Showing 384001 words to 387000 words out of 429394 words

Chapter 129 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1053

ta sake kawo wata maganar ba?
"Ko saboda Dady ya auri Mamah ne ya sakeki ba zaki koma ba?" Bibin ta sake jefa mata wata tambayar kafin ta bata amsa tace
"Zan gayawa Dady ya saki Mamah kawai ki dawo ni daman bana sonta takura mun takeyi kullum tayi ta mun fada idan nayi abu kuma ba haka takeyiwa su Mu'ayyad ba".

Murmushi yayi ya kalli Mama data rafka tagumi tun zamanta kuma batace komai ba yace mata
"Toh kinji kiyi magana ta tabbatar kin haqura indai ba kuma da sauran wani abu a ranki ba" seta janye tagumin tana cewa
"Toni me zance Alhaji ai ba yanzu ya kamata muyi maganar ba tuntuni ya kamata ace anyita tunda se yanzu tayi lokacinmu to ni banda lokacinta seta jira se randa nayi"

KHALIL

Ayyukansa yaci gaba dayi, wuraren qarfe hudu ya tashi kai tsaye gida ya wuce yayi mamaki dabe tarar da motar yaran a ajiye ba dan haka yayi tunanin ko Humaira ta aiki Mannirun ne, seda ya fara shiga gurin Hajiya ya kai mata Fruits din daya shigo dasu kafin ya wuce bangarensu, falon shiru se motsin Ruqayya da ya jiyo daga kitchen seya wuce sama qilan suna can. A falo ya tarar da Aryaan yana bacci da alama wasa yayi ya gaji baccin ya daukeshi ba tareda ya sani ba ya gyara masa kwanciya ya wuce dakinta yana tunanin toh ina sauran yaran suka shige tunda be gansu a bangaren Hajiya bama.

Humaira na zaune akan kujerar dake dakin tana shan Baqin lipton dan tun da suka dawo daga Asibin take kwance sallah kadai ke tada ita gaba daya kasala ta mata rubdugu se yanzu ta samu tayi wanka tasha ruwan Tea saboda cikinta da ya daure dalilin bata ci komai ba. A sanyaye tayi masa sannu da zuwa ya amsa yana qarasawa kusa da ita ya rungumeta ta gefe yana cewa
"Ya jikin?"
"Da sauqi, yau ka dawo da wuri" ta bashi amsa seya saketa yana cewa
"Yah kwana biyu ayyuka sun mana sauqi so far kusan duk wasu constructions da mukeyi mun kammala se ragowa shiyasa bana kewayen Site"

"Toh Allah ya taimaka ya kawo wasu ayyukan na Alkhairi" ta sake fada se ya amsa mata da
"Amin Baby" yana murmushi yana bala'in jin dadin yanda take masa addu'a a koda yaushe kuma yana ganin hasken hakan.
"Ina yaran naki naji gidan shiru ne?" Ya tambayeta seta ajiye kofin hannunta tana cewa
"Ban sani ba koda suka dawo sun shigo ina bacci dan ban dade da farkawa ba qila sun wuce islamiyya"
"Ok" ya fada kafin ya fita daga dakin zuwa nasa. Seda yayi wanka ya canza kaya ya fito sannan itama ta fito falon Saman ya kalleta tana zaune a spot dinda Umaimah take yawan zama sanda tana gidan, dukda ya canza kujerun falom saman dana qasa amma dukda haka wani lokacin idan ya kalli guraren da take yawan zama se yaga kamar ze ganta a gun. Kusada Humairan ya zauna ya kalli Aryaan dake baccinsa yace
"Ba za'a tashe shi ba kuwa baccin la'asar karya kasa na dare"

