lullube miki kwakwalwa ba inaga shi yake hanaki tunani dakyau" Yaya Naziyya ta fada, Umaimah kuwa kukan gaske ta fashe dashi tana cewa

"Wallahi Yaya Naziyya sedai idan Khalil mata ya fara nema shine kadai ze saka yaqi kulani kusan wata uku"
"Wata uku?" Suka hada baki gurin fada, ta gyada musu kai cikin tabbatarwa tace

"Tsakani da Allah bayan ya tafi har kudi ya turo akan na bishi nace bazanje ba. Ni wallahi bana son tafiye tafiye tun Asali kuma kun sani kuma idan mukaje wani guri qara damuna yakeyi kusan ko yaushe muna tare koya fita baya dadewa yake dawowa duk gajiya nakeyi a maimakon na huta shiyasa wannan karon nace masa ba zanje ba shine fa yayi fushi har ya gama zamansa be kirani ba se sau daya kuma daya dawo ma baya shiga harkata daga gaisuwa shikenan tsakaninmu, nayi duk abinda zanyi har kaina na kai masa amma yayi mun wukaqanci" ta qarass cikin kuka sosai se aka rasa me magana a cikinsu dakyar Nuratu ta iya cewa

"Amma Umaimah kinyi wauta waya ce miki kana nunawa Miji ka gaji da buqatarsa? Tsanarki zeyi tunda bazaki iya biya masa buqata ba baki da wani amfani a gurinsa. Ke bama zaki godewa Allah bakya aikin komai se zaman gida ba, ni yanzu nace me? Wallahi har mantawa nakeyi da wani abu Sex kwata kwata hankalina ma baya kaiwa kanshi kina kallo kullun sena fita aiki banida lokacin kaina ballantana na hutu amma dukda hKa ban taba qin Amsa kiran Mijina ba. A na gaji wani lokacin rabi bacci rabi ido biyu a hakan zan biya masa buqatarsa, wani lokacin a Asibitin ze nemeni haka zanje amma ke kici kisha ki kwanta kuma a hakan kike cewa kin gaji gaskiya kiyiwa kanki fada"

"Duk bazaku gane ba" ta fada kafin taci gaba Maman Asad ta katseta da cewa
"Daman ai bazamu gane ba, kuma da ki????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ke cewa tunda ya dawo yaqi kulaki ta ina ze kulaki kuwa baki san kin masa laifi bane, koda ya dawo kin bashi haquri?
"Haquri kuma? Ni me nayi masa da zan bashi haquri naga nima ya shiga haqqi na ya tafi ya barni tsahon lokaci a gida baya ko kira yaji ya muke" Umaimah ta fada tana zumbura baki Maman Asad tace

"Ahaf ai na sani to shi ce miki akayi maye ne da ze kulaki bayan ke baki san kin masa ba daidai ballema ki bashi haquri? Ko kuwa tunda ga Namamajo daga kinyi masa karairaya shikenan ya manta duk laifin da kaika masa se ya sakko yaci gaba da binki gara ya nuna miki ai koda abin ko babu shi ze rayu kinga se ki jiqa abinki kisha tunda rowarsa kike masa.

Ke baki san idan miji ya qauracewa matarsa shine qololuwar horon da zeyi mata ba ko Aa se shirme da hauka kika saka a gaba a wautar ki idan jarabarsa ta tashi dole ze kawo kansa to kici gaba tsinuwar Mala'iku kadai ta isheki ai.
Yadai kamatu zuwa yanzu ace kinyi hankali kuma kema kin isa ki gayawa wani yanda yavkamata yayi ba ace kullum ke ake yiwa fada ba. Zaman auran nan fa ibadah ne Umaimah yana kuma da dokoki da sharudda ba kara zube ake yinsa ba, idan baki nutsu kinbi Allah ba wuta zaki kai kanki a banza babu ruwan Khalil dan yana shiru baya ce miki komai akan abinda kikeyi Shi Allah babu ruwansa zeyi miki hukunci daidai da abubuwan da kika aikata"

Haka suka ringa yi mata fada da Nasiha tare da bata shawarwari tayi laqwas kamar ta dauka harda yar kwallarta ta kuma Alqawarin zata gyara idan Khalil ya dawo zata bashi haquri in sha Allahu ba za bashi haquri basu bar gidan ba seda sukayi sallar Azahar ta dafa musu Indomie sukaci sannan sukayi Haramar tafiya zasu biya gidan Anty Hafsa. Bayan tafiyarsu ta tashi yin tuwon shinkafa da Miyar Yakuwa saboda Khalil yana sonsa. Hauwa ta kira ta daukar mata Mu'ayyad dukda jan kunnen da suka gama shi mata akan hakan amma bataji ba.

Ta tuqa tuwanta ta malmale ta hada miyar gaba daya gidan ya dauki qamshin girki dan Umaimah gwana ce gurin iya sarrafa abinci musamman na gargajiya qyuyace take hanatayi. Seda ta sake gyara gidan ta turare ko ina kafin qarfe shida ta gama komai har Mu'ayyad an dawo mata dashi ta masa wanka ta shirya shi tsaf suka zauna jiran Khalil

Tunda ya shaqi qamshin turare daya cakude dana girkin da yayi ya saki murmushi, har ga Allah yayi missing komai nata, dole ta saka yake nesanta kansa da ita dan yana so ta fahimci girman laifinta tayi nadama amma abin ya gagara.
Da sallama ya shiga, fuska babu yabo babu fallasa daidai nan ta shafa Addu'ar da takeyi ta miqe tana cire Hijabin da tayi sallah tayi masa sannu da zuwa. A sama ya amsa yana nufar dakinsa yana kallon yanda take kallonsa se yaga kamar jikinta a sanyaye yake ba kamar yanda ya saba ganinta ba, tabe baki yayi ya shige daki yasan wani wasan kwaikwayon ta shirya kuma.

Wanka ya farayi, yana bandakin wayarsa daya ajiye akan gado ta dauki qara, a jikinsa yaji cewar Hadiza ce dan ta kirashi yana tuqi yace idan ya tsaya ze kirata yasan taji shiru ne ta sake kiransa dan ita kuma haka take da nacin tsiya bata da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login