Showing 123001 words to 126000 words out of 429394 words

Chapter 42 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

1032

sake bari ta mayar dashi Soko ta qibin umarninsa sannan tazo tana masa kissa da kisisina tayi zaton ze sakko ba saboda ga Jarababbe.

Wankan ya shiga yayi, a kan bedside drawer ya tarar da Butar shayi da cup se madarar ruwa wadda yake amfani da ita se qaramin Bowl data zubo wani abu kamar cookies kamar cake. Seda ya sakawa qofar dakin key kafin ya shafa mai a jikinsa sama sama ya koma gefen gadon ya tsiyaya ruwan shayin a kofi se tashin qamshi yakeyi irin yanda yake so amma idan ba ita tayi ra'ayi ba farin ruwan fanfo zata tafasa ta zuba masa a flask ta bakinta da fada can ya gane.

Tas ya cinye cookies din ya sha shayin ya ture kayan gefe ya haye gado, se a sannan ya kunna wayarsa da tunda ze hau jirgi ya kasheta. Saqon Hadiza ne ya fara shiga na barka da Safiya sena Juma'a ya biyo bayansa, yayi murmushi yana mayar mata da amsa kafin ya danna mata kira dan yana so yaji muryarta. Seda gabansa ya fadi sanda yaji motsin Umaimah tana taba qofar, Hadiza ta daga wayar kamar wani munafuki yayi qasa da murya yace mata
"Sorry Dija zan kiraki" kafin tace wani abu ya kashe wayar.

Daga kan gadon cikin daure murya yace
"Ya akayi ne" qirjinsa na dukan saba'in saba'in saboda tsoron ko Umaimah taji maganar da yayi a waya, Umaimah dake tsaye a waje ta harari qofar cikin kissa tace
"Ban gane ya akayi ba mace zata shiga dakin Mijinta ka ringa tambayarta ya akayi wai meye ma dalilin rufe qofar da key?"
"Bacci zanyi bana son damuwa please, idan qarfe daya tayi ban tashi ba ki tasheni" ya bata amsa kafin yaja bargo ya rufe jikinsa ya juya baya kamar tana cikin dakin.

Baqinciki ya shaqe wuyan Umaimah ita Khalil ze wukaqanta dan ma yaga tana ta tasa ko, wallahi badan da abinda take nema ba ko kallo be isheta ba tunda ai ita ya kamata tayi fushi ya tafi yawonsa ya barta kusan wata biyu kamar wata gantalalliya. Kwafa tayi ta koma cikin palour ta zauna, tayi niyyar har girki tayi masa amma yayiwa qaton kansa badai yaci na rana ba sedai da dare idan taga dama tayi.

Khalil kuwa yanajin ta matsa daga qofar ya sake kiran Hadiza suka shiga hira dukda a hankali yake maganar kuma cikin takatsantsan ita kanta Hadiza seda ta tambayeshi lafiya tajishi haka yace mata babu komai, sunyi kusan minti goma kafin sukayi sallama saboda tace masa ta tashi aiki zata wuce gida ya ajiye wayar babu dadewa bacci ya dauke shi bayan ya saita alerm dan ya san indai Umaimah ce sedai ya kwana yana baccin nan ba tashinsa zatayi ba musamman da ya rufe mata qofa.

Tana nan zaune tana danne danne a waya har Azahar tayi, bataji motsin fitowar se tambayar ta da yayi ina Mu'ayyad, a firgice ta dago kamar mara gaskiya, yana tsaye akanta yayi wanka ya saka manyan kaya Light blue din shadda data karbeshi sosai ya kafa hula daman Khalil ba daga baya ba gurin iya saka hula, haka nan taji wani abu ya soketa, ba yanzu ya fara saka manyan kaya ba musamman da yake yau juma'a amma haka kawai taji kwalliyar tasa ta yau tayi yawa ga uban turare daya fesa seta tura baki tana kallonsa tace

"Gaskiya kaje ka canza kaya kayi kyau da yawa ba zaka fita a haka ba"
"Se kizo ki cire mun ai, ina tambayarko kina yi mun wani shirme" ya bata amsa yana kallonta. Gefe ta kalla ta tunzura baki tace
"Ai shikenan, amma wallahi duk wadda ta kalleka Allah ya isa".