"Ai kasan shi da kafiya seda na hanshi baccin a daki ashe daya fito kwanciya yayi anan na tashe shi yanzun ma yaqi farkawa se nauyin bacci kamar wani babba" Humaira ta fada tana sake tada yaron amma ko gezau data dago shi ze janye ya koma da alama baccin ne a kansa sosai.
"Ai dashi da Bibi bansan inda sula samo kafiyar nan ba har gara itama, dazu fa a makaranta da Manniru yaje daukarsu" (nan ya bata labarin yanda sukayi) se ta kama baki tana cewa
"Gaskiya kafa dena abinda kakeyi ba yanzu ake ji ba gaba ce abin dubawa wai tayaya za'ayi ace komai Bibi take so shi za'ayi a gidan nan?"
"Baki san sunan Hajiya ne da ita ba kuma gata matata ai dole nayi abinda tace" ya fada da sigar tsokana seta hade fuska tana cewa
"Ba wasa nakeyi ba Yaya Khalil maganar Allah itace tun yana danye ake tankwarashi. Yanzu abinda kayi mun shekaran jiya shiru kawai nayi amma naji haushi sosai wlh ya za'ayi tayi laifi ina mata fada a gabanta ka nuna abinda tayi be kai nayi fada ba har kace mata ta tafi ta kwanta kuma ko a jikinka? Shekara takwas ai ba wata takwas bace da zata ringa yiwa mutane barna kuma baza'a tsawatar mata ba gaskiya karka sake yi mun haka ko a gaba idan yaro yayi ba daidai ba in ba zaka taya muyi musu fada ba karka sa mun baki kuma yanzu banda wulaqanci a makaranta zata je tana ihu da birgima akan abu kuma kayi mata gobe ma kace ta maimaita kenan".

Kallonta ya ringayi yanda take kumfar baki a kan abinda be kai ya kawo ha a ganinsa kenan amma duk tabi ta haqiqance seya kama hannunta yana cewa
"Yanzu meye abun fushi a maganar shekaran jiya da har kika riqe a ranki Bottle water ne fa ta dauka tayi Alwala shine abintada jiniyar wuya kika ringa fada kamar wadda tayi alwalar da Mangyada ko Madara sannan maganar yau ni na amsa mata jiya kan za'a kaisu kinga ai bazan saba mata alqawari ba"

"Ai shikenan" ta bashi amsa dan zuciyarta ta qulu da maganar tasa tunda bega rashin dacewar abinda yakeyi ba seya ci gaba ita dai ba zata fasa tsawatarwa duk wanda yayi ba daidai ba a cikinsu sedai yaji haushi tunda idan sun lalace qarshe ita za'a zaga ace ta musu mugunta tunda ba ita ta haifesu ba. Ganin da yayi ta hada rai yasa ya ringa rara gefe amma tayi masa shiru bata cewa komai suna nan zaune har aka kira Magriba ya tashi yayo alwala ita ma ta shiga daki da Aryaan daya farka daga bacci, yanda ya shigo a firgice bayan an idar da sallah ya bata tsoro. Ta kalle shi tace
"Lafiya?"
"Ina fa lafiya, har yanzu yaran nan basu dawo daga Islamiyyar ba, kuma na tambayi Sammani ina Manniru yake dan motarsu bata nan yace tunda ya tafi dakko su daga Boko be dawo ba which mean basu je islamiyyar ba kenan ma ashe gashi ina ta kiran wayarsa bata shiga" Khalil dinya fada a kidime take itama hankalinta ya tashi ta miqe tsaye tana cewa
"Number sa bata shiga kuma Sammanin bashi da wani layin nasa da za'a kira?"
"Number sa daya ce babu wata" ya bata amsa yana zagaye dakin, tunanin inda yaransa suka shiga yakeyi kar fa wani abu ya same su.

"Toh ba kace ya kaisu gurin Mamansu ba ka kira can mana kaji" Humairan ta fada cikin damuwa se yayi saurin zaro wayarsa dan ya manta da can din ma. Number Mama ya kira a kashe, baya tsammanin Abba na gida dan haka kai tsaye zuciyarsa ta bashi ya kira Umaiman. Da ka ya zuba numberta dake haddace, sunan da yayi saving ya fito 'WIFE' da Emojin Heart guda biyu daga shi har Humairan dake kallon wayar wani abu ya daki zukatansu sedai kowanne da kalar nasa, tabbacin da aka bashi na wayar a kashe take itama yasa shi jan tsaki ya juya yana cewa
"Bari naje gidan na gani" kafinta ce masa wani abu ya fice daga dakin da saurin gaske har yana hada hanya seta bishi da ido wani abu me daci yana taso mata, number wayarta da Sweetheart yayi saving amma shine ita da basa tare hau yau be canza mata suna a wayarsa ba.

