Showing 417001 words to 420000 words out of 429394 words

Chapter 140 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1044

kamar ze kifa qara yunqurawa yayi yana yin taku biyu ya sakeyin baya kamar wanda Jiri yake diba seta riqeshi a jikinta, yanda taji zuciyarsa na bugawa da qarfi ya saka ta ce masa
"Ka zauna Dady bari na dakko Mayafina mu tafi Asibiti baka da lafiya" swya girgiza mata kai dan harshensa ya masa nauyi Mu'ayyad dai na tsaye a bayansu ya harde hannaye a qirji ya miqa masa hannu ya matso dakyar ya iya cewa
"Ku kamani muje sama Jiri kawai nakeji nayi stressing kaina da yawa da nayi bacci zan dawo daidai".
Badan ta yarda ba kawai dan ya kafe akan lafiyarsa qalau din suka kamshi zuwa saman saboda yanda jikinsa ya saki ba zata iya riqeshi ita kadai ba. Har kan Gado suka kaishi ya zauna ta fita da sauri ta dakko masa ruwa tana fita Bibi ta shiga da kukanta tana cewa
"Dady wai Momy au...."
"Shut up and get out" ya buga mata razananniyar tsawar data saka Humaira sakin Bottle din hannunta babu shiri ta toshe kunne, Bibin da yayiwa tsawar kuwa rikicewa tayi ta durqushe a gurin kukan data shigo dashi ya bace bat se rawa da jikinta ya dauka kamar mazari saboda tsoro.

Kallonsu yayi gaba daya se kuma yaji wani iri a hankali yace
"I'm sorry, banyi niyyar na tsorata ku ba. Ina buqatar hutu yanzu ku fita kawai kar wanda ya sake shigowa idan bani na buqata ba". Yana rufe baki Bibi ta fice da gudu har sannan jikinta rawa yakeyi dan tunda take Dadyn be taba daga mata murya balle yayi mata tsaya irin haka, Humaira ma fita tayi jiki a sanyaye a ranta tana tunanin to meya faru ne me ya saka Khalil din birkicewa haka?

Kallon Mu'ayyad yayi dake tsaye ko gezau beyi ba har sannan hannayensa harde yana kallon Khalil din shima, wani abu me daci ya hadiye kafin ya bude baki da kyar yana kallonsa yace
"Wa zata aura?"
"Nima ban sani ba, tace ka kirata nasan zata gaya maka" ya bashi amsa seya daga masa kai kawai dan maganar qara harzuqo masa zuciya takeyi. Ya ringa juyi akan gado yama rasa tunanin me zeyi, aure? Umaimah? Abubuwan da suka ringa masa yawo a kwakwalwa kenan. Har gurin qarfe goma ya gagara qulla komai, kamar ya kirata yanda ta buqata to me zece mata ko me zata ce masa ma idan ya kiratan? Badai aure zatayi ba taje tayi shi meye nasa a ciki?

Yana kwance yana malelekuwa, tunawa da yayi da ko sallar Magriba beyi ba gashi har anyi Isha tuni ya sakashi miqewa dole yana dafa bango saboda ciwon da kansa yake masa ga jiri ya shiga bandaki. Seda ya watsa ruwa kafin ya rama sallolinsa, yana zaune ya janyo wayarsa dake kan gado dan tun yana sallah take kawo haske saboda a silent take, missed calls din Humaira ya gani seya miqe jikinsa a matuqar sanyaya ya fita daga dakin. Tana zaune a falo gaba daya ta firgice itama baya zaton ko abinci taci ya qarasa kusa da ita ya zauna murya babu amo yace
"Ina yaran?"
"Sunyi bacci" ta bashi amsa tana kallonsa seya kallo agogon dake jikin bango, goma harta gota ashe ba qaramin lokaci ya bata a kwance ba. Janta yayi jikinsa yana cewa

