Showing 381001 words to 384000 words out of 429394 words

Chapter 128 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1046

samu ba fa Humaira"
"Amma da wahala baka san yanda ake jiba" tayi saurin katseshi se yace mata
"Na sani da wahala amma karki butulcewa Allah ki kalli fa a yanayin da muke ciki amma dukda haka yayi ikonsa ya azurtamu da wannan cikin ai murna ya kamata kiyi ba kuka ba".

Shiru tayi tana qoqarin rage kukanta a zuciyarta tunani takeyi shikenan kawai se a ganta da ciki bayan ita ba wani abu tayi ba wai to shi daman cikin daga sama ake samun sa ko yaya tunda dai na Aryaan tasan sunyi abinda ake samu wannan fa?
"Ki share hawayenki kinji kiyi Addu'a Allah ya raya mana in sha Allahu kuma cikin salama zakiyi rainon cikin ki haifeshi ba tareda wahala ba. Ina son yara da yawa fa Humaira ina da burin na tara zuri'a kamar yara Goma sha haka duk nawa amma daga biyu kin karaya to wa kike so ya tara mun su?" Ya fada yana jan hancinta ta janye daga jikinsa tana cewa

"Nidai uku zanyi tunda Maman Bibi tayi uku ai six sun isheka"
"Ina dozen zakiyi in aka hada da nata ukun kinga 15 kenan s nayi Manaji" ya tsokaneta aiko ta zaro ido tana cewa
"Tabdi qarya da ciwo wlh ba zan iya ba kawai ka haqura da abinda Allah ya baka shikenan banda ma kai biyar din ma ai Allah yasa musu Albarka ko?"

"Haba mana nida nake zaton in kika fara haihuwa har sena ce ki bari kodan kasancewar ke kadai aka haifa a gidanku shine daga biyu zaki ce ba haka ba?" Seta miqe tana sake ce masa
"To ai da dabansan ya cikin yake ba nima goma nace zan haifa idan na girma amma yanzu na fasa" ta shige Toilet ya bita da kallo yana mamakin yanda bakinta ya bude sosai yanzu ta rage shirmen yarintar da takeyi da koda yake tana shekaru Ashirin ne fa yanzu tabbas hankali ya ratsata tasan me take so da wanda bata so a yanzu. Yana zaune ta fito sega Nurse ta shigo dakin itama ta sake dubata ganin zafin jikin ya sauka ta bashi takaddar magungunan da aka rubuta musu da next appointment dinta ta basu.

A mota suna tafe babu me cewa komai lokaci lokaci yake kallonta yanda tayi shiru alamar tayi nisa a tunani seya kama hannunta ta daga kai ta kalleshi ya sakar mata murmushi yana cewa
"Komai zeyi daidai da yardar Allah kinji ki qara haquri"
Murmushi ta maida masa kafin ta kwantar da kanta jikin kujera tana cigaba da tunanin da takeyi a ranta. Da suka isa gidan seda ya rakata ta kwanta kafin ya wuce gurin Hajiya dan da wuri suka fita be samu ya shiga ba bayan sun gaisa take tambayarsa jikin Humairan yace da sauqi yana shafa kai dan be santa yanda ze fadawa Hajiya maganar cikin ba, bari kawai yayi akan idan lokaci yayi da kanta zata gani be jima ba ya wuce office dan ya rigada ya makara ma.

Guraren qarfe biyu Driver su Bibi ya kirashi, bayan ya daga yake ce masa
"Alhaji, me sunan Hajiya ce gata nan tana ta kuka harda birgima a qasa nayi nayi ta shiga mota mu tafi taqi hatta da Malam sunyi banbaki amma ta kafe ba zata shiga ba" Khalil ya dafa kansa yana jinjina rigimar Bibi dan haka yace ya bata wayar tana karba kuwa ta fasa masa kuka me hade da ihu taqi cewa komai
"Me akayi miki kike kuka har kina birgima a qasa?" Ya tambayeta seta tsagaita kukan dukda haka murya na sarqewa tace masa
"Tun jiya na tambayeka yau zamuje gurin Momy kace toh na gaya masa shine yace shi baka gaya masa baze kaimu ba ni kuma in dai ba gurin Momy ze kaimu ba bazan hau motar ba" ta qarasa tana sake fashewa da wani ihun da seda ya janye wayar daga kunnensa. Lallashinta ya shigayi akan ta bari su fara zuwa gida idan yaso sukayi wanka se a kaisu amma taqi daga qarshe ma ta yarda wayar dan yana jin tsawar da wani ya mata yana cewa
"Akan me zaki jefar masa da waya idanta fashe fa?"

