Showing 102001 words to 105000 words out of 429394 words

Chapter 35 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

973

naje na mutu a gun haihuwa na bar jariri " Umaimah ta fada tana kallonta, Naziyya ta girgiza kai cikeda takaici tace

"Eh idan kin haihu se a nade miki babyn a fatar jikinki ai tunda ke sakarya ce baki san abinda ya kamata ba kuma ko mutuwar kikayi ai baza'abar Dan tsirara bako dole yana buqatar kayan da za'ayi masa amfani dasu"

"Toh idan kuma dan ne yazo babu rai fa" Umaimah ta sake fada se Naziyya ta shiga tafa hannu tana cewa
"Ko wacce me cikin duniya tanawa kanta fatan sauka lafiya banda ke Umaimah? Nan maganin Zaqi ance da aka kawo miki kinqi sha wai Honey yace ba'aso me ciki na shaye shayen magunguna barkatai ko zakiga Honey a labour room, Allah ya saukeki lafiya idan kuma silar tafiyar ce Allah ya karbi shahadarki kinji" Naziyya ta fada tana miqewase kawai Umaimah ta fasa mata kuka ta saki baki tana kallon ikon Allah to kukanna menene kuma?

Cikin Kuka Umaiman tace
"Wato daman fata kike mun na mutu ko toh in sha Allahu lafiya lau zan haihu in reni Dana ko Yata"

"Fatan mu a kullum kenan Allah ya raba ku lafiya, kinga bari naje daman Mama ce jiya mukayi maganar nace zan shigo naji ya ake ciki tunda naji bari na wuce" Naziyya ta fada tana sabar jakarta dan bazata iya da jidalin Umaimah ba kafin ta qulla mata wani sharrin kuma tace tayi mata.

Naziyyan na fita ta share hawayenta ta shiga tattare kayan da suke gurin, ta gyara ko ina tsaf ta kunna turare daidai aka fara kiran sallar magriba ta wuce tayi Alwala ta tayarda Sallah, tana cikin lazumi taji ana buga Get taje ta bude bayan data tambayi waye, Rufaida ce sabe da yarta Anam da gani daga unguwa take tace

"Amarya kin ganni da magriba ko wallahi in gaya miki ashe na manta muqullina a cikin gida shi kuma ya fita ya kulle se yanzu dana dawo ina sauri na duba banganshi ba"

"Wai irin haka akwai ciwo musamman ka dawo kana da wani uzuri ki shigo ciki toh kafin ya dawo".
Ciki suka shiga Rufaida ta yi Alwala Umaimah ta na yiwa Anam wasa harta idan kafin ta tashi ta kawo mata ruwa da abinci ta karba tana cewa
"Kamar kin san Yunwa nakeji wani biki naje in gaya miki abu dai tsiya tsiya ko yar shinkafar dai aka saba babu"

"Allah ya rufa asiri toh" Umaimah ta bata amsa tana danna Remote ta kunna musu Zee world. Kamar an matsi bakinta ta waiwaya ta kalli Rufaida take cin abinci hankali kwance Shinkafa da wake da mai da yaji taji danbun nama tace mata

"Dazu kuwa Zainab Ladan tazo gidan nan"
"Wacece Zainab Ladan kuma?" Rufaidan ta tambayeta se tace
"Wannan ta sabon group din da kika sakani mana baki ganeta ba Zainab Ladan wadda naji suna cewa Zeezy QQ"

"Zeezy Qarya Qarya zaki ce mun, me tazoyi gidan nan shegiya wato ta ganki kalar lasa shine zata maqale miki yaushe ma kuka fara mutunchi har da zata zo gidanki?" Rufaida data ture abinci gefe ta fada tana kallon Umaimah.
*Assalamu alaikum barkanku da wannan lokaci,to damuna tazo fa gida saida kamshi, Turaren 2SISTER HEAVENLY SCENT ba yabon kai ba idan aka kona a daki kamshi har Maqota .2sisters sunada nau'in turaruka kamar haka:*
*Turaren wuta kala kala*,
*Humra baka da fara,*
*Kwalacca,*
*Air freshener da sauransu*
*Masu biki bayan sallah 2sisters suna yin na rabo,za ku iya siya ku bada gudummawa akan parashi me sauki daidai aljihunku.*