Yana shirin tambayarta shi take yiwa Allah ya isan ko kuma wadda zata kalleshin suka jiyo bugun qofa da qarfi. Tsaki yaja ya fita, seda ya tambayi waye kafin ya bude qofar jin muryar mace yasan baze wuce jama'arta ba tunda tun a kwanaki ya lura yanzu tana hulda da maqota suna shige da fice a gidan.
Hauwa dake goye da Mu'ayyad ta gaishe shi ya amsa yaron ya juyo da sauri ya kalleshi seya hau zillo yana bangala dariya alamar ya ganeshi, sakko masa shi tayi ya karbeshi ya rungumeshi a qirjinsa yanajin qaunar yaron tana sake ratsashi.

Ya qara girma da wayo sosai akan lokacin daya tafi, tsawar da Umaimah ta katsawa Hauwa data saki baki tana kallon su Khalil dince ta dawo dashi daga shauqin kewar Dansa. Masifa take mata akan kallon meye ta kafe su dashi kamar wata mayya
"Wayace ki zo ma yanzun kuma da kika shigo meya hana ki wuto ciki kaitsaye zaki tsaya kina kallonsa kamar wani sa'anki" Umaimah ta fada cikin daga murya, Hauwa tayi rau rau tace
"Yaqi zamane Anty se kuka yakeyi sannan ya bata kayan jikinsa shine Mama tace na dawo dashi idan ya huta se mu koma".

Kallon kayan jikin nasa Khalil yayi se a sannan yaga bacin da sukayi da kamar gasarar koko komenene har sun bushe, fuska a hade ya miqawa Umaimah shi jin ana kiran sallah yace
"Kiyi masa wanka ki canza masa kaya, kar a sake fitar mun da yaro wani guri kinji na gaya miki" ta karbeshi ya bude Get din, tana tsaye ya fita da Mota ya dawo ya sake rufewa kafinta raka bayansa da harara tareda jan dogon tsaki seta juya kan Hauwa data sunkuyar dakai tun masifar data farayi mata tace

"Daga yau se yau karki sake shigowa gidan nan idan Mijina yananan, kuma ko a hanya kika ganshi karki kuskura ki nuna kin sanshi ballantana ki gaidashi idan kuwa na sani zaki gane kurenki".
Kallonta Hauwan tayi a ranta tace ikon Allah a fili kuwa se tace
"Toh Anty tayaya zan san idan yana gida kuma ko yanzun ai bugawa nayi bansani ba shiya zo ya bude kinga bazanqi gaishe shi ba"

Ciki ta juya ta bita tana cewa
"Daga yau ki bar zuwa sedai idan ni na kiraki" Hauwa ta amsa da "Toh Anty".
Wanka ta saka tayiwa Mu'ayyad din ya ringa tsala kuka kuwa tana falo tana mata masifar me take masa yake kukan tace babu komai ashe da ruwan sanyi take masa wankan kuma garin daman da sanyi. Haka ya ringa Atishawa bayan gama wankan amma sam hankalinta be kai ba, ta dauko mata kaya ta shirya shi ta dama masa abincinsa shima dakyar suka dura masa ana gamawa ya dawo dashi ta ringa surfawa Hauwa masifa se kace ba ita tace tayi masa durar ba, ita dai data samu ta gyara masa jikinsa yayi bacci ta sulale tabar mata gidan.

Khalil daga Masallaci gidan Hajiyarsa ya wuce, a can yaci abincin rana tana tambayarsa su Umaimah tareda qorafin meyasa be fada mata yau zasu dawo ba ai da anyi musu girki yace mata babu komai tafiyarce tazo musu babu shiri dukda haka tace se anyi na dare an kai musu ya gayawa Umaiman kar ta dora komai.
Yadan jima suna hira har gurin uku kafin yayi mata salkama ya kama hanyar Na'ibawa gidansu Hadiza, tiryan tiryan se gashi a qofar gidan daya saukesu waccen ranar har mamakin kansa yakeyi yanda ya iya ganewa, guri ya samu yayi parking yana tunanin ta inda ze gano gidan su dan baya so ya kirata surprising nata kawai zeyi.