Manniru Driver ya dauki wayarsa a qasa cikin qunar rai ganin Khalil din be kashe ba ya sakashi cewa
"Ranka ya dade jefar da wayar tayi"
"Ka kaisu Manniru amma ba ajiyesu zakayi ba ka jira su shiga su fito idan kun kusa qarasawa ka kirani a waya zan musu magana" Khalil ya fada a hankali daga nan ya kashe wayar zuciyarsa duk babu dadi, sam baya son damuwar yaransa amma fitinar Bibi kullum qara yawa takeyi tunda aka fara kaisu gidansu Umaimah yanzu basa sati biyu bata saka rigimar se sunje ba dukda basa kwana sedai au yini su dawo dan wani lokacin ma ita kadai ake kaiwa Mu'ayyad ya kance ai munje ranar nan Iman kuwa daman ko a jikinta saboda yan uwan take zuwa amma ita tana da bala'in qulafucin uwar ga dan banzan naci idanta fara roqon akaisu harse ya yarda zata barshi ya sarara ko jiyan nacin ta ringa masa ya amsa mata badan da gaske yake ba dan basuyi cikakken sati da zuwa ba ashe ita ta riqe shine taje tana creating scene a makaranta ze koma gida zasu hadu ne.

UMAIMAH
Kuka takeyi haiqan kamar ranta ze fita Abba ya zuba mata ido yana sauraronta ba tareda yace mata komai ba, seda ta haqurtar da kanta ta tsagaita kukan kafin taci gaba da cewa
"Na sani na tafka babban kuskure a rayuwata kuma kunada duk wani dalili na daukar ko wanne mataki a kaina. Na biyewa zuciya da zugar mugayen mutane na watsa muku qasa a ido na zubar muku da mutunchi a idon duniya Allah shine shaidata nayi nadamar abinda na aikata kuma a shirye nake dana gyara kuskurena hakan kuma baze yuwu ba har se na fita daga fushinku, Abba dan girman Allah dan Darajar Ma'aikin Allah ku dubi rauni na ku yake mun laifin dana aikata muku. Ku sassauta fushin ku akaina ko na samu ubangiji ya dubeni ya yafemun sauran laifukan dana aikata tsakani na dashi.
Wallahi nayi nadama nayi dana sani biyewa son rai" ta sake rushewa da wani kukan daya fi na farko ganin Abban na zaune still ko gezau a kallonta kawai yakeyi kamar wata talabijin. Sunkwashe kusan minti goma sha biyar a haka tana kukan kafin Abban ya nisa yace

"Toh ni abinda ban gane ba ni menene nawa a ciki Umaimah da kikazo kina bani haquri sannan duk tsahon lokacin nan se yanzu ne kikaga mun isa da ki bamu haquri ko me me kike buqata?"
Se tayi saurin tsayar da kukan tana cewa
"Wlh Abba badan baku isa bane a kullum nauyi da kunyar yanda zan tunkareku bayan duk abubuwan dana aikata a bayane ya hanani gurfana gabanku na nemi yafiyarku amma yanzu na gane bani da wata mafita domin fushinku a kullum qara dagulamun lissafi yakeyi. Abba kuyi haquri ku yafe wlh nayi nadama kuma in sha Allahu zan gyara kuskurena".