Khalil kuwa cikin qanqanin lokaci ya isa gidansu Umaimah saboda gudun da ya ringa shararawa a hanya idan wani abu ya samu yaransa be san yanda zeyi ba. Layin babu kowa saboda an shiga sallar isha, ya kasa haqurin jira se kawai ta kutsa kansa gidan bakinsa dauke da Sallama tareda taraddadin samunsu ko akasin haka dan rashin ganin Motarsu a waje ya qara daga masa hankali seda yayi sallama uku kafin ya shiga ainihin tsakar gidan daidai nan Umaimah ta fito daga daki jin kamar ana sallama sukayi ido hudu dashi yana tsaye daga bakin qofa yana jiran ganin giftawar wani.

Cikin qasa da seconds biyar ya qare mata kallo kafin ya dauke kansa sama saboda yanda zuciyarsa ta shiga wani bugu kamar zata fito, Umaimah kuwa ido ta zuba masa kamar farin shigar Maita, ta kasa gasgata Khalil ne da gaske ko kuma Mafarkan data sabayi ne amma kuma qamshin turarensa dake busata yasa ta ke son gasgata shi din ne da gaske ba mafarki ba
"Naji kamar ana sallama ko ba a nan bane?" Mama data leqo ta fada ganin Khalil a tsaye yasa ta fadada murmushinta tana cewa
"Au kaine? Shigo ciki mana ka tsaya a qofa kamar wani baqo".

Cikin takunsa me cike da nutsuwa ya giftata tamkar bega mutum a gurin ba qamshinsa ya cika mata hunhu ji ta ringayi kamar tana shaqar sabon numfashi seta rufe idonta ta bude ta sake rakashi da kallo harya shige falon Mama jikintavna wani irin sanyi kamar wadda ake daskararwa. Yanda Khalil din ya debeta ya watsar bema nuna alamar yaga mutum a tsakar gidan ba lallai abin Azimun ne. A sanyaye taja qafafunta ta matsa jikin bango zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, takai kusan minti biyar a tsaye kafin ta jiyo qamshin turaren sa yana sake tun karota, tayi saurin bude idanunta jin takunsa kusa da ita muryarta na rawa ta kira sunansa ya tsaya cak a inda yake ba tareda ya juyo ba tamkar kuma wanda aka tsikara yaci gaba da tafi da sauri ba kamar yanda ya fito daga dakin Maman yana tafiya a hankali ba.

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 82

Seda ya dauki kusan minti goma zaune a cikin motar kafin ya kunnata wayarsa dake ajiye kan kujera ta yi haske ya janyota ganin Sweetheart ke kiransa kafin ya daga ta katse se sannan ya lura da tarin missed calls din data yi masa da alama tun fitowarsa daga gidan take kira. Cikin mutuwar jikin da ganinta ya haifar masa ya sake kashe motar kafin yabi bayan kiran Humairan
"Habibi ina ka shiga tunda ka fita nake kira gasu sun dawo qila ma kun hadu a hanya dan motarka na fita tasu ta shigo" Humairanta fada cikin damuwa seya sauke ajiyar zuciya murya can qasa yace mata

"Sorry wayar a silent take bangani ba se yanzu gani nan zuwa gidan nima"
"Amma lafiya naji muryarka haka? Nagaya maka fa gasu sun dawo babu abinda ya samesu tun ranan suna gurin Mamansu shi kuma cajinsa ne wai ya qare shiyasa kaji wayar a kashe" ta sake fada saboda jin muryarsa da tayi wani iri seda yayi qoqarin saita kansa kafin yace