Glass din gefensa aka kwankwasaz qawar Hadiza ce me shegen rawar kan nan da baze ma iya tuna sunanta ba, sauke glass din yayi ta washe masa baki dole shima ya qirqiro murmushin da be kai zuci ba ya amsa sannun da take yi masa.
"Yau gaka a unguwarmu" ta fada tana qara fadada fara'arta,
"Eh wallahi gara da Allah ya kawo ki ma, daman neman wanda zan tambaya nakeyi tunda gaki ma shikenan" ya fada yana kallonta.
Murmushin dai ta kumayi tace
"Gurin wani kazo kenan da har ina tunanin..."
"Gurin wata dai, gurin qawarki Khadija nazo kinsan wancan ranar anan na tsaya ban san ina ne gidansu ba kuma bana so na kirata so nakeyi na shammaceta kawai se naje qofar gidan zan kirata" Khalil ya katseta kafin ta fara masa shirme.

Idan da ace hankalinsa akan Khausar yake da yaga sanda numfashinta ya tsaya na wani lokaci sakamakon jin abinda yake fada, abinda ta dade tana addu'a, tun ranar data fara ganinsa rana bata fito ta koma ba ba tareda ta roqi ubangiji daya mallaka mata shi ba shine yanzu zezo har qofar gidansu yana tambayarta gidansu wata, abinda take muradin samu daga gareshi ya mallakawa watanta kenan

"Khausar kinyi shiru kina kallona lafiya dai" ya fada yana kada yatsunsa akan fuskarta ganin ta tsura masa ido babu alamar kuma hankalinta yana kansa ne. Firgigit tayi kamar wadda ta tashi daga bacci kafin tayi qoqarin danne duk wani abu da takeji a ranta tace
"Yi haquri kaina ne yake ciwo magani na fito na karbo daman a Can Chemist din, bari na kwatanta maka babu nisa da ka kai qarshen layin nan kace a nuna maka gidan su Salim nan ne"
"Maimakon ki shigo ki rakani?" Ya tambayeta, seda ta dauke kukan dake shirin zubo mata kafin ta girgiza masa kai tace
"Aa, kaje kawai idan kan ya sauka qila kafin ka tafi zan shigo".

Motarsa ya kunna ya qara gaba, yana bacewa ganinta ta fasa ihu tareda zubewa a gurin kamar wadda ta hau iska seda Mahaifiyarta dake tsakar gida ta fito da gudu tana tambayar menene. Kuka Khausar takeyi tamkar ranta ze fita, tunda ta dora ido akan Khalil soyayyarsa tayi mata kamun kazar kuku, ta saka rai da samunsa a shirye kuma take da tayi duk me yuwuwa akan ta same shi shine yanzu ma Hadiza zata sake yi mata kwacen saurayi? To wallahi sedai kowa ya rasa a wannan karon ma ta gwammaci suci gaba da zama gaba dayansu har qarshen rayuwarsu ba tareda aure ba idan har bata samu abinda take so ba toh kuwa ba zata barwa Hadiza ba

Khalil kuwa kamar yanda ta bashi kwatance haka yabi, a can qasan layin ya samu yara ya tambayesu suka nuna masa gidan. Gidane qaramin na masu rufin Asiri ya samu guri yayi parking kafin ya aika daya daga cikin yaran akan yayi masa sallama da Hadizan.
Dawowa yayi yace tace ace bata nan abin ya bashi dariya daman ta gaya masa bata fita zance in har bata san da zuwan saurayi ba dan haka ya ciro wayarsa ya kirata.

Sosai tayi mamaki dan bata yarda dagaske bane seda ta ganshi. Har cikin gidan ta shiga dashi suka gaisa da Mahaifiyarta tana ta saka musu Albarka duk se kan Khalil ya qulle ya rasa gane me Hadizan ta gaya mata yake tsakaninsu da take irin wadannaj maganganun. A qofar gida suka qarasa zancen shida yaje da niyyar yin minti talatin ko qasa da haka se gashi ya kwashe kusan awa biyu ya rasa dalilin dayasa yake jin dadin hira da Hadizan kodan tana da hankali ne sannan gogaggiya ce a kan harkokin rayuwa saboda yanayin aikinta da mutanen da take mu'amula dasu shiyasa duk wata magana tata take zama ta hankali da nutsuwa.