"Kuyi haquri dazu na tsorata ku raina ne a bace ita kuma tazo tana yi mun kuka"
"Amma ka tsoratata sosai, dakyar tayi bacci tana ta kuka ni kaina kukan ne kawai yaqi zuwar mun amma tunzu nake so nayi, waye ya bata maka rai " da yaja ka huce akan mu?" Humaira ta fada tana dora kanta a qirjinsa, yanda zyciyarsa take bugawa ya sakata dagowa ta kalleshi ta sake cewa
"Kaji bugun zuciyarka kuwa? Dan Allah ka gaya mun meya sameka?"
Murmushi yayi yana maida kanta qirjinsa yace
"Babu abinda ya sameni, wani abu ne dai yake damuna amma na roqi Allah nasan ze yaye mun"
"Tunda kace Allah ka gama komai, amma idan ba zakaje Asibiti ba ka kira azo gida a dubaka dan wannan bugun zuciyar ya wuce normal ga jikinka ma yayi zafi"

"Humaira, na gaya miki lafiyata qalau da nayi bacci koma menene ze dena, ki dena damun kanki" ya fada a tausashe dole tayi masa shiru kusan minti biyar ta miqe ya kalleta yana tambayar ina zataje tace Abinci zata kawo masa
"Naqoshi, bazan iya ci ba" ya bata amsa kai tsaye, seta dauki dankwalinta dake ajiye tana cewa
"Gara naje na gayawa Hajiya kawai qila ita idan ta maka magana zakaji ya zakace mun lafiyarka qalau bayan gashi nan jikinka duk ya nuna baka da lafiya"
"Saboda kawai nace bazanci abinci ba shine zaki gayawa Hajiya? To ki kawo mun Tea, cikina ya cushe bazan iya cin wani abu me nauyi ba" ya fada yana kwanciya. Ta kawo masa Tea din da cake harda maganin ciwon kai dayace yana damunsa yana sha ya koma daki ya kwanta, damuwar data shiga ta sakashi dole ya saisaita kansa amma abin yafi qarfinsa, kafin safiya zazzabin gaske ya rufeshi da ciwon kai me tsanani sannan bugun zuciyarsa ya qaru sosai har qirjinsa yana dagawa. Duk yanda Humaira tayi dashi akan su tafi Asibiti yaqi, yasha paracetamol kawai yaci gaba da kwanciya a cewarsa stress ne daya samu hutu ze warware nan kusa qasan ransa Allah kadai yasan irin jinyar da yakeyi.

Idan ya tuna wai Umaimah zatayi aure zata zama mallakin wani bashi ba se yaji kamar yayita kwala ihu. Hajiya da taji shi shiru tun dare be shiga ba ga safiya tayi har gurin goma nan ba babu labarinsa ta taka dakyar saboda jiki daya motsa mata itama kwana biyu taje bangaren nasu dan ta duba ko lafiya ta saba yaran ma kafin su fita makaranta duk zasu shiga yau kuwa babu wanda ya leqata. A Kitchen ta tarar da Hunaira na hada masa faten dankali dan yaqi cin komai da sukayi na kari yace shi yake so, ta gaida Hajiyar, yanda ta ganta sukuku ya sakata tambayar lafiya take idon Humairan ya kawo ruwa tana gaya mata Khalil bashida lafiya tun jiya kuma yaqi yaje Asibiti. Hajiya ta ringa masa fada yanda taga jikin nasa dole ya tashi badan yaso ba suka tafi Asibitin ruwa aka fara daura masa kafin sauran gwaje gwaje ya biyo baya Likita yace musu da Malaria yar kadan se damuwa itace ta haddasa masa bugawar qirji da ciwon kan. Ranar a Asibiti suka wuni, Hajiya ta sakashi gaba da tambayar meyake damunsa da har yake neman ya kwantar dashi ciwo amma ya kafe akan babu komai shi ba damuwa bace ayyukane da suka masa yawa kwana biyu dan Anwar baya nan shine kawai gajiyace, badan ta yarda ba ta rabu dashi sedan likitan yace kar su ringa matsa masa su barshi ya samu wadataccen hutu tukunna.