*Location kano*.
*07068387382, 09161661999*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 29

"Bangane Qarya Qarya ba, yar qarya ce ko kuwa dai irin iskancin da yan group din suka sabane su sakawa mutum sunan banza" Umaimah ta fada itama tana kallonta can qasa zuciyarta na tsinkewa, Rufaida ta watsa shinkafa a baki ta taune tace

"Tab ke tambaya ma kikeyi yar qaryace ko yaya? Baki taba jin tana sheqa qaryar tata a group ba ko kiga ta turo abubuwa irin a zuwan ba nan zata turo ba ko tace yara ne sannan duk abinda yaka fada se tace ta sanshi ko tana dashi koda yake qawarki ce ke ya kamata ma ki bani labarin qaryar tata ai".

Tsaki Umaimah tayi tace
"Ni wallahi na dauka ma wani abun ne saboda duk tsomaye aka tara a group din shiyasa suke ganin duk abinda tayi ko ta fada qaryane, nifa shiyasa kikaga na dena magana sosai tunda wata tace wai ina maqe murya idan ina magana suka nemi sumin taron dangi nayi musu tas shiyasa na rage kula yan group din nan dan naga duk masu kalan wayewa ne suke claiming su wayayyu ne, Maman Nihal kuwa ni? dana ganewa ido na zahiri akanta ai bazan musa mata ba, ai da nasan kallon da kike mata kenan na yar qarya da dake zamuje gidanta wallahi ki ganewa idonki, amma ki shirya Wani satin bakin qanwarta dukda da bazanje ba amma yanzu ko dan ke da sauran munafukan yan group zamuje, ga katin nan ta kawo mun dauka ki gani" Umaimah ta qarasa tana miqa mata hadadden katin gayyatar Kamun da aka Rubuta sunanta wato Zainab Ladan a matsayin me gayyata.

Rufaida ta karba tana bude baki cike da mamaki tace
"Dan Allah dagaske yanzu duk wannan Aljannar duniyar da take daukar hoto a ciki ki cemun gidanta ne, kinga wasu danqara danqaran daham da take sakawa kuwa kai ni Umaimah ina tantama gani nakeyi kamar dakko hoton irin hamshaqan matan nan takeyi a IG"

"Se kiyi ai, nan nan Third Get gidanta yake cikin sabuwar Abuja, qarshen tika tika dai ki shirya muje bikin qanwarta ki ganewa idonki" Umaimah ta sake fada,
"Aikuwa Allah ya kaimu dole ma naje na kashe qwarqwatar ido na dan indai da gaske itace wannan hamshaqiyar dole bikin na manya ne za'a gwangwaje.

Umaimah dai shiru tayi, tana jin kamar ta gayawa Rufaida zancen aron sarqarta da tayi amma tayi shiru haka suka ci gaba da hira har kusan takwas da rabi kafin mijinta ya kirata akan ya dawo suka fita ta rakata daidai sanda Khalil shima yayi fakin a qofar gidan.
Haka aka qarasa cinye sati daga Umaimah har Rufaida babu wanda ya samu zuwa bikin Hamida qanwar Maman Nihal, a ranar Umaiman ta tashi da ciwon Mara dan har seda sukaje Asibiti aka ce ba haihuwa bace da saura itama Rufaidan ashe Anam ce tayi fama da zazzabi seda aka kwana biyu ta shiga take gayawa Umaimah daga nan suka yanke idan Umaimah zataje asibiti zata rakata se su je gidan.

An yi bikin Hamida da kwana uku Maman Nihal ta aiko mata da uban hilin kayan fulawa na gara harda su soyayyun kaji da dambunsu ko wanne cikin Farin bokiti qarami, me delivery ta bawa ya kawo mata tana zaune kawai aka kirata wai ga saqo inji Maman Nihal Janbulo lokacin Habiba Qanwar Khalil da Sharifa qanwarta yar dakin Anty suna gidan saboda anyi hutun makaranta sukaje tayata zama saboda Khalil din be cika zama sosai ba saboda aiki.