"Babu komai fa nazo gidan nima suka ce sun tafi gani nan ina hanyar dawowa" daga haka sukayi sallama. Yana tuqi amma gaba daya hankalinsa baya kan Titin, wani irin mix emotions ke damun sa. Ganin Umaiman ya haddasa masa abubuwa da yawa ta tuna masa da wancan daren daya zama baqin dare a rayuwarsu gaba daya abubuwan da suka faru suka ringa dawo masa kamar a sannan suke faruwa a bangare daya kuma daga can qasan zuciyarsa yana jin wani abu na motsa masa akanta. Allah shine shaidarsa yana son Umaimah irin son da be taba yiwa wata Halitta shi ba. Yana jinta har cikin jini da jijiyarsa amma ta barar da damarta tayi masa abinda idan harda gaske shi dan Halal ne kamar yanda take fada koda ace ita kadai ta rage mace a doron duniya ze zabi ya qare rayuwarsa babu aure domin ta keta alfarmar wadanda baya hada komai dasu. Tabbas idan da ace iyakar abinda tayi masa ne tabbas ze iya yafe mata ya rungumeta suci gaba da zama Albarkacin son da yake mata da zuri'ar dake tsakaninsu amma a yanzu baya zaton akwai wani uzuri da ze iya yi mata daze kankare tarin laifukanta a zuciyarta data sauran Ahalainsa.

Maganar da Mama tayi masa bayan shigarsa akan Bibi ta tsaya masa a rai, ya gagara ganin abinda yakeyi mata da kowa yake cewa yana lalata ta shin laifine dan ya samarwa da yarsa abinda take so Alhali yana da halin hakan? Shi haka kawai duk cikin yaran tafi shiga zuciyarsa hakan kuma ya samo Asali da suna da kuma kammanin Hajiyarsa data dauka kuma shi baya nuna banbanci tsakaninta da yan uwanta kamar yanda ake cewa yanayi kawai ita tafi sakewa dashi kuma tafi tambayarsa yayi mata abu shiyasa amma suma duk wanda ya nemi abu a gurinsa ai yanayi masa ba wai ita kadai ba yana wadannan tunane tunanen ya isa gida. Yaran har sunyi wanka suna cin abinci ya shiga falon sukayi masa sannu da zuqa gaba daya ya amsa ba tareda ya kalle su ba ya haye sama.

Har suka kwanta Humaira na lura da yanayinsa dukda yanda yake ta qoqarin kawar da komai amma seda ta fahimci wani abu tayi kwanciyarta ta barshi a zaune yana danne dannen laptop data tabbatar babu abinda yakeyi kawai dan ya dauke hankalinta ta zata aiki yakeyi ne dan haka tayi baccinta ta barshi.
Khalil kuwa tambaya ce baya so tayi masa dan besan amsar da ze bata ba gaba daya ganin Umaiman ya haifar masa da wani yanayi mara dadi, juyi yayi tayi akan Gadon tunani kala kala suna yawo a kwakwalwarsa daya gaji gashi ya kasa bacci ya tashi ya dauro Alwala ya fara sallah har seda yaji ya fara jin bacci kafin ya sallame yayi addu'a ya kwanta. Abinda be tabayi ba tsahon lokacin rabuwarsu se gashi daren yayi mafarki da ita cikin wani yanayi me firgitarwa dan tana daure da sarqoqi wani mutum yana janta tana miqa masa hannu tana kuka akan yazo ya ceceta yayi yunqurin miqa mata nasa hannu wani haske me tsananin kaifi ya kashe masa ido har ya hanashi sake hangota se amsa kuwwar Kukanta yake ji a kunnensa tana fadin
"Khalil ka taimakamun ka gaya musu ban aikata ba".

A gigice ya farka daga baccin yana salati ya kalli Humaira data miqe zaune itama tana kallon cikin wani yanayi, tana bacci taji ya kama hannunta da matuqar qarfi yana kiran Umaimah da har seda ta farka sedai yanayin data ganshi ta tabbatar koda mafarkin Umaiman yayi tofa bame dadi bane. Addu'a ta ringa tofa masa kamar yanda shima yake tayi zufa na keto masa kamar babu Sanyin Ac a dakin ga jikinsa na rawa yanda kasanwanda aka rutsa da wuqa a mafarkin. Seda suka kwashi wasu mintuna a haka kafin ya daidaita nutsuwarsa ya koma ya kwanta tareda janta jikinsa ta zame be takura mata ba ya saketa dan har sannan bawai jikinsa ya gama daidaita bane