"Toh Alhamdulillahi dama abinda ake so da mumini idan yayi kuskure ya gane ya tuba ya kuma guji sake maimaita kuskuren a gaba idan har dagske kikeyi kinyi sahihin tuba ina fatan Allah ya shiga Al'amuranki Umaimah ya duba miki ya rabaki da duk wani abu dayake ingizaki ga sabon Allah ya rangwanta miki zafin zuciyarki dake kaiki ga aikin dana sani. A bangarena na dade da yafe miki, domin da banyi miki afuwa ba da baki samu yancin zama a cikin gidan nan ba zan sallawa duniya kene kamar yanda kika dade da sallama mata kanki amma bamyi hakan ba mun rungumeki a kullum kuma muna miki fatan shiriya
Sannan maganar Yafiya da akwai wadanda yafi kamata da ki nemi yafiyarsu bayan mu, idan har dagske kinyi nadama ki nemi yafiyar ubangiji a farko kan sabawar da kika masa sannanki nemi yafiyar wadanda kika zalunta domin kinsan ubangiji baya yafe haqqin bawa da dan uwansa bawa ya dauka dan haka in har kina so kiga daidai Umaimah dole sekin sauke haqqin wadanda kika dauka" Abba yayi maganar cikin nutsuwa.

Umaimah taja majina kafin tace
"Nagode Abba kuma in sha Allahu bazan sake komawa ga abinda na aikata a baya ba ku tayani da addu'a"
"Allah yayi miki Albarka ya shiga cikin lamuranki, shikenan zan iya tafiya?" Abban ya sake fada dan yana shirin fita tayi masa dirar mikiya tana shiga kuma ta fasa masa kuka, saurin girgiza kai Umaimah tayi kafin tace
"Aa Abba bashi kenan ba dan Allah Abba zaka tayani roqan Mama"
"Ni yanzu waya tayaki roqona?" Ya fada yana kallonta seta marairaice tace
"Abba kai da sauqi amma Mama fushinta ya zarce naka wlh na rasa ta yanda zan tunkareta Abba ko dakinta bata bari na shiga duk yanda kuma naso nayi mata maganar seta nunamun ita ban mata komai ha kaga kenan ta qullaceni da yawa".

Shiru Abban yayi kafin yace
"Shikenan kiyi ta qoqarin kyautata mata kuma karki dena bata haqurin har se sanda ta sakko ta saurareki abinda kika aikata Umaimah dole badan mu muka haifeki ba babu yanda zamuyi dake da tuni wata maganar akeyi yanzu dan kinyi mana cin fuskar da badan zuciyar musulunci ha da sanin tasirin da bakinmu da fushinmu zeyi akanki dole muka taushi zukatanmu amma ya wuce tunda har kin gene kuskurenki kin nemi afuwa nayi miki itama kuma nasan zata sakko a hankali in sha Allahu"

"Nagode Abba Allah ya saka da Alkhairi ya qara girma" ta fada cikin murnar samun daidaito da Mahaifinta ya amsa mata da
"Amin, Allah yayi muku Albarka keda sauran yan uwanku Ubangiji ya dubeku ya tsare ku daga dukkan sharri" ya fada yana dafa kanta. Tare suka fito daga dakin, Mama da Anty na tsakar gidan a tare suka musu kallo daya suka dauke kai Abba ya yi murmushi yana kallonsu yace
"Zan fita" suka hada baki gurin yi masa a dawo lafiya Umaimah ma tayi masa bakinta yaqi rufuwa saboda farin cikin da take ciki seda Abban ya fita kafin ta matsa inda Mama take ta durqusa gabanta tace
"Mamame za'a dafa da rana?"
"Girkin Antyn kune ai banawa ba" Maman ta bata amsa seta juya ta kalli Anty data dauke kai ta hade fuska tun fitowarsu da Abban kafinma tayi mata magana tace
"Ki barshi zanyi da kaina ai naga kun shirya da Abban naki".

