Showing 63001 words to 66000 words out of 429394 words

Chapter 22 - Halin Kishi Book 1 Hausa Novel Complete

17 Jan 2025

970

shegen surutun nan ce bata gani tayi shiru, ita kuwa Habiba da yake miskika ce guri ta samu ta zauna tana qarewa palour kallo gurin ya mata kyau ga qamshi me dadi da sanyin Ac yana tashi.

A cikin daki kuwa Umaimah na shiga tun kafin tayi magana Khalil ya tareta da cewa
"Karki kuskura ki tayar mun da hankali a daren nan, babu sannu da zuwa babu komai se ki tsareni da wasu tambayoyinki marasa kan gado akan me danki ne ni ko yaya da zaki tsareni kina tuhuma a gaban yara Habiban ce baki sani ba ko kuma salon se kin jawo abinda rai ze zo yana baci ne? Ko kuwa bani da ikon shigo da wanda naga dama naga dai cikin gida nane bana wani ba"

Umaimah datayi shiru tana jinsa se ga hawaye shaa sun fara zubo mata ta fara magana cikin kuka tace
"Yanzu kawai saboda na tambayeka suwaye ka shigo dasu shine zaka fara yi mun gorin gidanka ne banawa ba amma dai nice matar gidan kuma ina da haqqi akan duk wanda ze shigo mun seda yardata. Kuma ni ai bance bansan Habiba ba, ita dayar me kama da Sadaka Yallan da kuka taho da ita nake tambayarka wacece, amma shikenan in sha Allahu bazan sake magana ba ko kasuwa zaka dakko ka kawo cikin gidan nan tunda abin ya zama harda gori" wiii ta saki kuka.

Kallonta kawai Khalil yake takaici kamar yayi me dan yarinyar ta gama raina masa hankali, jifa yanzu idan wani yaji ai se a zata wani mugun laifi ko wata baqar magana ya gaya mata shi beyi kuka ba se itace me bakin kuka?
Volume data qarawa kukannata kamar wadda yake duka yasakashi janyota jikinsa cikin takaici yace

"Wallahi Umaimah idan baki saurara ba sena hukuntaki da irin hukuncin da jikinki seya gaya miki, badai yau har kin samu damar tayar da tsiyatakunki ba? ki bari na riqeki gobe idan ance ki bude baki ki gayamun magana bazakiyi ba" kafin ma ya dire maganar ta hadiye kukan ta hau share fuskarta dan ba mantawa tayi da baqar wahalar data sha a hannunsa jiya ba, kawai gatan daya mata ya gasa mata jiki da maganin daya bata ne suka taimaka mata amma wunin yau duk idan ta tuno dare zeyi ji take gaban ta na faduwa.

Yanda take goge fuskar tana ajiyar zuciya se ta bashi dariya da tausayi,
"Maza ki wanko fuskarki muje ku gaisa na aiki Khalifa yana hanyar dawowa ze wuce dasu gida" ya fada yana riqe kafadunsa, seta daga masa kai ta wuce bandakin ta wanko fuskar ta tsane da towel ta fito har sannan yana tsaye a tsakiyar dakin.
"Muje" ya fada yana nuna mata hanya, seta marairaice fuska dan bafa ta haqura ba se ya gaya mata wacece wannan yarinyar

"Khalil dan Allah wacece ita?" Ta fada a marairaice, se ya juyo ya kalleta fuskarsa da murmushi yace

"Wato koma me zanyi bazaki fasa halinki ba ko? Toh Iman ce Autar Anty Uwa qanwar Hajiya ai kinsanta ko? Habiba ma ta girme ta ko nine shugaban masu son mata babu abinda zan tsinta a jikin waccen yarinyar kin dai san tayi mun kadan".

Gaba tayi ta barshi ya bita a baya yana murmushin takaici, tayi qoqarin gaske ta dora fara'a a fuskarta suka gaisa da yaran basu jima ba zega Khalifan ya kirashi akan yana qofar gida, fita yayi ya bude masa suka shigo tare ya karbi kayan daya kawo masa ya shige dasu shi kuma ya zauna suka gaisa da Umaimah a mutunche ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo harda dambun nama tana ta jan Habiba da hira idan Iman ta saka baki seta dan harareta kafin zata amsa, haka suka dan zauna kafin sukayi musu sallama suka tafi.