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 89

A gida da suka koma yanda taga yaran na dararewa musamman Bibi yar gaban goshinsa amma ta kasa ko zuwa kusa dashi ta maqale jikin kujera yasa Hajiyan ta sake shan jinin jikinta ta kuma gasgata zarginta dan taji qishin qishin din zancen auran Umaimah ta tabbata maganar tazo kunnensa kenan tunda jiya sunje kenan shine dalilin ciwon nasa. Bata ce masa komai ba ta daiyi masa gargadin rage tunani da kuma shan magani yadaiji abinda likita yace. Seda yayi sati a kwance dukda yaji sauqi amma jinyar zuciyarsa bata warke ba irin damuwar da gidansa gaba daya ta shiga ya sakashi qarfafa kansa dole ya koma walwalarsa amma duk sanda ya tuna zancen Umaimah zatayi aure se qirjinsa ya buga idan a tsaye yake seya zauna da addu'a da komai ya samu nutsuwarsa ta daidaita, yana so ya kirata, yana so yayi magana da ita amma yana tsoron abinda hakan ze haifar. Baya so rauninsa yayi yawa harya kasa daurewa, ya rigada yayiwa kansa alqawarin rabuwa da ita ta har abada ya tabbata kuma a yanda take ji a zuciyarsa muddin ya hadu da ita komai ze kwance masa yasan baze iya tsallakewa tarkon Sonta ba.


Haka yaci gaba da lissafin kwanakin da suka rage ta zama matar waninsa, a tsayin lokaci yayi rama da kana ganinsa zaka fahimta amma ya fake da cewar aiki ne, waya ya siyawa Bibi da qaton Makeup kit da tace tana so zata koya tuntuni a matsayin ban haqurin tsawar da ya mata data saka take gudunsa tun lokacin, yanda ne tada zancen Momynsu ba suma sunyi hankali babu Wanda ya kuma masa maganar amma fa kana kallonsu suma kasan basuda walwala kamar baya tun Humaira na damuwa harta zuba musa ido kawai dan ta kasa gane menene musabbabin damuwarsu gaba daya, tsakaninta dasu Addu'a akan koma menene Allah ya shiga ciki ya yaye musu.

UMAIMAH
Tun tana saka ran kiran Khalil harta cire taci gaba da kaiwa Allah kukanta kawai tana cigaba da roqon gafararsa. A bangaren shirye shiryen biki tuni sunyi nisa, wannan karon ma Anty ta dage dayi mata jiqe jiqe da tsume tsume, ita kam ta rasa yanda zata misalta karamci irin na Antyn, idan da ace ta kasance me dogon tsinkaye ada da bata kyamaci kishiya har haka ba, ya kamata ace Antyn ta zame mata kyakykyawan misali da zesa ta saki zuciyarta akan dukma wadda zatazo ta tarar da ita amma ta gagara yin hakan sema ya zamana ita ta ringa jin zafin kishin Antyn a maimakon Mama da suka hada Miji daya da ita.

Sati hudu suka shude wanda ya rage saura sati hudu cif auransu da Abdulwahab kamar yanda aka saka rana. Lafiya lau suke waya tareda duk wasu shirye shiryensu dan hatta gidan da zata zauna a Abujan ana can anata aikin gyara da fenti, ya gaya mata kuma yana da kusan komai na amfani dan haka kartace zata yi wasu kayan daki idan taje duk abinda babu ko taga beyi mata ba daga baya s su canzadata gayawa Maman Asad tace babu damuwa dukda haka akwai abubuwan da ya kamata ta siya kamar kayan Kitchen dasu Bedsheets da sauran kayan qyaleqyale na gida amma dai zasu jira saura sati daya biki dayace za'aje a ga gurin in yaso daga nan se su qarasa shawarar abinda ya kamata suyi. Da suka gayawa Mama cewa tayi duk yanda sukayi daidai ne dan bikinsu ne se Anty da take tayasu shirye shiryen.
Sunyi waya da Abdul din ranar Alhamis ya sanar mata Juma'a ze shigo Kano, tun tafiyarsa bezo ba irin yana kuma yana daga dalilan da suka shi qara aure saboda zamansa yafi yawa acan ita kuma Khadija ta kafe akan ba zata iya zaman Abujan ba daya rasa dalilinta na hakan. Shiri sosai Umaimah ta ringayi na tarbarsa. Maman Asad bata gari Qanwar Mijinta ta haihu ta tafi suna Jigawa kuma se Lahadi zata dawo dan haka a nan gidansu zata tarbeshi. Yanda ta kasa zaune tana ta hidimar hada masa abubuwan motsa baki tun ana gobe ze dawo din yasa Anty sakata gaba da tsokana, Mama dai nata ido idan Anty ta sakota a maganar sedai tayi murmushi tace sunfi kusa a zuciyarta kuwa kullum cikin godewa Allah takeyi da Al'amuran suke zuwa a sauqaqe, taji matuqar dadin yanda Umaiman ta ajiye komai ta karbi zabin da Allah yayi mata. Auran nan da zatayi ba qaramin faranta mata yayi ba sannan ga Mijin data samu yaron kirki a kullum addu'arta kenan kar Allah ya jarabci Umaiman da abubuwan data aikata a baya gashi Addu'arta ta karbu tana kuma fatan kar ta basu kunya ta zauna lafiya da Mijinta karya zamana tuban muzuru tayi idan taje tajo dadi halinta na baya ya dawo dukda tana mata kyakykyawan zaton tuba tayi na gaske.