Yanda tayi maganar seta bawa Mama da Umaiman mamaki har seda Mama ta kasa daurewa tace
"Kamar yaya zakiyi da kanki saratu ba doka Alhaji ya kafa cewar ita zatayi aikin gidan nan ba ko kunyi dashi yace miki ya janye ki karbi aikinki?" Seta kalli Maman bayan data miqe tsaye tace
"Aa kawai dai zan karbi aikina tunda har sun fara shiga daki su fito suna dariya kinga alama tana nuna gwamnatinta ta dawo kenan gara na karbi aikina da kaina kafin a maidomun tunda daman bani nace a karba ba" ta shige dakinta Mama ta bita da kallo dan sam bata fahimci abinda Antyn take nufi ba mema ya bata mata rai yanzu yanzu bayan hira sukeyi cikin nishadi daga fitowar Alhaji da Umaimah seta canza fuska me yake faruwane?

Ita dai Umaimah na zaune ta sunkuyar da kai Mama ta kalleta tace
"Kinji abinda tace ai se ki wuce inda wani abinda zakiyi kiyi"
"Babu abinda zanyi yanzu sedai ko in akwai Aikin da zanyi miki" Umaiman ta fada cikin ladabi, Mama ta girgiza mata kai alamar babu seta narke fuska kalar tausayi tace
"Jiya naga an kawo miki kayan wanki tunda akwai wuta sena goge miki".
Bata zata Maman zata amsa ba taji tace
"Toh, amma kiyi a hankali karki qona mun kaya nasanki ba iya guga kikayi ba" seta miqe cike da murna tana cewa
"Bazan qona ba In sha Allah" ta shige dakin Maman.

Tsalle ta buga kamar yarinya ta fada kan gadon Maman da rabon data ganshi a ido bare ta hau tun dana da yanci tayi juyi akai se kuma tayi saurin sauka tana dariya kamar wata fagal, kayan ta diba ta fita falo ta jona Iron ta fara gugar Mama ta shigo ta zauna haka ta ringa gugar dukda ba magana sukeyi ba amma taji dadin yau gashi sun zauna inuwa daya da Maman ga kuma Abba sun shirya. Ta bude baki yafi sau nawa da niyyar yiwa Maman magana seta kasa duk kuma tana ankare da ita har aka kira sallar Azahar ta ajiye Gugar ta fita ta dauro alwala Anty na hidimar girki tayi mata sannu bata tsammanin ta amsa a ranta tace
"Kyaji dashi idan ma baqin ciki kikeyi na shirya da ubana sedai ki mutu" ta wuce falon Maman a can tayi sallah Mama ta ringa Mamaki ganin yau Umaimah ce take sallar Nafila bayan ta idar da Azahar din tayi Raka'a biyu sannan ta zauna tana lazumi Umaimanda Farillar ma yinta take kawai dan ta zama dole idan ta idar kuwa bata tsammanin tana Addu'a dan minti biyu yayi yawa ta tashi daga gurin se gashi yau bayan ta idar tafi minti talatin zaune tana lazumi kafin ta daga hannu tana addu'a nan ma ta dade kafin ta shafa sannan taci gaba da gugar bata dade da ci gaba ba suka jiyo karadin Bibi se gata ta fado falon ta watsar da jakar ta a bakin qofa da gudu ta fada kan Umaimah da tayi saurin janye Iron din ganinta nufota

"Ke kuma ya haka daga ina kike harda uniform kin fadowa mutane daki babu sallama haka akeyi?" Mama ta fada kafin ta bata amsa Mu'ayyad da Iman suka shigo da sallama, seda suka cire takalmansu kafin suka shiga ya durqusa a gaban Maman ya gaisheta ganin haka itama Iman tayi yanda yayi Maman ta amsa cikin kulawa sannan ya juya ya gaida Umaimah dake ta kallonsu

