Showing 423001 words to 426000 words out of 429394 words

Chapter 142 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

952

da take tsaye, badan bata yarda dasu ba sedai shedan baya raina qofa ko yaya take. khalil da Umaiman masoya ne da ko Makaho ya shafa yasan suna qaunar Junansu kuma shedan na matuqar son irin lokutan nan na rauni dan ya shigar da lamarinsa. Har qasa ya durqusa yayiwa Mama sallama yana sake yi mata Allah ya sanya Alkhairi tace baze jira Abinci ba yace Aa, Anty suna gidan Amarya yin jere yayi musu sallama ya tafi Umaimah daki ta wuce ta kife a gado taci gaba da Gamsheqar kuka, Mama ta duba Envelope din daya bari, Daloline a ciki bata san ko nawa bane dan ba sanin kansu tayi ba amma suna da yawa ta rufe envelope din ta zazzage kayan cikin ledar, wani dan Akwati ta gani me kyau ta bude shi Zobuna manya ta gani guda biyu da Awarwaro suma guda biyu na gold se sauran takracen fashion Dan kunnaye, zobe Agogo, Ribbon turaruka wasu yan qanana na Mai kusan guda biyar ba'a budeau bama se Hijabi guda daya dogo da carbi ta ringa mamakin wadannan kuma daga ina? Wata farar takadda ta gani ta dauka yayi rubutu kamar haka
"Kayanki da suka rage a dakina, kudi kuma na kayan furnitures dinki ne da Abba ya hana a diba" ina miki fatan Alkhairi".
Jikin Maman yayi sanyi laqwas, duk yana ajiye da kayanta tsahon lokaci kenan ita kam bata san wane kalar So Khalil yakewa Umaimah ba, komai idan ya faru tabbas akwai hikima me yawa tattare da faruwarsa ta tabbatar a irin wannan zazzafar soyayyar zasu iya halaka gaba daya ma. Da Abba ya dawo ta dauki kayan gaba daya ta kai masa ya ringa juya kai yana cewa
"Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi a tsakaninsu, haqurin da sukayi Allah yasa ya zame musu kaffara.

Se bayan Isha yan jere suka dawo jiki a sabule, Umaimah na daki har sannan tasha kuka ta haqura tana ta jan carbi Naziyya ta shiga ta sameta tana cewa
"Tab wannan gida naku Umaimah se ace Allah ya zaunar lafiya, kinga kishiyar taki kuwa? Aba kamar Kazar mayu amma masifar dake cikinta tafi girman giwa. Hana mu shiga gidan tayi fa tasa aka kulle get, seda megidan yazo da kansa ashe shima ba kwallo bane tantirin dan Tijarane in gaya miki suka ringa rashin mutunchi a tsakar gida ya zageta ta zageshi mudai kamar mu juyo Mama Asiya tace ai ba zancen juyowa haka muka shiga muka jera abinda ya sawwaqa. Keda meya hana kice ya kama miki gida tunda kinsan yanda tsarin gidan nasa yake?"

Kallon Naziyyan ta ringayi dan sam ta gagara gane inda kalamanta suka dosa, zancen matarsa be dameta na amma shidin da take cewa sunyi zage zage a tsakar gida a gabansu ya daure mata kai matuqa hartace
"Kabir din?"
"Shifa, ai bakiga abin mamaki ba, tube kaya yayi daga shi se vest da gajeran wando yace su daku har yana ce mata kar dan ta ganmu ta dauka ze raga mata mu ba baqin da zeji kunya bane kai ai yau nikan naga abinda ya isheni. Ba wannan bama, Daki biyu ne fa ya baki daya sama daya qasa, falonku daya haka kitchen, kujeru dai daman ba'a rigada an dakko ba da su Fridge da cooker suna inda aka siya mukace a barsu idan kun daidaita kin samu gurin ajiyesu seki dakko, an dai saka gadaje ragowar duk abinda be shiga ba su Kayan kitchen da sauran tarkace suna gidan Hajiyayye tun muna can da muka kira Mama tace ayi abinda ya samu wanda be samu guri ba mu kai can mu ajiye".