Ranar Juma'ar da Abdulwahab ze dawo bata fita aiki tun safe ta shiga qarasa shirye shiryen da batayi ba. Ya sanar mata jirgin safe ze biyo kuma a unguwarsu ma zeyi sallar Juma'a dan yayi missing dinta sosai yana so yazo ya ganta shiyasa ta dage qarfe daya ta gama komai Yasir tasa ya gyara mata falon baqin Abba tun safe bayan tayi wanka ta dauki garwashi ta zuba turaren wuta daga wanda akayi mata na auren takai falon wani abu ya ringa taso mata data tuna shekarun baya sanda Khalil yake zuwa wajenta. Ta saka turaren ta qara gyara gurin kafin ta kulle ta koma daki. Seda tayi sallar Azahar kafinta shiga rangada masa kwalliya, tunda suka fara haduwa da Hijab yake ganinta da safa dan haka ta qudurce yau zatayi masa kwalliya saboda kamar yanda Hausawa sukace wai ka gaida me gaisheka, Abdul din ya cancanci duk wata kulawa da tarairaya daga gareta saboda yanda yake ji da ita zaka rantse be taba son wata Mace ba se a kanta.

Ta shirya tsaf ta haye gado tana zaman jiran wayarsa yace mata gashi a waje dan an sakko daga masallacin unguwar tuni batayi aune ba se ji tayi ana kiran sallar data tabbatar da La'asarce, agogo ta kalla uku da rabi da minti takwas mamakin ma dadewarta a zaune haka tayi seta miqe jiki a sabule tana tunanin to ina ya tsaya kuma be kirata ya gaya mata ba. Wayarsa ta shiga kira sedai aka matar Mtn ta sanar mata a kashe take, mamaki ya qara kamata, sunyi waya gurin sha daya yana sake jaddada mata da cewar a unguwarsu fa zeyi sallar juma'a to kardai wani abun ne ya faru dashi? Da wannan zulumin tayi sallar La'asar ta fito Mama na gyara zogalen da zatayi miyar dare Anty na daka mata gyada a turmi suka kalleta Mama tace

"Har baqon naki ya tafi ne?"
"Ai bana jin yazo ma ko dan ga Zobon da aka masa can a Fridge din dakina bata dauka ba fasa zuwa da ranar yayi?" Anty ta fada seta ja kujera ta zauna kawai zuciyarta na tsinkewa ta rasa me zatace musu ma.
"Kinga ana magana tayi wa mutane banza kamar bataji" Mama ta sake fada seta dago idonta ya fara tara hawaye tace
"Befazo ba Mama kuma na kira wayarsa a kashe" se Mama ta harareta tace
"Toh shine zakiyi kuka? Daman banda son zuciya ma mutum ya dawo daga wani gurin tsahon lokaci baze zauna da iyalinsa ba seya kwaso qafa ya taho gurin gaibu ita ta gidan ce miki tayi bata iya girki da tarairayar miji ba kenan da zata sako shi ya taho daga dawowarsa" Anty tayi dariya tana cewa