Bayan sun karbo saqon ta bincike tas bata ga abinda take tsammani ba koda yake ya za'ayi ta bawa me delivery sarqa ya kawo mata itama ta bada tata ya kai mata ai ganganci ne seta shiga kiranta a waya, sau biyu ta kira wayar ta qaraci ihunta ba'a daga ba, tunanin yi mata magana a WhatsApp tayi dan daman tunda suka fara bikin basu yi waya ya kai sau uku ba sedai a WhatsApp shima atsaitsaye saboda Zainab din itace kamar uwar Amarya ita ce akan komai.

Dadi taji ganin tana online tayi mata sallama tareda godiyar kayan da aka kawo har tana cewa sunyi yawa kafin tace mata
"Da zan bada sarqar ki ya kawo miki se naji tsoro ban san ko na gida bane kin saba harka dashi kuma nayi kiran wayarki baki amsa ba"

"Kedai kice kina mun tunin sarqar ki Amma ni tawa ko shekara zatayi babu damuwa ki ci gaba da ajiye mun, taki kuma abinda yasa ban bayar ya taho da ita ba gaskiya ban sanshi ba wata ce ta hadani dashi Walid nake so na bawa ya kawo miki dan ma bazan samu shigowa da kaina ba dan yanzu haka ma kin ganni muna Aiport zamu tafi America kai Amarya, kinsan da na gaya miki babu yan rakiya se fa jiya uban mijin yace wai bazeyuwu ace babu wanda yaje yaga dakinta ba" Maman Nihal ta turo mata da dogon voice note, Mamaki ya kama Umaimah dan gaskiya bata tuna sunyi zancen Amwrica za'a kai Hamida ba ta dai gaya mata a Tarauni gidanta yake amma Mijin a Abuja yake aiki bayan biki zasu tafi can to qila kuma chanjin shawara suka samu abun na masu dashi, Vn din tayi mata tace

"Toh Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, babu damuwa ki bawa Walid din idan yazo kinga ma sena bashi takin"

"Kawo miki in sha Allahu bari naje an fara kiran mu idan mun sauka zamuyi magana" Maman Nihal ta bata amsa kafin ta sauka offline.
Warkaja min su sukaji gaba dayi da kayan gara, koda Khalil ya tambayi daga ina tace masa Mama ce tasa akayi mata tace tana so ya ringa mata fadan cin zaqi dukda be yarda Maman bace ta bayar sedai idanda kudinta ta saka akayi mata zata fake da cewa Mama qarshe da Habiba da Sharifa zasu wuce ya kwashe ya raba musu suka tafi dashi.

Seda aka kwashe sati biyu babu Maman Hanif babu labarin zuwan Walid, da farko Umaimah ta shiga damuwa amma data tuna akwai tata sarqar a hannunta se taga babu amfanin damuwar dan ko riqe waccen tayi tasan taci riba akanta dan wannan tafi tata daraja ko daga gani a ido ma.

Sati biyu a tsakani ta tashi da naquda, cikin ikon Allah zuwan su Asibiti a qasa da awa biyu se gashi ta haifo qaton danta me kama da Khalil kamar yayi kaki ya ajiye, haka suka tafi ziqau babu ko kyallen da za'a lullube jariri dashi dan dama shi Khalil be san ana tafiya da wasu kaya ba, a tasa wautar ma a Asibiti akw bayarwa duk se ayi maka bill ka biya shiyasa be taba ma tambayarta wani ko da akwai abinda za'a tanada ba, kayan barka da Hajiyar sa tayi masa magana kadai ya sani kuma ya gama dasu dab tuni ya bada kudin komai yace kar su siyi riguna dan basusan abinda za'a haifa ba.

Metron din tayi musu uzurin qila basu san haihuwa bace tunda a EDD dinta na farko ma tana da sauran kusan sati daya dan haka ta ari zani a gurin wata da take labor itama aka nannade yaron bayan an gogeshi tacewa Khalil yaje ya kawo abubuwan buqata.

Kaitsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, kamar daga sama taji labarin haihuwar ga kuma zancen ai basu je da komai ba dan shi bema san me za'a dauka ba koda yake daman me suka ajiye a cikin gidan. Fada ta ringayi masa ta hada duk abinda ya kamata daga wanda suka siya sannan suka wuce can gidan tace ya dibo mata kaya kala uku masu zani, dakyar aka samu daya qarshe se dogayen riguna ya diba suka wuce Asibitin acan suka tarar da Mama da Anty harda Maman Asad dan ita ya fara kira ya gayawa ita kuma ta gayawa su Maman.

Sun tarar da Mama akan Umaimah tana surfa mata fada ga Jaririn da ya sha nadi a zanin Atamfa saboda sanyi a hannun Anty, Hajiya ce ta shiga tayi sasanci Mama tace
"Banda wauta da shirme Hajiya ka taho haihuwa babu ko rigar da za'a sakawa Jariri, daidai da Pad da zatayi amfani da ita fa se ara akayi ni na rasa me yake damun wannan yarinyar sam ace bazata ringa abu irin na masu hankali ba"

"Haquri za'ayi abin barkar dai an samu kai qalau duk komai daga bayane gashi nan an kawo se a mayarwa da wadanda akayi aron a gurin su" Hajiya ta fada tana nuna mata qatuwat Akwatin data shaqo da duk abinda tasan za'a buqata, hatta Tissue paper sedata dakko. Mama bata haqura ba seda ta kuma yi musu tas daga ita har Khalil din kafin ta kama hanya Salman da ya kaisu ya maida ita gida ta bar Anty dan daman abinda ya kaita kenan taje ta karantawa Umaiman.

A Asibitin suka kwana se washe gari aka sallame su aka wuce da ita gidanta tareda Anty da zata zauna mata kwana bakwai zuwa ayi suna kafin su koma can gidansu taci gaba da wanka dan haka sukeyin Al'adarsu.

Khalil be saka a ransa ze bari ta tafin ba dan baya jij ze iya rabuwa da Dan babyn nasa da yake ji kamar ya hadiye shi tsabar qauna, ance dashi yake kama amma shi yafi hango kamannin Umaimah a fuskar yaron dan idonsa, bakinsa duk nata ne hancin ne da yanayin fuskar irin nasa kawai shidai Addu'arsa Allah yasa karya kwaso masa halin Tijararta.

Jego me kyau Anty ta dage tanayi mata suna samun kulawa daga ita har yaronta da Khalil yayiwa huduba da sunan Mahaifinsa Umar Bayero zasu ringa kiransa da Mu'ayyad, ranar kwana biyar aka kawo kayan barka daga gidansu Khalil, kaya wane kaya dan bayan wanda ya bada kudi aka siya yan uwa da abokanan arziqi sun ringa kai nasu Aka hado komai rigijib lefen dangata aka kaiwa Umaimah washe gari kuma aka kawo na gidansu shima sunyi qoqari sosai da sosai sukayi Babyn da ita kanta kaya.

A ranar Maman Asad ta karbo mata dinkunan kayan da zatayi fitar suna dasu Wanda daban Khalil ya bada kudin aka siye su, kayane kala biyar Atamfa biyu, Lace biyu se Shadda guda daya da sukayi anko dashi zasu saka da safe. Duk wani abin amfanin suna an tanada kama daga abinci da sha da kayan rabo sunyi komai cikin tsari ranar suna aka yankawa Yaro manyan ragunansa guda biyu ga su Biscuit alawa da dabino duk wanda ya shigo barka yan unguwa se an bashi.

Da safiyar tasha kwalliya da danyar? shaddar da sukayi anko da Khalil, Habiba ce tayi mata dauri me kyau dan ita din gwana ce gurin kwalliya dan ma Umaiman tace ba sannan za'ayi mata make up seda yamna dan haka hoda da man lebe kadai ta saka aka ringa kashe musu hotuna da babynsu daya sha kaya na alfarma yana ta bacci abinsa.