Jikin Umaimah ya ninka da sanyaya zuciyarta ta ringa bugawa da jin sabon Al'amari, duk zancen gida da wani waye be dameta ba kamar abinda Kabir din yayi kenan kurane da fatar akuya yazo mata da suffar Kamala ashe kwankwararran Dan tasha ne tunda Namijin da ze tube a gaban dangin matar da bata rigada ta tare a gidansa bama yace zeyi dambe da matarsa ta gida ai ko ya isa Executive Dan tasha. Tsabar rudewar da tayi bata ko iya fitowa daga daki ba tana jin su a tsajar gida suna ta maida zance, Kabir din ya ringa kiranta amma taqi daga wayar, to me zata ce masa ko me zece masa ita kam wannan aure ma bata ga yuwuwarsa ba gaskiya ba abinda ta shiryawa ba kenan aure take so tayi na Ibada ko babu jin dadi tana buqatar kwanciyar hankali.

Da Asuba tana idar da sallah ta tafi qofar dakin Abba ta tsaya jiransa dan daren jiyan har mafarki ta ringayi wai ana kaita sun hadu shida matar sun mata dukan tsiya. Abba ya gama saurarar qorafin data zo dashi kafin yayi murmushi yace
"Tun jiya Antynku ta gaya mun komai kuma nayi takaici matuqa da jin abinda ya faru amma ya muka iya da hukuncin ubangiji? Kiyi haquri bawa baya gujewa qaddararsa abinda zan gaya miki kawai kiji tsoron Allah ki saka a ranki kinyi aure dan ibadah dama kowanne aure da kalar qalubalensa a yanzu ne zakiyi zaman aure na haqiqa dan a baya kinyi rayuwa ne irin wadda ke kika tsarawa kanki dan haka kiyi haquri" ta ringa kuka, kenan Abba yana nufin a haka zataje ta tare gidan Kabir din kome? Allah ma ya sani ba zata iya ba, ita daman ba wani sonsa take ba lallantana ace taje tayi haquri ta tafi falon Mama ta dasa mata kukan dukda Al'amarin itama ya shammaceta amma haka ta dake ta maida mata magana tamkar ta Abban tana gaya mata qaddararta ce dan haka tayi haquri se taga qila sanadiyyarta ya shiryu su dena Tijarar da akace sunayi daga shi har Matar.

Ranar ko gyaran jikin da take bata iya zuwa ba ba, cike take da zullumi, wato dukda ta samu afuwar wadanda ta zalunta a baya haqqin aure data wulaqanta na nan yana bibiyarta.
"Allah karka jarabceni da gidan aurena na tuba nayi nadama ubangiji ka karbi tubana ka sassautamun" ta fada tana tsananin kuka. A karo na bar katai Kabir ya sake kiran wayarta bata dauka ba tana tsaka da kukan sejin sallamatsa tayi a tsakar gida ta zabura ta leqa danta tabbatar shidinne kuwa yau ko Shaddar da yake sakowa babu T-shirt ce da wandon Jins ya tsuke abinda kamar wani qaramin yaro takaici ya kawo mata wuya, haskensa da da take gani ya dusashe cike da takaici ta kalleshi se wani doka mata murmushi yake yana cewa
"Na kasa samun nutsuwa tun jiya nake kiran wayarki bakya dauka lafiya? Me yasami idonki haka suka kumbura?"

A maimakon ta bashi amsa se ta sake fashewa da wani kukan takaicin kawai ta juya daki, yayi kamar ze biya suka hada ido da Mama da tun sallamarsa ta fito itama seya sosa kai itama cike da takaici tace masa
"Shiga mana" ta juya daki abinta tuququn baqin ciki na taso mata. Da tayi haquri a inda Allah ya ajiyeta ai da bahakaba, tana zaune cikin rufin Asiri da wadata ta raina ni'imar da ubangiji yayi mata daman idan baka gode masa ba zaka godewa Azabarsa.