Wayarsa da ake ta kira ce sakasu katse hirar da sukeyi, gabansa ya bada Rass ganin me kiran, kafin ya daga wayar ta katse se a sannan ya ga tarin missed calls din da tayi masa har goma haka nan yaji jikinsa ya dauki rawa, a iya saninsa babu abinda ze saka Umaimah jera masa wadannan kira sedai rashin lafiya ko kuma ta ganshi ko ta samu labarin yaje gurin wata a zuciyarsa ya raya Allah yasa rashin lafiya ce dan ta fi masa sauqin tashin hankali akan ace Umaimah ce ta ganshi ko taji labarin yaje hira gurin wata mace.

Sallama yayiwa Hadiza ya shiga mota tana tambayarsa lafiya ganin yanda ya rikice lokaci daya yace mata babu komai ta shiga gida zasuyi magana. Seda ya bar Titin Na'ibawa gaba daya kafin ya samu gefen hanya ya gangara ya tsaya. Kamar wanda zeje gaban Alqali ya bada shaida haka ya ringa gyaran muraya yana gwada yanda zeyi magana dan harga Allah hankalinsa a tashi yake.
Daurewa yayi ya danna kiran wayarta.

*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS>???>???*

*=؞?Barkan mu da warhaka en uwa mata, bugu da qari ba kadai a bangaren kayan gyaran aure ingantattu ta tsaya ba, ta na bada magunguna na musulunci akan cututtuka na yau da kullum wanda suke damun al'umma.*
*Cututtuka irin su matsanaicin ciwon mara a lukuta mabanbanta ko kuma lokacin al'ada, daukewan al'adan lokacin daukewan bai zo ba, al'ada ya rinqa wasa, rashin sha'awa ko ciwon kai, ciwon qirji wanda aka rasa gane kanshi ana tunanin ulcer ne, kuma anyi maganin amma har yanzu ba a dace ba, matsalar Ashiq wato aljanin soyayya(wannan sai bayan tambayoyi sannna za a tabbatar). Ciwon ciki, hawan jini, ciwon sugar, ciwon hanta, typoid/malaria, basir, ciwon baya da qafa, ciwon qashi da kuma matsalar infertility, duk da haihuwa Allah ne ke badawa amma kuma a wasu lokutan akwai cututtuka da kan kama mahaifa ko kuma reproductive system din mace wanda su kan iya hanata daukan ciki. Cututtuka irin su Endeomatriosis, cervicitis, fibroids, etc.*

*Ku karzayo domin lafiya uwar jiki=ت?=ت?, sannan ta bangaren gyaran aure, sumayyas herbal ta lashi takobin qara zage damtse wajen inganta kayayyakin ta domin samun maslahan ku a* *rayuwar ku da auratayyan ku. Aure dai ibada ne a don haka gyaran aure wajibi ne, musamman idan kin samu in da zaki gyara kan ki da kayayyaki na kwarai wanda basu da illa ga lafiya kuma ba irin kayan da zasu Kai ki ga halaka ba,su saki rasa imanin ki duk wai da sunan gyaran aure. Ah ah er uwa ayi hattara kar garin neman gira a rasa ido.>??? @&? Allah ya tsare mana imanin mu=?O?=?O?*
*Garzaya ki dannan link din kuma kiyi saving number ta domin kuwa akwai alfano mai yawa.*
*Wa.me/+2347031876677*
*Ko kuma akan Instagram*

*https://www.instagram.com/p/CqQJVrVIdjq/?igshid=MzRlODBiNWFlZA==*
*Allah ya biya mana buqatun mu na alkhairi amin.*


*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?
Page 34

Har wayar ta qaraci ihunta bata daga ba, ya sake kira nan ma haka, ajiyar zuciya me qarfi ya saki ya zari tissue ya goge zufar sata tsatstsafo masa a goshi dukda Ac motar a kunne take. Key yayiwa motarsa ya koma kan titi yaci gaba da tafiya. Tunawa da yayi beyi sallar La'asar ba dan yana qofar gidansu Hadiza aka kira yasaka shi neman Masallaci akan hanya yayi sallar sa. Tunanin inda zeje yakeyi, kamar ya koma gidan Hajiya sa seya tuna tace masa zataje barka matar dan qawarta ta haihu haka nan ya yanke shawarar zuwa ya gaida Mama babu bata lokaci ya kama hanya.