"Toh Allah dai yasa lafiya amma ko dazu ina ji yana jaddada mata a unguwar nan zeyi salla keep nga ko indai ya fito din da doke zezo kuma dai ai ba zata hanshi fita sallar Juma'a bako sedai idan wani gurin yayi kiyita gwada wayar tasa dai dan wannan dabge gaskiya baya wuce shi ba"
"Idan kuma rabon mune ai shikenan" Mama ta sake fada yana miqewa Umaimah dai ta zabga tagumi tana sake gwada kiran Abdulwahab se ta shiga amma har wayar ta qaraci ringin be daga ba tana katsewa ya turo mata da saqo akan ze kirata.
"Kinga ta shiga Anty amma be daga ba ya turo mun text wai ze kirani" ta fada tana nunawa Anty wayar ta kalla tana cewa
"Yawwa to ai haka yafi qila wani abun yakeyi ze kirakin inya gama.
Shiru shiru be kirata ba har aka kira magriba lokacin ta gama cire rai da zuwansa dan qila dai ta bakin Mama ko Matarsa ce ta hanshi fita ya kashe waya wannan tunanin ya bata mata rai, kumallon mata ya motsa ta idar da sallar ta ????####### #
# # #
################### #!#"###$#%#&#'#(#)#*#+#,#-#.#/#0#1#2#3#4#5#6#7#8#9#:#;#<#=#>#?#@#A#B#C#D#E#F#G#H#I#J#K#L#M#N#O#P#Q#R#S#T#U#V#W#X#Y#Z#[#\#]#^#_#`#a#b#c#d#e#f#g#h#i#j#k#l#m#n#o#p#q#r#s#t#u#v#w#x#y#z#{#|#}#~##?#jiyo Yasir a tsakar gida da Abokinsa ta kwala masa kira yana shiga tace yaje ya kwaso kayan Abincin data ajiye a sitting room, Nuratu data zo gidan ta taso daga aiki tace
"Kice rabo na ne ya rantse da kamar karna biyo" Umaimah tayi mata banza ta nemi plastic robobi ta debi komai tace ta huta girki idan ta koma daman daga ita se Dr yaran na gidan Kakanninsu duk Umaimah najin su suna buduri da abincin da tun jiya take wahalar shiryawa bata ko fito daga dakin ba bare ta kulasu.

Wasa wasa har gari ya waye be kirata ba kamar yanda yace kuma idan ta kirashi wayar zatayita ringing harta katse baze dauka ba tun tana daukar abin a matsayin wulaqanci har ya koma bata tsoro, to meya faru kuma? Ita tayi masa wani abun ko kuma daga bangarensa ne wani abu ya faru daya saka baya amsa kiran nata kuma shi be kirata ba? Weekend ya qare dakyar ta iya fita aiki saboda yanda damuwar Abdulwahab take neman kwantar da ita. An cinye sati guda cur be kirata ba kuma idan ta kira ita baya dauka Alhalin tana ganin sa online yanayin status idan ta masa magana ze bude amma baya bata amsa abinya dameta qibar data farayi duk ta zube a satin saboda ko abincin kirki bata iyaci, lissafin saura sati uku biki akeyi amma Ango ya shareta to meya faru? Tana da buqatar qarin bayani a gurinsa idan ma wani abun tayi masa kamata yayi ya fada mata bawai ta hanyar wannan horon ba.

Mama kanta ta shiga damuwa tunda ta shaida mata bata samunsa a waya idan ta kira baya dagawa har seda ta yiwa Abba maganar a cewarta ko ze tuntubi Alhaji Zakari yaji lafiya kar aje wani abun ne ya sameshi basu sani ba yace mata babu komai, ya tabbatar idan da wata damuwa kafin ma su tuntuba zasu sanar dasu su zuba ido koma menene Allah ya shiga ciki kawai.
Ranar Juma'ar data kama sati daya cif daya kamata yazo din da daddare tana kwance a daki Abba ya kirata a waya yace taje falonsa ta sameshi ta zura Hijabinta ta tafi tana shiga gabanta ya fadi saboda yanda ta taraddasu jigum jigum ta samu gefe ta zauna tana gaishe da Baba Abdullahi da Baba Liman. Baba Liman din ne yayi magana cikin sanyi yace mata

"Yanzu waliyyan Abdulwahabu suka tashi daga nan kuma sunzo bamu haquri ne akan cewar Dansu ya janye daga neman auranki bisa wasu dalilai sannan sunce mu baki haquri a madadinsa yace yana jin nauyinki dalilin dayasa ya gaza daukar wayarki kenan dan haka kiyi haquri ki kuma yi addu'a Allah yasa hakan ya zame miki Alkhairi daman Allah yayi ba mijinki bane shidin kinga babu yanda za'ayi"
"Yo haqurin me zaka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login