Umaimah kuwa tana shiga daki Kabir ya bita duk ya rikice yana tambayarta me akayi mata
"Dan Allah ki gaya mun in ba so kike nima na miki kukan ba" ya fada yana matsawa kusa da ita tayi saurin direwa daga gadon tana jifanta da wani mugun kallo tace
"Karka kuskura ka tabani, gara da Allah yasa na gane wanene kai tun kafin na shiga gidanka dan haka yanzu base anjima ba saki na zakayi dan bazan iya zama da Tantiri mara nutsuwa irinka ba"
"Ikon Allah" Kabir din ya fada yana gyara zama kafin ya tuntsure da wata dariya kamar sabon shigan hauka yana cewa
"Tantiri na tantiriya" yasake kwashewa da dariya seta tsaya kawai tana kallonsa yayi me isarsa kafin yasha kunu yana jifanta da wani kallon raini yace

"Sa'arki daya a cikin gidanku nake da wlh sena gurje miki baki akan zagina da kikayi kuma bari na fada miki tun a nan ni ba lusari bane irin sakaran Mijinki na baya da kike zagi kamar Almajirinki ya shanye kallon da bae gamsheni ba idan kika mun casaki zanyi ahto na san jiya yan gidanku sun gaya miki yanda naci uwar Abida to basuga komai ba dan haka duk wani gigi da rashin mutunchinki ki haqa rami a nan ki binneshi karki ce zaki gidana dashi. Ke banda ma ina neman wadda zata ringa cimun uwar Abida dan itama ba kyalle bace kina zaton zan aureki ne bayan duk labaranki da nake dasu? Bafa wani sonki nake can can ba ni inaga ma Asiri kika mun wlh amma babu komai ai na taimaka miki na rufa miki asiri dan wlh badan niba sedai ki qare rayuwarki a gidan nan babu me tsautsayin da ze kwasheki dan haka tun wuri ki shiga hankalinki jibi qarfe hudun yamma za'a kaiki ki shirya in ma kika bata mun rai ba zaki tare ba anan zan barki kiyi ta zama kuma wlh na sake kira baki daga mun waya ba se na miki rashin mutunchi".

Kamar mutum mutumi haka ta zama har ya gama Tijararsa ya fita ya bar mata dakin, ta zube akan guiwoyinta hannu akai a fili ta furta
"Na shiga uku ni Umaimah" tana sake fashewa da sabon kuka, da wannan zata zauna wato pretending ya qare ya fito mata a zahirinsa kenan shikenan rayuwarta ta shiga lahaula ita kam. Da yammacin ranar Hajiya tazo kamar yanda Khalil ya gaya mata Umaimah ta kasa daga kai ta kalleta ita kuwa ko a jikinta ta ringa mata addu'a da saka albarka tareda nasihohin da seda suka saka Mama ta zubda hawaye. Cikin dattako ta ringa tariyo mata kuskurenta na baya tana fada mata yanda zata kaucewa sake maimaita su, tsadaddun Food flask ta kawo mata saiti biyu da Jug shima me shegen kyau se wasu kaya a Leda da tace Habiba ce tace akawo mata taso ta biyo Hajiyar,
"Kin san abokiyar takun saqarki na gidan ita ta hanata zuwa amma tace na karbo mata number ki zatazo miki har gida idan kin tare"

Dan Allah Hajiya ku yafemun, ki roqar mun suma su yafe mun abinda nayi musu" Umaiman tayi magana a karon farko dan tunda ta gaida Hajiyar take kuka, Hajiya ta jata jikinta tana cewa
"Sau nawa zan maimaita miki Umaimah mukam baki mana komai ha idan ma da akwai mun yafe, Allah ya rigada ya qaddaro duk abubuwan da suka faru bamu da yanda zamuyi kuma na godewa Allah da hakan yasa kika gane kuskurenki kuma kika gyara daman haka ake son mumini na kwarai idan yayi kuskure ya gane ya tuba ya nemi yafiyar ubangiji sannan ya guji sake maimaita abun a gaba, Allah yayi muku Albarka ya cigaba da yi muku jagora a rayuwa in sha Allahu zanzo idan kin tare naga dakinki kinji" haka ta ringa lallaba Umaiman har tayi shiru ta bar kukan, ta jima sosai a gida har seda tayi sallar Magriba Abba ya dawo suka gaisa kafin Driver daya kawota yake jiranta ya dauketa suka tafi.