Ganin da tayi Khalil nata wani shan qamshi da farko itama seta share shi, har suka ci abinci ta gyara gurin se ya dakko system dinsa ya kunna ya shiga danne danne tana yi masa magana ze amsa ta ba tareda ya dago ya kalleta ba se kuma duk taji babu dadi tayi shiru kawai tana kallon Tv gashi ita ba waya ba dan ta bayar da kyautar wayarta tunda ta saka ran ze siya mata wata.

Har gurin goma saura suna zaune ita tana kallon da ba fahimta takeyi ba shi kuma yana ta aikinsa lokaci lokaci yana satar kallonta a ransa yana sake jinjina halinta. Wato bazata iya bashi haquri ba kenan ai kuwa zega qarshen gudun ruwanta. Qarfe goma na bugawa ya rufe system din ya shiga tattara kayayyakinsa yana kallonta yace
"Seda safe, karki manta ki kashe komai kafin ki kwanta" ya wuce ya barta a gurin ta rakashi da kallo baki a bude, ita ze wulaqanta akan dan wancan abin daya faru ze tashi ya barta wai idan ta gama ta kashe komai ta kwanta?

Yana dab da shiga dakin ya jiyo shashsheqar kukanta, be tsaya ba ya shige ciki abinsa ya ajiye kayan hannunsa kafin ya wuce bandaki yayi wanka. Seda ya bata lokaci yayi shirin baccin sa tsaf kafin ya fito palour lokacin Hajjajun tayi kuka ta qoshi baccin wahala ya dauke ta a qasan carpet data sauka tana birgima kamar wata qaramar yarinya, seda ya kashe kayan kallon data bari kunne da Ac kafin ya dawo daidai kanta ya tsaya yana qarewa fuskarta kallo a fili yace

"Drama Queen kenan" kafin ya sunkuya ya dagata gaba dayanta ya fara tafiya da ita ta bude ido, baki da kware zata fasa masa wani ya hanata damar yin hakan ta hanyar rufe mata bakin da nasa, be direta ko ina ba se kan gadonsa.

Yanda ya gaya mata seya hukuntata kam ta karbi hukunci me tsanani dan irin tausayi da lallabawar da ya ringa yi mata jiya sam yau din babu su, gashi daman kamar fami ne gurin har yafi jiya yi mata zafi. dirzarta yayi son ransa duk kuka da magiyar da ta ringayi masa be saurara ba seda ya gaji dan kansa kafin yaja gefe yana mata dariyar mugunta, ya kuma hada mata ruwa me shegen zafi ita dai ta jera masa Allah ya isa tafi cikin kwando a zuciyarta ta kuma quduri niyyar tunda shi mugune bazata sake yin abinda ze hado su dashi ba ballantana ya ci zalinta.

Haka suka ci gaba da cin kwanakin Amarcinsu cikin wata irin soyayya da tattalin junansu, sosai take qoqari gurin kiyaye duk abinda baya so haka tana nazartar abinda yafi so da wanda yafi yabawa idan tayi. A cikin wata daya da auransu Sabgar Aza room ce dai ta kasa sabawa da ita dan Khalil din jarumi ne na gaske, ta kuma fahimci baya gajiya da abin dan baya tsallaken rana idan ma ba tayi masa wuta wuta ba beqi ayi sau biyu ko uku ba wannan abun ne yake damunta da har ya saka ta fara rama dukda kyau da gogewa da fatarta ta qarayi amma ta rame.