Kafin Azahar gida ya dinke da jama'a daga bangarenta har zuwa Na Khalil ta ko ina se bubbulowa sukeyi dole se wangale Get din gidan akayi suka saka kujeru tu daga waje har ciki dan daman an tanade su kafin yamma su koma cikin Wani Kango dake gefensu na Mijin Maman Hibban ne su Anty Hafsa suka roqi alfarma aka ara musu tunda taqi bari a fita a kama guri kamar yanda sukayi Na Nuratu sunce duk da haka se sun dakko Dj sunci uwar sabada yau Umaimah Qiriniya tayi Da.

Tunda tayi kwalliyar shaddar Anty Hafsa take baza ido taga ta saka sarqarta taga wayam se wata fashion me kyau ta saka se tayi tunanin ko ta bari ne da yamma idan tayi kwalliya sannan zata saka haka kuwa akayi bayan la'asar me kwalliyar da suka kira ta gama tsatsowa Umaimah kyanta dukda ba wata me yawa akayi mata ba, ta daura mata gwagwgwaronta fuskar nan ta fito tas kamar ranar ne auransu da Khalil tasha kwalliya da wani Dan ubansun Lace da akayi mata dinkin fitted Bubu ta cikata saboda qibar da tayi se hakan ya qara fitar da kyan dinkin da kwalliyarta.

A dakin Khalil ta qarasa shiryawa tana tsaka da saka dankunne Anty Hafsa ta shiga dakin cikin kwalliya tana kallonta tace
"Kai Umai kinyi kyau masha Allah daman ga Khalil can a waje bari a kirashi yazo kuyi hoto kar kwalliyar ta tafi a banza" harta juya idonta ya kai kan sarqar data saka seta dawo tana cewa

"Aa ya haka? Wai ina sarqar ki ne da kike ta fama da wasu fashion malama dakko ta ki saka ko kuwa daman dan ki ajiye aka siya miki"
"Kin rigani jira nakeyi in idar da Sallah nima nayi mata magana tun safe nake saka ido naga ta saka ban gani ba" Anty Laure data idar da sallah ta fada. Se Umaimah ta shiga zare ido, gaban Safe box din Khalil ta isa ta bude gurin security swta kalli Anty Hafsan tace
"Ya kulle kuma bansan password din ba"

"Se ki kirashi a waya ya gaya miki ai meye amfanin siyan ta idan bazaki saka a gani ba" Anty Laure ta sakw fada tana miqa mata wayarta,bata da mafita ta karba ta hau danne danne a ranta tana shirya yanda zata kufcewa wannan tuhunar tasu, to me zata ce musu? Kusan kwana goma kenan rabon da suyi magana da Maman Nihal, daman tunda tace mata ta tafi America suka dena waya a WhatsApp suke chatting tace mata Walid din ya koma makaranta daga baya kuma tace wai ta manta ta tafi da key din dakin nata sedai idan ta dawo kuma zasu biya Saudiyya suyi Umara a taqaice dai se nan da kusan wata daya take shirin dawowa daga baya ma ya zama idan tayi mata magana baya tafiya duk da har sannan Umaiman bata kawo komai a ranta ba, se jiya data kira layin Maman Hanif din taji ya shiga har ta daga se kuma ta kashe daga nan kuma take ta kira baya shiga abinda yasa hankalinta ya tashi kenan da rashin sanin abinda take nufi da ita kuma ta rasa dawa zatayi maganar tunda babu wanda yasan sanda akayi sedai idan ta tuna da tata a hannunta hankalinta yana kwanciya yanzun ma gudun tambayoyi ne ze hana ta saka ta Maman Hanif din.

"Anty yace baze iya ratso cikin mata ya shigo ba kuma fingerprint ne security din" Umaimah data gama qayar qarya ta fada, Anty Hafsa da Anty Laure suka kalli juna kafin suka fita suka barta ta qarasa shirinta a ranta ta qudure zuwa gobe idan bata samu Maman Hanifa gaskiya zata bada akai sarqar nan kasuwa a siyar, ta cire kudin tata ta siyi wata ragowar ta tura mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login