Washe gari haka aka tattarata aka kai gidan KB da take ji kamar kurkuku aka kaita. Basu tarar da matar gidan ba dan muqullin qofa ma yaronsa ya bawo ya kawo musu daga Kasuwa se bayan sun shiga sannan wasu Mata suka zo a matsayin yan uwansa suna ta bada haqurin rashin zuwa dauko Amarya wai wadanda aka saka su kaisu ne basu je da wuri ba sun tafi kuma ya kirasu yace ai har an kawo Amarya ma. Ita dai tana lafe akan gado ta kasa yin koda kwakwkwaran motsi tunin wannan sabuqar rayuwa data shigo kawai takeyi seda yan rakiyar tata sukayi Magriba kafin kowacce ta kama gabanta aka barta ita kadai tsuru kamar mayya a gida. Ta gaji da zaman daki ta fito tana leqa falon, qato ne ya kuma tsaru dakyau dakuna uku ne a ciki da a zaton ta daya na matar gidan daya kuma qila na yara ga qofar kitchen nan da take hango ciki saboda qofar irin ta glass ce batayi gigin shiga ba ta koma daki taci gaba da jan carbi har akayi Isha babu Ango babu matar gida tana zaune har ta fara gyangyadi sannan taji motsin ana taba Get ta zabura ta miqe, Windon dakinta a cikin compound din yake dan haka ta leqa, motar Kb ta gani ya fito yaci uwar babbar riga kamar gaske ya ringa kwaso ledoji yana shiga dasu falo harya gama kafin ya shiga dakin lokacin ta koma bakin gado ta zauna.

Bakinsa a washe kamar wani soko ya nufeta yana cewa
"Sorry Amaryata mun barki ke kadai, go slow aka samu yau a hanyar Kasuwa na fito tun kafin Magriba amma babu hanya kuma na tsaya na siyo miki kazar Amarci" ya qarasa yana wani kashe mata ido daya. Takaici kamar ta kwada masa mari seta juya fuska tareda jan tsaki ya tsaya cak a inda yake murmushin fuskarsa yana bacewa yace
"Na miki uzurin yau kadai amma ki sake mun tsaki ki gani, dallah malama tashi an ma fasa tarairayar taki zanje nayi wanka kafin na fito ki shirya mun Abinci a Dining kuma ki dumama komai kafin k ajiye".
"Wato auran yaro dai beyi ba" ta fada a zuciyarta kafin ta miqe tabi bayansa dan ta tabbata bayan Tijara ga danyan kai a tattare dashi shiyasa har yake gwada yar qashi da matarsa to ita dai na zata bashi wannan qofar ba, umarni dai in ya bata zatabi tunda qinyin kamar ta sabawa Allah ne baya ga haka ita ba zama ya kawota gidansa ba gara ta koma taci gaba da zaman gidansu ya fiye mata alkhairi akan wannan rayuwar takurar da ake neman jefata.

Seda ta dumama komai kamar yanda yace ta shirya masa akan Dining din nama ne sunfi kala biyar harda wani farfesu, shi ta bari a microwave din ta koma daki kafin ya sakko, tana shiga taji yana kwala mata kira kamar ze tashi gidan ta koma yana tsaye daga kan Matakalar bene Matar gidan da bata san sanda ta dawo ba na tsaye daga bakin qofarta ita kuma wata busashishiyar mace fara tas kamar Aljana ta harde hannaye tana kallon Mijin shi kuma ya kalli Umaimah data fito ta tsaya tana kallonsu gaba daya
"Kin gama Baby" ya fada yana mata wannan murmushin nasa data tsana a yanzu seta daga masa kai ta fara tafiya hanyar kitchen din tana cewa
"Saura pepper soup din bari na dakko"