Seda suka cika wata da aure kafin ta fara fita duk irin nacin da take masa idan ze fita tace zata bishi baya yarda, da daddare ranar ya kaita gidansu ta gaida Hajiyarsa. Kaya sosai ta diba daga akwatun lefenta ta dora da kudi irin wanda yake bata saboda sallamar baqin da suke dan zuwar mata sanna ta sake hada kayan kwalliya a wata ledar daban na Habiba. Khalil be san dasu ba seda sukaje gidan, sosai Hajiya taji dadin zuwanta ta cika ta da kayayyaki tana ta sa musu albarka kafin ta dora da fadan tsabara data kai musun tayi yawa dan Atamfa ce super ta dakko da wani dandatsetsen Lace harda Mayafi ta kaiwa Hajiyar, kudin kawai ta karba tace ta gode amma ta juya da kayan dan tayi amfani dasu aka zuba mata ba na rabarwa ne, Umaimah bata ji dadi ba haka ta dakko suka dawo Habiba ko se tsalle take da murnar kayan kwalliyar dan Hajiyar na fara fada ma ta kwashe nata tayi sama karma ace itama a juya dasu.

Kwana biyu a tsakani ya kaita gidansu, wannan tun da safiyar ranar da zasuje yace mata karta dauki komai zasu tsaya a hanya suyi tsaraba haka kuwa akayi tsaraba sosai sukayiqa yan gidan bayan isha suka isa abin dadi suka tarar da Nuratu da Mijinta a gidan suma sunje zo kaga murna aka ruguntsume kowa tana tsokanar yar uwarta wai ta chanza Mama ko har kwallar farin ciki ta share na ganin Umaiman tata tayi hankali ta zama cikakkiyar mace.

Da zasu tafi Anty ta kirata dakinta ta bata wata leda tace zasuyi waya, har zata fita ta tsayar da ita tace

"Umaimah kinyi kyau amma kin fada ko mu fara shirin taron megida ne ko kishiya".

Fuska ta yatsina dan dagaske itama taga ramar da tayi dan kayanta da suke cikata dam yanzu sun dan sassauta mata, babu kunya bare tsoron Allah tace

"Wallahi Anty wancan mutumin ne mugu duk shi yake ramar dani, wai idan mutum yayi masa abu bazeyi magana ba sedai ya qullaceka se munje bacci sannan ze sameni kamar sakwara ya daka ni ni wallahi har na fara tunanin ma na gudo gida ku kirashi kuyi masa magana dan gaskiya na fara gajiya tun ban rame na zama kwarangwal ba a ringa zaton wani ciwon ne dani ba'asan shi yake zuqeni da jarabarsa ba".

Zukudi Anty tayi ta rafka tagumi tana jinta seda ta dasa aya kafin tace
"Uhm Allah ya rufa asiri kowa da haka ta saba ai Umaimah, kije zangayawa Mama in yaso se a harhado miki abubuwan da zasu taimaka miki ki dena ramar"

"Ni kawai Anty kiransa zakuyi ku masa magana dan wallahi baki san irin abinda yake mun bane..."

"Ai bana ma so na sani Umaimah kije Allah ya bada haquri ki ringa shan fruits sosai zasu taimaka miki ki kuma cire tsoro a ranki ramar zata dena" Antyn tayi saurin katseta jin tana neman baro mata aiki, daga haka sukayi sallama suka kama hanyar gida ranar ba'a tsaya doguwar hira ba saboda washe gari Khalil ze koma aiki dan haka suna komawa wanka sukayi suka kwanta dan sunci abinci a gida.

WASA FARIN GIRKI


Assalamu Alaikum mutanen Kwarai=?M?
Shin kina son kwarewa fannin girke girken zamani,snacks da sauransu
Hajiya ta=؃? ga dama ta samu Mun bude online class wanda zamu koyar da girkin zamani yanda ake sarrafasu ta hanyoyi da dama& Akan kudi qalilan 200 ga mutane 10& daga bisano ze koma 300 kacal kedai kawai tura kudin ki ta wann acct din& ..
1509536481
Rabiatu Nuhu Aliyu
Access bank
https://chat.whatsapp.com/IL3QnKmFxojAATF6WkzGxK
8142548705
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* =?L?

Page 20

"Amarya ina kwana? Yau na taki sa'a kin hau online kenan, toh ki taho ganin baby na haihu jiya da daddare yanzu muka dawo gida ma" ta fada bayan da Umaimah ta daga kiran, Umaimah data hade rai da farko tana jiran jin dalilin kiran seta saki fuska dan a duniya tana sonyara tana kuma son taji waniya haihu.