S?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 eda ya tsaya yayi musu tsaraba kamar yanda ya saba baya tana zuwa gaida surukan nasa haka nan ko babu yawa seya riqe wani abun. A qofar gida ya hadu da Yaya Aminu wanda shima zuwansa kenan suka gaisa kafin suka shiga cikin gidan tare. Mama bata nan taje gidan Anty Hafsa dan tun Rasuwar Mijinta bata cika lafiya ba, shiyasa kusan duk sati Maman ko Anty wani zeje ya gansu dukda akwai yar Uwan Abban su Goggo Halima dake zaune tareda ita kafin ta gama takaba.

Be jima a gidan ba ya ajiye musu tsarabar daya je da ita ya tafi bayaj Anty ta hada masa kayan Mu'ayyad tana masa tsiyar ashe shi yayi kira Umaimah ta gudu babu sallama. Haka ya ringa yawo a gari bashi ya koma gida ba se da yayi sallar Isha. Da fargabar abinda ze tarar ya bude Get ya shiga da motarsa. Seda ya kwashe kusan minti biyar a bakin qofa yana gwada budeta yana fasawa, qin amsa wayarsa da kuma rashin fitowarta ta tareshi suka qara sakashi a rudanin abinda ze tarar haka dai yayi shahada ya tura qofar da sallama ya shiga.

Tana kishingide akan kujera ta miqr qafafunta akan centre table. Skin tight ne fari a jikinta ya matse ta tsam? iyakarsa qaurin ta ga sarqar qafa silver data saka. Fuskarta ya kalla zuwa qirjinta se yayi sauri dauke kansa saboda yanda Armless rigar data saka bata boye komai na jikinta na, daman iya karta saman cibi kuma ta net ce ganin kamar bata ji shigowarsa ba ya saka shi hade fuska ya kama hanyar dakinsa se a sannan ta kalle shi, fuska a sake sabanin yanda yayi tunani tace
"Sannu da zuwa Honey"
"Yawwa ya amsa mata yana qarasawa inda Mu'ayyad yake akan tabarmar sa ta zuba masa kayan wasa.

Dagashi yayi ya kalli Umaimah da itama su take kallo yace
"Ya naji kansa da zafi sannan hancinsa kamar a toshe yake"
"Haqori ne inaga" ta bashi amsa daidai nan yaron yayi Atishawa me qarfi se khalil ya sake kallonta yana cewa
"Baki dena kunna masa Ac kuna kwana da ita bako, gashinan mura ta kamashi" seta zumburi baki ba tareda ta bashi amsa ba ya wuce dakinsa da yaron a hannunsa yanayi masa gwaranci ta rakashi da harara kafin itama tabi bayansa.

Ajiye yaron yayi akan gado yana sauke numfashi daidai nan ta turo qofar ta shigo ya zabura kamar mara gaskiya amma ganinta da Try da ruwa akai ya sakashi dai daita nutsuwarsa ya sake kame fuska. Ruwan ta miqa masa ya karba a ransa yana ayyana abubuwa da yawa. Wannan ladabin nata na gaske ne ko kuwa tarko take dana masa kafin ta fara buyagin nata.

"Dazu kin kirani wayar tana silent ban cire ba tunda naje masallaci na kira kuma baki daga ba" ya tambayeta yana cire rigarsa, seta ce
"Eh, daman so nake na gaya maka Unit ya qare lokacin kuma ina kallon wani series ne se kawai na ahiga gidan Maman Anam na qarasa bayan na dawo kuma Khalifa yazo ya kawo Abinci shine ya saka mana".

"Akan Unit ne kika mun ten missed calls na zata ma wani abun ne ya faru kuma da ya qare ba zaki kunna Solar ba" ya fada jin dalilin kiran da gaba daya ya saka jininsa ya kusan hawa saboda farga ba ashe shirmenta ne kawai,
"Toh idan da solar tana yi zan kiraka nema ai saboda taqiyi ne ya saka nake amfani da Nepa har Unit dinma yayi saurin qarewa" ta bashi amsa tana harararsa qasa qasa, se yaja qaramin tsaki yace
"Meya sameta? Kin qara dora mata abinda yafi qarfinta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login