"Kan kutumar uban nan Kabiru, kitchen dina kace ta shiga tayi maka girki ko Yaya" Abida ta fada har sannan tana tsaye a bakin qofarta, Umaimah ta waiwaya ta kalleta sau daya ta qarasa shigewa kitchen din, shi kuwa kan Dining ya wuce abinsa ya zauna yana duba abubuwan data ajiye ta fito ta bowl gadan gadan Abida tayi kanta ta kauce mata saboda abinda ke hannunta da zafi bata ma zata da niyya tayi kan nata ba seda taga ta sake durfafota babu bata lokaci ta dauke Umaiman da mari abinda ya sakata sakin kwanon naman ya fadi qasa ya fashe ya watsar musu a qafafu musammab Abidan dan a kan qafarta ma ya fadi ta fasa ihu tana cewa
"Kika qona ni, wlh bazan yarda ba se kin gane kurenki yau a gidan nan" Marin da Kb ya kwasheta dashi ya sakat sakin Umaimah babu shiri se kuma ta juya kansa ta shiga zaginsa kamar bama gujiya Abu kamar wasa se gani tayi ya tube jallabiyya damben da taji labarin sunyi se gashi akan idont?????#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#?#$a kici kici suka kama kokawa ya sameta ya ringa tamola da ita yana bugawa da qasa amma saboda qarfin zuciya irin nata bakinta be mutu ba ta ringa zaginsa, ita dai taja gefe tana kallon ikon Allah, ya gama casa Abida ta bakinsa da fada kafin ya kalleta a fusace yace

"Ku gyara gurin, kuma wlh se anyi lissafi kun biyani kudina ai ke kinsan ban gaji Asara ba daga kudin namana harna plate din tunda bada kudin uban wata a cikin ku na siya ba" ya wuce fuu ya dirarwa Namansa ya hau ci Umaimah kam taga abinda ya girmi tunaninta yau, wannan bala'i har ina ko awa biyar cikakkiya batayi a gidan ba. Duk dukan dayawa matar nan ga mamakinta haka ta tashi ta dakko tsintsiya se ita kuna ta hado ruwan mopping suka gyara gurin kamar yanda yace Abidan na kuka tace
"Wlh se kin san kin qona ni kuma kinsa ya dakeni" ta shige dakinta seya kalli Umaimah data rakata da kallo yana cewa
"Zo nan sweetheart bar yar abu ta kazan uba yanda kika san Jaka in ba'a daketa ba bata gane komai, zo kici kazarki da Allah karta bata mana daren Amarcin mu dan na fara chaji kinsan hadi me kyau aka mun saboda na gurji Amarci son raina".

Badan kar itama ta karbi rabon dukan ba ta qarasa amam ta gagara cin komai se madara kofi daya itana dan ya matsa mata ne, yana tsaye ta wanke komai daya bata ta adana sauran abubuwan kafin ta shiga dakinta nan ma ya kafa ya tsare wai ta shirya su hau sama. Yanda tsarin qasan yake haka saman shima yake harda kitchen da komai dagani daman tsarin mata biyu akayi tunma daga yanda Matakalar take acan gefe za'a iya yin katanga a cireta daga falon a fasa qofa ta waje amma saboda baqar mugunta beji ze iya yin hakan ba. Ya bude mata dakinta na saman suka shiga, gadon da aka saka harya fi na Qasan kyau, babu batun sallah balle aje ka wata soyayya ko tarairayar dayace daman ya fasayi ya afka mata, ta ringa kuka kamar zata hadiyi zuciya ta mutu, shekara takwas rabonta da abun gashi a yanayin da yazo mata shiyasa taji jiki matuqa shi kuwa sambatu harda na banza fadi yake babu Asararre irin Mijin daya sakota shi kam idan da wannan dadin ko uwarsa zata kashe ai ya yafe mata baqin cikin maganganun nasa suka qara qume mata zuciya, be barymta tayi bacci ba sannan tsabar bala'i tun Asuba ya tasheta wai taje ta hada masa abin kari da wuri ze fita ta rasa me zata ce masa tafiya kanta dakyar takeyi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login