"Masha Allah me aka samu?" Ta fada muryarta a washe, se Rufaidan ta amsa mata da cewa
"Macece Zulaiha, sunan babarsa ya saka"
"Allah raya zan shigo in Allah ya yarda"

"Toh shikenan se kinzo, kinji voice din dana miki ko? Zanyi adding naki zakiji dadin groups din akwai qaruwa sosai kuma duk yawanci matan unguwarnan suna ciki kinga zaki qara sanin mutane" Rufaidan ta sake fada daganan sukayi sallama bayan da Umaimah tace ta sakatan ko group din meye haka se Allah da ta nace seta sakata a ciki suna kashe wayar kuwa tayi adding nata.

Groups uku ta sakata, Qasaitacciyar mace, Mutaimaki kanmu se wani Matsalolin ma'aurata wanda yake a kulle Admin ne kadai suke magana. Daga yanayin sunayen taji groups din sun mata daman yanzu Halima qawarta suke magana tace zata bada number ta a sakata a groups saboda abubuwa da yawa zaka koya ka kuma samu waye war kai akan wasu matsalolin dakanka zaka iya warware su.

Tana nan zaune tana aikin danna waya se ji tayi ana kwada kiran sallar Azahar tayi firgigit ta miqe tana salati
"Kai ashe haka lokaci ya tafi ina zaune babu abinda nayi" ta fada a fili kafin ta wuce jikin socket ta jona wayar a chaji ta shiga daki. Seda tayi sallah ta wuce kitchen, doyar data narke dazu ta dumama ta daketa a turmi, tana da ragowar stew ta diba bayan ta hada shayi ta koma cikin palour tana ci tana duba saqonnin da suka shigo a sababbin groups din da aka sakata.

Group din Matsalolin Ma'aurata ta fara budewa ganin shine me saqonni kadan, ta dafe qirji tareda gwalalo ido tana karanta bayanin da Admin din ta turo ganin abin ya girmi qaramin kanta ya sakata ta tsallake ta wuce kan videos da hotunan aka turo tareda saqon wanda sun rigada sun bude kansu

"Innalillahi na shiga uku ni Umaimah group din yan iska matar nan ta sakani" ta fada tana cilli da wayar saboda mugun gamon da tayi a video data bude jikinta in banda rawa babu abinda yakeyi kwakwalwarta na qara hasko mata masha'ar da akeyi a cikin video to meye amfanin wannan? Kuma group ance saboda Matan aure daman abinda ake koyawa a ciki kenan Batsa? Ta yiwa kanta tambayar.

Wayar ta dakko Allah ya taimaketa bata fashe ba bata bata lokaci ba ta goge chats din tsaf bayan ta shiga gallery ta goge hotuna da videos din data bude kafin ta koma ta fice daga group din yanzu ace Khalil ya dauki wayar yaga wannan aika aikar wane kallo zeyi mata ita ko da wane baki zata fara masa bayani?

"Allah kayi mana maganin masifa da bala'i su kuma masu yin wadannan rubuce rubucen da tura video ka shirye su" ta fada a fili tana rafka tagumi. Abin ya daure mata kai da yawa daman tun suna makaranta Nabila tana cikin ire iren wadannan groups din na matan aure wani lokacin haka za'a turo rubututtuka akan sirrin kwanciyar aure ko makamantansu harda ma video a lokacin suyi ta mata fada sai tace wai gara ta koya ta san komai kafin lokacinta wanda ita dai a iya saninta ta san wannan ilimine da bashi da malami ko baka sani ba da zarar lokacinka yayi ka shiga Ajinsa zaka sani amma shine wasu marasa tsoron Allah suke fakewa da fadakarwa suna yada badala a cikin Al'umma suna lalata yaran mutane dan da yawan matan da suke taruwa a groups din da sunan Matan aure qananan yara wanda basu kai matakin ace sun san wannan abin da wata babbar banzar take zama tana koya musu ba Allah dai ya rufa asiri ya ganar da masu ganewa.