Humaira ko tsaki taja a zuciyarta ta juya masa baya babu bata lokaci kuwa bacci yayi awon gaba da ita shi kuwa haka ya ringa juyi ya gagara komawa baccin har aka kira sallar Asuba kafin ya tashi yayi wanka ya fita masallaci. Kwanaki biyu da suka biyo baya duk haka yayi su sukuku shi kansa bazece ga abinda yake damunsa ba amma jikinsa gaba daya babu qarfi, da Hajiya ta matsa masa da tambayar me yake damunsa ne dole ya qarfafa jikinsa ya koma sabgoginsa daman Humaira koda wasa bata ma nuna masa ma tasan abinda yakeyi ba, daya ware dinma shareshi ta ringayo seda yayi ta rara gefe yana lallashinta kafin ta sakko suka koma daidai amma qasan ranta danuwa ce fal akan abubuwan da taga suna faruwa. Haka rayuwa taci gaba da gangarawa, seda cikinta ya shiga wata shida kafin mutane suka farga dashi.

Ranar da Hajiya ta gama tabbatar da cewar cikine har kuka tayi tasa aka dafa abinci me yawa aka fita dashi akayi sadaka, Khalil kp kasa hada ido yayi da ita a dole kunya yake ji ita kuwa ko a jikinta ta ringa bige bigen waya tana shaidawa yan uwanta da abokanan Arziqi matar Khalil nada ciki yanda kasan be taba haihuwa ba sedai duk wanda ta gayawa yasan me take nufi, shaida musu takeyi Khalil din ya samu lafiya sun kuwa taya su murna tareda fatan Alkhairi kafin tofin Alatsine ya biyo baya akan Umaimah datayi masa sanin wannan tonon silili. Hajiya Hauwa kanta barka suka ringayiwa Juna ita da Hajiyan, tace mata
'Kinsan ta da zurfin ciki, tun kwanaki nale hasashen cikin amma tace na haka ba to tunda kasan ga yanda abu yake kinga ba zaka matsanta ba ashe iyashege ne kawai irin nata yanzu da baze boyu ba ai kowa ya sani Allah ya inganta shi kuma ya bashi lafiya me dorewa".

Jalilah kuwa ta samu abin yi, daga shi har Humairan bata bari ba dukda yanda take bala'in jin kunyarta amma idan ta tasata a gaba da tsokana seta kusa kuka take qylaeta, saboda ta samu iya shege ma cewa tayi ta haqura ita ce Hussaina yanzu shi ya zama Hassan din dan haka yanzu a qanwar Miji take dole ta tsonaketa
"Haba nidai nace ashe su Khalil anji garau an shiyasa ko gidan nan aka zo ba'a jinku kunyi muqus a daki ana biyan bashi, dan Allah tun yaushe ka koma duty?" A gaban Hajiya tayi masa tambayar yanda kasan qasa ta tsage ya shige cikinta Hajiyar kanta seda ta dafa kai tana jinjina hali irin na Jalilah, bata haqura ba taci gaba da zaro zance dayaga babu sarki se Allah dole ya shafawa idonsa toka ya mata ta yan barikin shima yace mata
"Kedai ki bari shekara uku ai ba nan bace nida ita duk munji jiki yanzu kuwa da lafiya ta samu ai dole mu biya bashi " Hajiya dai se tashi tayi ta barsu dan ba zata iya da wannan fitsara ta tagwayen nata ba.

BAYAN WANI LOKACI
Misalin qarfe goma na safe suka fito shida Humairan da ze sauke a Asibiti zataje Awo, dakyar take daga qafarta saboda yanda cikin me watanni takwas a sannan yayi girma sosai dan yafi na Aryaan, fuskarta a hade ta shiga motar haka shima tashi dukda shi yana qoqarin hadiye bacin ransa dayi mata uzuri akan abinda take masa. Tagiya sukeyi babu me tanka dan uwansa ta juyar da fuska tana kallon waje lokaci lokaci yake waiwayawa ya kalleta Ya rasa abinda yake damun Humairan kusan wata biyu kenan ta canza gaba daya daga yanda ya santa a kullum cikin takalar rigimarsa takeyi abu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login