"Tashi ki fita ki cire takalmin nan a waje da zaki gama tako dattin makaranta dana gari kike taka mun daki babu sallama bare gaisuwa qanwarki ma ta fiki hankali". Baki Bibin ta zumbura tana qara maqalqale Umaimah Mama ta zare mata ido tana daga maficin dake gefenta tace
"Sena zaneki da wannan idan baki tashi ba futsararriya kawai me irin halin uwarta" seta miqe tana bubbuga qafa irin na taba????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? rarrun yara ta fita tana zuwa saitinta kuwa ta kwada mata maficin a baya da qarfi ta kwalla qara kuwa kafin ta kwanta a gurin zata fara birgima ganin Maman ta fizgo wayar caja daga jikin socket yasa ta take da gudu ta fice daga dakin
"Ja'ira daki tsaya dana cire miki iyashegen da yake damunki"

"Yanzun nan ta gama birgima a school Mama saboda Driver yace baze kawo mu nan gidan ba seda ya kira Dady har wurgar masa da waya tayi a qasa" Mu'ayyad yayi maganar cikin nutsuwa tamkar Mahaifinsa se Mama ta riqe baki tace
"Eh ba shakka ai daman barewa ba zatayi gudu danta yayi rarrafe ba to kuwa uwarki zakici bamu gama da wata bama balle ki tashi ki fitine mu, yanzu Ina Dtiver yana waje ko ajiye ku yayi ya tafi?"
"Ina ga ya tafi naji tace masa se anjima ze dawo ya dauke mu" Mu'ayyad din ya sake fada se Mama tace
"Dabdi itace ma me gaya masa abinda zeyi kenan?"
"To ai Mama shima Dady se abinda take so yakeyi ba shiyasa take yin haka ba ta ringa mun rashin kunya a school a gaban friends dina kuma idan na doketa ta gayawa Dady ni yayi mun fada kuma a gida ma ko Mamah ce tayi mata fada Dady baya so" yanda yayi maganar zaka gane jin haushin abun har ransa

"Ai kuwa ya dakko hanyar da bazata bille ba kuma tilas ya gyara wadda bata tashi a sangarce bama ta fitini mutane balle wadda tun tana qarama babu kwaba ai kuwa ba'a taki gaskiya ba".

Umaimah dai kanta na qasa ta gagara cewa komai kan wannan magana da Mama take yaba mata ita da yarta seta shiga tattara kayan gugar data gama ta shige mata dasu daki ta ajiye akan gado se anjima idan ta yarda zata shirya mata su a wardrobe. Dakinta ta wuce can ta tarar da Bibin kan gadonta a kwance tana ganin Umaiman ta tashi da sauri ta rungumeta tana cewa
"Momy nayi missing dinki da yawa"
"Kai Bibi se kace ba last week kuka zo ba me yasa zaki ce se an kawo ku yau daga makaranta bayan akwai islamiyya yau?"

Baki ta tura tana cewa
"Ni Momy so nakeyi na ganki kuma indai baki dawo gidanmu ba kullum haka zan ringa cewa se an kawo ni kefa kika ce zaki dawo gashi an yi wata da yawa baki dawo ha Dady ma idan na tambayeshi yaushe zaki dawo baya cemun komai Momy kodai kema irin na Mamansu Halima Dady ya sakeki ba zaki dawo gidan mu ba?"

Rasa abinda zata gayawa yarinyar tayi dan haka ta wuce bakin gadon ta zauna Bibin ta sake binta tana maimaita mata tambayar still tayi shiru seta zauna tana cewa
"Daman na sani Dady ya sakeki yanzu Mamah ce matarsa kenan muma step Mom ce kawai damu zata ringa maltreating namu yanda akeyiwa su Halima?"

"Me yasa kika fiya surutu Bibi Wacece Halima kuma me Steo Mom din tasu take yi musu?" Umaimah tayi qargfin halin fada se Bibin ta riqe hannunta tana cewa
"Momy Step mom dinsu Halima muguwa ce daman kuma mun karanta wani story book na wicked step mom, dan Allah Momy ki dawo kinji ni bazan iya zama a gidan bakya nan ba".

Kallonta ta ringayi yanda take maganganun da suka zarce wayonta to ita yanzu wane bayani zatayi mata da zata fahimta ba tareda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login