Wannan abun ya sakata ajiye wayar ta shiga aikin gida jiki a sabule har aka kira La'asar bata gama goge goge ba. Se gurin qarfe biyar ta samu ta kintsa gidan, ta shiga wanka kenan ta jiyo horn din motar Khalil gabanta ya bada ras shaf ta manta da ya gaya mata da wuri ze dawo tayi abincin rana dashi nan da nan ta shiga tunanin qaryar da zata shirga masa, haka tayi wankan tayi ta fito tana lankwashewa ido zuru zuru kamar mara lafiya ta jingina da bango tana jan numfashi daidai danda Khalil din ya shiga dakin da sallama.

"Lafiya Babe meya sameki?" Ya fada yana qarasawa kusa da ita ya ruqota jikinsa.
"Subhanallahi ya naji jikinki da dumi zazzabi kikeyi?" Ya sake fada yana taba fatar jikinta data kwararawa ruwan zafi dukda zafin da akeyi a garin, daman tayi ne saboda ya dauka zazzabin takeyi.

"Tunda ka tafi kaina yake ciwo dakyar na iya tashi nayi aikin gida ma na sake kwanciya se yanzu na yi wanka kuma naji zazzabi yana neman rufeni" ta fada tana matso kwallar qarya.
Gaba daya yabi ya rikice ya zaunar d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ita a gefen gado se faman sannu yake mata tana ita kuwa tana qara lankwashe wa.

"Bari na dakko miki kaya muje asibiti ko ga jikin nan da zafi" ya fada yana bude wardrobe dinta, seta sake marairaice masa, kar aje Asibiti suce babu abinda yake damunta dan haka tace
"Aa kabarshi nasan zuwa anjima ze dena daman kwana biyun nan haka nake yi idan ka fita zan tajin babu dadi yamma nayi kuma zan warke"

"Yanzu baki da lafiya shine zakiyi shiru baki fada mun ba har kwana nawa? Bana so karki sake yimun wasa da lafiyarki, duk idan kikaji ba daidai ba ki gaya mun muje Asibiti karki sake zama da ciwo a jikinki" Khalil ya fada cikin bacin rai, shiru tayi daga neman hanyar kare kai ta sake kunno wata matsalar.
Ba yanda ta iya ya tasata a gaba suka wuce asibiti yana ta mata mitar qin gaya masa bata da lafiya da batayi ba ya kuma jaddada mata idan sunje duk abinda yake damunta ta gayawa likita, kamar ta gaya masa gaskiya itafa lafiyarta qalau shiririta ta zauna bata yi aikin gida da wuri ba shi yasa ta masa qarya amma dai tayi shiru dan a yanda ya hasalan nan bata san yanda zasu kwashe ba kuma.

Kai tsaye wani private Asibiti me kyau ya kaita, babu bata lokaci aka bude mata file kafin suka zauna jiran ganin likitan dan sun tarar da mutum biyu a gabansu. Da suka shiga gurin likitan ya tambayeta me yake damunta shiru tayi seda Khalil din ya zazzare mata ido kafin ta yanko qarya tace kanta da cikinta ne suke ciwo se jiri wannan kuma da gaske kusan sati daya kenan ko a zaune setaji kamar jiri na dibanta, data gayawa Mama se tace mata ta ringa yawan shan ruwa kuma ta ringa hutawa da tayin kuma ta samu sauqi amma yanzu tunda an qureta duk ta harhada qarya da gaskiya tace suna damunta.

Tambayarta yayi yaushe tayi Al'ada na qarshe ta gaya mata se a sannan ta tuna ya kamata ace tun satin daya wuce ma jinin ze dawo mata amma bezo ba, da yake wani lokacin yana mata delay shiyasa ma bata damu ba amma dai be taba qara har sati daya ba.

Test din jini dana fitsari likitan ya basu bayan daya auna jininta ya dudduba idonta suka wuce gurin biyan kudi daga nan ya rakata qofar lab din ta shiga shi kuma ya tsaya daga waje

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login